2025-06-28@23:36:52 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6123

«a cikin kasarta»:

    Yau Asabar, kwamitin kula da raya kasa da aiwatar da gyare-gyare ta kasar Sin (NDRC), ta ce ta ware yuan miliyan 100, kwatankwacin dala miliyan 13.95, kari kan yuan miliyan 100 da ta ware a ranar Larabar da ta gabata, domin taimaka wa ayyukan agaji a kudu maso yammacin Sin. Mummunar ambaliyar ruwa ta sake dawowa a gundumar Rongjiang ta lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin, lamarin da ya sanya hukumomin wurin sake ayyana matakin koli na tunkarar ambaliya, daga karfe 12:30 na rana a yau. Hukumomi a yankin na kwashe mazauna daga wuraren da lamarin ya shafa. Zuwa karfe 6 na yamma, gundumar ta tsara aikin gaggawa na kwashewa tare da tsugunar da iyalai 11,992 da daidaikun...
    Jiya Jumma’a 27 ga watan Yuni ne, aka kaddamar da wani aikin hadin-gwiwar kafafen yada labaran kasar Sin da kasashen waje daban-daban, mai taken “Ziyara a jihar Xizang don tunkarar zamanantarwa” dake karkashin jagorancin cibiyar watsa labarai ta harsunan Asiya da Afirka ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, da ofishin fadakar da al’umma na kwamitin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin reshen jihar Xizang mai cin gashin kai ta kasar, da gidan rediyo da talabijin na jihar, da kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na Qinghai-Xizang na kasar Sin, inda aka gayyaci manyan ’yan jaridu gami da shahararrun masu amfani da shafukan sada zumunta na intanet guda 20, don watsa labarai game da jihar ta Xizang. A...
    Iran ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kuma a hukumance kan zaluncin ‘yan sahayoniyya da Amurka Mataimakin babban jami’in kula da harkokin kasa da kasa na ma’aikatar shari’a kuma sakataren hukumar kare hakkin bil’adama ta Iran ya yi la’akari da matakin wuce gona da iri na baya-bayan nan da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka yi kan cibiyoyin makamashin nukiliya, da kafofin yada labarai, da cibiyoyin kiwon lafiya na Iran, da kuma wuraren zama, gidajen yari da birane da kauyuka, a matsayin misali karara na keta dokokin kasa da kasa da hakkokin bil’adama. A cikin wata wasika da ya aike wa kwamishinan kare hakkin bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya Volker Türk Nasser Seraj mataimakin shugaban hukumar...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta san mika wuya ba, kuma tana rubuta tarihin mutunci da jinin shahidanta A jawabin da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi bayan halartar jana’izar shahidan Quds ya jaddada cewa: Iran ba ta san ma’anar mika wuya ba, yana mai fayyace cewa tarihi zai shaida cewa Iraniyawa sun zubar da jininsu tare da kin ba da kasarsu da mutuncinsu. Araqchi ya bayyana a shafinsa na Instagram cewa: “Duk da zafi da rashi na shahidansu kwatsam, amma tunaninsu yana nan a cikin zukatan masu hankali, da kuma zukatan al’ummomi masu zuwa, kuma suna sane da yin riko da Imani da hanyarsu, kuma za su ci gaba da bin tafarkinsu.”...
    Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Iran za ta ci gaba da tace sinadarin Uranium a cikin kasarta Jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya bayyana cewa: Iran tana jaddada matsayinta na cewa dole ne ta gudanar da ayyukan tace sinadarin Uranium a cikin kasarta, yana mai cewa: “Kungiyar masu sa-ido zata iya kasance a Iran, amma ba za ta maye gurbin Shirin Iran na cikin gida ba.” Jakadan Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Irawani a wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Al-Monitor, ya kara da cewa: “Iran ta kasance tana neman mafita ta hanyar lumana don tunkarar matsalolin da ake iya fuskanta...
    Darakta Janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA ya bayyana cewa: Ba zai iya tabbatar da cewa Iran na kera makamin nukiliya ba! A wata hira da tashar talabijin ta Faransa LCI, Darakta Janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA Rafael Grossi ya bayyana cewa: Ba zai iya tabbatar da cewa Iran tana kera makamin nukiliya ba. Grossi dai ya fuskanci tambayoyi da kalubale da dama daga mai gabatar da Shirin, kan ko Iran na daf da kera makamin nukiliya? Ya amsa a cikin halin shakku, yana mai cewa a cikin rahoton ya nisanci zargin Iran da kokwarin kera makamin nukiliya domin babu tabbas kan zargin. Da aka tambaye shi ko Iran na kera makamin nukiliya?...
    Wani mummunan hatsari ya afku a Masar inda ‘yan mata 18 suka mutu sakamakon fashewar wata motar dakon mai Wani mummunan hatsarin mota ya afku a kasar Masar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mata 18 da direban bas a kan hanyarsu ta zuwa gonar inabin domin girbin inabin. Hatsarin ya afku ne a ranar Juma’a a kan hanyar yankin da ke gundumar Menoufia, bayan wata babbar mota ta yi karo da motar bas din da ke dauke da ‘yan matan 18. Dukkansu sun fito ne daga kauye daya, Kafr El-Sanabseh, a gundumar Menoufia, kuma dukkansu ‘yan kasa da shekara 21 ne. Hotunan wannan mummunan hatsarin da aka yi ta yawo da su a shafukan sada zumunta, sun nuna...
    A nata bangare hukumar CAEA ta ce za ta hada hannu da hukumar kula da makamashin nukuliya ta duniya IAEA da sauran abokan hulda daga kasashe masu tasowa, wajen inganta kirkire-kirkire da raya makamashin nukiliya. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Masana da jami’ai a Nijeriya, sun yaba wa ci gaba na a-zo-a-gani da karin kuzarin da ake samu a hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Nijeriya, suna masu bayyana kokarin da aka yi zuwa yanzu a hadin gwiwar bangarorin biyu a tafarkin zamanantar da kansu. Masanan sun bayyana haka ne yayin taro na biyu na bayan taron FOCAC da aka yi ranar Alhamis a Abuja, babban birnin kasar. Cibiyar nazarin dangantakar Sin da Afrika dake Nijeriya ce ta shirya taron mai taken “Hada Hannu Wajen Zamanantar da Sin da Afrika da cimma shirye-shirye 10 na Hadin Gwiwa a Cikin Al’ummar Sin da Afrika mai Makoma ta Bai Daya a Ko da Yaushe.” Da yake jawabi, daraktan cibiyar nazarin Sheriff Ghali...
    Ya ce yana matuƙar daraja lokutan da suka gudanar tare. Ya roƙi Allah ya bai wa iyalan Dantata da Dangote, Masarautar Kano, da al’ummar jihar da ƙasar baki ɗaya haƙuri da juriyar rashin wannan babban mutum. “Allah Ya jikan shi Ya sa Aljannatul Firdaus makomarsa,” in ji Buhari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mustapha ya ce idan lokaci ya ƙure kuma ba a samu amincewa daga Madina ba, za su dawo da gawar zuwa Kano domin a yi masa sutura. Don haka, har yanzu ba su yanke shawarar ainihin inda za a binne shi ba. Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata ya rasu yana da shekaru 94, kuma mutane da dama sun aike da saƙon ta’aziyyarsu, ciki har da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Alhaji Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso da wasu shugabanni da dama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Ya ci gaba da cewa, Hukumar ta NPA, ta yi kasafin da dara haka, na wannan adadin, musaman ganin cewa, ta na burin, kara inganta ayyukanta, yadda za su yi dai-dai, da yadda ake gudanar da ayyukan, a sauran Tashoshin Jiragen Ruwa na duniya. Shugaban Hukumar ya kuma sanar da cewa, a shekarar 2024, Hukumar ta NPA, kudin shigar da ta yi hasashen Tarawa daga na Naira biliyan 865.39, sun karu zuwa Naira biliyan 894.86. “ Wannan ya nuna yadda Hukumar ta NPA, ta mayar da hankali da kuma kara zage Damtse wajen ganin ta Tarawa Gwamnatin Tarayya kudaden shiga, masu yawa,”  A cewar Dantsoho. Shugaban ya kuma bayyana cewa, kudaden shigar da Hukumar ke hasashen Tarawa a shekarar ta...
    Mai magana da yawun hukumar raya hadin-gwiwa da sassan kasa da kasa ta kasar Sin, Li Ming, ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, Sin ta riga ta kaddamar da ayyuka kimanin dubu 15 na inganta kwarewar ma’aikata karkashin hadin-gwiwarta da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sama da 180, inda aka horas da kwararrun ma’aikata fiye da dubu 500 a bangarori daban-daban, al’amarin da ya taimaka wa kasa da kasa samun ci gaba. Kana kuma, akwai ’yan kasashen Afirka da dama wadanda suka yi amfani da manufofi da dabarun kawar da talauci da suka koya a kasar Sin, don taimaka wa ayyukan yaki da fatara a kasashensu.   Kakakin ya kara da cewa, tun daga shekaru sama da 70 da...
    Duk ana dora alhakin yadda lamarin cinikin Bayi ya bunkasa kan wani mutum dan asalin kasar Birtaniyya da ake kira da suna,John Hawkins. Hawkins  shi ne mutumin da ya kara daukaka, bunkasa,da zamanan har da lamarin cinikin Bayi”manufa anan yayi  gyare- gyare daga yadda Turawan kasar Fotugal suka fara da barinsa,ya yi masa kwaskwarima,zuwa lamarin kasuwanci mai daraja”. Jiragen ruwa suna tasowa daga Kasar Birtaniya ko kuma Ingila  da Bindigogi, Madubi,da kuma Giya,Jiragen na zuwa wani wurin da ake kira da suna inda ake daukar Bayi a kai su  kasar ko kasashen da suka saye su, yanzu wurin ana kiransa da suna yankin Neja Delta inda daga can ne kuma za ‘a fara tafiya, har sai sun kai inda zasu...
    An yi wa marigayi Alhaji Aminu Ɗantata jana’izar Salatul ‘Ga’ib’ a garin Kano. An yi sallar ne a masallacin Umar bn Khattab da ke kan titin Gyadi-Gyadi. Za a binne Aminu Ɗantata a Madina — Iyalansa Mangu: Gwamnatin Filato ba ta aiko da wakilai don yin ta’aziyya ba — Sarkin Zazzau  Sheikh Ibrahim Khalil, Shugaban Majalisar Malamai na Jihar Kano, tare da Sheikh Ibrahim Aminu Daurawa, ne suka jagoranci sallar. Manyan baƙi da dama sun halarci jana’izar, ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, mambobin majalisar zartarwa na Jihar Kano, manyan ‘yan kasuwa da wasu mutane. Aminiya ta ruwaito marigayi Alhaji Aminu Dantata, ya rasu a birnin Abu Dhabi, kuma za a birne shi a Madina...
    Albarkacin ranar yaki da miyagun kwayoyi ta kasa da kasa, ofishin dakile miyagun kwayoyi na kasar Sin ya gabatar da rahoton halin da kasar take ciki a wannan bangare, inda alkaluma suka nuna cewa, a shekarar 2024, hukumomi masu alaka sun binciki laifuka masu nasaba da miyagun kwayoyi fiye da dubu 37, da cafke masu aikata laifukan dubu 62, baya ga kama miyagun kwayoyi ton 26.7. Adadin laifuka masu nasaba da miyagun kwayoyi da aka bincika ya ragu da kashi 12.9%, yayin da yawan masu aikata laifukan da aka cafke ya ragu da kashi 5.6% bisa na makamancin lokacin a shekarar 2023. Ban da wannan kuma, Sin ta yi kokarin sauke nauyin dake wuyanta, inda ta shiga a dama da...
    Iyalan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata, wanda ya rasu, sun bayyana cewa ya bar wasiyyar cewa a birne shi a Birnin Madina na ƙasar Saudiyya. Majiyoyi daga cikin iyalansa sun bayyana cewa marigayin ya buƙaci a birne shi kusa da uwargidansa a Madina a duk lokacin da ya rasu. Mangu: Gwamnatin Filato ba ta aiko da wakilai don yin ta’aziyya ba — Sarkin Zazzau  ‘An kashe ’ya’yana da mijina da ’yan uwana a hanyar ɗaurin auren ɗana’ A gefe guda kuma, Majalisar Malamai ta Jihar Kano ta yi wa marigayin sallar Ga’ib a Masallacin Aliyu bin Abu Talib da ke unguwar Dangi. Cikin wata sanarwa da ta fitar, majalisar ta bayyana cewa za a yi masa sallar ne duk d gawarsa...
    Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Filato ba ta aiko da wani wakili zuwa Zariya domin yi wa iyalan waɗanda aka kashe a Ƙaramar Hukumar Mangu a Jihar Filato, ta’aziyya ba. Aminiya ta ruwaito, yadda wasu matasa suka farmaki motar wasu ’yan ɗaurin aure su 31, inda suka kashe 13 daga cikinsu. Aminu Ɗantata: Na roƙi Allah kada Ya ba ni abin da mutane ba za su amfana ba Za a yi wa Aminu Ɗantata Salatul Ga’ib a Kano Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da jagoran shugabannin addinai, Tsohon Ministan Matasa da Wasanni Solomon Dalung, ya jagoranci wata tawaga zuwa fadarsa domin yin ta’aziyya. Sarkin ya gode wa tawagar bisa wannan ziyara,...
    Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da wani hari da fararen hula’yan ’yan ƙasar suka kai wa sojojinta. An kai wa dakarun rundunar sojojin ko-ta-kwana na Isra’ila hari ne a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan. Yahudawa ’yan share wuri zauna suka kai wa sojojin na Isra’ila harin ne a yayin da sojojin ke aiwatar da wani samamen tare da yin kame a yankin, mai suna Kafr Malek. Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce, “fararen hula ’yan Isra’ila sun yi wa jami’an ruwan duwatsu tare da cin zarafin sojojin ta jiki da ta baki, ciki har da kwamandan rundunar.” Yunwa ta kashe yara 66 a Gaza ‘An kashe ’ya’yana da mijina da ’yan uwana a hanyar ɗaurin auren ɗana’ Yadda aka...
    Nasarar da kungiya ta samu a matakin rukuni za a ba ta Dala miliyan biyu, canjaras kuma miliyan daya, wadda ta cinye kofin kuma za ta samu ladan Dala miliyan 40. Ganin yadda kungiyoyin Turai suka mamaye gasar, Afirka na fatan samun karin dama a nan gaba, ma’ana a Karara nahiyar Afirka yawan kungiyoyin da za su dinga wakiltar ta. Wasu na fatan kungiyoyin Afirka da ke cikin gasar za su ja hankalin duniya zuwa nahiyar ko da kuwa gasarta ta zakaru ba ta iya yin hakan ba, da kuma kawo musu kudi idan aka kwatanta da takwarorinsu. Sabuwar gasar African Footbal League da hukumar CAF ta kaddamar a 2023 ba a sake yin ta ba, duk da irin rigingimun...
    – Lokacin: Asabar 2:00 na rana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Har yanzu dai gwamnatin Syriya ba ta komai ba game da barna da hasarar rayuka da makamai da kuma jiragen da ake amfani da su da ta sararin samaniyarta ke haifarwa ba. Shafin Intanet na kafar Enab na kasar Syria ya wallafa wani labari a ranar 15 ga watan Yuni game da shirun da gwamnatin Syriya ta yi kan karakainar da jiragen yaki da makamai masu linzami ke yi a sararin samaniyar kasar. Wani mai sharhi ya fada wa Enab cewa gwamnatin Syriya ta yanke shawarar tsayawa tsakiya kan lamarin ne kasancewar tana daukar Isra’ila da Iran a matsayin abokan gabarta. Ya ce: “Babu daya daga cikinsu da za ka bayyana shi a matsayin abokin al’ummar Syriya, kuma dukkaninsu sun...
    Mahaifin angon da ’yan uwan angon na jini da danginsa na daga cikin mutane 13 da aka yi wa kisan gilla a hanyar ɗaurin auren ango, inda aka ƙona gawarwarkin wasunsu a cikin motar da ta ɗauko su, a yankin Mangun da ke ƙaramar Hukumar Mangu ta Jihar Filato. Mahaifiyar angon, Malama Faji Sani da ke zaune a ƙauyen ɗan Bami Anguwar Rimi a ƙaramar Hukumar Kudan ta Jihar Kaduna, ta shaida wa Aminiya cewa mijinta da ’ya’yanta biyu da ƙannenta biyu da kuma kishiyarta, na cikin mutanen da aka kashe su a harin na ranar Juma’a da dare. Ta ce mijin nata, Alhaji Sani, wanda da shi suka dogara, ya rasu ya bar ’ya’ya 13 da jikoki da dama....
    Iran ta gudanar da gagarumin jana’izar tare da karramawq ga kwamandojinta da masana kimiyyar nukiliya da wasu ’yan kasar da Isra’ila ta kashe a yankin kwana 12 da aka gwabza a tsakanin ƙasashen. Iran ta shirya gagarumin jana’izar a ƙwaryar birnin Tehran kwana huɗu bayan Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da ɓangarorin biyu ke iƙirarin nasara a yaƙin da aka fara ranar 13 ga Yuni, 2025. A safiyar Asabar daruruwan dubban mutane ne suka fito ɗauke da tutocin ƙasar suna wake-waken jinjina domin karrama kwamandojin da suka kwanta dama a wurin jana’izar. Mutanen sun kuma riƙa daga hotunan mamatan a matsayin waɗanda suka yi mutuwar shahada, a yayin da suke la’antar Isra’ila da Amurka. Daga cikin...
    A safiyar yau ne aka gudanar da tattakin jana’izar shahidai kimani 60 a nan Tehran, wadanda suka hada da kwamandojin sojojin kasar da da masana fasahar Nukliya da sauran mutane maza da mata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto cewa, an fara tattakin Jana’izar ne daga danganlin inkilabi ko juyin juya hali har zuwa dandalin yenci dake tsakiyar birnin na Tehran . Ana dauke da gawakin shahidan rufe da tutan Iran a cikin akwatuna. Daga cikin manya-manyan bakin da suka halarci tattakin har da shugaban kasa Dr Masoud Pezeshkiyan da kuma wasu ministocinsa . A ranar 13 ga watan Yuni ne HKI ta fara kaiwa kasar Iran yaki inda ta kashe mutane da dama daga daga ciki...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, yana daukar shugaban hukumar makamashin Nukliya ta duniya IAEA Rafael Grosi a matsayin wanda ya ingiza HKI kaiwa kasar Iran hare-hare a ranar 13 ga watan Yuni. Ya kuma kara da cewa, Grossi a halin yanzu ya matsa yana son zuwa kasar Iran don ya dubi irin barnan da Amurka ta yiwa cibiyoyin nukliyar kasar Amma Iran ta ce ba zata bashi daman haka ba. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na X ya kuma kara da cewa tuni majalisar dokokin kasar suka jingije aiki da hukumar saboda halayen munafursi na shugaban hukumar ta IAEA zuwa lokacinda Iran ta fahinci cewa...
    An ji karar jiniyoyin gargadi a wurare da dama a HKI suna tashi bayan sun hango malamai masu linzami wadanda sojojin Yemen suka cilla daga kasar zuwa haramtacciyar kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kafafen yana labaran yahudawan na cewa sun yi shirin kakkabo makaman kafin su isa. Amma basu bada rahoton yawan barnan da makamai suka yi ba bayan shigowarsu haramtacciyar kasar. Yahudawan sun bayyana cewa an ji karar jiniyar gargadi a yankunan Beersheba, Dimona da kuma garuruwan da suke kewaye da su a safiyar yau Asabar.  Majiyar sojojin kasar Yemen sun bayyana cewa sun cilla makaman kan haramtacciyar kasar Isra’ila ne saboda ci gaba da kissan kiyashin da take a zirin gaza.
    Gwamnatin kasar Iran ta kai korafi a gaban hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD dangane da yakin da HKI da kuma Amurka suka kaiwa kasar na tsawon kwanaki 12, wanda yayi sanadiyyar rasa rayukan mutane fiye da 600. Nasir Siraj wani jami’in ofishin jakadancin Iran a MDD ya mikawa kwamitionan hukumar Volker Türk  a jiya Jumma’a . Kafin haka dai ministan kiwon lafiya na kasar Iran ya bayyana cewa mutane 627 suka rasa rayukansu a yayinda wasu 4,870 suka ji rauni a yakin kwanaki 12 wanda wadannan kasashe biyu suka keta hurumin sararin samaniyar kasar.  Yakin ya zo karshe ne bayan da HKI ta shelanta tsaida yaki ita kadai. Korafin ya bayyan cewa abinda wadannan kasashe biyu suka yi...
    Iran ta gudanar da gagarumin jana’izar tare da karramawq ga kwamandojinta da masana kimiyyar nukiliya da wasu ’yan kasar da Isra’ila ta kashe a yankin kwana 12 da aka gwabza a tsakanin ƙasashen. Iran ta shirya gagarumin jana’izar a ƙwaryar birnin Tehran kwana huɗu bayan Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da ɓangarorin biyu ke iƙirarin nasara a yaƙin da aka fara ranar 13 ga Yuni, 2025. A safiyar Asabar daruruwan dubban mutane ne suka fito ɗauke da tutocin ƙasar suna wake-waken jinjina domin karrama kwamandojin da suka kwanta dama a wurin jana’izar. Mutanen sun kuma riƙa daga hotunan mamatan a matsayin waɗanda suka yi mutuwar shahada, a yayin da suke la’antar Isra’ila da Amurka. Daga cikin...
    Kasashen Kenya da Tanzaniya da kuma Uganda sun gabatar da kasafin kudin da ya mayar hankali kan zabuka da tattalin arzikin kasashen. Galibi kasafin kudin kasahen Afirka kan mayar da hankali wajen cimmma muradunsu na tattalin arziki da ci gaba. Kasafin kudin kasashen Afirka na 2025 na kunshe da muradun ci gaba da bunkasar abubuwan more rayuwa da kuma ingantuwar al’amuran yau da kullum a kasashen. Kunshin kasafin kudin kasashen Afirka na 2025 ya ware gagarumin kaso a fannin inganta abubuwan more rayuwa da ayyukan kyautata rayuwar al’umma da kuma bunkasa tattalin arzikin kasashen. Kowace shekara kasashen Afirka na ware makudan kudade a kasafin kudadensu. A wannan makala mun zakulo kuku kasashen Afirka 10 da suka fi girman kasafin kudi,...
    Indomie , shahararriyar kampanin taliyar indomie a Najeriya, ta sanar da kaddamar da sabon gangamin ta mai taken Ingantaccen Abinci Domin Nasara. Wannan gangamin yana jaddada rawar da abinci mai gina jiki kamar Indomie ke takawa wajen ciyar da nasarar iyalai da Karin lafiyar su a Arewacin Najeriya. Shekaru da dama kenan da aka san taliyar Indomie da inganci, daɗi da arha a gidajen ‘yan Najeriya. Tallan talabijin na Ingantaccen Abinci Domin Nasara ya kapu Akan wannan manufa, inda ya ke nuna Indomie a matsayin abokin tafiya wajen cinma nasarar dukkan iyalai na faɗin ƙasa. Nasara Ta Hanyar Abinci Mai Gina Jiki An ƙaddamar da gangamin ne a ranar 6 ga Yuni, 2025, Munaso mu kara jaddada jajircewar Indomie wajen...
    “Muna bayar da wannan a matsayin gargadi kai tsaye ga gwamnatin Nijeriya a matakin tarayya da na jihohi. Ka da a bari a zubar da jinin wadannan ‘yan Nijeriya marasa laifi ya tafi a banza.” Shittu, ya lura da cewa hakurin al’ummomin da ake ci gaba da yi wa kisan gilla ba shi da iyaka, ya kara da cewa rashin kamawa da gurfanar da masu aikata laifukan tare da hukuntansu yana nuna gazawar gwamnati. “Muna bukatar a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa, kuma na gaskiya kan wannan kisan kiyashi da kamawa tare da gurfanar da duk wadanda ke da alhakin wannan danyen aikin.  “Muna san a biya isasshiyar diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa, haka kuma a...
    Allah Ya yi wa hamshakin Attajiri, Alhaji Aminu Ɗantata rasuwa. Alhaji Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekaru 94 bayan fama da rashin lafiya. Ɗaya daga cikin attajirai mafiya arziki a nahiyar Afirka, ya rasu ne a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE.)
    Allah Ya yi wa hamshakin Attajiri, Alhaji Aminu Danata rasuwa. Alhaji Aminu Danata ya rasu yana da shekaru 94 a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE)
    Wasu daga cikin jami’an sojojin HKI sun yi furuci da cewa, an ba su umarni ne da su rika bude wuta akan Fararen hula Falasdinawa da suke zuwa cibiyoyin karbar kayan agaji, suna jaddada cewa, wadanda su ka kashe din ba su yin wata barazna a gare su. Jaridar “Haarezt” ta ‘yan sahayoniya ta buga rahoton da ya kunshi furucin sojojin nasu da su ka tabbatar da cewa; An ba su umarni ne da su rika harbin duk wanda su ka gani a kusa da cibiyoyin raba kayan abinci. Jaridar ta kuma ce; Sojojin sun yi amfani da kowadanne irin bindigogi da su ka hada da manya wajen harbin fararen hula Falasdinawa. Yawan Falasdinawan da su ka yi shahada a...
    Ana neman tono gawar tsohon Gwamnan Jihar Oyo, marigayi Otunba Christopher Adebayo Alao-Akala, domin yin gwajin jini (DNA) da nufin tantance halastattun ’ya’yansa da za su ci gadon dukiyar da ya bari. Batun tono gawar ta kunno kai ne bayan taƙaddama ta yi tsami a tsakanin ’ya’yan tsohon gwamnan a kan rabon gadonsa. Babbar ’yar marigayin mai suna Uwargida Oluwatoyin Alao-Aderinto ce ta shigar da ƙara a gaban Mai Shari’a Taiwo na Babbar Kotun Jihar Oyo ta hannun lauyanta, Oladipo Olasope (SAN), inda ta roƙi kotun ta bayar da umarnin tono gawar mahaifin nasu daga kabarinsa domin yin gwajin ƙwayar halittarsa ga wasu mutane bakwai da ke iƙirarin cewa su ne halastattun ’ya’yan marigayin. Uwargida Aderinto ta shigar da ƙarar...
    Tashar talabijin din Aljazira ta bayar da rahoton da yake cewa; Rashin abinci mai gina jiki da karewar madarar jarirai a yankin Gaza, ya sa jarirai biyu sun yi shahada. Majiyar asibitin Nasar ta a  birnin Khan –Yunus dake kudancin Gaza, ta ambaci cewa jariran biyu sun rasa ransu ne saboda rashin abinci mai gina jiki da kuma madarar jarirai.
    Minsitan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci ya kira yi shugaban kasar Amurka Donald Ttump da ya daina yin maganganun da ba su dace ba akan jagoran juyin musulunci Ayatullah sayyid Ali Khamnei. Abbas Arakci ya kara da cewa; Ko kadan  Tehran ba za ta bari wani mahaluki ya ayyana mata makoma ba, idan kuwa har aka kai ta bango ta za ta bayyana hakikanin karfin da take da shi. A jiya Juma’a ne dai shugaban kasar ta Amurka ya yi maganganu na rashin labadi akan jagoran juyin musulunci, sannan kuma ya kara da cewa, zai sake kawo wa Iran  hari idan ta koma tace sanadarin uranium. Jamhuriyar musulunci ta Iran dai ta sha jaddada cewa ba za...
    Kamfanin Dillancin Labarun “Mehr” ya nakalto cewa;  Tun da jijjfin safiyar yau Asabar ne tasoshin jiragen kasa da na safa-safa su ka cika makil da masu son halarta babban filin Juyi na Tehran da can ne zai zama masonin rakiyar shahidan zuwa makwancinsu na karshe. Ana iya ganin dubun dubatar mutane da su ka fito daga kowane bangare na al’ummar Iran domin halartar jana’izar ,yara, mata, masana da kwamandojin soja,  wacce ta  fara da misalin karfe 8;00 na safiyar yau agogon Tehran. Adadin shahidan da ake jana’izar tasu a yau, sun kai 60, za kuma a rufe su ne a makabartar “Baheshti-Zahra” wacce take kunshe da shahidan juyin juya halin musulunci. A shirnmu na rana za a ji cikakken bayani...
    Tallan na talabijin ya bayar da labarin rayuwar Binta, ya kuma mayar da hankali akan irin tasirin da abinci mai kyau ya ke da shi wajen tallafawa iyali. Da labarin ya yi nisa, mun gano Binta tun daga ƙuruciya zuwa shigarta makarantar koyon aikin likitanci. Hakan ya nuna yadda abinci mai kyau da goyon bayan iyali ya ke taka muhimmiyar rawa wajen cin nasara a rayuwa. Binta ta girma tare da cin abinci mai gina jiki ta hanyar cin taliyar Indomie tun da fari. Indomie tun da daɗewa tana da yaƙini kan cewa ciyarwa bai tsaya kawai ga jiki ba ne. Har da taimakawa wajen cikar buri da samar da makomar kowanne yaro zuwa mataki na gaba. Shi ya sa...
    Hukumar samar da bunkasa da hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Sin ta gabatar da taron manema labarai a yau Juma’a, inda aka yi karin haske game da yadda Sin take baiwa kasashen Afirka tallafi da samun bunkasa tare da su cikin hadin gwiwa. An ce, ya zuwa yanzu, Sin tana taimakawa kasashen Afirka fiye da 21 a bangaren kimiyyar aikin gona, inda ta tura musu kwararrun aikin gona fiye da 200. Kazalika, bangarorin biyu suna hadin gwiwa wajen gudanar da ayyukan dake da nasaba da na’urorin wutar lantarki da horar da kwararru da habaka da karfinsu da sauran bangarori. Kana suna kaddamar da ayyukan samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, ciki har da samar da...
    Tawagogin tattauna batutuwan cinikayya da tattalin arziki na Sin da Amurka, sun kara tabbatar da bayanan tsarin aiwatar da muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma yayin tattaunawar da suka yi ta wayar tarho a ranar 5 ga watan nan na Yuni, da karfafa sakamakon da aka cimma a tattaunawar cinikayya da tattalin arziki da aka yi a Geneva. Kakakin ma’aikatar kula da cinikayya na Sin ne ya bayyana haka yau, inda ya ce an tabbatar da bayanan ne bayan bangarorin biyu sun ci gaba da tuntubar juna bayan tattaunawa mai ruwa da tsaki da suka yi a birnin London a ranekun 9 da 10 ga wata. Ya ce Sin za ta bi tsarin doka wajen sake nazari da...
    Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya ziyarci iyalan ’yan ɗaurin aure da aka kashe a Jihar Filato. Tun da farko, Hakimin Basawa, Haruna Abubakar ne, ya wakilci Sarkin lokacin da lamarin ya faru, saboda Sarkin ya yi tafiya. Bom ya kashe mutum hudu da raunata 21 a Yobe Ganduje ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar APC Sarkin, ya bayyana baƙin cikinsa bisa wannan mummunan lamari, inda ya roƙi iyalan da su ɗauki wannan a matsayin ƙaddara. Ya yaba da yadda suka yi haƙuri kuma suka bar komai ga hukuma, ba tare da ɗaukae doka a hannunsu ba. Sarkin ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kaduna na ƙoƙarin ganin an bi wa waɗanda abin...
    A yau Jumma’a 27 ga watan Yunin ne a hukumace aka bude hanyar jigilar kayayyaki ta kasa da kasa da za ta rika aiki a kai a kai, daga Urumqi, yankin jihar Xinjiang ta kasar Sin zuwa Addis Ababa na kasar Habasha. Wannan kuma ita ce hanyar jigilar kayayyaki ta farko daga Xinjiang zuwa Afirka da kuma tasowa daga can.   Hanyar jigilar kayayyakin daga Urumqi zuwa Addis Ababa na gudanar da tafiye-tafiye na zuwa da dawowa kowace Litinin da Alhamis. Bude sabuwar hanyar ba wai kawai ya kaddamar da wata hanya ce mai sauri ta yadda ‘ya’yan itatuwa masu inganci da sauran kayayyakin aikin gona na musamman na jihar Xinjiang za su isa Afirka kai tsaye ba ne, har...
    Ya kafa cibiyar ‘Yakubu Gowon Centre’, wadda da farko ta maida hankalinta ne kan zaman lafiya, da raba rigima, daga baya kuma sai ta ta fadada ayyukan da take yi da suka hada da lamarin kula da lafiya, musamman ma yadda za a kawo karshen, cuta mai karya garkuwar jiki, Zazzabin maleriya,  da kuma cutar Hanta da aka fi sauran kamuwa da ita. Yanzu cibiyar ta yi hadin gwiwa da Hukumar ci gaban sashen Arewa maso gabas (NEDC) saboda a hana yaduwar cutar Hanta mai saurin kamuwa,a Jihoihn sashen  wadanda suka hada da Adamawa,Bauchi, Gombe, Borno, Taraba,da kuma Yobe. Gowon ya ci gaba da kasancewa mai hannu a cikin lamurran da suka shafi zaman lafiya, shirya yin addu’oi saboda kasar...
    Kwanan baya, jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Cing-te, ya fitar da wani bayani a fili, inda a ciki ya canja asalin tarihin kasar Sin, kana ya musanta cewa yankin Taiwan wani yanki ne na kasar Sin tun da da can, kuma, ya kauce wa yin tsokaci kan jerin takardun dokoki na kasashen duniya, wadanda suka bayyana yankin Taiwan a matsayin wani yanki na kasar Sin bayan yakin duniya na biyu. Kazalika, ya kalubalanci kuduri mai lamba 2758 na babban taron MDD da dokokin kasashen duniya. Babu shakka, abin da Lai Cing-te ya yi ya sa ya zama abokin gaban dukkan al’ummomin kasar Sin, da yawansu ya zarce biliyan 1 da miliyan 400, kana ya mai da shi kansa...
    Aƙalla mutum ɗaya ne aka tabbatar da mutuwarsa tare da wasu biyar suna jinya bayan da wata babbar mota ƙirar tirela ta ƙwace ta kutsa cikin kasuwar Mile Six da ke Jalingo babban birnin Jihar Taraba. Shaidun gani da ido a wurin sun bayyana cewa, duk ƙoƙarin da direban motar ya yi na hana afkuwar lamarin ya ci tura. Ƙudan zuma ya tarwatsa ɗaliban da ke jarrabawar NECO ’Yan sanda sun kama ɓarayi 5, sun ƙwato kuɗi da makamai a Gombe Aƙalla motoci biyu ne suka yi mummunan lalacewa a lamarin. Jami’an Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) da hukumar tsaro ta farin kaya sibil defens (NSCDC) da kuma rundunar ’yan sandan Najeriya (NPF) sun halarci wurin da jajantawa yankin...
    Taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na lokacin zafi na Davos, wanda aka gudana a tsakanin ranar 24 zuwa ranar 26 ga watan nan da muka ciki, a birnin Tianjin na kasar Sin, ya samu halartar wakilai kimanin 1800 daga kasashe da yankuna sama da 90, adadin da ya kai koli cikin tarihi. Kamar yadda babban daraktan dandalin Davos Borge Brende ya bayyana, “in muka duba yanayin kasashen duniya, za a gane cewa, wakilai a fannonin masana’antu da kasuwanci na kasashe da dama, suna fatan zuba jari a kasar Sin, tare da zurfafa hadin gwiwar cinikayya dake tsakaninsu da kasar Sin.” A halin yanzu, kasuwannnin kasar Sin suna ci gaba da samun kyautatuwa da karuwa, lamarin da ya samar...
    Koyon ilimi ta kafar sadarwa ta zamani yana kara bayyana muhimmancin koyarwa musamman, ma ga wadanda suka dade suna koyon.Akwai samfuna dadama wadanda ake amfani dasu wajen koyarwa wadanda ana tsara su ko shiryasu ne domin su kasance daidai,da fahimtar dalibai.Irin yadda ake bi ko amfani da hanyoyi wajen tabbatar da cewar an samu inganta bunkasar dabaru,kai harma da ci gaba da tunawa da lamarin tattalin arziki domin ci gaban wanda zai taimakawa mutum. Ida ana bukatar damarmakin da za’a fahimci abin ya zahirance,kamata yayi ayi amfani da manhajar da ta dace, ko tayi daidai da bukatun manya wadanda suke wani kamfani.   Ta yaya ilimin da ake samun damar mallakarsa zai daidaita yadda rashin shi ke damuwar duniya gaba...
    An watsa shirin talibijin mai taken “Yawon bude ido a Tuscany” a Florence na Italiya, da babban rukunin gidan radiyo da talibijin kasar Sin CMG da hukumar yawon bude ido ta yankin Tuscany na Italiya suka tsara da kuma gabatar cikin hadin gwiwa. Shugaban CMG Shen Haixiong da babban jami’in hukumar sun shaida bikin gabatarwar, kuma sun yi musanyar ra’ayi mai zurfi game da daukar shirye-shirye cikin hadin gwiwa da gabatar da albarkatun yawon bude ido da kiyaye al’adu da sauransu. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
    Wasu gungun ƙudan zuma sun kai hari tare da tarwatsa ɗaliban da ke rubuta jarrabawar Hukumar da ke shirya jarrabawar kammala sakandare ta ƙasa ta Najeriya (NECO) a makarantar sakandaren kimiyya ta Mairi da ke Maiduguri a Jihar Borno. Wannan hari na ba-zata da gungun ƙudan zumar suka kai ya tilastawa ɗalibai da malaman makarantar tserewa daga harabar makarantar domin neman tsira. Shugaban APC na ƙasa Ganduje ya yi murabus NDLEA ta kafa cibiyar kula da masu shaye-shaye a Yobe  Shaidun gani da ido sun ce, sun ga ɗalibai na barin litattafai da takalma da jakunkuna, har ma da kekunansu yayin da suke gudu daga makarantar. A cewar wani ɗalibin da ke jarabawar da ya nemi a sakaya sunansa ya...
    Ofishin kula da aikin harba kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ba da labari cewa, jiya Alhamis da karfe 9 da mintuna 29 na dare agogon Beijing, ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20, wato Chen Dong da Chen Zhongrui da Wang Jie sun cimma nasarar fitowa daga akwatin gwaji na Wentian, yin tattaki a waje na tsawon sa’o’i 6.5, da kuma komawa akwatin, bisa taimakon na’urori masu hannun injin dake tashar sararin samaniya da jagorancin masu nazarin kimiyya da fasaha dake doron kasa. Yayin da suke aiki a waje, Chen Dong da Chen Zhongrui sun cimma nasarar hada na’urorin kiyaye tashar sararin samaniya daga sassan wasu na’urorin da aka daddasa a sararin samaniya, da binciken na’urorin dake waje...
    Yau Jumma’a da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Senegal Ousmane Sonko da shugaban kasar Ecuador Daniel Noboa a birnin Beijing, fadar milkin kasar Sin. Wadannan shugabannin biyu sun zo kasar Sin ne domin halartar taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na lokacin zafi na Davos. A yayin ganawarsa da Ousmane Sonko, Xi Jinping ya ce, kasar Sin tana son zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Senegal, tare da aiwatar da “Manyan matakai 10 bisa hadin gwiwar abokantaka” yadda ya kamata, da kuma kaddamar da karin ayyukan tallafawa al’umma, tare da sa kaimi ga kamfanonin kasar Sin su zuba jari a kasar Senegal domin raya sabbin makamashi, da gina ababen more rayuwa na...
    “Yunwa da talauci ba wai abubuwa ne da suka shafi al’umma ba ne kawai, su ne ke haifar da rashin tsaro, laifuka, tashin hankali, da kuma wargajewar al’umma, wadannan al’amura suna haifar da mugun yanayi, talauci yana haifar da rashin tsaro da rashin tsaro, sannan kuma ya kara zurfafa talauci. “Wadannan yunkurin a bayyane suke ta hanyar kara tallafi ga shirye-shiryen samar da abinci, habaka karfin aiwatar da doka, da ababen more rayuwa don tallafawa samarwa da rarraba noma. “A ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, ONSA, muna ci gaba da hada kai da ayyukan motsa jiki da marasa karfi a fadin rundunonin soja, jami’an leken asiri, hukumomin tsaro, da masu ruwa da tsaki na gwamnati da...
    Sojojin Sama sun kai gagarumin farmaki sansanonin ’yan bindiga da ke Jihar Neja a ranakun Laraba da Alhamis. Wannan farmaki na zuwa ne a matsayin ramuwar gayya bayan da ’yan bindiga suka kai hari kan wasu dakarun Najeriya a kwanan nan. ’Yan sanda sun kama ɓarayi 5, sun ƙwato kuɗi da makamai a Gombe Ribas: Duk wani rikici tsakanina da Fubara ya ƙare – Wike A cikin wata sanarwa da rundunar sojin sama ta fitar a shafinta na sada zumunta, ta bayyana cewa an kai harin ne a ƙarƙashin wani shiri da ake kira FANSAN YAMMA, wanda nufinsa shi ne kawar da barazanar da ’yan ta’adda ke haddasawa. Sanarwar, wadda ta samu sa hannun Daraktan Yaɗa Labaran rundunar, Air Commodore...
    Duk da haka, a cikin ‘yan shekarun da suka wuce, rashin daidaituwa na jiki ya bayyana. Jami’ai sun fara fitar da takardun tambayoyi domin samun kudi a wasu kwanaki kafin a fara jarabawar, inda ‘yan kasuwa marasa kishi, dillalai, da malalata dalibai suka lalata shirin. Wannan ya gurgunta kyawawan manufofin WAEC da ta bada fatawa da kuma kawo cikas ga ingancin takaddun shaida. Abubuwan da suka faru na baya-bayan nan sun kara jaddada lalacewar tsarin ilimin kasar. Kusan wata guda da fitowar WASSCE, matsalar tsara JAMB ta tilasta wa dubban daliban UTME a jihohi shida da wasu sassan Legas yin jarrabawar bayan an basu maki kadan. Wannan abin takaici ya sa wata daliba da abin ya shafa ta kashe kanta...
    Dickson ya goyi bayan buƙatar gudanar da bincike kan jinkirin aiwatar da kasafin yana mai jaddada cewa matsalar ba ta shafi rashin kudi ba tare da kira ga majalisar ta umarci kwamitocin kasafin kudi su gudanar da bincike cikin mako guda su kuma kawo rahoto. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta samu nasarar kama wasu ɓarayin daji da suka addabi garin Bajoga da ke Ƙaramar Hukumar Funakaye. Wannan na daga cikin ƙoƙarin da rundunar ke yi wajen yaƙar masu aikata laifuka a faɗin jihar. Ribas: Duk wani rikici tsakanina da Fubara ya ƙare – Wike NAJERIYA A YAU: Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Hana Mata A Arewa Koyon Ilimin Kimiyya? A wata sanarwa da Kakakin Rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar, ya bayyana cewa an kama mutum huɗu da ake zargi da kai wa wani matashi mai suna Muhammed Ahmed hari, wanda ke zaune a Unguwar Matasa, Bajoga. An ce ɓarayin sun kai masa hari da makami cikin dare, inda suka tsoratar da shi da...
    Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya tabbatar da cewa tattaunawar da suka yi da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta kawo ƙarshen duk wata rigima da ke tsakaninsa da Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara. A daren ranar Alhamis ne Shugaba Tinubu, ya jagoranci wani zaman sulhu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, tsakanin Wike da Gwamna Fubara da kuma wasu daga cikin ’yan majalisar Ribas da aka dakatar. NDLEA ta kafa cibiyar kula da masu shaye-shaye a Yobe  Tinubu ya rattaba hannu kan sababbin dokokin haraji Bayan ganawar, Wike ya yi magana da manema labarai, inda ya tabbatar da kawo ƙarshen rikicinsa da Fubara. “Dukkaninmu mun amince mu yi aiki tare da Gwamna, kuma...
    Ya kara da cewa, babban makasudin kafa cibiyoyin da kudaden jama’a shi ne bunkasa masana’antu, da rage bukatar musayar kudaden waje, da samar da fa’idoji masu yawa ga kasar nan. Idu ya ce IDCs, musamman Cibiyoyin shiyyoyi hudu, sun cika da manyan injina don yada ilimin fasahar masana’antu da fasahar da za su yi tasiri matuka kan yunkurin kasar na samar da masana’antu. Ya bayyana damuwarsa cewa, “A tsawon shekaru, kusan dukkanin IDCs, ma’aikata da kayan aiki a yi asarar su kuma wasu kayan aikin sun daina aiki. “Duk da cewa gwamnatin tarayya ta mika wadannan cibiyoyi ga hukumar kula da masu kananan sana’o’i ta kasa (SMEDAN) tsawon wasu shekaru a yanzu, babu wani abin da aka yi gaba daya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Haka shi ma, shugaban ADC, Cif Ralph Okey Nwosu, ya karyata amincewa da ADA, yana mai cewa batun zama jam’iyya kawance lokaci ya riga ya shude. Ya ce sake bijiro da kawance a hukumance ya faru ne wannan makon, bisa ga shawarar daga dukkan masu ruwa da tsaki. A cewar wani rahoto, NNCG ta yi rajistar ADA a hukumance ga INEC. Wasikar neman rajistar ADA daga INEC an sanya hannu a kai daga shugaban kungiyar na wucin gadi, Cif Akin A. Rickets, da sakataren kungiyar na wucin gadi, Abdullahi Elayo. Hadakar ta kuma gabatar da takardu masu muhimmanci, daga cikin su akwai kundin tsarin mulkin jam’iyyar da aka bayar da manufifinra da tambari da kuma bayanan taron kafa ta. Wasikar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ta bayyana cewa, an kashe ‘yan bindigar da dama yayin wannan gumurzu da ya dauki tsawon wasu awanni ana fafatawa da sojojin. Koda-yake dai a cewar rundunar sojin, an kashe musu wasu daga cikin jami’ansu; yayin musayar wuta da ‘yan bindigar a daidai wancan lokacin. Baya ga haka, rundunar sojin ta kuma kara da cewa; wasu sojoji hudu sun jikkata sakamakon harbin bindiga daga ‘yan ta’addar, amma kuma suna nan suna samun kulawa a asibiti. Har wa yau, rundunar sojin ta kuma bayyana wadanda suka mutun a matsayin cikakkun Jarumai, wadanda suka tsaya tsayin daka, domin kare matsayinsu da kuma mutuncin kasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
    Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta  kafa karamar cibiyar kula da muggan kwayoyi a Damaturu babban birnin jihar Yobe. Kwamandan hukumar a Jihar, Abdulazeez Ogunboye  ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Damaturu a wani bangare na bikin ranar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta duniya ta shekarar 2025. Tinubu ya rattaba hannu kan sababbin dokokin haraji Sheikh Dahiru Bauchi ya cika shekara 101 a duniya Ogungboye ya kara da cewa cibiyar wacce tun daga lokacin da ta fara aiki na daya daga cikin nasarorin da hukumar ta samu a jihar. “An shigar da mutane tara da suke ta’ammali da muggan kwayoyi a cibiyar, daga cikin su...
    Ya kuma yi watsi da ikirarin da ake yi na cewa ‘yansanda na taimakawa wajen magudin zabe, yana mai bayyana irin wadannan zarge-zarge a matsayin mara tushe, tare da cewa aikin ‘yansanda a lokacin zabe ya takaita ne kawai wajen samar da tsaro da tabbatar da zaman lafiya. “Mu ba ’yan bangar siyasa ba ne, mu kamar alkalan wasa ne, aikin ‘yansanda ya takaita ne kuma ya ta’allaka ga samar da tsaro a lokacin zabe, gwargwadon yadda ya kamata, ba za mu yi zabe ba, jama’a ne za su kada kuri’a, INEC ta kidaya, muna sa ido. “Kuma wannan ita ce matsayarmu, sannan kuma hanyar da za a bi domin cimma nasara ita ce, sake sabunta hadin gwiwa tsakanin hukumomi,...
    Misali, a lokutan hare-haren, an kone gidaje da dama, inda wasu ahali ma, wanda yawansu ya kai, har zuwa 15, aka shafe su, daga doron kasa, a lokacin da suke kan bacci, a gidansu. Wasu daga cikin wadanda suka tsallake Rijiya da baya daga hare-haren na ‘yan ta’addar, sun bayyna yadda ‘yan ta’addar, suka cinnawa wasu shaguna da ke a wata kasuwa, da ka mayar a matsayin wajen kwanan, ‘yan gudun hijira, wuta. Duk da kokarin da wasu matasa da kuma kokrin jami’an tsaro na dakile maharani, hakan ya faskare su, hatta wani daya daga cikin jami’in tsaro da aka tura wanzar da tsaro, ya rasa ransa. Duk a 2025, a watan Afiiru an kai hare-hare a Logo da Ukum,...
    Daga ƙarshe dai Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sa hannu kan sababbin dokokin haraji guda hudu da a baya suka jawo cece-kuce da zazzafar muhawara a faɗin Najeriya. An dai sanya hannun ne a fadar shugaban kasa ta Aso Rock da ke Abuja ranar Alhamis, inda shugaban ya ce dokokin za su bunkasa harkokin hada-hadar kudade da tattara haraji a kasar. NAJERIYA A YAU: Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Hana Mata A Arewa Koyon Ilimin Kimiyya? Sheikh Dahiru Bauchi ya cika shekara 101 a duniya A kwanan nan ne dai Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da kudurorin su zama doka bayan tafka zazzafar muhawara a zaurukan majalisun guda biyu. Daga cikin waɗanda suka halarci bikin saka hannun akwai Shugaban...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Doctor Zainab Muhammad na daya daga cikin mata a Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da kudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da kalubalen da wasu matan dake yankin Arewa suke bayyanawa suna fuskanta wurin karantar fannin. Doctor Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci daya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba har da mazan ma na kauracewa wannan karatun. Zainab Kwararriyar likita ce wacce ta shahara wurin kula da marasa lafiya a asibitoci. NAJERIYA A YAU: Yadda ‘Yan Najeriya Za Su Kula Da Lafiyar Jikin Su DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi?...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jiya Laraba 25 ga watan Yuni ne, a birnin Rome na kasar Italiya, aka kaddamar da gagarumin bikin nune-nunen kayan al’adu na murnar cika shekaru 55 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Italiya, karkashin hadin-gwiwar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, da ma’aikatar raya al’adu ta Italiya, da gidan adana kayan tarihi na wayin kan dan Adam na Italiya, da cibiyar koyon fasahohin zane-zane dake birnin Rome na Italiya, da kungiyar wasan kwallon kafar Italiya da sauransu. Bikin na nuna nagartattun kayayyakin al’adu sama da dari biyu da shahararrun masu zane-zane, da magadan al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba, da sauran wasu masu aikin fasahohin al’adu na kasar Sin fiye da 100 suka...
    Firaministan Sin Li Qiang, ya bayyana a yau Alhamis cewa, tattalin arzikin Sin zai ci gaba da zama mai bayar da gudunmuwa ga ci gaban tattalin arzikin duniya, kuma fadada da ingantuwar babbar kasuwar kasar Sin za ta ci gaba da samar da kyakkyawar gajiya da za ta kara damarmakin cinikayya da zuba jari ga sauran kasashe.   Da yake jawabi yayin bikin bude taro karo na 10 na kwamitin gwamnonin Bankin Raya Ababen More Rayuwa na Nahiyar Asiya (AIIB), Li Qiang ya tabbatar da kudurin Sin na fadada bude kofa da kokarinta na ganin dunkulewar tattalin arzikin duniya, wanda wani yunkuri ne da zai samar da sabbin damarmakin ci gaba a fadin duniya. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana...
    Shettima zai kuma ziyarci manyan masana’antu da gonaki a sassa daban-daban na Habasha. Masana’antun sun haɗa da Adama Industrial Zone, Mojo Poultry Farm, Shera Dibandiba Mojo Family Farm, Lume Avocado Nursery, da Bishoftu Pea Youth Farm. Wannan ziyara na da nufin ƙarfafa dangantaka tsakanin Nijeriya da Habasha, musamman a fannin noma da masana’antu. Firaminista Abiy zai kuma shirya wata liyafa ta musamman a Fadar Shugaban Kasar domin girmama Shettima da tawagarsa, a matsayin alamar ƙarfafa dangantakar diflomasiyya da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu. Nijeriya da Habasha na da daɗaɗɗen tarihin aiki tare, musamman a fannonin tsaro, kiyaye zaman lafiya da kuma haɗin gwiwar tattalin arziƙi. Wannan ziyara na da burin ƙarfafa wannan dangantaka da kuma samar da damar haɗin gwiwa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Albarkacin cika shekaru 55 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Italiya, an shirya bikin kaddamar da shirin talibijin mai taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” da CMG ya gabatar, a jiya Laraba a birnin Rome, hedkwatar kasar Italiya. Za a fara watsa wannan shiri a kafofin yada labarai na kasar fiye da 30.   An dauki da kuma tsara wannan shiri ne a garin Zhengding na lardin Hebei da Xiamen na lardin Fujian da Hangzhou na lardin Zhejiang da kuma Dunhuang na lardin Gansu da sauran wuraren da Xi Jinping ya taba kai rangadi ko aiki a can, don yin karin haske kan kokarin da Sin take yi wajen zakulo mafarin al’adun Sinawa, da kiyaye kayayyakin al’adu da sauran...
    Ban da haka kuma, wani babban dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin tallafa wa sauran kasashe a fannin aikin likitanci, shi ne akidarta ta “kafa al’ummar duniya mai kyakkyawar makoma ta bai-daya”. A cikin gidan kasar, an yi nasarar kawar da talauci, da kokarin neman wadatar da dukkan al’ummun kasar, lamarin da ya sa ake samun jituwa a tsakanin al’umma, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa. Saboda haka, kasar Sin na ganin cewa, kamata ya yi, a yi kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasashe daban daban na bai-daya, inda za a dinga rage gibin dake tsakanin kasashe, da na zaman rayuwar al’ummu daban daban, ta yadda za a iya daidaita matsalolin da dan Adam ke...
    Adedeji ya ce har zuwa sa’o’i biyu kafin sanarwar, sunan hukumar shi ne FIRS, amma yanzu sunan ya koma NRS. Ya bayyana cewa sabuwar hukumar ba za ta tsaya kan tattara haraji kawai ba, domin yanzu tana damar tattara sauran kuɗaɗen shiga da ba na haraji ba. Hakazalika, za ta yi aiki cikin ’yanci tare da bin ƙa’idojin bayyanan aiki da bin diddigin nasarori. Ya ƙara da cewa sabuwar hukumar za ta mayar da hankali sosai wajen cimma nasarori, kuma za ta yi aiki da ƙwarewa kamar yadda ake yi a sauran ƙasashen duniya. Shi ma shugaban kwamitin gyaran haraji na fadar shugaban ƙasa, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa ko da kuwa doka na da kyau, idan ba a aiwatar...
    Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda ya bai wa Hukumar ƙididdiga ta jihar damar gudanar da ƙidayar almajirai da makarantun Islamiyya a jihar. Babban jami’in ƙididdiga na jihar, Farfesa Saifullahi Sani wanda ya bayyana hakan a Katsina ranar Alhamis, ya ce maƙasudin gudanar da ƙidayar shi ne tsara dabarun inganta tsarin. ’Yan sanda sun kashe ’yan fashi da ƙwato makamai a Kaduna An tallafawa iyalan ’yan sanda da Naira miliyan N13.4m a Borno Babban jami’in ƙididdigar ya bayyana hakan ne yayin wani muhimmin taro na yini ɗaya da masu ruwa da tsaki a jihar. Sani ya ce, “Manufofin ƙidayar sun haɗa da samar da cikakkun bayanai na dukkan Makarantun Alkur’ani da kuma samar da cikakken tsarin yaran da ba su zuwa...
    Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda ya bai wa Hukumar ƙididdiga ta jihar damar gudanar da ƙidayar almajirai da makarantun Islamiyya a jihar. Babban jami’in ƙididdiga na jihar, Farfesa Saifullahi Sani wanda ya bayyana hakan a Katsina ranar Alhamis, ya ce maƙasudin gudanar da ƙidayar shi ne tsara dabarun inganta tsarin. ’Yan sanda sun kashe ’yan fashi da ƙwato makamai a Kaduna An tallafawa iyalan ’yan sanda da Naira miliyan N13.4m a Borno Babban jami’in ƙididdigar ya bayyana hakan ne yayin wani muhimmin taro na yini ɗaya da masu ruwa da tsaki a jihar. Sani ya ce, “Manufofin ƙidayar sun haɗa da samar da cikakkun bayanai na dukkan Makarantun Alkur’ani da kuma samar da cikakken tsarin yaran da ba su zuwa...
    An harbe wasu mutum biyu da ake zargin ’yan fashi da makami ne a ranar Talata a yayin wani artabu da jami’an tsaro suka yi a unguwar Makera da ke Kakuri a Jihar Kaduna. Rundunar ta kuma kama wasu mutane biyu da ake zargin tare da ƙwato tarin makamai da kayayyaki masu daraja da aka sace daga mazauna garin. An tallafawa iyalan ’yan sanda da Naira miliyan N13.4m a Borno Yadda aka kama mai garkuwa da mutane yana tsaka da cin kasuwar shanu a Neja A cewar kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, lamarin ya fara ne da misalin ƙarfe 3:10 na tsakar dare, inda wasu ’yan bindiga 8 suka kai hari a rukunin gidaje na Estate...
    Yawan gawarwakin da aka tsinta bayan harin duk na mabiyansa ne. Ɗaya daga cikin su, Bashari Maniya, wanda tsohon ɗan bindiga ne da ya ce ya tuba kuma ya fara taimaka wa jami’an tsaro, shi ma ya mutu bayan motar da yake ciki ta faɗa rami mai zurfi. Manga ya bayyana cewa ba da bindiga aka kashe Maniya ba, saɓanin jita-jitar da ke yawo. “Sabuwar mota ce, kuma ba su san dajin sosai ba. Yayin da suke gudu a cikin daji, sai suka faɗa cikin wani rami mai zurfi. Motar ta kife, kuma an kasa ciro ta cikin sauƙi,” in ji shi. Ya ce lokacin da aka zo taimaka musu, an same su a cikin motar a sume. Motar ba...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta gabatar da cakin kuɗi Naira 13 da dubu ɗari 4 da 28 da ɗari 6 da 59.95 ga ’yan uwan ​​’yan sanda 10 da suka mutu a bakin aiki. Taron gabatar da kuɗin wanda aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Maiduguri, na da nufin bayar da tallafin kuɗi ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu. Yadda aka kama mai garkuwa da mutane yana tsaka da cin kasuwar shanu a Neja ’Yan sanda sun kama mutum 5 kan kisan Kanawa 2 a Benuwe Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana hakan ne manema labarai a hedikwatar rundunar da ke garin Maiduguri. Kwamishinan ’yan sanda, CP Naziru...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta gabatar da cakin kuɗi Naira 13 da dubu ɗari 4 da 28 da ɗari 6 da 59.95 ga ’yan uwan ​​’yan sanda 10 da suka mutu a bakin aiki. Taron gabatar da kuɗin wanda aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Maiduguri, na da nufin bayar da tallafin kuɗi ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu. Yadda aka kama mai garkuwa da mutane yana tsaka da cin kasuwar shanu a Neja ’Yan sanda sun kama mutum 5 kan kisan Kanawa 2 a Benuwe Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana hakan ne manema labarai a hedikwatar rundunar da ke garin Maiduguri. Kwamishinan ’yan sanda, CP Naziru...
      Bello, a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Muawiyah Yusuf, ya bayyana matukar bacin ransa da alhininsa kan wannan mummunan harin.   Sanata Bello wanda kuma tsohon gwamnan jihar Neja ne, ya yi jinjina ga sojojin da suka rasa rayukansu a bakin aiki, inda ya bayyana su a matsayin jarumai na kasa wadanda suka sadaukar da rayuwarsu domin kare zaman lafiya da ‘yancin Nijeriya.   Ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan sojojin da suka rasu, yana mai addu’ar Allah ya kara musu lafiya, ya basu hakurin juriya da irin wannan rashi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    An kama daya daga cikin mutanen da ake zargi da yin garkuwa da mutum uku a ƙauyen Daku da ke Gwagwalada Abuja lokacin da yake tsaka da cin kasuwar shanu ta Izom da ke Guraran jihar Neja. Rahotanni sun ce a ranar tara ga watan Yunin 2025 ce dai aka sace wasu makiyaya su biyu da wani direba a kusa da kauyen na Daku. An sace mutanen ne lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida daga kasuwar ta Izom. ’Yan sanda sun kama mutum 5 kan kisan Kanawa 2 a Benuwe Ba zan yi Tinubu ba a 2027 matukar ya canza Kashim Shettima – Sheik Jingir Mutanen da aka sace ɗin dai a wancan lokacin sai da suka biya...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benuwe, sun kama mutum biyar da ake zargi da hannu a kisan wasu matasa biyu ’yan asalin Jihar Kano. Waɗanda aka kashe sun haɗa da Jamilu Ahmad da Barhama Suleiman, kuma an kai musu hari ne cikin daren ranar Litinin a unguwar Agan, kusa da ƙofar shiga Makurdi. Gwamnatin Neja ta rufe Jami’ar IBB bayan ɓarkewar rikici 2027: Zan karɓi kowane irin muƙami da Tinubu zai ba ni — Sanata Barau An yi jana’izarsu a ranar Talata a Babban Masallacin Abuja, inda manyan jami’ai suka halarta, ciki har da Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf. An birne su a maƙabtar Gudu, inda Ribadu da Gwamna...
    Rahotanni sun bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai karkashin jagorancin wani fitaccen kasurgumin dan bindiga mai suna Babaro sun kwace iko da jagorancin karamar hukumar Kankara a jihar Katsina. Wani mai sharhi kan harkokin tsaro,  Bakatsine ne ya bayyana hakan a wani sharhi da aka wallafa a shafinsa na X, yana mai cewa, maharan sun kashe mazauna yankin da dama, tare da hana ayyukan noma, da kuma haddasa durkushewar ayyukan kasuwanci na yau da kullum a yankin. “Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan bindiga karkashin jagorancin babaro sun kwace iko da jagorancin karamar hukumar Kankara, jihar Katsina. An hana noma daga Marabar Kankara zuwa ‘Yantumaki, an kashe mutane da dama, an yi garkuwa da wasu, kiwon lafiya ya durkushe. Mazauna garin...
    Gwamnatin Jihar Neja, ta rufe Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU) da ke Lapai saboda matsalolin tsaro da suka janyo mutuwar wasu ɗalibai. Sakataren Gwamnatin Jihar, Abubakar Usman, ya ce an ɗauki wannan matakin ne saboda rashin tabbacin tsaro da ke barazana ga rayuwar ɗalibai da ma’aikata. Yadda na kuɓuta daga harin Filato — Wani mutum 1447: Yau ce ranar sabuwar shekarar Musulunci – Sarkin Musulmi Gwamna Umaru Bago ya amince da rufe jami’ar nan take, kuma za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai an samu sauyi. “Lafiyar kowa, musamman ɗalibai da malamai, na da matuƙar muhimmanci ga gwamnatin Jihar Neja,” in ji sanarwar. “Mun yi matuƙar baƙin ciki da abin da ya faru, kuma muna ɗaukar matakan...
    Ɗaya daga cikin baƙin da suka tafi ɗaurin aure daga Zariya, Abbas Rufa’i, ya bayyana yadda ya kuɓuta daga harin da wasu matasa suka kai musu a Ƙaramar Hukumar Mangu da ke Jihar Filato. A cewarsa, “Da muka tsaya a hanya domin yin tambaya, na fito daga motar domin neman hanya. Amma sai na ga yadda mutanen da ke wajen suka fara mana wani irin kallo. Gwamnatin Gombe za ta sayi takin N8.8bn don tallafa wa manoma 1447: Yau ce ranar sabuwar shekarar Musulunci – Sarkin Musulmi “Na ji ɗaya daga cikinsu yana cewa, ‘a kashe su gaba ɗaya, a ƙone motar.’” Rufa’i ya ƙara da cewa, “Na cire rigata, na shiga cikin daji har na sai da na samu...
    Majiyoyi sun kuma ce “an kashe adadi mai yawa na ‘yan bindigar”.   Shugaban karamar hukumar, Abbas Adamu Kasuwan-Garba, ya ce harin ya kara firgitar da manoman yankin.   Ya ce taimakon gaggawa daga barikin soji na Kontagora ya tilastawa ‘yan bindigar tserewa zuwa dazuka.   Ya kuma ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da shanu, sun farfasa shaguna tare da kwashe kayan abinci da kayayyaki masu daraja a shagunan mutanen yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ƙoƙarinta na bunƙasa noma da samar da isasshen abinci, Gwamnatin Jihar Gombe ta amince ta sayi tan 10,000 na taki, wanda ya yi daidai da buhu 200,000 domin shirin noman daminar bana. Kwamishinan Harkokin Noma na Jihar, Dokta Barnabas Musa Malle, ya ce za a kashe Naira biliyan 8.8 wajen sayen takin. 1447: Yau ce ranar sabuwar shekarar Musulunci – Sarkin Musulmi 2027: Zan karɓi kowane irin muƙami da Tinubu zai ba ni — Sanata Barau Ya ce hakan na nuna yadda gwamnatin jihar ke ƙoƙarin tallafa wa manoma da kuma ƙara samar da abinci a jihar. Dokta Malle ya ce, “Gwamnati ta fito da sabbin hanyoyin aiki sama da yadda aka yi a baya, kuma za a raba...
    Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Jama’atul Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheik Sani Yahaya Jingir, ya ce ba zai goyi bayan takarar Bola Tinubu ba a zaben 2027 matukar ya canza Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa. Ya bayyana hakan ne yayin wani taron wa’azi a masallacinsa na ’Yan Taya da ke Jos, babban birnin jihar Filato. Aminiya ta rawaito cewa a zaben 2023 da ya gabata dai Sheikh Jingir ya goyi bayan Tinubu sannan ya umarci magoya bayansa da su ma su yi haka a wancan lokacin. Gwamnatin Kano ta ba da hutun sabuwar shekarar musulunci Za mu ci gaba da tattaunawa da Iran kan yarjejeniyar nukiliya — Trump Jita-jitar da ake yadawa dai a kan cewa akwai yiwuwar Tinubu...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kula da lafiya na nufin yin abubuwa da ke kare mutum daga kamuwa da cututtuka da kuma tabbatar da cewa jiki na aiki yadda ya kamata.   Wannan ya haɗa da cin abinci mai gina jiki, motsa jiki akai-akai, da dai sauran su. Sai dai a wannan zamani ‘yan Najeriya ba kasafai suke kula da lafiyar jikin su ba, a mafi yawan lokuta ma sai ciwo ya kwantar da mutum sannan yake tunawa da likita. Ko wadanne matakai ya kamata ‘yan Najeriya su ringa dauka wajen kare kan su da ma lafiyar jikin su? NAJERIYA A YAU: Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar Hannu DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin...
    Dan wasan mai shekaru 40 ya zura kwallaye 93 sannan ya taimaka wajen zura 19 a wasanni 105 da ya buga a dukkanin wasannin da ya buga a kungiyar ta Saudiyya, amma har yanzu bai samu nasarar lashe kofi a gasar ba, a kakar wasan da aka kammala kwanan nan, Al Nassr ta kare a matsayi na uku a teburin, inda ta rasa gurbi a gasar cin kofin zakarun yankin Asia na shekara mai zuwa kuma a maimakon haka za ta buga gasar AFC Champions League 2.   Bugu da kari, Al Nassr a halin yanzu ba ta da koci tun bayan da ta raba gari da babban kocinta Stefano Pioli a ranar Laraba, wanda ya zama koci na uku...
    “Na yi aiki a kamfanin NNPC kuma na tafi da mutuncina, babu wanda ya zarge ni da wata zamba a tsawon zamana a Kamfanin, mutanen da ke yada wannan labarin na karya na kamawa da tsare ni kawai suna haka ne domin son su bata min suna.”   Mista Ajiya ya ce a shirye yake a kowanne lokaci don kare martabarsa da kuma tsawon shekaru da ya yi a hukumar ta NNPC, inda ya ce, “Ina kasar nan kuma a kowacce rana da kuma duk lokacin da EFCC ta bukaci na bayyana a gabansu zan zo”. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
    A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Mozambique Daniel Francisco Chapo, suka mikawa juna sakon taya murnar cika shekaru 50 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasashensu. A cikin sakonsa, shugaba Xi ya bayyana fatansa na kara hadin gwiwa da Chapo, a fannin yayata dadadden zumuncinsu bisa wannan zarafi mai kyau, da kuma zurfafa hadin gwiwarsu bisa tabbatar da ingantacciyar shawarar “ziri daya da hanya daya”, da kuma dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da sauransu. A nasa bangare, Chapo ya ce, kasarsa na fatan zurfafa huldar bangarorin biyu, bisa tushen mutunta juna, da samun ci gaba da cin moriya tare, da kuma habaka hadin kai, da kiyaye tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya kuma bukaci al’ummar Musulmi da sauran al’ummar Kano da su yi amfani da wannan dama wajen yin tunani a kan ayyukan da suka yi a cikin shekarar da ta gabata, tare da yin addu’o’in zaman lafiya da hadin kai da ci gaba a jihar da kasa baki daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tun da farko, Gwamna Aliyu ya ce, gwamnatinsa ta bullo da shirin ne domin ta saukaka farashi da kashi 20 ta hanyar saukar da farashin kayan abinci kasa warwas. Gwamnan ya ce, an tsara shrin ne domin saukakawa ma’aikatan jiha, na kananan hukumomi da masu karbar fansho ta hanyar samar da nau’ukan kayan abinci kamar shinkafa, gero, alkama, masara, dawa, man girki da taliya a cikin farashi mafi sauki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp