2025-11-27@23:00:34 GMT
إجمالي نتائج البحث: 724

«ware Dala biliyan»:

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana jimaminsa kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, lamarin da ya ce ya kaɗu matuƙa da ya samu labarin. Tinubu ya ce jagoran na ɗarikar Tijjaniya mutum ne mai daraja da ƙima, sannan ya bayyana shi a matsayin madubi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa. Rasuwarsa za ta ba babban giɓi a Najeriya,” in ji shugaban. Shi ma Tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana rasuwar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi a matsayin rashi babba ga al’ummar Musulmi na Najeriya da ma Afirka baki ɗaya. A wata sanarwa da Atiku ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, ya bayyana marigayin da babban malami wanda ya koyar da addini...
    Kasashen Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi Allah wadai da “karuwar yawan tashin hankalin” da yahudawa ‘yan gudun kama wuri zaman ke yi wa fararen hular Falasdinawa, tare da yin kira ga Isra’ila da ta kare al’ummar Yammacin Kogin Jordan. “Wadannan hare-haren dole ne a daina su. Suna kawo cikas ga kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya da kuma tabbatar da tsaron Isra’ila mai dorewa,” in ji ministocin harkokin waje na kasashen hudu a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa. Sun kuma yi maraba da ” bayyanannar adawar” da shugaban Amurka Donald Trump ya nuna kan yunkurin mamaye Yammacin Kogin Jordan kuma sun sake nanata adawarsu “ga duk wani nau’in mamayewa, ko na bangare, ko na...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kaduwa da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Fitaccen malamin ya rasu a Bauchi ranar Alhamis yana da shekaru 101. Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka A cikin wata sanarwa da Kakakin shugaban, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin jagoran da ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa, wa’azi da jagorantar al’ummar Musulmi. Tinubu ya ce rasuwar malamin ba wai asara ce ga iyalansa da almajiransa kawai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya. “Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba ne kuma murya ce ta daidaito...
    Daga Bello Wakili Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karɓi labarin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi cikin alhini da jimami. Fitaccen malamin da ke Bauchi ya rasu ne a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2026, yana da shekaru 101. Shugaban Ƙasan ya yi jimamin rasuwar jagoran Darikar Tijjaniyya, yana bayyana shi a matsayin ginshiƙin ɗabi’a wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa da wa’azi. Shugaba Tinubu ya ce rashinsa babban rashi ne ba ga iyalansa da dimbin mabiyansa kaɗai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya. Shugaban Ƙasa ya tuna da albarka da goyon bayan da ya samu daga marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a lokacin yakin zaɓen 2023. “Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba, mai cike da natsuwa da hikima....
    Daga Bello Wakili Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karɓi labarin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi cikin alhini da jimami. Fitaccen malamin da ke Bauchi ya rasu ne a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2026, yana da shekaru 101. Shugaban Ƙasan ya yi jimamin rasuwar jagoran Darikar Tijjaniyya, yana bayyana shi a matsayin ginshiƙin ɗabi’a wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa da wa’azi. Shugaba Tinubu ya ce rashinsa babban rashi ne ba ga iyalansa da dimbin mabiyansa kaɗai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya. Shugaban Ƙasa ya tuna da albarka da goyon bayan da ya samu daga marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a lokacin yakin zaɓen 2023. “Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba, mai cike da natsuwa da hikima....
    Daga Sani Sulaiman   Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya yi jimami kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2025, yana da shekaru 102. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Mista Emmanuel Bello, ya sanyawa hannu. Gwamnan ya ce rasuwar wannan babban malami babban rashi ne ga kasa, yana mai nuna cewa a wannan lokaci ne ake matuƙar bukatar irin gudummawar da yake bayarwa, duba da kalubalen da kasar ke fusfuskanta. Ya kara da cewa marigayi Sheikh ya koyar da ilimi da zai ci gaba da jagorantar kasa kan...
    Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi, a matsayin babban rashi ga al’umma. Gwamnan ya bayyana malamin a matsayin jagoran haɗin kai, zaman lafiya, da fahimtar juna tsakanin Musulmi da mabiya addinai daban-daban. ’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa A cikin saƙon ta’aziyya da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya sanya wa hannu, gwamnan ya ce Gwamnatin Jihar Bauchi tana alhinin rasuwar malamin. Dahiru Bauchi, ya rasu da safiyar ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamba, 2025 a Bauchi, yana da shekara 102. Gwamnan, ya ce Sheikh Dahiru Bauchi babban malami ne na addinin...
    Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta bukaci maniyyatan aikin hajjin 2026 da su gaggauta biyan kudin kujerun su kafin ranar 24 ga watan gobe. Darekta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taro da shugabannin sassa na hukumar da shugabannin shiyya da sauran ma’aikatan hukumar a Dutse babban birnin jihar. Yana mai cewar, hukumar aikin hajji ta kasa wato NAHCON ta bayyana ranar 5 ga watan Disamba da ta kayyade a matsayin ranar rufe biyan kudin kujerun aikin Hajjin 2026 a fadin kasar nan. Ya bayyana cewar ranar itace ranar karshe da hukumar aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta kayyade na biyan kudin kujerun...
    Daga Salihu Tsibiri Tsohon shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana tabarbarewar tsaro da ake fuskanta, wato ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma hare-haren ’yan bindiga, a matsayin barazana ga  siyasar ƙasar nan gabanin zaɓen 2027. Ya yi wannan tsokacin ne a jawabinsa yayin bude zaman taron musamman na yini biyu da Majalisar Wakilai ta shirya kan halin tsaro da ƙasar ke ciki. Alhassan Ado Doguwa, wanda ya yaba da ayyukan da hukumomin tsaro ke ci gaba da gudanarwa, ya ce halin da Arewa ke ciki abin takaici ne ƙwarai, la’akari da yawan mutanen da ke hannun masu garkuwa da kuma waɗanda ke rayuwa cikin tsananin rashin tabbas. Tsohon shugaban ya jaddada cewa duk da cewa...
    Pars Today – Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, yana mai jaddada muhimmancin Pakistan a yankin, ya ce haɗin gwiwa tsakanin Tehran da Islamabad a fannoni daban-daban yana taimakawa wajen kawo kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankin Ali Larijani, Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, ya ce da sanyin safiyar Talata da ya isa Islamabad cewa Pakistan muhimmiyar ƙasa ce a yankin kuma tana da matsayi mai kyau wajen tasiri ga yanayin tsaro na yankin. A cewar Pars Today, ya ƙara da cewa a matsayinta na maƙwabciyar gabas ta Iran, Pakistan ma tana taka rawa a al’adu, kuma dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu ta daɗe tana da zurfi kuma ta tarihi. Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Jamhuriyar Musulunci...
    Wata gobara ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Mafa da Jihar Borno ta lalata matsugunan wucin gadi guda 40 tare da kayan abinci da sauran kayan gida. Kamar yadda rahoton ke nunawa cewar, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:20 na safiyar Laraba. An tuntuɓi hukumar kashe gobara ta tarayya da ta Jiha nan take, yayin da ƙungiyoyin sintiri ƙarƙashin jagorancin DPO na Mafa suka taimaka wajen daƙile cunkoson jama’a da kuma hana satar kayayyaki. Daga ƙarshe rahoton da ke garin na nuna cewar an kashe gobarar ba tare da an samu rahoton raunuka ko asarar rayuka ba. Har yanzu ba a tantance adadin kadarorin da suka lalace ba, kuma ana ci gaba da bincike kan musabbabin...
    A ranar Alhamis da ta gabata ce karamin kwamiti mai kula da al-amuran nahiyar afirka a majalisar dokokin kasar Amurka ya bude tattaunawa dangane da zargin da shugaban kasar Donal Trump yake yin a cewa ana kashe kiristoci a tarayyar Najeriya fiye da duk wata kasa a duniya. Wanda hakan ya say a yi barazanar daukar matakan soje idan akwai bukatar haka don kawo karshen kissan. Jaridar Premium times ta nakalto Chris Smith dan majalisan da ya jagoranci taron yana fadar cewa zargin Trump gaskiya ne kuma shi a karan kansa ya kai ziyara tarayyar Najeriya har sau uku a baya inda sakamakon ya tabbatar da hakan. Sannan Bishop Wilfred Anagbe daga jihar Benue wanda ya halarci taron ta kafar...
    Iyalai da ‘yan uwan wadanda aka kashe a lokacin zanga-zangar da ta kawo karshen gwamnatin tsohuwar Firaminstar Bangaledash Sheikh Hasina a bara, sun yi maraba da hukuncin kisa da wata kotun birnin Dhaka ta yanke mata. An samu Sheikh Hasina da laifin cin zarafin bil adama tare da ba ‘yan sanda umurnin kashe masu zanga-zanga, inda aka yanke mata hukuncin a bayan idonta. Gwamnatin Bangaledash ta bukaci Indiya da ta tasa keyar Hasina da ke gudun hijira a can domin ta fuskanci hukuncin. Wakiliyar BBC ta ce  Hukumomin Indiya na cewa suna ci gaba da bibiyar lamarin tsakanin Sheikh Hasina da mahukuntan Bangaledash kuma hakan na nufin Indiya na neman wata hanyar diflomasiyya akan lamarin.   BBC
    Mutum uku da wani yaron babbar motar kaya sun rasa ransu bayan wayar wutar lantarki kashe su a lokacin wani bikin nadin sarauta a unguwar Idimu da ke Ƙaramar Hukumar Alimosho ta jihar Legas, bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Talata, 11 ga watan Nuwamba, kuma an gano cewa yaron motar, wanda ba a tantance sunansa ba tukuna, ya mutu nan take a wurin. Najeriya ta ɗora alhakin taɓarɓarewar harkokin tsaronta kan Amurka Babu addinin da ake yi wa kisan ƙare dangi a Binuwai — Gwamna Alia Rahotanni sun ce wani mazaunin unguwar da aka karrama da sarauta ne ya shirya taron cashiyar a titin Anjorin domin murnar nadin. Sai dai yayin da ake tsaka da bikin,...
    Gwamnatin Tarayya ta ɗora alhakin dawowar hare-haren ta’addanci, ciki har da sace dalibai mata a jihar Kebbi da kai hari a coci a jihar Kwara, kan kalaman da Amurka ta yi kwanan nan a kan Najeriya. Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya ce sakonnin da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa, inda ya zargi Najeriya da “kisan kiyasin Kiristoci” tare da barazanar tura sojojin kasarsa, sun kara wa wasu ƙungiyoyin ’yan ta’adda kaimin kai hare-hare. Babu addinin da ake yi wa kisan ƙare dangi a Binuwai — Gwamna Alia Yadda maganin sauro ya yi ajalin magidanci da iyalinsa a Kano “Kalaman da Amurka ta yi kwanan nan sun kara wa wasu ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya da ke son...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mata da dama da aka yi garkuwa da su na shiga wani irin mawuyacin hali yayin da suke hannun wadanda suka sace su, suna fuskantar rayuwar kaskanci, da cin zarafi, da muzgunawa da wasu irin yanayi wanda sai ka tausaya musu. Irin wadannan mata a wasu lokutan basa tsira da rayukansu, a wasu lokutan kuma ko sun tsira, sukan shiga halin ciwon damuwa wanda ke daidaita musu rayuwa, a wasu lokutan ma har sai sun ji kamar su dauki rayuwar su. NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Shirin Najeriya A Yau na...
    Tauraron ƙwallon ƙafar ƙungiyar PSG da ƙasar Morocco, Achraf Hakimi, ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana.  
    Fitaccen ɗan wasan gaba na Najeriya da ke taka leda a ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya, Victor Osimhen, ba zai halarci bikin karrama gwarazan ‘yan wasan Afirka na 2025 ba. Osimhen, wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afirka a 2023, ya bayyana cewa ya koma Turkiyya ne domin duba lafiyarsa, bayan raunin da ya samu a wasan da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta doke Najeriya. Tankin ruwa ya kashe mutum 4, wasu sun jikkata a Jigawa An yanke wa shugaban ISWAP hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari A yau Laraba ne Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) za ta sanar da sunayen gwarazan ‘yan wasan nahiyar na shekarar 2025, a yayin babban bikin da za a gudanar a Morocco. Za...
    Shugaban ƙungiyar masu sayar da tsofaffin ƙarafa a jihar Gombe, A.A. Laja, ya ce gobarar da ta tashi a kasuwar tsofaffin ƙarafa da ke kasuwar katakon jihar ta jawo masa asara da ta kai sama da Naira miliyan 500. Lamarin ya faru ne a daren Laraba, inda wutar ta ƙone shaguna fiye da 30 da ke ɗauke da kayan kasuwancinsa. Sanatan Enugu ya mutu a Birtaniya ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ A.A Laja, wanda ya yi magana da wakilinmu jim kaɗan bayan aukuwar lamarin, ya ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 10 na dare, ta kuma ci gaba da ci har zuwa karfe 4:00 na Asuba, saboda rashin isowar jami’an kashe gobara cikin...
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa dole ne kudirin Amurka da MDD ta amince da shi ya tabbatar da kare hakki da yancin Falasdinawa a sahun gaba samar da kasar Falasdinu. Jakadan Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeed Iraqini, ne ya bayyana haka, a matsayin martanin ga amincewar da kwamitin Tsaro ya yi da daftarin kudirin Shugaba Donald Trump na Amurka game da Gaza. Iran ta yi gargadi akan amfani da wannan kuduri a hanyar da za ta keta ko ta wargaza hakkokin al’ummar Falasdinawa ba, musamman ‘yancin cin gashin kai da kuma kafa kasar Falasdinawa mai cin gashin kanta. A Kudurin da aka amince dashi jiya Litinin, Iran ta jaddada damuwar da wasu membobin...
    Hukumar ƙwallon ƙafar Afirka CAF, ta bayyana cewa bayan tankade da rairaya da ta yi, a yanzu ’yan wasa uku kacal ne suka rage a takarar gwarzon nahiyyar na bana. A wata sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana Achraf Hakimi da Mohamed Salah da Victor Osimhen, a matsayin sauran ukun da suka rage a takarar gwarzon dan ƙwallon ƙafar Afirka na bana. Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno Hakimi, kyaftin din Morocco, ya lashe kofuna daga ciki har da Champions League a PSG — na farko a tarihin ƙungiyar — da Ligue 1, da European Super Cup, da kuma kai wa zagayen ƙarshe...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi November 17, 2025 Manyan Labarai Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka November 17, 2025 Manyan Labarai Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda November 17, 2025
    Sheikh Ahmad Gumi ya yi martani kan kiraye-kirayen da ake yi na kama shi, inda ya ce masu yin kiran na yi ne domin kawar da rawar da yake takawa wajen magance matsalar ’yan bindiga a Arewa. Gumi, ya ce duk ganawar da yake yi da ’yan bindiga yana yi ne domin samar da zaman lafiya, kuma hukumomin tsaro sun san da komai. Ɗan Najeriya ya kashe mahaifinsa, ya yanki ƙannensa da wuƙa a Amurka Tsaro: Na kan yi kuka duk lokacin da na ji an kashe wani — Akpabio Maganar ta sake fitowa fili ne bayan da ya sake jaddada cewa tattaunawa hanya ce da za ta iya kawo ƙarshen tashin hankali a karkara. A cikin dogon saƙon da ya...
    Iran ta yi gargadin cewa tsanantar ayyukan sojojin Amurka a yankin Caribbean da Latin Amurka na haifar da babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro na duniya, kuma ta yi kira da a girmama hurumi da cikakken yancin Venezuela. A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghai, ya ce barazanar Amurka na amfani da karfi kan zababiyar gwamnatin Venezuela ya saba wa dokokin kasa da kasa. Ya kuma bayyana cewa irin wadannan ayyuka tamkar keta ka’idojin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, musamman haramta amfani da karfi. A daya bangaren kuma, M. Baghai ya yi Allah wadai da hare-haren da Amurka ke kai wa jiragen kamun kifi na Venezuela a matsayin misalai na kisan gilla ba...
    Kyaftin ɗin tawagar ƴan wasa matan Nijeriya ƴan ƙasa da shekara 17 (Flamingos), Shakirat Moshood, na cikin jerin ƴan wasa uku da suka kai matakin ƙarshe domin lashe ƙyautar Matashiyar Ƴar Wasan CAF ta 2025. Sauran ƴan wasan da ke fafatawa da ita su ne Moha El Madani daga Morocco da Adji Ndiye ta Senegal. Moshood ta yi fice a manyan wasanninta a gasar cin kofin Duniya na mata ƴan ƙasa da shekara 17 ta FIFA a 2025, ko da yake tawagar da Bankole Olowookere ke jagoranta ta tsaya a zagaye na 16. A duk tsawon gasar, ta kasance ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasan da suka yi ƙwazo a tawagar da kyakkyawan salon wasa. Wasu Mahara Sun Kashe Mata...
    Kungiyar Editocin Nijeriya (NGE) ta yi gargadi cewa yanayin da tattalin arzikin da kasar nan ke ciki ya jefa kafofin yada labarai cikin wani mawuyacin hali. Kungiyar ta kuma yi kira da a soke dokokin da ke takura ‘yancin ‘yan jarida. Shugaban NGE, Mista Eze Anaba, ya bayyana haka ne a jawabin maraba da ya yi a Taron Editocin Nijeriya Gabadaya (ANEC) mai taken “Dimokuradiyya, Gudanarwa da Hadin Kan Kasa: Rawar da Editoci ke Takawa,” wanda aka gudanar a dakin taro na Tarayya, Abuja. Ya yi nanata cewa halin tattalin arziki a kasar ya tilasta wasu gidajen jarida rufewa, yayin da wasu da ke kokarin ci gaba da aiki ba sa iya biyan albashin ma’aikata. A cewarsa, wannan lamari ne...
    A kwanakin nan ana samun raguwar kujerun maniyyata aikin Hajji daga Najeriya, abin da ya jawo fargaba ga masu shirin zuwa kasa mai tsarki da kuma masu hidimar su. A da, Najeriya na samun kujeru sama da dubu casa’in daga gwamnatin Saudiyya, amma cikin shekaru kadan da suka gabata adadin ya ragu zuwa kusan dubu sittin da biyar.   Kazalika a yanzu gwamnatin na saudiyya ta bayyana cewa idan har maniyyatan Najeriya basu biya cikakken kudaden hajjin bana ba, to akwai alamun sake rage yawan kujerun zuwa dubu hamsin. NAJERIYA A YAU: Dalilan Malaman Jami’oi Masu Zaman Kansu Na Shiga Ƙungiyar ASUU DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma Ko yaya...
    A wani muhimmin mataki na inganta harkar lafiya a matakin ƙasa, Karamar Hukumar Gwarzo ta kaddamar da sabuwar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko (PHC) da aka gina a garin Dankado, da ke cikin gundumar Sabon Birni. Taron kaddamarwar, wanda ke nuna wani sabon ci gaba a tsarin raya jama’a, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, da wakilan al’umma. Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo, Dakta Mani Tsoho Abdullahi, wanda Mataimakinsa, Alhaji Abdulmumin Garba Lakwaya, ya wakilta, ya tabbatar da jajircewar gwamnatin sa wajen tabbatar da cewa kowane yanki a cikin karamar hukumar na da damar samun ingantacciyar kiwon lafiya mai sauƙin samu da araha. Ya yaba wa Kakakin Majalisar Dokoki ta Gwarzo, Ahmad Shehu Sabon Birni, da sauran kansiloli bisa...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran ta damu da ci gaba da karuwar zaman tankiya tsakanin Afghanistan da Pakistan bayan karuwar fadan kan iyaka tsakanin makwabtan biyu. A wata tattaunawa ta wayar tarho da Ministan harkokin wajen Afghanistan Mawlawi Amir Khan Muttaqi a wannan Lahadi, Araghchi ya ce Iran a shirye take ta taimaka wajen samar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu na musulmi. Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya kuma jaddada muhimmancin inganta hulda da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu don tabbatar da rabon ruwa daga kogin Harirud. Sojojin Pakistan da Afghanistan sun gwabza a watan da ya gabata, inda aka kashe mutane da dama  a tashin hankali mafi muni tun bayan da Taliban ta kwace iko...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Da zarar damuna ta fara bankawana, yanayi na sanyi da zafi kan fara sallama, wanda hakan kan zo da rashin lafiya dake yaduwa a cikin alumma.   Ko wadanne dalilai ne suka sa ake samun yaduwar rashin lafiya a wannan lokaci? NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
    A bana ne ake cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya na kin tafarkin murdiya, gami da kawo karshen mulkin mallakar kasar Japan a yankin Taiwan da dawo da shi kasar Sin. Kwanan nan ne CMG wato babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin ya wallafa jerin wasu rahotannin talabijin guda biyar dangane da batun dawowar Taiwan kasar Sin. ’Yan jarida ma’aikatan CMG ne suka dauki rahotanni da bidiyo a yankin Taiwan, inda suka yi amfani da kwararan shaidun tarihi, don mayar da martani ga wasu kalaman karya da ke cewa wai “matsayin Taiwan ba shi da tabbas”, tare kuma da bankado markarkashiyar mahukuntan jam’iyyar DPP...
      Sunana Abdulhamid Ado (Danbayaro): Inna lillahi wa inna ilaihirraju’un. Na ji ba dadi na ji komai sai da ya tsaya min har tsahon lokaci, abun ba zai musaltuba, sai dai kawai mu ce Allah ya ji kan Mal. Nata’ala. Mutum ne mai barkwanci, ga zumunci na gaske, ba a yin gulma da shi, baya boye wa mutum gaskiya, kuma baya cin hakkin mutum, kuma abun hannusa baya rufe masa ido. Kuma indai ya samu abun duniya ko baka sani ba sai ya kira ka an ci da kai, harkar sa ba bakin ciki yana da hali mai kyan gaske. Wata rigar san yi da ya kawo mana ‘location’ ya raba mana dukkan ‘crew’ sai da ya bamu, ina ganin...
    Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Jibrin Barau, ya nemi Shugaban Amurka, Donald Trump, ya janye barazanar da ya yi wa Najeriya kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Trump, ya yi barazanar ɗaukar matakin soji a kan Najeriya saboda zargin ana zaluntar Kiristoci. Barazanar Trump: Ya kamata shugabannin Najeriya su farka daga bacci — Bishop Kukah Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso Rock Barau ya ce maganar da Trump ya yi ba ta dace ba, kuma ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa. A cikin wani bidiyo da aka fitar a ranar Juma’a, Mataimakin Shugaban Majalisar, ya ce Najeriya, a matsayinta na ƙasa mai cin gashin kanta, ba za ta yadda a ci zarafinta ko a tsangwame...
    3. A Hangen Nesansa wajen jagorancin al’umma, ya mayar da hankali kan masana’antu, sabunta ababen more rayuwa da kuma gina Dan’adam; domin mayar da Jihar Nasarawa matsayin wata babbar cibiyar zuba jari a Nijeriya da horar da aikin injiniya tare da kyautata jin dadin al’ummar jihar; an zabi Injiniya Abdullahi A. Sule a matsayin Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025. Injiniya Abdullahi Sule: Wanda Ya Fi Yin Fice Kan Harkokin Masana’antu A Duk Fadin Arewa 4. Shugabancinsa ya yi matukar kawo sauye-sauye a Jihar Ekiti, musamman ta hanyar gudanar da mulki na adalci, sabunta ayyukan more rayuwa, karfafa matasa da fadada aikin gona; sakamakon tawali’un da yake da shi da horon da ya samu wajen tafiyar harkokin kudi da gina jama’a tare...
    Sudan na fuskantar matsalar jin kai mafi girma a duniya a daidai lokacin da ake kara samun karuwar fada a Darfur da El Fasher Asusun Kula da kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi gargadin cewa: Matsalar karancin abinci mai gina jiki ta kara ta’azzara a Sudan, yana mai tabbatar da cewa matsalar karancin abinci mai gina jiki ta wuce matakin gaggawa a cikin sama da kashi 60 cikin 100 na yankunan. A halin yanzu, shugaban Majalisar Gudanar da Mulki a Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya jaddada kudurin rundunar sojin kasar na tabbatar da tsaron dukkan iyakokin Sudan da kuma murkushe ‘yan tawayen. Wani sabon gargadin Majalisar Dinkin Duniya ya sanya Sudan a kan gaba wajen fuskantar bala’in...
    Hafsan Sojin Sama na Najeriya, Air Marshal Sunday Aneke, ya umarci dukkanin kwamandojin rundunar da su ƙara ƙaimi wajen yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta ta sama  A yayin wani taron da suka gudanar da Abuja a ranar Laraba, Aneke, ya umarci kwamandojin da su kai hare-hare masu yawa domin kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa. Za a gudanar da wasannin ƙwallon yashi a Abuja An amince da hukuncin yi wa malamai ɗaurin shekara 14 kan lalata da ɗalibai Ya ce, “Dole ne yayin kowane aiki a nuna ƙwarewa da ƙaunar ƙasa.” Mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce taron ya mayar da hankali kan duba dabarun aiki da kuma ƙarfafa haɗin kai a tsakanin kwamandoji....
      Sakamakon kwamitin, wanda ke dauke da kusan shafuka 40 ya bayyana shawarwari kan gyare-gyare da matakan da za a dauka na gaggawa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu  November 5, 2025 Labarai Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista November 5, 2025 Labarai Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio November 5, 2025
    Mai horar da tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta Super Eagles, Eric Chelle, ya ce yana da kwarin gwiwar cewa Nigeria za ta lashe kofin nahiyar Afrika na 2026. Gasar da za a buga a kasar Maroko, Challe ya jadda kwarin gwiwarsa, bisa kafa hujja da zaratan yan wasan da Nigeria ta ke da su. Za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025, karo na 35 daga ranar 21 ga watan Disamba da tawagogi 24 za su fafata, domin lashe babban kofin tamaulan na Afirka. Wannan shi ne karon farko tun 1988 da Maroko ta karɓi baƙuncin wasannin babbar gasar tamaula ta Afirka da take fatan gudanar da bikin da zai ƙayatar da duniya.
    Sojoji sun daƙile wani harin ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Shanono da ke Jihar Kano, inda suka yi nasarar hallaka 19 daga cikin ’yan ta’addan. Bayanai sun ce sojojin sun fafata da ‘yan bindigar ne da yammacin ranar Asabar bayan samun bayanan sirri a yankunan Unguwar Tudu da Unguwar Tsamiya.
    Daga Yusuf Zubairu Kauru  Al’ummar Karamar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna sun shiga halin kaka-ni-ka-yi duba da yadda rayukansu ke kasancewa cikin hadari yayin da suke gonakinsu. A wata tattaunawa ta wayar tarho, wani jagoran matasa, Junaidu Ishaq, ya bayyana cewa kusan shekaru biyar ke nan da hare-haren ’yan bindiga ke ta faruwa akai-akai, wanda ya bar al’umma cikin fargaba da ƙuncin rayuwa. Ya ce manoma suna shiga gonakinsu ne cike da fargaba domin komi na iya faruwa yayin da suke aiki a gonakin. Mazauna yankin sun bayyana cewa Kauru, wadda aka fi sani da yawan gonaki da ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci a jihar Kaduna, yanzu manoma ba sa iya shiga gonakinsu cikin kwanciyar hankali saboda...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik November 2, 2025 Daga Birnin Sin An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu November 2, 2025 Daga Birnin Sin Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya November 1, 2025
    Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya soki Shugaban Amurka, Donald Trump, bisa kiran Najeriya “ƙasa mai matsala ta musamman” kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Sani, ya ce kalaman Trump sun samo asali ne daga bayanan da ba su da tushe, da wasu mutane suka ba shi domin su tayar da fitina a Najeriya. Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia ta yi tazarce da kashi 97 an ƙuri’u A ranar Juma’a ne, Trump ya wallafa rubutu a shafinsa na sada zumunta cewar Kiristanci yana cikin hatasri a Najeriya. Ya yi iƙirarin cewa ’yan ta’adda sun kashe dubban Kiristoci, amma ya ce Amurka za ta yi duk mai...
    Dan wasan da ya lashe kyautar a bara, Ademola Lookman na Nijeriya ba ya cikin jerin ‘yan wasan da aka lissafo a bana, inda hukumar kwallon kafa ta Afirka (Caf) ta samar da kwamitin kwararru wanda ya zakulo masu horarwa da ‘yan wasan da suka “Taka rawar gani” a tsakanin 6 ga watan Janairu zuwa 15 ga watan Oktoban wannan shekara. An bayyana sunan mai horar da tawagar ‘yan kwallon kafa ta kasar Cape Berde, Bubista a matsayin mai neman lashe kyautar mai horarwa mafi kwazo bayan jagorantar tawagar kasar ta Blue Sharks wajen samnun gurbin gasar kofin duniya a karon farko a tarihi. Haka nan tawagar ta tsibirin Cape Berde na cikin masu gogayyar lashe kungiya mafi hazaka a...
    “Amurka ba za ta tsaya kawai tana kallo ba yayin da irin waɗannan ta’addancin ke faruwa a Nijeriya da sauran ƙasashe. “Mun shirya, muna da ƙarfi da niyyar kare Kiristoci a faɗin duniya,” in ji Trump. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano October 31, 2025 Manyan Labarai Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi October 31, 2025 Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025
    Gwamna Inuwa ya kuma jaddada bukatar bin ka’idojin kariya a harkokin sufurin ruwa, inda ya yi kira ga shugabannin kananan hukumomi, da shugabannin al’umma, da direbobin kwale-kwale da hukumomin da ke da ruwa da tsaki da sauran wadanda suka dace su kara kaimi wajen ganin ana kiyaye duk ka’idojin kariya don magance sake afkuwar ibtila’in a nan gaba. Ya umurci Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA) da Majalisar. Karamar Hukumar Nafada su bayar da duk wani tallafin da ya dace ga iyalan da abin ya shafa tare da hada hannu da hukumomin da abin ya shafa don inganta tsaro da wayar da kan al’ummomin da ke yankunan kogi. Gwamna Inuwa Yahaya ya yi addu’a yana mai cewa “A madadin...
    Madagascar ta sanar da kafa sabuwar gwamnati wadda ta kunshi fitattun ‘yan adawa guda uku a manyan mukamai na ministoci. An gabatar da majalisar ministoci mai mambobi 29, wacce ta kunshi mata 10, a wani biki da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Yavoloha da ke babban birnin kasar, Antananarivo. Shugaban rikon kwarya Michael Randrianireina ya bayyana a lokacin bikin cewa manyan abubuwan da sabuwar gwamnatin ta sa gaba sun hada da yaki da rashin adalci, aiwatar da matakan tsuke bakin aljihu, da kuma samar da yanayin kasuwanci mai dorewa. Ya kara da cewa kowane minista dole ne ya samar da sakamako mai kyau cikin watanni biyu, yana mai gargadin cewa rashin yin hakan a cikin wannan lokacin zai zama gazawa...
      Da yake sharhi game da wannan batu a wani rubutu da ya yi a Facebook a ranar Alhamis, Sheikh Gumi ya ce, Sanda ta yi matukar nadama kuma ya tabbata ba halinta ba ne irin wannan mugun aiki face aikin shaiɗan ne ya yi sanadiyyar iftila’in, ba don son ranta ba ne. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC October 30, 2025 Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai October 30, 2025 Manyan Labarai Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar October 30, 2025
    Shugaban karamar hukumar Gwarzo, Dr. Mani Tsoho, ya yi gargaɗi ga mazauna yankin kan mummunan ɗabi’ar shan magani ba tare da shawarar likita ba, yana mai bayyana hakan a matsayin babban haɗari ga lafiya da ka iya janyo matsalolin da ke barazana ga rai. Dr. Tsoho ya yi wannan gargaɗi ne yayin da yake ziyarar duba asibitin Gwarzo General Hospital, inda ya gana da marasa lafiya, ya duba yadda ake gudanar da ayyuka, tare da yabawa ma’aikatan lafiya bisa jajircewarsu wajen kula da jama’a. Ya nuna damuwa cewa, yawancin matsalolin lafiya da ake fuskanta a cikin al’umma na faruwa ne sakamakon amfani ko wuce gona da iri wajen shan magunguna ba tare da shawarwarin ƙwararru ba. Ya shawarci jama’a da...
    Killace Gaza da gwamnatin mamayar Isra’ila take ci gaba da yi tun bayan tsagaita bude wuta ya yi sanadiyyar mutuwar masara lafiya 1000 a yankin Majiyoyin lafiya na Falasdinawa sun tabbatar a yau Alhamis, 30 ga watan Oktoban shekara ta 2025 cewa: Tun bayan tsagaita bude wuta, gwamnatin mamayar Isra’ila ta hana shigar da kayan aikin likita da kayayyakin bukatu cikin Gaza, yayin da marasa lafiya dubu suka mutu sakamakon tsauraran matakan tsaro da kuma rufe hanyoyin shiga cikin yankin. Majiyoyin sun bayyana cewa kashi 10% ne kawai na bukatun lafiya suka shiga yankin Gaza, kuma babu na’urorin MRI masu aiki a yankin Gaza. Dr. Muhammad Abu Salmiya, Darakta Janar na Al-Shifa Medical Complex, ya bayyana cewa tun bayan karshen...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki October 29, 2025 Daga Birnin Sin An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest October 29, 2025 Daga Birnin Sin An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin October 29, 2025
      Zhai Kun, mataimakin shugaban kungiyar nazarin yankin kudu maso gabashin Asiya na Sin, kuma farfesa a jami’ar Peking, ya bayyana cewa, tun daga sigar 1.0 zuwa 2.0 har zuwa 3.0, an samu ci gaba mai zurfi ta hanyar sabbin ka’idoji na fasahar zamani da kare muhalli, da sabunta tsarin amince da ka’idojin juna, da kara karfin hadin gwiwar samar da kayayyaki, inda ya inganta yankin ciniki daga matsayin “kara adadi” zuwa “ingantacciyar bunkasa”. A yayin da ra’ayin bangaranci da babakere ke takura tsarin hadin gwiwa na duniya, wannan sabon tsarin ya samar da wata hanya iri ta Asiya don kiyaye tattalin arzikin duniya mai bude kofa. (Amina Xu) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Yi Taron Tataunawa...
    An sanya dokar hana zirga-zirgar jama’a a Dar es Salaam, babban birnin Tanzania, bayan da ɗaruruwan mutane sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsarin gudanar da zaɓen ƙasar. Bayanai sun ce masu zanga-zangar sun riƙa yaga hotunan Shugaba Samia Suluhu Hassan tare da ƙona wani ofishin ’yan sanda, yayin da suke zargin cewa akwai son kai da rashin gaskiya na fifita jam’iyya mai mulki, tare da neman gwamnati ta gyara tsarin zaɓe da kuma ba kowa damar faɗar albarkacin baki. Gwamnati ta bai wa ASUU N2.3bn domin biyan bashin albashin malamai Sassauci na yi wa Maryam Sanda ba afuwa ba — Tinubu Zanga-zangar dai ta ɓarke ne yayin da ake tattara sakamako bayan kammala kaɗa ƙuri’a a zaɓen na...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC October 29, 2025 Labarai COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa  October 29, 2025 Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci October 29, 2025
    Ƴan sanda a kasar Tanzania sun saka dokar hana zirga-zirga a fadin kasar bayan zanga-zangar da ta barke yayin zaben shugaban kasa da ya rikide ya koma tashin hankali a wasu sassa daban-daban na kasar. Rahotanni sun nuna cewa, zanga-zangar ta barke ne musamman a birnin Dar es Salaam da wasu garuruwa yayin da jama’a ke nuna rashin jin daɗi kan yadda ake gudanar da zaben shugaban kasar. Masu zanga-zangar sun yi zargin cewa akwai son kai da rashin gaskiya a tsarin zaben, kuma sun  nemi  gwamnati ta gyara tsarin zabe da kuma ba kowa damar fadin albarkacin baki. A cewar jami’an tsaro, an sanya dokar ne domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Sai dai wasu kungiyoyin kare hakkin dan...
    Shugaban kasar iran Mas’ud pezeshkiyan ya aike da sakon taya murna ga takwaransa na kasar Turkiya Rajab dayyib ardogan da ma alummar kasar na farincikin zagayowar ranar da kasar ta samu yancin kai, kuma ya jaddada muhimmancin kara kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu. Iran da Turkiya suna da alaka mai zurfa ta tarihi aladu da kuma dabarun yaki, a daidai lokacin da ake samun sauyi a yankin , akwai bukatar kasashen biyu sun kara hadin guiwa a fannonin kasuwanci tsaro da kuma diplomasiya, sakon na pezeshkiyan ya nuna aniyar iranta fifita yin hulda tsakanin kasashen biyu Akwai abubuwa da dama da suka yi kama da juna tsakanin kasashen biyu masu abokantaka da yan uwantaka, pezeshekiyan, ya kara da cewa ta...
      Don haka, an mayar da hukuncin kisa na Maryam Sanda zuwa shekaru 12 a gidan yari, wanda hakan ya nuna tana da kasa da shekaru shida na zama a gidan gyaran halin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC October 29, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa October 29, 2025 Manyan Labarai Tsoron Boko Haram Ne Ya Sa Jonathan Ya Fasa Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II October 29, 2025
    Shugaba Bola Tinubu, ya janye afuwar da ya yi wa Maryam Sanda da masu laifukan da suka haɗa da kisan kai, safarar miyagun ƙwayoyi da sauransu. Maryam Sanda, wadda aka yanke wa hukuncin kisa saboda zargin kashe mijinta, ba ta cikin sabon jerin sunayen wadanda aka yafe wa laifi. Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya tabbatar a ranar Laraba cewa an cire sunayen mutane kimanin 50 daga tsohon jerin bayan ce-ce-ku-ce daga jama’a. “Bayan duba martanin jama’a, Shugaba Tinubu ya umarci a cire sunayen wadanda aka samu da manyan laifuka kamar garkuwa da mutane, safarar miyagun kwayoyi, da fataucin mutane daga jerin wadanda aka bai wa afuwa,” in ji Onanuga. Ya kara da cewa an dauki wannan...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa duk da jajircewar kungiyar na mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da ita, firaministan gwamnatin Isra’ila yana kokarin karya sharuddanta. Hazem Qassem, kakakin kungiyar, ya ce “Mun yi wa masu shiga tsakani bayani kan cikas din da ke hana neman gawarwakin fursunonin Isra’ila kuma mun nemi su samar mana da karin kayan aiki.” Mai magana da yawun Hamas ya kuma bayyana cewa: “Mun sanar da Alkahira game da ayyukan bincike na ‘yan Isra’ila, kuma muna ci gaba da sanar da masu shiga tsakani game da ci gaban binciken. Duk da tsagaita wuta da aka yi tsakanin gwamnatin Tel Aviv da kungiyar Hamas, sojojin Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare. Na...
    Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta bayyana damuwa kan yadda wasu ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a Najeriya ke cikin wadanda ake zargin suna taimakawa wajen daukar nauyin ta’addanci a sassan Najeriya. Hukumar ta gargaɗe su da masu hakar ma’adinai da su guji zama hanyar safarar kuɗaɗen haram ko tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci ta kowace hanya, tana mai jan hankalinsu da su daina harkokin da ke hana ci gaban tattalin arziki da tsaro a ƙasar. Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ne ya faɗi haka a Ibadan, hedikwatar Jihar Oyo, yayin taron wayar da kai da horaswa na rana ɗaya da aka shirya domin masu haƙar ma’adinai da ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a jihar. Taron ya samu haɗin...
    Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta bayyana damuwa kan yadda wasu ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a Najeriya ke cikin wadanda ake zargin suna taimakawa wajen daukar nauyin ta’addanci a sassan kasar. Hukumar ta gargaɗe su da masu hakar ma’adinai da su guji zama hanyar safarar kuɗaɗen haram ko tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci ta kowace hanya, tana mai jan hankalinsu da su daina harkokin da ke hana ci gaban tattalin arziki da tsaro a ƙasar. Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ne ya faɗi haka a Ibadan, hedikwatar Jihar Oyo, yayin taron wayar da kai da horaswa na rana ɗaya da aka shirya domin masu haƙar ma’adinai da ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a jihar. Taron ya samu haɗin...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu October 28, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno October 28, 2025 Manyan Labarai APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba October 27, 2025
    A ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 1945, wato bayan da kasar Sin ta samu nasara a yakin kin harin mayakan Japan, kasar ta Sin ta karbi yankin Taiwan daga hannun Japanawa da suka yi rabin karni suna mamayar yankin, inda suke aiwatar da mulkin mallaka. Sa’an nan zuwa ranar 25 ga watan Oktoban bana, babban yankin kasar Sin ya gudanar da biki na musamman don tunawa da dawowar yankin Taiwan cikin harabar kasar. Dangane da batun, dimbin kafofin watsa labaru na kasashe daban daban suna ganin cewa, bikin da aka shirya ya nuna nasarar da Sinawa suka samu a yakin duniya na biyu, kana ya shaida cewa, Taiwan wani yanki ne na kasar Sin, wanda ba za a iya...
    Gyaran da aka fara ya yi daidai Nambobi suna ba da labarin wani ɓangare na labarin,  amma suna bayyana lamarin ne kawai, amma suna bayyana lamarin gaba ɗaya. A shekarar 2023, FIRS ta samu Naira Tiri liyan12.36, abinya zarce kuɗaɗen da ake tsammanin shigowa daga gare ta, har ma wuce kashi 7 na kuɗaɗen shigar da ake sa ran da ake zata kawo, hakan kuma shi yasa mafi kayu ɗin kuɗaɗen shigar da aka samu a tarihin tara kuɗaɗen haraji. A shekarar 2024, an kuɗaɗen shigar suka ƙaru da—Naira Titiliyan 21.7, ba kamar na shekarar 2023 ba , inda aka nsamu Naira Tiriliyan19.7. Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar Gwamnan Bauchi...
      Wannan nasara mai ban mamaki ta sa kungiyar Niger Tornadoes ta koma matsayi na biyu a teburin gasar, inda yanzu take da maki 17 a kasan Nasarawa United. Hakazalika, sakamakon ya bar Kano Pillars a cikin mawuyacin hali a gasar yayin da ta ke matsayi na 19 da maki 8 kacal. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus October 25, 2025
    Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) reshen Jihar Gombe, ta bayyana alhini bisa rasuwar Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar, Laftanar Kanar Abdullahi Bello (mai ritaya). Haka kuma hukumar ta bayyana jimami kan da ɗan sandan da ke tsaron kwamishinan, Sajan Adamu Husaini, da direbansu, wadanda suka rasu a wani mummunan hadarin mota da ya afku ranar Juma’a. Sojoji sun daƙile harin ISWAP a Borno An ba da tallafin N2m ga iyalan jami’in NSCDC da aka kashe a Jigawa  A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na NSCDC a jihar, SC Buhari Sa’ad, ya fitar, Kwamandan hukumar, Jibrin Idris, ya ce rasuwar babban rashi ce ba ga iyalan mamatan kawai ba, har ma ga Gwamnatin Jihar Gombe da al’ummar...
    Aikin, wanda ke wakiltar tashar fitar da ɗanyen fetur ta farko da kamfanin Afirka mai zaman kansa ya bunƙasa a ƙasar, yana nuna babban jarin da ya wuce dala miliyan 400 a matakin farko, inda ake sa ran kuɗin zai ci gaba da bunƙasa har ya haura dala biliyan 1.3. GEIL, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Anthony Olusegun Adegbulugbe, wani sanannen malami kuma ƙwararren masani a fannin tsare-tsaren makamashi, yana da ƙwarewa mai sosai a tsawon shekaru masu yawa. Yana aiki a matsayin shugaban jami’ar Joseph Ayo Babalola da ke Jihar Osun, ya kuma kasance babban mai ba da shawara kan makamashi ga tsohon shugaba ƙasa, Olusegun Obasanjo. Haka kuma ya kasance shugaban shirin “National Gas to Power” na Nijeriya kuma ya...
    Yana magana ko jawabi cikin hankali, amma kuma shawarwarin da yake badawa suna da matuƙar amfani wajen kawo gyaran wurare da dama. Mai ilimi, tsara yadda za’a ɓullo ma al’amura, mutunci ga kuma kwarjini da ƙwarewa An haife Kalu 5 ga Mayu, 1971, a Agbamuzu, a ƙaramar hukumar Bende ta Jihar Abia State, tarihin rayuwar Kalu ya fara ne daga aiki da kuma samun tallafin ƙaro ilimi. Yana da digirin digirgir PhD a tsarin al’umma da kuma karatun abinda da wayo ake koyonsa (Jami’ar Abuja), da kuma LL.M akan ta’addanci da taimakawa kan jin ƙai  (Distinction, daga Jami’ar Kalaba), da MBA daga Jami’ar Oɗford Brookes  (UK), da kuma LL.B (Hons.) daga Kalaba. Ya cigaba da karatu— halin yanzu yana karanta...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Kiwon Lafiya Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka October 25, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu October 25, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello October 25, 2025
    Ana haka ne Gwamna Babagana Umara Zulum ya kai ziyara ƙaramar hukumar, inda ya gana da Misis Duaka a cibiyar lafiya da misalin ƙarfe 8 na dare, lokacin da sauran ma’aikatan duk sun tashi. Wannan aiki na sadaukarwa, juriya da biyayya ga aikinta, ya sa Gwamna Zulum ya fahimci cewa ta himmatu wajen kula da lafiyar mutanen Mafa, mahaifar sa. Gwamnan dai a wasu ziyarce-ziyarcen da ya kai har sau biyu, ya ware ta, ya kuma yaba wa sadaukarwar da ta yi, tare da yaba mata kan yadda ta tsaya tare da jama’arsa duk kuwa it aba ‘yar asalin yankin ba ne. Kyautar kwazo da rikon amana da ta samu ya zo ne a lokacin da Gwamna Zulum, wanda ya...
    Ba wai nasara kawai ba ce; saƙo ne, cewa masu horarwa na Nijeriya na iya kai wa matakan duniya, kuma ƙwarewar gida har yanzu tana da muhimmanci. Hanyar Da Ba A Yawanta Binta Labarin Madugu ba na nasara cikin dare ɗaya ba ne, yana yi ne sannu a hankali da ƙwarewa mai ɗorewa. Daga farkon ayyukansa na horarwa ya fara da Adamawa United da ƙungiyar mini-football ta Nijeriya, zuwa aiki a matsayin mataimakin mai horarwa a gasar WAFCON huɗu (2012, 2014, 2018, 2022), ya gina suna saboda natsuwa, sassaucin dabaru, da basira. Lokacin da ya karɓi cikakken jagorancin Super Falcons a shekarar 2024, da yawa sun yi shakku kan iya cika takardun zama wasu ƙwararrun masu horarwar na ƙetare da...
    Aƙidar Dr Bello abu ne mai saƙin gaske kuma akwai hikima a ciki sosai. Shi ne kuma samar da ingantacciyar kiwon lafiya wand aba wai sai kana da kuɗi mai yawa ba. Tsarinsa shi ne haɗa yi wa mutane aiki, ilimantar da su tared fda kuma tsugunar da su. Wannan mataki ne da yake tabbatar da an samun cikin gaggawa da kuma sauƙin gaske.. Daga Legas zuwa Kano, daga Ondo zuwa Kuros Riba, kungiyar CFDF tana tafiya da kayan aiki na tafi da gidanka da kuma rundunar likitoci masu tiyata na sa kai, masu aikin jinya, da ma’aikatan jinya. Kowace manufa asibiti ce mai motsi – duba marasa lafiya, yin hadaddun tiyata, da bayar da shawarwari da tallafin abinci mai...
    “Gudanar da harkokin kuɗaɗe ba bayar da taimako ba ne, haƙƙi ne.”  Ƙoƙarin Cike Gibi Tare Da Gina Makoma Mai Kyau Lokacin da OPay ya shiga fannin harkokin kuɗaɗe na zamani a Nijeriya, ƙalubalen ya kasance bayyane suke, kusan rabin yawan mutanen Nijeriya ba su da damar samun shiga harkokin kuɗaɗe. Waɗanda suka kafa kamfanin sun gano cewa yawancin ‘yan Nijeriya sun yin isa da bankuna, tsarin yana haifar da jinkiri, kuma tsarin yana da barazana mai yawa. OPay ta kasance mai sauƙin gudanarwa, wani tsarin kuɗi na wayar hannu da ya dace da rayuwar yau da kullum ba tare da tangarda ba. Daga biyan kuɗi ta walat zuwa biyan kuɗin kayayyakin more rayuwa, daga sayan katin waya zuwa mu’amaloli...
    A shekarar 2008, Skales ya shiga gasar Zain Tru Search kuma ya lashe yankin ArewaTsakiya na gasar. A lokacin, ya riga ya saki waƙarsa ta farko “Must Shine”, wacce ta samu yawan fitowa a tashoshin Rhythm FM a Lagos, Jos, da Abuja. Ana tuna shi da burinsa na zama babban mawaƙi da sha’awar ilimi, ya ɗauki sunan mataki SKALES, wanda ke nufin “Seek Knowledge, Acƙuire Large Entrepreneurial Skills”. Daga baya ya koma Lagos, inda ya sanya hannu kan yarjejeniyar rikodi da Empire Mates Entertainment (E.M.E.) a shekarar 2009. Waƙarsa ta shekarar 2009 “Heading for a Grammy”, wadda take waƙar ƙarfafa kai, ta samu wahayi ne daga ƙalubalen rayuwarsa a wancan lokaci. Skales yana ɗaya daga cikin manyan mawaƙan da suka...
    Sauyin shugabannin tsaro dai ya nuna matakin da Tinubu ke ɗauka wajen sake fasalin tsaro, amma kuma ya buɗe sabon babi na tattaunawa kan yadda ake kula da tsofaffin hafsoshin da suka ba ƙasa hidima tsawon shekaru. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi October 25, 2025 Manyan Labarai Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin October 25, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe October 25, 2025
    A ƙarƙashin jagorancinsa mai hangen nesa, hukumar NUPRC ta zarce burinta na samun kuɗaɗen shiga har da kashi 84.2 cikin ɗari, tana motsawa da ƙarfafa tattalin arziki da sauyi mai zurfi a fannin masana’antar. A matsayinsa na shugaban farko na CCE, Injiniya Komolafe ya haɗa da ƙwarewa ta injiniya da fahimtar doka cikin ƙwarewa don inganta aiwatar da Dokar Masana’antar Mai (PIA), inda ya kafa tsare-tsaren kula da aiki bisa gaskiya, ɗorewa, da bin ƙa’idar ƙwarewar duniya. Jagorancinsa ya haifar da ci gaban fasahar zamani, inda aka gudanar da mafi fa’idar tsarin neman lasisi a tarihin Nijeriya, tare da aiwatar da manufar “Haƙowa ko Barin Filin” (“Drill or Drop”), wanda ya farfaɗo da filayen haƙar mai da suka daɗe a...
    Lokacin da Etuh ya zama wanda ake maganarsa  musamman ma idan an taɓo maganar Takin zamani,  masana’antar ta kama hanyar lalacewa saboda ‘yan baran da sun mamaye ta, ga kuma cuwa-cuwa da ta yi wa wurin katutu, lamarin da ke sa ba a iya gane manoman gaskiya. Duk da hakan ba ta sa Etuh ya yi ƙasa a gwiwa ba wajen haɗa kan da ya yi da gwamnatin tarayya, Etuh ya taimaka wa tsarawa da kuma gabatar da lamarin Takin zamani na Shugaban ƙasa Bola Tinubu (PFI),lamarin da ya kawo gaggarumin ci gaban aikin gona, domin kuwa an samu raguwar farashi,ya kuma samar da wata kafa inda manoma suke samun Takin zamanin kai tsaye. Sakamakon haka ya sa yanzu...
    Mahaifin Rukayya, Muhammad Adamu mazaunin ƙauyen Bayan Dutse da ke Wailo, a gundumar Kubi cikin ƙaramar hukumar Ganjuwa a ranar 17 ga watan Oktoba ya kai rahoton caji ofis ɗin Soro ya ke shaida cewar wani matashi mai suna Auwal Dahiru mai shekara 17, ya kai farmaƙi wa yarsa da ƙoƙarin kasheta da kwaƙule mata idanuwanta.  Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil a ranar Litinin, ya ce, lokacin da ‘yansanda suka samu rahoton faruwar lamarin cikin gaggawa a ƙarƙashin Baturen ɗansanda da ke kula da caji ofis ɗin Soro, CSP Aliyu Mohammad Goni, sun kai agaji inda lamarin ya faru. A lokacin da aka ɗauki Rukayya zuwa asibitin koyarwa na...
    A shekara biyu kaɗai,ya yi ƙoƙarin maida Jihar Kaduna da aka sani da rarrabuwar kai, yanzu ta koma tsintsiya ɗaya sanadiyar hakan. Yin gyara ta hanyar ci gaba Gwamna Sani ya hau kan karagar mulki ne a shekarar 2023 ba a matsayin wanda ya iya lamarin siyasa sosai ba, sai dai mai son kawo agyara. Aikinsa na farko ba siyasar bace —mutane ne yafi maida hankali kansu. Ya fara ƙaddamar da lamarin gaggarumin ci gaban ƙauyuka ta yadda abin ya zama a kowace ƙaramar hukumar akwai aikin da ake yi.Gina hanyoyi, asibitoci,  makarantu, kasuwanni an fara gigginasu a ƙananan hukumomi  23 . Cikin ci gaban daya samu sun haɗa da: Haɓaka ƙananan asibitoci 225 inda aka mayar da su matsayi...
    Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa gobara ta lalata rumfuna 529 daga cikin rumfuna na wucin gadi a Kasuwar Shuwaki da ke ƙaramar hukumar Gari, Jihar Kano. Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Alhaji Saminu Abdullahi, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Kano. A cewarsa, hukumar ta samu kiran gaggawa misalin ƙarfe 3:25 na rana daga Abdulmalik Muhammad na ofishin kashe gobara na Gari, yana sanar da aukuwar gobara a kasuwar. Ya bayyana cewa, da zarar sun samu bayanin, hukumar ta aika jami’ai da motocin kashe gobara zuwa wurin domin kashe wutar tare da hana ta yaduwa zuwa sauran sassan kasuwar. Saminu ya ce yankin kasuwar yana da fadin kimanin...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu October 24, 2025 Manyan Labarai Dauda Lawal Gwarzon Gwamnan 2025: Ceto Zamfara Domin Ci Gaba October 24, 2025 Manyan Labarai Buƙatar Daƙile Badaƙalar Amfani Da Takardun Karatun Bogi A Nijeriya October 24, 2025
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A cikin ‘yan watannin da suka gabata, an sake ganin karuwar hare-haren Boko Haram da ISWAP musamman a yankin Arewa maso Gabas. Kazalika, ko a kwanan nan ma anga irin wadannan hare hare.   Wadannan hare-haren sun fi karkata kan sansanonin sojoji, inda ake samun asarar rayuka da dama, da kuma lalata kayan aikin gwamnati. Rahotanni daga Borno da Yobe da ma wasu sassan kasar nan sun nuna yadda ‘yan ta’adda suka sake samun karfi wajen kai hare-hare cikin dare, tare da amfani da dabaru irin na soji da kuma kayan yaki na zamani. Wannan lamari ya jawo tambaya daga al’umma: shin wannan karin hare-hare alama ce ta dawowar kungiyar Boko Haram da...
    A yau Alhamis 23 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya karyata wani rahoto na zuki-ta-malle da wata cibiyar bincike ta Amurka ta bayar kan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ta Yamma. Ya yi nuni da cewa, rahoton ya kawo rudani ga ra’ayoyi na kaifin basira, sannan daga bangare guda kawai aka tattaro shi, kuma har ma ya ruwaito wasu bayanan da ba a tantance ba, tare da shafa kashin kaji da kuma muzanta hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen yammacin Afirka. Wannan ya kasance wani bakon abu a fili kuma abin kyama. An ba da rahoton cewa, cibiyar nazarin al’amura ta Amurka ta Atlantic Council, ta fitar...
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa  zata kara karfafa dankon zumunta da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa NAFDAC. Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka a lokacin da mahukunta hukumar NAFDAC suka ziyarce shi a ofishin sa dake Dutse babban birnin jihar. Ya bayyana farin cikinsa da ziyayar, inda ya jaddada bukatar aiki tare domin cimma dukkan nasarar da ake bukata a tsakanin hukumomin biyu. Da yake bayani dangane da shirin da hukumar alhazan take yi, Labbo yace dukkanin shirye-shirye sunyi nisa na rigistar kujerun aikin hajji shekarar 2026. Yana mai cewar, hukumar NAFDAC tana cikin masu ruwa da tsaki na hukumar jin dadin alhazan jihar. Alhaji Ahmed Labbo, yayi nuni...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Babaganaru Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars October 22, 2025 Labarai Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta October 20, 2025 Wasanni Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara October 20, 2025
    Hukumar Kula da Harkokin Ƙwallon Ƙafa a nahiyyar Afirka (CAF) ta fitar da sunayen ‘yan takarar da za su lashe kyautar CAF ta shekarar 2025 – rukunin maza. Cikin wata sanarwa da CAF ta wallafa a shafinta na intanet, ta ce an yi la’akari da rawar da ’yan wasa da masu horarwa suka taka wajen bunƙasa kwallon ƙafa a nahiyar Afirka da ma duniya baki ɗaya. Hukumar ta ce fitattun masu takarar sun ba da muhimmiyar gudunmawa a fagen tamaula wanda za a yi la’akari da rawar da suka taka a tsakanin ranar 6 ga Janairu zuwa 15 ga Oktoba, 2025. Idan Tinubu ya gaza zai yi wuya a samu shugaban da zai yi nasara — Shehu Sani Waɗanda ke...
      Mummunan lamarin na ranar Talata ya kasance kwatankwacin abin da ya faru a watan Janairu kamar yadda rahotanni suka ce, mutane sun taru a kauyen Essa, suna kwasar mai daga wata tankar mai da ta kife, daga nan kuma sai ta fashe wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 35, da jikkata wasu sama da 40, tare da lalata dukiyoyi na miliyoyin naira. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki  October 22, 2025 Manyan Labarai Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi October 22, 2025 Labarai Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025 Na Jaridar Leadership: Dauda Lawal October 22, 2025
    Wannan tsarin na taimaka wa yara su samu ilimi mai zurfi da zai ba su damar daidaita da tsarin rayuwarsu na yau da kullum. Makarantun suna da ɗakunan kwana, gidajen malamai, wutar lantarki mai amfani da hasken rana, rijiyoyin burtsatse, kujeru, kayan karatu, da cibiyar koyon sana’o’i kamar ɗinki, sassaƙa, kwamfuta, da sauransu. Haka kuma, gwamnan ya gyara Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a ta Jihar Zamfara da kuma Kwalejin Fasaha da Kimiyya ta Zamfara (ZACAS). A ɓangaren lafiya kuwa, gwamnatinsa ta gyara asibitoci da cibiyoyin lafiya da dama a faɗin jihar. Don rage mace-macen mata da jarirai a yayin haihuwa, ya ɗauki ƙarin ma’aikatan lafiya, tare da samar da magunguna da kayan aiki, tare d harkar kyautata kiwon...
      Cikakken bayani na tafe… ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja October 22, 2025 Manyan Labarai Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi October 21, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja October 21, 2025
    Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta bayyana baƙin cikinta game da gobarar tankar mai da ta tashi a ƙaramar hukumar Katcha ta Jihar Neja, inda mutane 38 suka rasa rayukansu. A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta jajanta wa jama’a da gwamnatin Jihar Neja, musamman iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma Gwamna Mohammed Umar Bago. Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya  Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya “Tunaninmu yana tare da iyalan da wannan mummunan lamari ya shafa. Muna godiya ga ma’aikatan agajin gaggawa bisa taimakon da suka bai wa waɗanda abin ya rutsa da su,”...
      Har ma abun da ba kasafai ake gani ba, tattalin arzikin Sin yana cike da karfin tinkarar duk wani hadari da ka iya kunno kai. Ba sabunta kayayyaki kirar kasar da kara musu inganci kadai aka samu ba, har ma abokan cinikin kasar a ketare suna ta kara yawa.   A jiya Litinin ne aka bude cikakken zama na 4 na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 a nan Beijing, inda za a tattauna da kuma ba da shawarwari kan shirin shekaru biyar-biyar na 15 na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin. Kasashen duniya na sa ran cewa, kasar Sin za ta ba da sababbin damammarkin neman samun ci gaba ga duniya, bisa ga...
    Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sanar da shirinsa na ɗaga darajar Kwalejin Jinya ta Nafisatu da ke Kwankwaso zuwa cikakkiyar Jami’ar Kiwon Lafiya albarkacin bikin zagayowar ranar haihuwarsa. Taron na wannan Talatar, 21 ga watan Oktoban 2025, ya gudana ne a garinsa na Kwankwaso da ke Karamar Hukumar Madobi, inda aka yaba da ci gaban da makarantar ta samu tun daga kafuwarta a 2019 zuwa yanzu. Tinubu ya naɗa sabon Minista Alƙaluman wucin-gadi na nuna Paul Biya ya lashe zaɓen Kamaru Kwankwaso ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin ƙara buɗe damammaki ga mata matasa su sami ilimin kiwon lafiya mai zurfi. Ya jaddada cewa makarantar ita ce ta farko a Najeriya da ke karɓar dalibai...
    Sun ce wadanda suka mutu yawancinsu wadanda suka je kwaso man fetur ne a lokacin da tankar ta yi hatsari kafin fashewar.   Shugabannin Direbobin Tankar Mai na Jihar Neja (PTD) da Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas ta Nijeriya (NUPENG) ta kasa, Kwamared Farouk Mohammed Kawo, sun tabbatar wa LEADERSHIP faruwar lamarin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba October 21, 2025 Manyan Labarai NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi  October 21, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu October 21, 2025
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar Cerebral Palsy, wato tsukewar ƙwaƙwalwa, na daga cikin manyan matsalolin lafiyar yara da ke tasowa tun daga haihuwa. Wannan cuta tana faruwa ne sakamakon rauni ko lalacewar wani ɓangare na ƙwaƙwalwa da ke kula da motsi, magana, da daidaiton jiki. A mafi yawan lokuta, cutar tana bayyana ne tun daga ƙuruciya, a wasu lokutan kuma kamar yadda masana kiwon lafiya suka bayyana, cutar na faruwa ne tun kafin a haifi yaro. Ko ta waɗanne irin hanyoyi wannan cuta take kama yaro? NAJERIYA A YAU: Shin Ya Kamata A Saki Shugaban IPOB Nnamdi Kanu? DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A...
    Zakaran kyautar Ballon d’Or ta bana, Ousmane Dembele, ya shiga cikin sahun ’yan wasan ƙungiyar Paris Saint-Germain (PSG) da za ta kece raini da Bayer Leverkusen a gasar Champions League, bayan ya shafe makonni shida a jinya. Dembele, wanda ya samu rauni a cinya yayin da yake wakiltar ƙasar Faransa a farkon watan Satumba, ya shafe makonni yana jinya a cibiyar lafiya ta musamman da ke Qatar, kafin komarwarsa atisaye a makon da ya gabata. Gwamnonin Kano, Katsina da Jigawa sun ƙulla yarjejeniyar bunƙasa wutar lantarki Yadda Morocco ta kafa tarihin ɗaga Kofin Duniya na FIFA U20 Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa AFP ya ruwaito cewa, kociyan PSG, Luis Enrique, zai yi farin ciki da dawowar Dembele, la’akari da yadda...
    Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta samu nasara a karo na biyu a gasar Firimiya ta Nijeriya (NPFL) bayan ta doke abokiyar hamayyarta Kano Pillars da ci 2–1 a wasan da suka buga a yau Lahadi a filin wasa na Sani Abacha, Kofar Mata, Kano. Rabiu Ali, kyaftin ɗin Kano Pillars, ne ya fara jefa ƙwallo a ragar Barau FC a minti na 20 da fara wasa. Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Ibrahim ya farke ƙwallon ga Barau FC a minti na 50, sai kuma Stanley da ya ƙara ta biyu wanda ya tabbatar wa Barau FC nasara a wasan. NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3 Kocin Kano Pillars...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Oyo, ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Lawal Faruƙ da ake zargin ya bankawa tsohuwar masoyiyarsa wuta bayan da dangantakar su ta yi tsami. Majiyar PUNCH Metro ta samu labarin a ranar Alhamis cewa, lamarin ya faru ne a barikin sojoji da ke Ibadan babban birnin jihar. Jami’an tsaro sun kama ’yan bindiga 2, sun ƙone sansaninsu a Kogi Ba mu ji dadin yi wa mahaifinmu afuwa tare da riƙaƙƙun masu laifi ba – Iyalan Herbert Macaulay Wani ƙwararre a fagen yaƙi da ’yan tada ƙayar baya, Zagazola Makama wanda ya bayyana yadda lamarin ya faru a shafinsa na sada zumunta na X, ya bayyana cewa, wanda ake zargin ya yi iƙirarin cewa shi...
    An fara gina magudanan ruwa domin dakile afkuwar ambaliyar ruwa a kananan hukumomin Malam Madori da Kaugama dake jihar Jigawa. Tawagar Injiniyoyin jihar karkashin jagorancin Daraktan kula da ambaliyar ruwa da zaizayar kasa, Injiniya Mukhtar Muhammad Usman sun ziyarci kananan hukumomin domin duba yadda aikin ke gudana. Haka zalika Daraktan da mataimakin sa Injiniya Mahdi Isyaku da sauran ma’aikata ssn ziyarci wurin da ambaliyar ruwa tayi ta’adi a garin malam Madori. A lokacin da tawagar ta fara auna fili da tona magudanun ruwan, daraktan ya ce an fara aikin tona magudanar ruwa mai tsawon kilomita 2 a matsayin wani ɓangare na aikin karkatar da ruwan da ya lalata wurare zuwa sabon wurin da aka tsara. Yana mai cewar,...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yan Nijeriya Na Dab Da Fita Daga Halin Kuncin Talauci – Shettima  October 17, 2025 Labarai Yadda ‘Yan Bindiga Ke Zafafa Hare-hare A Jihohin Arewa Maso Yamma October 17, 2025 Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025
    Baya ga yi masu afuwa, Shuagaba Tinubu, ya kuma karama su da lambar yabo ta kasa. ‘Yan Ogonin su tara, sun dai fuskanci shari’a ne, bisa zarginsu da kitsa kisan sarakunan Ogoni Albert Badey, Edward Kobani, Theophilus Orage da kuma Samuel Orage. Kotu ta tuhumi ‘yan Ogonin su tara, ta kuma yanke masu hukuncin rataya a ranar 10 ga watan Numambar 1995. Hukucin na Kotun, a wancan lokacin, ya haifar da hatsaniya tare da yin suka daga bangaren manyan shugabannin kasasshen duniya, daidaikun mutane da sauran kungiyoyi, musaman duba da cewa, an yanke masu hukuncin ne, a lokacin da ‘yan kasar ke nuna tsanar mulkin soji, biyo bayan soke zaben shugaban kasa, da ake da yakinin an yi sahihin zabe...