Amurka Ta Dakatar Da Tura Makamai Zuwa Kasar Ukraine Saboda Kada A Sami Karancinsu A Gida
Published: 2nd, July 2025 GMT
Gwamnatin shugaban Donal Trump na Amurka ta bada sanarwan rage yawan wasu makaman da take aikawa kasar Ukraine.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran na nakalto majiyar Fadar Majiyar fadar white House na bayyana cewa pentagon ko ma’aikatar tsaron kasar ta bada rahoton cewa rumbun ajiyar makaman kasar yayi kasa sosai don haka akwai bukatar a dakatar da aikawa kasar Ukraine wasu makaman, kamar garkuwan kare sararin samaniya da kuma makamai masu taimaka mata wajen kare kanta.
Labarin ya nakalto Anna Kelly kakakin fadar white house na cewa an dauki wannan matakin en don sanya Amurka a gaba, duk da cewa ba zata dakatar da bawa kawayenta taimakon da ya dace ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Kammala Aikin Agajin Gaggawa A Yankin Da Ambaliyar Ruwa Ta Afku
Kasar Sin ta kawo karshen aikin bayar da agajin gaggawa mafi girma a gundumar Rongjiang da ke lardin Guizhou, a yankin kudu maso yammacin kasar da misalin karfe 10 na safiyar ranar Lahadi, yayin da aka kammala ruwan saman da aka tafka kamar da bakin kwarya kamar yadda mahukuntan yankin suka bayyana.
Lardin Guizhou da wasu larduna masu iyaka da shi da ke kudu maso yammacin kasar Sin sun fuskanci mamakon ruwan sama tun daga ranar 18 ga watan Yuni, lamarin da ya haifar da mummunar ambaliyar ruwa, inda lamarin ya fi muni a yankin Rongjiang.
Mahukuntan yankin sun raba yankin zuwa kashi bakwai a matsayin wadanda ambaliyar ta fi shafa tare da kwashe mazauna zuwa wasu manyan wurare masu tudu. An kwashe fiye da mutane 40,000 zuwa wurare masu aminci tun karfe 6 na yammacin ranar Asabar saboda rigakafin hadarin ambaliyar.
Kasar Sin ta ware karin kudi yuan miliyan 100, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 13.96 daga cikin kasafin kudin gwamnatin tsakiya don tallafa wa ayyukan ba da agajin gaggawa da farfado da lardin Guizhou da ambaliyar ruwan ta shafa, inda hakan ya kara adadin kudin da aka ware zuwa yuan miliyan 200, kamar yadda hukumar raya kasa da gudanar da gyare-gyare ta kasar ta bayyana. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp