Sheikh Na’im Kasim: Muna Da Karfin Ci Gaba Da Bugawa Da Abokan Gaba
Published: 29th, June 2025 GMT
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi Hizbullah ta mika makamanta a cikin wannan lokacin da yaki bai kare ba, kuma HKI tana cigaba da keta tsagaita wutar yaki.
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya bayyana masu tunani irin wannan da rashin Sanya hankali a cikinsa.
A jawabinsa na dararen Muharram a jiya Asabar, babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; Nauyi ne da ya rataya a wuya gwamantin kasar ta takawa HKI birki akan keta tsagaita da take yi wanda take kai wa fararen hula hare-hare.”
Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Babu yadda za a yi Hizbullah ta ci gaba da Sanya idanu ba tare da iyaka ba, domin mu Mabiya Imam Hussain ( a.s) kuma a kodayaushe muna bayar da taken da yake cewa; Ba Za Mu Yarda Da Kaskanci Ba.”
Har ila yau, Sheikh Na’im ya kuma ce; Duk wadanda suke cewa ana bai wa HKI uzurin ta kawo hari, su daina, domin ba ta da bukatuwa da wani uzuri da za ta fake da shi, abinda yake farwua a Falasdinu da Syria shi ne babban dalili akan hakan.:
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; Isra’ila tana neman mai Rauni ne ta afka masa, wannan kuwa shi ne abinda ba zai faru da mu ba, domin mun sami tarbiyya ne ta rashin amincewa da kaskanci.
Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce: Muna da karfin bugawa da Isra’ila, idan har ya zamana shi kadai ne zabinmu, kuma za mu yi nasara domin mun dogara ne da Allah.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: magatakardar kungiyar
এছাড়াও পড়ুন:
Iran: Janar Hatami ya karbi bakuncin babban hafsan hafsoshin sojin Afirka ta kudu
Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya tabbatar da cewa, Isra’ila da Amurka ne suka bukaci a tsagaita bude wuta cikin gaggawa bayan da suka fuskanci martani mai tsanani a lokacin da suka kaddamr da hare-hare kan kasar Iran.
A yayin da yake karbar bakuncin babban kwamandan rundunar tsaron kasar a Afirka ta Kudu, Janar Hatami ya ce, hukumomin Isra’ila da Amurka sun yi amfani da dukkan karfinsu wajen kai wa Iran hari, amma sun kasa cimma burinsu.
Har ila yau, ya bayyana matakin da Afirka ta Kudu ta dauka na shigar da kara kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila a kotun kasa da kasa a matsayin wata babbar Jarunta, yana mai jaddada cewa tarihi zai tabbatar da wannan muhimmin mataki.
Har ila yau, Laftanar Janar Hatami ya bayyana cewa, dukkanin kasashen biyu suna da Akida ta adawa da mulkin mallaka, yana mai cewa: Matukar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Afirka ta Kudu suna da kyakkayawan hadin gwiwa da juna, to kuwa tabbas za su yi tasiri wajen mara baya ga al’ummomin da ake zalunta, da kuma kalubalantar babakere na ‘yan mulkin mallaka.
A nasa bangaren, kwamandan rundunar tsaron kasar a Afirka ta Kudu, Laftanar Janar Rodzin Mafwania, ya ce ziyarar Iran a yau ba ziyarar soji ba ce kawai, a’a sakon siyasa ne, kuma ta zo a daidai lokacin da ya dace mu bayyana ra’ayinmu ga al’ummar Iran masu son zaman lafiya.
Kuma ya ci gaba da cewa: “Muna tsayawa tsayin daka wajen goyon bayan wadanda ake zalunta da kuma wadanda aka raunata a duniya, shi ya sa muka shigar da kara a gaban kotun kasa da kasa domin hukunta wadanda suka aikata laifuffukan ibadar jama’a.”
Wakilan Hamas sun isa a Alkahira don tattaunawa kan sabuwar shawarar tsagaita wuta a Gaza
Wata majiyar Falasdinawa ta shaida wa AFP cewa “Masu shiga tsakani na aiki don samar da wata hanyar cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta” wadda za ta sa a sako dukkan sauran fursunonin da ake tsare da su a Gaza “a rukuni guda.”
Shawarar na iya hadawa da “tsagaita bude wuta na kwanaki 60, sannan kuma a yi shawarwarin tsagaita bude wuta na dogon lokaci, da kuma yarjejeniyar musayar dukkan fursunonin Isra’ila da suke da rai da wadanda suka mutu, a cikin rukuni guda,” a cewar majiyar.
Tawagar kungiyar Hamas karkashin jagorancin Khalil al-Hayya ta isa kasar Masar domin halartar shawarwarin tsagaita wuta a zirin Gaza.
Tun da farko dai kamfanin dillancin labaran AFP ya nakalto wasu majiyoyi suna cewa wasu manyan mambobin Hamas na kan hanyar zuwa Alkahira domin ganawa da jami’an Masar a wani bangare na kokarin shiga tsakani. Wata majiya ta lura cewa ziyarar ta kasance “bisa gayyatar Masar,” ta kara da cewa al-Hayya zai gana da jami’ai “don tattauna sabbin abubuwan da suka faru a tattaunawar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni.”
Wani kusa a Hamas ya shaidawa AFP cewa kungiyar “ba ta sami wata sabuwar shawara daga bangaren Isra’ila ta hanyar masu shiga tsakani ba, amma tana nan a shirye don cimma yarjejeniyar idan Isra’ila ta yanke shawara.”
Ya jaddada cewa Hamas na neman kawo karshen yakin na dindindin, da kuma dage takunkumin da Isra’ila ta kakaba na hana shigar da abinci da kayan agaji zuwa yankin Zirin Gaza.
Habasha: Madatsar ruwanmu amfanin dukkanin kasashen yankin ne
Ministan Ruwa na Habasha Habtamu Etfa ya jaddada cewa, babbar madatsar ruwa ta kasarsa amfanin dukkanin kasashen yankin ne.
Etfa ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, kamar yadda shafin yanar gizo na Ethiopian Monitor ya bayyana cewa, ” kwararar kogin Blue Nile ya karu a lokacin noman rani, yayin da muka ga raguwar ambaliya da kuma jinkiri fiye da wata guda.” Ya jaddada cewa abin da muke hasashe kuma muke bayyanawa yau da kullun ya tabata a aikace.”
Ya kara da cewa, “Grantin Renaissance Dam na Habasha ba kawai ya kara yawan filayen noma da ake nomawa a kasashen da ke gabar kogin Blue Nile ba, har ma ya taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyi daga bala’in ambaliya da ke barazana ga yankin.”
Bayanin na Ministan Ruwa na Habasha ya zo ne a daidai lokacin da ake samun karuwar tashe-tashen hankula a yankin game da sarrafa ruwan Nilu, inda Habasha ke fuskantar suka daga kasashen Masar da Sudan dangane da tasirin da madatsar ruwan ke da shi kan raguwar Ruwan da ke kwarara a cikin kasashensu.
Nijeriya Da Isra’ila Na Kara Karfafa Alaka A Tsakaninsu
Nijeriya da Isra’ila sun sake jaddada aniyarsu ta karfafa haɗin gwiwar tsaro a fannoni daban-daban, kamar batun yaƙi da ta’addanci, musayar bayanan sirri, samar da kuɗin tsaro da kuma bayar da horo na musamman ga jami’an tsaron Nigeria.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar haɗin gwiwa wadda Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen Nijeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da Mataimakiyar Ministan Harkokin Waje ta Isra’ila, Sharren Haskel-Harpaz suka fitar bayan wani taro na musamman da suka gudanar a Abuja.
Sanarwar, wadda mai magana da yawun Ofishin Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen, Dokta Magnus Eze ya fitar, ta ce taron ya nuna alaƙa mai ɗorewa da muhimmanci tsakanin bangarorin biyu.
A yayin taron, wakilan bangarorin biyusun tattauna batutuwan da suka shafi tsaro a duniya, musamman yaƙi da ta’addanci, da kuma inganta hulɗar siyasa da tattalin arziki.
Ministocin biyu sun jaddada aniyarsu ta yin aiki tare wajen samar da bayanai na sirri kan barazanar ta’addanci a duniya, musamman kan hanyoyin samar da kuɗaɗen da ke ɗaukar nauyin ta’addanci.
Najeriya na daga cikin kasashe masu alaka mai karfi tsakaninsu da Isra’ila, musamman a bangarorin da suka shafi batutuwan tsaro da kuma noma.
Bankin Duniya Zai Kashe $300m Domin Inganta Rayuwar ’Yan Gudun Hijira A Arewacin Nijeriya
Bankin Duniya ya amince da bayar da dala miliyan 300 domin aiwatar da wani sabon shiri da zai inganta rayuwar ’yan gudun hijira da kuma al’ummomin da suka ba su matsugunni a Arewacin Nijeriya.
Bankin ya bayyana cewa a ƙarƙashin shirin mai suna Solutions for the Internally Displaced and Host Communities Project wato SOLID, wanda aka amince da shi a ranar 7 ga Agusta, za a lalubo hanyoyin da za a bi wajen taimakon ’yan gudun hijira, da ma garuruwan da suke rayuwa a ciki.
Ya bayyana cewa shirin SOLID zai ruɓanya ƙoƙarin da gwamnati ke yi da ma wanda sauran abokan hulɗa suka riga suka gudanar, ciki har da Shirin Farfado da Yankunan Da Rikici Ya Shafa (MCRP).
Haka kuma, bankin ya jaddada cewa rikice-rikicen tsaro da rashin kwanciyar hankali da ke gudana a yankin sun raba mutane fiye da miliyan 3.5 da muhallansu, lamarin da ya shafi ababen more rayuwa, wanda a cewar bankin hakan ya sa ababen more rayuwan suka yi ƙaranci a garuruwan da suke zama.
Daraktan Bankin Duniya a Nijeriya, Mathew Verghis, ya ce: “Muna farin cikin ƙaddamar da wannan shiri mai matuƙar tasiri da zai taimaka wa Nijeriya magance ƙalubalen da take fuskanta wadanda suka shafi ’yan gudun hijira”
Za a aiwatar da shirin ne ta hanyar tsari na haɗin gwiwar al’umma, tare da shigar dukkan bangarorin gwamnati da kuma haɗin kai da ƙwararrun abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Habasha: Madatsar ruwanmu amfanin dukkanin kasashen yankin ne August 13, 2025 Bankin Duniya Zai Kashe $300m Don Inganta Rayuwar ’Yan Gudun Hijira A Arewacin Nijeriya August 13, 2025 Nijeriya Da Isra’ila Na Kara Karfafa Alaka A Tsakaninsu August 13, 2025 Kasashe 27 Sun Bukaci Isara’ila Ta Kawo Karshen Hana Shigar Da Abinci A Gaza August 12, 2025 Iran: Duk Wani Sabon Hari, Zai Fuskanci Mummunan Martanin Soji August 12, 2025 Larijani: Iraki Ba Ta Karbar Umarni Daga Iran August 12, 2025 Iran: Ma’aikatar Harkokin Waje Ce Ke Kula Da Lamarin Makamashin Nukliyar Kasar August 12, 2025 Armenia Ta Tabbatarwa Iran Zata Kula Da Muradunta Bayan Yarjeniya Da Azarbaijan A Amurka August 12, 2025 Araqchi: Kisan Kiyashi A Gaza Babban Abin Kunya Ne Ga Gwamnatocin Yammacin Turai August 12, 2025 Larijani Ya Ce: ‘Yan Gwagwarmaya Sun San Abubuwan Da Suka Dace August 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci