Tsangayar Kwalejin koyar da aikin Jinya ta Jihar Jigawa dake garin Birnin kudu ta gudanar da bikin kaddamar da sabbin dalibai 116 da za su yi karatun difloma ta kasa da babbar difloma ta kasa karon farko na shekarar karatu ta 2024 zuwa 2025.

A jawabinsa wajen taron kaddamar  da daliban,  kwamishinan ma’aikatar lafiya na jihar Jigawa Dr.

Muhammad Abdullahi Kainuwa, ya ce aikin sa na farko daga samun wannan mukami shi ne batun kafa hukumar Gudanarwar Kwalejin da sake fasalin Kwalejin, wanda hakan ya bada damar tantancewa da kuma samun amincewar Cibiyar kula da makarantun aikin Jinya ta Najeriya.

Yana mai cewar, daukar wannan mataki ya bada damar kara yawan dalibai da Kwalejin take dauka daga 120 zuwa 240, wanda hakan zai bada damar yaye dalibai masu yawa.

A cewarsa, jihar tana da ma’aikatan jinya 1,669 wanda ke nuni da gibin 1,883 in aka kwatanta da bukatar irin wadannan ma’aikata 3,552 domin kula da marasa lafiya a asibitoci.

Dr Kainuwa ya kuma taya murna ga tsangayoyin Kwalejin da ke Babura da Birnin kudu bisa kyakkyawan sakamako da suka samu a jarrabawar da ta gabata, inda su ka zamo kan gaba a tsakanin jihohin kasar nan.

Ya bayyana kiwon lafiya a matsayin kan gaba cikin kudurorin Gwamna Malam Umar Namadi guda 12, yana mai jaddada aniyar gwamnati na cigaba da bada kulawa sosai ga harkokin lafiya wanda yanzu haka ana inganta matsakaitan asibitoci 181 da kayan aiki da sauransu.

A jawabin shugaban Hukumar Gudanarwar Kwalejin Malam Salele Abdul, ya bukaci iyayen dalibai da kada su saki hannu bayan samun guraben karatu a kwalejin, domin kuwa akwai bukatar cigaba da ba su kulawa domin su kai ga nasara zuwa karshen karatunsu.

Malam Salele Abdul ya bayyana kwamishinan lafiya Dr Muhammad Kainuwa a matsayin Garkuwan Aikin Jinya bisa nasarorin da aka cimma a lokacinsa.

Kazalika, ya godewa wakilan hukumar gudanarwar da shugabannin Kwalejin bisa gudummawar da su ke bayarwa ga cigaban harkokin kealejin.

Tun da farko a jawabinsa, shugaban Kwalejin koyar da Aikin Jinya ta Jihar Jigawa, Malam Garba Adamu, wanda ya bayyana kudurinsa na ci gaba da samar da kyakkyawan yanayin koyo da koyarwa, ya kuma baiwa iyayen dalibai tabbacin horas da ‘ya’yansu kan doron Ilimi da kyakkyawar tarbiyya.

Daraktar Kwalejin Aikin Jinya Hajiya Rasheeda Musa Ya’u ta gabatar da sabbin daliban 116 maza da Mata ga Magatardar Kwalejin Malam Muhammad Sale Korau wanda ya lakana musu rantsuwar kaddamarwa.

Shima a jawabinsa, shugaban kwamatin shirye shiryen taron kuma shugaban sashen koyar da Aikin Jinya na kwalejin Malam Abubakar Garba Muhammad, ya ce bikin kaddamar da daliban na daga cikin sharuddan Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’oi da Manyan Makarantu ta Kasa wato (JAMB) domin fara karatun Difloma ta kasa da Babbar Difloma ta kasa a fannin aikin jiyya.

Ya kuma godewa dukkan wadanda suka bada gudummawa wajen samun nasarar taron.

Sakataren kungiyar ma’aikatan Jiyya ta kasa reshen jihar Jigawa Comrade Nurse Kamal Ahmad ya isar da sakon shugaban kungiyar ga taron, yayin da mukaddashin shugaban sashen kula da ayyukan jiyya na ma’aikatar lafiya Nurse Aminu Isa da iyalai da abokan arzikin dalibai na daga cikin maharta taron.

 

Usman Mohammed Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa Kwalejin Aikin Jinya da Aikin Jinya aikin Jinya ta Aikin Jinya ta da aikin Jinya

এছাড়াও পড়ুন:

Ambaliya: Zulum ya bada umarnin tallafa wa mutanen Damboa da Askira-Uba

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jajanta wa mutanen da ambaliya da guguwa suka shafa a ƙananan hukumomin Damboa da Askira-Uba.

A cikin kwanakin da suka gabata, ruwan sama mai yawa ya haifar da ambaliya a ƙauyukan Wovi da Gumsuri na Damboa.

Majalisar Dokokin Filato ta zaɓi sabon shugaba David Mark ya fice daga PDP, ya shiga haɗaka don ƙalubalantar Tinubu

Wannan ambaliya ta yi sanadin mutuwar mata biyu, kuma ta lalata gidaje da raba mutane da muhallansu.

A wani ɓangare kuma, guguwa mai ƙarfi ta afka wa garin Rumirgo da ke Askira-Uba, inda ta lalata gidaje da dukiyoyin jama’a.

Dauda Iliya, mai bayar da shawara na musamman ga Gwamna Zulum kan harkokin yaɗa labarai, ya fitar da sanarwa, inda ya ce abin da ya faru abin tausayi ne da baƙin ciki.

Gwamna Zulum ya ce: “Na yi baƙi ciki da ambaliyar da ta faru a Wovi wadda ta yi sanadin mutuwar mata biyu, da kuma lalata gidaje a Gumsuri.

“Haka kuma abin ya yi muni a Rumirgo inda guguwa ta lalata gidaje. Muna addu’a Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu, ya kuma mayar wa waɗanda suka rasa dukiyarsu da mafificin alheri.”

Gwamnan ya umarci Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), da ta tallafa wa waɗanda lamarin ya shafa.

Ya kuma tabbatar wa mutanen yankin cewa gwamnati za ta taimaka musu.

Zulum ya ce: “Na riga na umarci hukumar SEMA da ta kai kayan agaji zuwa Gumsuri da Wovi cikin gaggawa. Haka kuma, an riga an tura kayan agaji zuwa Rumirgo.”

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa tana ƙoƙari wajen daƙile irin wannan iftila’i a gaba, tare da yin kira ga jama’a da su riƙa kula da bin dokoki don kaucewa irin wannan yanayi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Hori Ma’aikatan Lafiya Su Kara Kokari Wajen Rike Aikin su
  • Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Irin Aniyar Da Gwamantinsa Ta Kudurta Wajen Kare Tsaron Kasa Da Al’ummarta
  • Ambaliya: Zulum ya bada umarnin tallafa wa mutanen Damboa da Askira-Uba
  • Aragchi: Hare-Haren HKI Ya Kara Rashin Zaman Lafoya A Yankin Yammacin Asiya
  • ’Yan sanda sun kama matashin da ya kashe mahaifiyarsa a Jigawa
  • Uwargidar Gwamnan Kaduna Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Noma Ga Mata Manoma
  • Xi Jinping Ya Jaddada Niyyar Gina Babbar Kasuwar Kasa Ta Bai Daya, Tare Da Raya Tattalin Arziki Na Teku Mai Inganci
  • APC ta sa ranar taron Majalisar Zartarwa bayan murabus ɗin Ganduje
  • Magidanci ya kashe matarsa da adda a Yobe