Wadda ke damfara da sunan matar gwamnan Katsina ta shiga hannu
Published: 14th, March 2025 GMT
Hukumar EFCC ta kama wata mata da mijinta bisa zargin yin sojan gona da sunan mai ɗakin Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Fatima Dikko Radda, wajen damfarar kuɗi Naira miliyan 197.75.
An gurfanar da su a gaban babbar kotun Jihar Kaduna, tare da wasu mutum biyu da ake zargi suna taimaka musu wajen aikata laifin.
EFCC ta ce mutanen huɗu sun haɗa kai wajen amfani da sunan Hajiya Fatima Dikko Radda don samun canjin dala daga wani mai sana’ar canji.
Matar ta gabatar da kanta a matsayin Fatima Dikko Radda, tana buƙatar a yi mata canjin dala.
Mijinta kuma ya samar da layukan waya da aka yi wa rajista da sunan Fatima Dikko Radda, domin a rikita tunanin mai amfani da manhajar ‘True Caller’.
Bayan matar ta nemi a yi mata canjin dala, sai suka turawa mai canjin lambar asusun banki da zai tura kuɗin kafin ta aika masa da dalar.
Da farko, ta karɓi Naira miliyan 89 daga hannun wani mutum mai suna Aminu Usman, da nufin za ta tura masa dala 53,300.
Daga baya kuma, ta sake karɓar Naira miliyan 108, tana mai cewa za ta tura masa dala 118,000.
EFCC na ci gaba da bincike kan lamarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Damfara Uwargidan Gwamnan Katsina Fatima Dikko Radda
এছাড়াও পড়ুন:
Kotun Ta Ci Tarar Hukumar NYSC Kan Haramtawa ‘Yan Bautar Ƙasa Mata Sanya Siket Da Tauye Musu ‘Yanci
Umarnin NYSC ta amince da sanya siket ga mata masu hujjar sanya wa saboda addininsu. Umarnin NYSC ta dawo da su ta ‘yan matan da suka shigar da ƙarar tare da ba su takardar shaidar kammala NYSC. Kotun kuma ta bayar da umarnin bai wa kowacce daga cikinsu kuɗaɗe har ₦500,000 a matsayin diyya saboda tauye musu ‘yancin su.
Kotun ta kuma bayyana cewa cin zarafi da muzantawar da suka fuskanta daga hannun jami’an NYSC ya ci karo da ‘yancinsu na yin addini da bayyana shi a aikace.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp