An Kashe ‘Yan Kungiyar Shabab 19 A Kasar Somaliya
Published: 1st, July 2025 GMT
Sojojin kasar Somaliya sun sanar da kai wani farmaki a kudancin kasar da ya yi sanadiyyar kashe 19 daga cikin ‘yan kungiyar ‘al-shabab’.
Sanarwar wacce tashar talbijin din ‘almayadin’ ta nakalto ta ce, sojojin na Somaliya sun kai harin ne a jiya Litinin da dare a yankin Jubayi, wanda kuma bayan kashe ‘yan kungiyar an kuma jikkata wasu da dama.
Ma’aikatar tsaron kasar Somaliya ta kuma ce; sojojin kasar sun yi nasarar kama makamai masu yawa a tare da kungiyar ta ‘al-shabab’.
A cikin watan Disamba na shekarar da ta shude ma dai sojojin na Somaliya su ka yi nasarar kashe ‘yan kungiyar su 130 a jahohin Gulmadag, da Jubaland.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Kan Al’ummar Benuwe, Sun Kashe ‘Yansanda 4
Wani matashi a yankin wanda ya bayyana sunansa da Kaase, ya ce ‘yan bindigar a yunkurinsu na farko sun yi kokarin afkawa garin Daudu amma jami’an tsaro suka dakile su, sai suka tafi Tse Asongu da Asha amma al’ummar garuruwan duk sun gudu kafin isowar su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp