Rasuwar Dantata Babban Rashi Ne Ga Afirka – Atiku
Published: 28th, June 2025 GMT
Atiku, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a 2023, ya bayyana Dantata a matsayin jarumin da ke ɗaukar kasada a harkokin kasuwanci, wanda ya ce wata muhimmiyar ɗabi’a ce ta manyan masu saka hannun jari.
Ya yaba da yadda Dantata ya sauya kasuwancin danginsu daga saye da sayarwa ta hanyar gargajiya zuwa aikin gine-gine da injiniyanci na zamani, wanda hakan ya samar da dubban ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya.
Atiku ya kuma nuna girmamawa ga Dantata bisa irin taimakon da yake yi wa jama’a cikin sirri ba tare da neman ɗaukaka ko yabo ba.
“Ya kasance mai dukiya sosai amma bai taɓa nuna girman kai ba, wannan ɗabi’a ce da ba kowa ke da ita ba,” in ji Atiku.
“Ya kasance abin koyi kuma tushen ƙarfafawa ga mutane da dama.”
Ya ƙara da cewa Dantata mutum ne mai son zaman lafiya wanda ya guji maganganun da ke kawo rabuwar kau, kuma ya jajirce wajen ƙarfafa zaman lafiya a tsakanin ‘yan Nijeriya.
Atiku ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta girmama Dantata ta hanyar sanya sunansa a wani muhimmin gini ko cibiyar gwamnati, domin tunawa da gudunmawarsa ga ci gaban al’umma da tattalin arziƙin ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Rasuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Babban Dalilin EFCC Na Yi Wa Tsohon Gwamnan Sokoto, Tambuwal, Tambayoyi
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta yi wa tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aminu Tambuwal, tambayoyi kan zargin fitar da wasu kuɗi har Naira biliyan ₦189 ta hanyar cire kuɗin daga banki.
Rahotanni sun nuna cewa, Tambuwal ya isa shalƙwatar EFCC a Abuja da misalin karfe 11:30 na safiyar yau Litinin, inda yake ci gaba da fuskantar tambayoyi daga jami’an bincike kan zargin. Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar ko za a tsare shi ba na dogon lokaci ba.
Ku Yaƙi Cin Hanci Ba Ƴan Adawa Ba – ADC GA EFCC EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Akwa IbomMajiyoyi daga EFCC sun tabbatar da cewa an tsare shi ne kan zargin fitar da kuɗi a bainar jama’a wanda ke saɓawa dokar hana safarar kudi masu nauyi ta shekarar 2022. An ce, “Mun ware dukkan zarge-zargen da suka shafi Tambuwal, saura ya bayar da bayani.”
Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ƙi yin bayani kan lamarin lokacin da aka tuntuɓe shi. Ana sa ran tsohon gwamnan zai bayar da amsa kan yadda aka samu irin waɗannan manyan fitar kuɗi a lokacin mulkinsa a Jihar Sokoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp