Shugaban kasar Iran ya soki lamirin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA

A wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a yammacin jiya Lahadi, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da dabi’ar nuna fuska biyu daga Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya, yana mai cewa irin wannan dabi’a ta nuna fuska biyu za ta janyo rugujewa da haifar da matsaloli da dama ga tsaron yankin da ma duniya baki daya.

A yayin wannan tattaunawa, shugaba Pezeshkian ya ce, wadannan ayyuka na nuna fuska biyu sun haifar da matsaloli da dama ga harkokin tsaro na yanki da na duniya, kuma ana sa ran hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA za ta mutunta haƙƙin kasashe da guje wa ɗabi’a nuna fuska biyu a fagen ayyukanta da kuma kare haƙƙin ƙasashe membobinta.

A martanin da shugaban kasar Faransa ya nuna dangane da matakin Iran na dakatar da hadin gwiwa da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, shugaba Pezeshkian ya soki yadda babban sakataren hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA ke bayar da rahotannin da ba su dace ba kan shirin makamashin nukiliyar Iran da kuma rashin yin Allah wadai da harin da aka kai kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, wanda ya saba wa dokokin kasa da kasa.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: hukumar kula da makamashin nukiliya ta

এছাড়াও পড়ুন:

Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka

An kulle Fadar Shugaban Kasar Amurka ta White House tare da wasu gine-ginen gwamnati da dama, sakamakon harbin ɗan bindigar da ya raunata sojoji biyu a kusa da fadar.

A yayin, an harbe masu tsaron fadar biyu har lahira.

Gwamna Patrick Morrisey da farko ya ce an kashe sojojin, amma daga baya ya ce yana samun “rahotanni masu karo da juna” game da halin da suke ciki, yana mai da cewa za a fitar da ƙarin bayani idan an tabbatar.

A cikin wani rubutu a shafin X, ya ce, “Yanzu muna samun rahotanni masu cin karo da juna game da halin sojojin biyu, kuma za mu bayar da ƙarin bayani idan mun samu cikakken rahoto.

“Addu’o’inmu suna tare da waɗannan jarumai, iyalansu, da dukan al’ummar Amurka.”

A cewar rahotanni, Shugaba Donald Trump yana gidansa na hutu a Mar-a-Lago da ke Palm Beach, Florida, a lokacin da lamarin ya faru.

Mai magana da yawun Fadar White House, Karoline Leavitt, ta ce cikin wata sanarwa: “Fadar White House ta san da wannan mummunan lamari kuma tana bin diddigi. Shugaban kasa ya samu cikakken bayani.”

’Yan sandan birnin Washington DC sun ce an kama wanda ake zargi da harbin.

Sojojin National Guard sun kasance a Washington DC tsawon watanni a matsayin wani bangare na matakin Trump na yaki da laifuka a babban birnin ƙasar.

A cikin wani rubutu a dandalinsa na Truth Social, Trump ya ce: “Dabban da ya harbi mambobin National Guard biyu, wanda dukkansu suka ji rauni mai tsanani kuma yanzu suna a asibitoci daban-daban, shi ma ya ji rauni sosai, amma duk da haka, zai ɗanɗana kuɗarsa.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • An Zabi JMI A Cikin Majalisar Zartarwan Ta Hukumar Yaki Da Makaman Guba Ta Duniya CWC
  • Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka
  • Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya
  • Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta
  • Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yawaba Pakistan Saboda Goyon Bayanta
  • Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran
  • An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
  • Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja
  • Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza