Najeriya ta kammala dawo da alhazan da suka yi Aikin Hajjin bana
Published: 2nd, July 2025 GMT
Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta sanar da kammala dawo da dukkan alhazan da suka yi Aikin Hajjin bana gida Najeriya daga kasar Saudiyya.
A cikin wata sanarwar da Daraktar Yaɗa Labarai ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar ranar Laraba, ta ce jirgin karshe dauke da alhazai 88 ya bar birnin Jiddah da misalin karfe 10:30 na safe dauke da alhazan jihar Kaduna da Katsina.
A cewar hukumar, hakan ya kawo karshen jigilar da aka shafe kwana 20 ana yi tun ranar 13 ga watan Yuni.
A sakonsa na bankwana ga alhazan, shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bayyana godiyarsa ga Allah kan kammala aikin cikin nasara.
Ya kuma bukaci alhazan da su ci gaba da yi wa Najeriya addu’ar Allah ya kawo mata karshen tarin matsalolin da suke addabar ta.
Farfesa Abdullahi ya kuma tunatar da su cewa Aikin Hajji ibada ce da take nuna zaman lafiya da kwanciyar hankali, sannan ya buƙace su da su ci gaba da zumuncin da suka ƙulla a tsakaninsu lokacin ibadar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya.
Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja.
Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaroYa ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025.
ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025.
A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da yajin aikin, don haka dukkanin malamai za su daina aiki a lokacin yajin aiki.
Wannan yajin aikin na zuwa ne duk da cewa har yanzu gwamnati da ASUU na ci gaba da tattaunawa don warware matsalolin da suka daɗe suna fama da su.
Wasu daga cikin matsalolinsu sun shafi batun albashi, kuɗaɗen alawus-alawus, da kuma yarjejeniyar da aka cimma tun shekarar 2009 tsakanin ɓangarorin biyu.
Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya bayyana a ranar Laraba cewa gwamnati na matakin ƙarshe na tattaunawa da ASUU da sauran ƙungiyoyi don warware matsalolinsu.
Ya kuma ce gwamnati ta riga ta fitar da Naira biliyan 50 don biyan haƙƙoƙin malaman da suka cancanta, yayin da aka sake sakin wasu Naira biliyan 150 a kasafin kudin 2025 domin biyan buƙatun jami’o’i.