Aminiya:
2025-07-03@01:55:35 GMT

Ambaliya: Zulum ya bada umarnin tallafa wa mutanen Damboa da Askira-Uba

Published: 2nd, July 2025 GMT

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jajanta wa mutanen da ambaliya da guguwa suka shafa a ƙananan hukumomin Damboa da Askira-Uba.

A cikin kwanakin da suka gabata, ruwan sama mai yawa ya haifar da ambaliya a ƙauyukan Wovi da Gumsuri na Damboa.

Majalisar Dokokin Filato ta zaɓi sabon shugaba David Mark ya fice daga PDP, ya shiga haɗaka don ƙalubalantar Tinubu

Wannan ambaliya ta yi sanadin mutuwar mata biyu, kuma ta lalata gidaje da raba mutane da muhallansu.

A wani ɓangare kuma, guguwa mai ƙarfi ta afka wa garin Rumirgo da ke Askira-Uba, inda ta lalata gidaje da dukiyoyin jama’a.

Dauda Iliya, mai bayar da shawara na musamman ga Gwamna Zulum kan harkokin yaɗa labarai, ya fitar da sanarwa, inda ya ce abin da ya faru abin tausayi ne da baƙin ciki.

Gwamna Zulum ya ce: “Na yi baƙi ciki da ambaliyar da ta faru a Wovi wadda ta yi sanadin mutuwar mata biyu, da kuma lalata gidaje a Gumsuri.

“Haka kuma abin ya yi muni a Rumirgo inda guguwa ta lalata gidaje. Muna addu’a Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu, ya kuma mayar wa waɗanda suka rasa dukiyarsu da mafificin alheri.”

Gwamnan ya umarci Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), da ta tallafa wa waɗanda lamarin ya shafa.

Ya kuma tabbatar wa mutanen yankin cewa gwamnati za ta taimaka musu.

Zulum ya ce: “Na riga na umarci hukumar SEMA da ta kai kayan agaji zuwa Gumsuri da Wovi cikin gaggawa. Haka kuma, an riga an tura kayan agaji zuwa Rumirgo.”

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa tana ƙoƙari wajen daƙile irin wannan iftila’i a gaba, tare da yin kira ga jama’a da su riƙa kula da bin dokoki don kaucewa irin wannan yanayi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ambaliyar ruwa Guguwa

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 10 a Borno

Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta ce dakarun tsaro na rundunar “Operation Hadin kai” sun kashe mayaƙan Boko Haram 10 yayin wata arangama a yankin Rann zuwa Gamboru Ngala da ke Jihar Borno.

Daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaron, Manjo Janar Markus Kangye ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Gwamnan Bauchi zai ƙirƙiro sabbin masarautu Sai bayan Magariba za a yi wa Dantata jana’iza a Madina

Manjo Janar Markus Kangye ya ce aikin kawar da ‘yan ta’addan da aka aiwatar ranar Litinin ya faru ne bayan rundunar ta lashi takobin kawar da sauran ‘yan Boko Haram/ISWAP da ke ɓuya a yankin Tafkin Chadi.

“Arangamar ta faru ne a lokacin wani aiki na haɗaka wanda aka shirya kuma aka aiwatar cikin dabara domin kawar da sauran ‘yan ta’addan Boko Haram/ISAWP da ke aika-aika a garuruwan da ke kan iyaka,” in ji Janar Kangye.

“Dakaraun da suka yi aiki bisa bayanan sirri sun danna cikin maɓuyar mayaƙan tsakanin Rann da Gamboru, inda suka yi ba-ta-kashi sannan suka kashe ‘yan ta’adda 10,” in ji sanarwar.

Ya ƙara da cewa bayan arangamar an samu makamai da yawa daga wurin, ciki har da bindigogin harbo jiragen sama.

Aikin wani ɓangare ne na dabarun karɓe iko da kudancin Tafkin Chadi da kuma hana zirga-zirgar ‘yan Boko Haram ta kan iyaka, a cewarsa.

“Ana nazari kan makaman da aka ƙwace yayin da ake ƙoƙarin gano waɗanda suka tsere da kuma sauran maɓoyar ’yan ta’adda a yankin,” in ji sanarwar.

Ya ƙara da cewa dakarun sojin Nijeriya, da haɗin gwiwar rundunar haɗin gwiwa ta MNJTF da kuma sauran jami’an tsaro sun zafafa ayyukansu a yankin Tafkin Chadi da sauran ɓangarori na arewacin Borno domin kakkaɓe sauran ‘yan Boko Haram a yankin

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwalejin Koyar Da Aikin Jinya Ta Jigawa Za Ta Fara Bada Shaidar Babbar Difiloma
  • Tinubu Ya Ƙaddamar Da Cibiyar Fasahar Da Aka Lalata Lokacin Zanga-Zanga A Kano
  • Amurka Ta Dakatar Da Tura Makamai Zuwa Kasar Ukraine Saboda Kada A Sami Karancinsu A Gida
  • Rikicin Gonar Gado Ya Yi Ajalin Mutum Ɗaya, An Ƙone Gidaje A Filato
  • Wakilan Kasashen Duniya Da Kungiyoyin Sun Je Ta’aziyya Mutanen Da Suka Yi Shahada A Yakin Iran Da H.K.Isra’ila
  • Ba Gaskiya Ba Ne: Ɓarayi Ba Su Sace Ɗan Uwan Gwamnan Zamfara Ba
  • Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 10 a Borno
  • NAJERIYA A YAU: Halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata guda bayan ambaliya
  • NAJERIYA A YAU: Halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata 2 bayan ambaliya