Kotu A Kasar Iraki Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Wadanda Suka Kashe Ayatullahi Baqir Sadr
Published: 1st, July 2025 GMT
Kotu a kasar Iraki ta yanke hukuncin kisa kan wadanda suka kashe Ayatullah Baqir Sadr da ‘yar uwarsa Alawiyya Bint al-Huda
Hukumar tsaron kasar Iraki ta sanar a ranar litinin cewa: Kotun hukunta manyan laifuka ta kasar ta yanke hukuncin kisa kan wadanda suka aiwatar da zaluncin kisa kan Ayatullahi Muhammad Baqir al-Sadr da ‘yar uwarsa Alawiyya Bint al-Huda.
Ofishin yada labarai na hukumar tsaron kasar Iraki ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Kotun hukunta manyan laifuka ta kasar ta yanke hukuncin kisa kan masu laifin Sa’adoun Sabri da Haitham Abdul Aziz, bayan da aka tabbatar da cewa suna da hannu wajen aiwatar da hukuncin kisa kan Shahadar Sayyid Muhammad Baqir al-Sadr da ‘yar uwarsa, Alawiyya Bint al-Huda a shekara ta 1980, tare da aiwatar da hukuncin kisa kan ‘yan kasar da suka hada da talakawa da masu arziki da kuma mambobin jam’iyyar Da’awa a lokacin rusasshiyar gwamnatin Saddam Husain.”
Hukumar ta kara da cewa: “Hukuncin ya zo ne a cikin tsarin kokarin tabbatar da adalci, kuma shi ne kololuwar ayyukan hukumar tsaron kasar, inda ta samu nasarar cafke wadanda ake tuhuma tare da gudanar da binciken da ya dace a karkashin kulawar kwararrun bangaren shari’a.”
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Iraki
এছাড়াও পড়ুন:
Malaman Sunna A Kasar Iran Sun Bayyana Gwagwarmaya Da HKI Wajibi Ne A Sharia
Malaman addinin musulunci daga mazahabar sunna kima 1300 sun tabbatar da cewa gwagwarmaya da HKI wajibi ne a addinin musulunci kuma wajibi ne a Sharia.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto bayanin da malaman suka fitar bayan taron da suka gudanar na cewa tallafawa falasdinawa wadanda HKI take kashewa wajibi ne a sharia. Kuma suna kira ga dukkan malaman sunnan su gane haka su kuma bayyanawa sauran musulmi musamman ahlussa kan cewa jihadi a kan yahudawa sahyoniyya wadanda suke mamaye da kasar Falasdinu wajibi ne ga wanda yake da ikon hakan.
Bayanin ya kara da cewa abinda Falasdinwa suka yi a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023M da kuma fara yakin Tufanul Aksa yana dai dai da sharia.
Daga karshe bayanin ya kara da cewa HKI ta kusan Rushewa. Sannan mamayar da kasashen yamma sukewa kasashen musulmi ya kusan kaiwa ga karshe idan All..ya yarda.