Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Kira Da A Gudanar Da Bincike Kan Wuce Gona Da Irin Amurka Da Isra’ila Kanta
Published: 28th, June 2025 GMT
Iran ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kuma a hukumance kan zaluncin ‘yan sahayoniyya da Amurka
Mataimakin babban jami’in kula da harkokin kasa da kasa na ma’aikatar shari’a kuma sakataren hukumar kare hakkin bil’adama ta Iran ya yi la’akari da matakin wuce gona da iri na baya-bayan nan da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka yi kan cibiyoyin makamashin nukiliya, da kafofin yada labarai, da cibiyoyin kiwon lafiya na Iran, da kuma wuraren zama, gidajen yari da birane da kauyuka, a matsayin misali karara na keta dokokin kasa da kasa da hakkokin bil’adama.
A cikin wata wasika da ya aike wa kwamishinan kare hakkin bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya Volker Türk Nasser Seraj mataimakin shugaban hukumar shari’a kan harkokin kasa da kasa kuma sakataren hukumar kare hakkin bil’adama ta kasar Iran ya bayyana cewa da gan-gan yahudawan sahayoniyya sun kai hari kan ginin gidan rediyo da talabijin na Iran da makamai masu linzami.
Ya yi nuni da cewa, wannan harin ya ruguza wasu cibiyoyin yada labaran kasar, tare da kawo cikas wajen yada labarai, sannan kuma abin takaici ma ya kai ga shahada da raunata ma’aikatan kafafen yada labarai wadanda su kadai ke da alhakin sanar da jama’a abubuwan da ke faruwa.
A daya bangaren Saraj ya ci gaba da cewa: Hare-haren da ‘yam sahayoniyya suka kai a kwanakin baya kan cibiyoyin kiwon lafiya, ginin kungiyar agaji ta Red Crescent, da motocin daukar marasa lafiya, da kuma yankunan da ke kusa da asibitoci, sun haddasa lalacewar ababen more rayuwa, wanda ya yi sanadin mutuwa da jikkatar fararen hula, tare da sanya tsoro da firgici a tsakanin jama’a.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Isra’ila: Da Gangan Muke Kashe Faladinawa A Wurin Karbar Taimakon Abinci
Wasu daga cikin jami’an sojojin HKI sun yi furuci da cewa, an ba su umarni ne da su rika bude wuta akan Fararen hula Falasdinawa da suke zuwa cibiyoyin karbar kayan agaji, suna jaddada cewa, wadanda su ka kashe din ba su yin wata barazna a gare su.
Jaridar “Haarezt” ta ‘yan sahayoniya ta buga rahoton da ya kunshi furucin sojojin nasu da su ka tabbatar da cewa; An ba su umarni ne da su rika harbin duk wanda su ka gani a kusa da cibiyoyin raba kayan abinci.
Jaridar ta kuma ce; Sojojin sun yi amfani da kowadanne irin bindigogi da su ka hada da manya wajen harbin fararen hula Falasdinawa.
Yawan Falasdinawan da su ka yi shahada a cibiyoyin raba kayan agaji sun kai 80, yayin da wani adadi mai yawa ya jikkata.
Tun farkon bude cibiyoyin agajin ne dai kungiyar Hamas ta bayyana shi da cewa; Sun zama wurin farautar Falasdinawa.
MDD ta ki shiga cikin shirin, saboda ta ce, manufarsa ita ce korar Falasdinawa daga Gaza da kuma wata manufar ta soja.