HausaTv:
2025-07-03@11:16:54 GMT

 Arakci Ya Mayar Wa Da Jami’ar Harkokin Wajen ” EU” Martani

Published: 3rd, July 2025 GMT

Minstan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya mayar da martani da kakkausar murya akan furucin jami’ar diplomasiyya ta tarayyar turai Kaya Jallas na cewa Iran ta dakatar da shirinta na makamashin Nukiliya, yana mai cewa; Jallas ta jahilci abinda dokokin NPT su ka kunsa.

Abbas Arakci ya ce; Idan manufar ganawa da kwamitin hadin gwiwa akan yarjeniyar Nukilar iran shi ne kawo karshen Shirin makamashin Nukiliyar Iran, to kuwa Jallas ta jahilci abinda yake kunshe a cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman Nukiliya.

Ita dai babbar jami’ar harkokin wajen tarayyar turai Jallas ta rubuta sako a shafinta na X cewa; Ya zama wajibi a bude tattaunawa da sauri da Iran akan yadda za ta kawo karshen shirinta na makamashin Nukiliya, kuma ficewa daga yarjejeniyar NPT ba zai zama mai taimakawa ba wajen warware batun da yake da alaka da Shirin makamashin Nukiliyar Iran.

Arakci ya kuma ce ; Wannan yana nufin cewa; rawar da tarayyar turai da kuma Birtaniya za su taka a cikin duk wata tattaunawa a nan gaba, za ta zama maras ma’ana.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnan Bauchi zai ƙirƙiro sabbin masarautu

Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya amince da kafa kwamitin mambobi 41 da nufin kafa sabbin masarautu a faɗin jihar.

Wata sanarwa da kakakin gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar ta bayyana cewa kwamitin ya ƙunshi fitattun mambobi 41 da aka zabo daga ɓangarori daban-daban, ciki har da sarakunan gargajiya, ƙwararru, malaman jami’a, wakilan ƙungiyoyin farar hula, lauyoyi, jami’an tsaro, da ƙungiyoyin addini.

Sanarwar ta ce, “Wannan shiri ya biyo bayan kiran da gwamnatin jihar ta yi tun da farko na gayyatar al’ummomi da su gabatar da buƙatunsu na sabbin masarautun gargajiya.

“Kwamitin yana da alhakin tantance waɗannan bukatun bisa ƙa’idar adalci, daidaito, shigar da kowa cikin harkokin siyasa da zamantakewa, da ɗorewar tattalin arziki.”

Alhaji Hamza Koshe ne zai jagoranci kwamitin, tare da Mai Shari’a Habibu Idris a matsayin Mataimakin Shugaba. Sauran mambobin sun haɗa da manyan jami’an gwamnati, masu ba da shawara na musamman, da wakilai daga Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), Ƙungiya Jama’atu Nasril Islam (JNI), Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Kungiyar ’Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), da kuma hukumomin tsaro daban-daban.

Farfesa Ibrahim Garba, wani masanin tarihi daga Jami’ar Maiduguri, yana cikin ƙwararrun da aka kawo don jagorantar kwamitin kan la’akari da al’adu da tarihi.

An shirya cewa Gwamna Bala Mohammed zai ƙaddamar da kwamitin ranar Alhamis, 3 ga Yuli, a Gidan Gwamnati, Bauchi, da karfe 10:00 na safe, in ji Gidado.

Ya ƙara da cewa duk wannan tsari na da nufin ƙarfafa masarautun gargajiya, inganta shigar jama’a cikin harkokin mulki, da kuma raya al’adun jihar. (NAN)

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mujallar “Foreign Policy”Ta Amurka: Isra’ila Ba Ta Yi Nasara A Yaki Da Iran Ba
  • Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Irin Aniyar Da Gwamantinsa Ta Kudurta Wajen Kare Tsaron Kasa Da Al’ummarta
  • Kasar Iran Ta Nuna Ire-Iren Makamai Masu Linzami Da Ta Mayar Da Martani Da Su Kan ‘Yan Mamaya
  • Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Iran Ta Bayyana Lokacin Ci Gaba Da Ayyukan Cibiyoyinta Ta Nukiliya
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Cewa: Ba Za A Iya Kawar Da Fasahar Nukiliya Da Karfi Ba
  • Gwamnan Bauchi zai ƙirƙiro sabbin masarautu
  • Shugaban Kasar Iran Ya Yi Kakkausar Suka Kan Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Ta IAEA
  • Shugaban kasar Iran ya soki lamirin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Ce; Dokar Majalisar Shawarar Musulunci Ta Kasar Kan Hukumar IAEA Dole Ne Aiki Da Ita