Aminiya:
2025-08-14@19:47:13 GMT

Ganduje: Dalori ya kira taron Majalisar Gudanarwar Jam’iyyar APC

Published: 30th, June 2025 GMT

Sabon Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Ali Bukar Dalori, ya shiga ofis, inda a halin yanzu yake jagorantar taron Kwamitin Gudanarwa na jam’iyyar.

.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Kano Ta Karbi Kudirin Karamin Kasafin Kudi Na Shekarar 2025

Majalisar dokokin jihar Kano ta karbi karin kudirin kasafin kudi na shekarar 2025 daga bangaren zartarwa na jihar domin tantancewa.

 

Bukatar, wacce aka mika ta wata wasika daga bangaren zartarwa, ta nemi amincewar majalisar ta kara kasafin kudi naira biliyan 169,522,463,294.82 domin daukar muhimman ayyukan raya kasa a fadin jihar.

 

Kakakin majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore ya bayyana cewa hukumar zartaswa na kokarin ganin an kara wa kasafin kudin domin gudanar da ayyuka masu ma’ana da za su shafi rayuwar mazauna.

 

Bayan sun yi duba, ‘yan majalisar sun mika kudirin dokar ga kwamitin kasafin kudi na majalisar domin tantancewa da daukar matakin da ya dace.

 

A wani labarin kuma, Majalisar ta kuma samu takarda daga bangaren zartarwa na tantance Barista Saidu Yahaya a matsayin sabon shugaban hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC).

 

Nadin ya biyo bayan cikar wa’adin tsohon shugaban Barista Muhyi Magaji Rimin Gado.

 

An mika sunan ga kwamitin majalisar kan korafin jama’a don ci gaba da aiwatar da doka.

 

Majalisar ta dage zaman ta ne zuwa washegari sakamakon kudirin da shugaban masu rinjaye, Lawan Hussaini Dala ya gabatar.

 

COV/Khadija Aliyu08164127760

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ya Bayyana Isra’ila A Matsayar ‘Yar Yaudara
  • Rashin aiwatar da doka na bai wa masu laifi ƙwarin guiwa — Ɗan majalisar Gombe
  • Shugaban Tinubu Ya Rantsar Da Farfesa Dakas James Shugaban Hukumar Gyaran Dokoki Ta Kasa
  • Majalisar Kano ta dakatar da ciyaman kan zargin karkatar da taki
  • An Yi Kira Ma’aikatan Watsa Labarai Su Tabbatar da Gaskiya A Ayukkan Su
  • ADC Ta Dakatar Da Shugabanta Da Wasu Jiga-jigai 3 A Kebbi
  • Wani Bangaren Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Da Ta Karbe Mulkin Jihar
  • Tambuwal: ’Yan Nijeriya Sun Soki EFCC Kan Rashin Kama Okowa, Ganduje Da Yahaya Bello
  • Tinubu na amfani da EFCC ya muzguna wa ’yan adawa — Atiku
  • Majalisar Kano Ta Karbi Kudirin Karamin Kasafin Kudi Na Shekarar 2025