’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 6, sun raunata wasu a Kwara
Published: 3rd, July 2025 GMT
Aƙalla jami’an tsaro shida ne suka rasu bayan wata arangama da suka yi da ’yan bindiga a yankin Gada Woro a kan hanyar Patigi da ke Ƙaramar Hukumar Edu a Jihar Kwara.
Waɗanda suka rasu sun haɗa da ’yan banga guda biyar da ɗan sanda ɗaya.
‘Mutum 600 da suka bace a ambaliyar Mokwa sun mutu’ Lakurawa sun kashe mutum 15 a harin ramuwar gayya a SakkwatoWasu sojoji biyu, ’yan sanda biyu sun samu raunin harbin bindiga a fafatawar da ta faru a ranar Litinin.
Waɗanda suka rasu sun haɗa da Mohammed Nma Dsuru daga Kokodo, Yanda daga Lafiagi, da Ndagi Saraka daga Edogi.
Rahotanni sun ce ’yan bindigar da yawansu ya kai ɗaruruwa sun kai wa tawagar jami’an tsaro farmaki a cikin daji, inda aka yi ta musayar wuta.
Wasu daga cikin waɗanda suka jikkata an kai su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin (UITH) domin samun kulawa.
Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna yadda aka fafata a dajin.
Wasu mazauna yankin sun ce lamarin ya fara ne a ranar Asabar, lokacin da aka sace wani fitaccen mai sayar da magungunan gona wanda ya dawo daga aikin Hajji.
’Yan bindigar sun shigo da babura, suka shiga gidansa da ke unguwar Taiwo da misalin ƙarfe 1 na dare sannan suka tafi da shi.
A ranar Lahadi, sun sake kai wani hari inda suka sace ɗan kasuwa mai sana’ar POS, Alhaji Yaman da wani mutum mai suna Usman.
’Yan banga sun samu nasarar ceto mutum ɗaya daga cikinsu.
Wasu daga cikin al’ummar yankin na zargin cewa wasu mazauna garin na taimaka wa ’yan bindigar a ɓoye, duba da cewa yawancin waɗanda aka sace matasa ne kuma fitattun ’yan kasuwa a yankin.
An yi ƙoƙarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar, Adetoun Ejire Adeyemi, amma ba ta ɗauki waya ko amsa saƙon da aka aike mata ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Arangama hari Jami an Tsaro Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
Hare-haren Isra’ila sun kashe mana mutum 935 a yaƙin kwana 12 — Iran
Hukumomin Iran sun bayyana cewa aƙalla mutum 935 ne suka rasa rayukansu a hare-haren Isra’ila yayin yaƙin kwanaki 12 da ya gudana tsakaninsu da ƙasar.
Cikin waɗanda suka mutu sun haɗa har da mata 132 da yara 38, kamar yadda mai magana da yawun Hukumar Shari’a, Asghar Jahangir, ya bayyana a wata sanarwa a ranar Litinin, wacce kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito.
Magidanci ya kashe matarsa da adda a Yobe HOTUNA: Sabon shugaban rikon APC APC ya jagoranci taron Majalisar GudanarwaA baya, Ma’aikatar Lafiya ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren Isra’ila ya kai 606, sannan mutane 5,332 da suka jikkata.
Jahangir ya ce hare-haren Isra’ila kan gidan yari na Evin da ke Arewa maso Yammacin Tehran sun yi sanadin mutuwar mutum 79, ciki har da fursunoni da ma’aikatan gidan yari, da mazauna yankin.
Ya kara da cewa gidan yarin Evin ya zama ba zai iya aiki ba, kuma an kwashe fursunonin, yana mai kiran harin a matsayin “tauye hakkin ɗan’adam da kuma karya dokokin kasa da kasa.”
A ranar 13 ga watan Yunin nan ne yaƙi ya tsakanin Isra’ila da Iran ya barke, lokacin da Tel Aviv ta ƙaddamar da hare-haren sama kan sansanonin soja, nukiliya, da fararen hula na Iran.
Amurka ma ta kai hari kan cibiyoyin nukiliya na Fordow, Natanz, da Isfahan na Iran, wanda ya ƙara tsananta rikicin.
Tehran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa kan Isra’ila, inda suka kashe aƙalla mutane 29 tare da jikkata fiye da 3,400, kamar yadda Jami’ar Hebrew ta Jerusalem ta bayyana.
Kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa yaƙin ya tsaya sakamakon wata yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta dauki nauyi, wacce ta fara aiki a ranar 24 ga Yuni.