Yunwa ta kashe ƙananan yara 66 a Gaza
Published: 28th, June 2025 GMT
Hukumomi sun tabbatar da mutuwar ƙananan yara 66 a sakamakon yunwa a yankin Gaza.
Yaran sun mutu a yayin da sojojin Isra’ila ke ci gaba da hana shigar da madarar yara da sauran kayan abinci da sauran kayan jinƙai da ake buƙata domin ceto rayuka zuwa Gaza.
Mutuwar yaran ta zo ne a daidai lokacin da hukumomin Gaza suka sanar cewa sojojin Isra’ila sun kashe wasu Palasdinawa 34.
Jami’an lafiya a Asibitin Al-Shifa da ke Gaza sun bayyana cewa an kawo gawarwakin wasu mutum 12 da sojojin Isra’ila suka kashe a filin wasa da Palasdinawa ke zaman mafaka, da wasu takwas da aka kashe a wani gida.
‘An kashe ’ya’yana da mijina da ’yan uwana a hanyar ɗaurin auren ɗana’ Yadda aka yi jana’izar kwamandojin Iran da Isra’ila ta kasheOfishin yaɗa labarai na hukumomin Gaza ya bayyana cewa ana matuƙar buƙatar kayan abincin domin ceto rayuwar musamman ƙananan yara da gajiyayyu da marasa lafiya.
Sanarwar Hukumar ta ce, “laifin yaƙi ne da tauye haƙƙin ɗan Adam ne abin da Isra’ila ke yi na amfani da salon hana faren hula samun abinci a matsayin makami.
“Wannan ya saɓa da yarjejeniyar Geneva da kuma dokokin ayyukan jinƙai na duniya.”
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Harin Ƴan Bindiga Ya Yi Sanadin Kashe Ɗansanda Da Wasu Mutane 4 A Kwara
Ƴan bindiga sun kashe mutane biyar, ciki har da wani Ɗansanda, a sabon harin da suka kai garin Babanla a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, kwanaki ƙalilan bayan kisan wasu matafiya uku da garkuwa da wasu biyu a yankin.
Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi, ta ce maharan sun kai ɗaruruwa akan babura ne suka farmaki garin, kuma suka kai hari ofishin Ƴansanda na yankin, sannan suka yi ɓarna a kasuwar garin. An kashe Kofural Adejumo Wasiu tare da wasu fararen hula huɗu.
NDLEA Ta Kama Fasto Bisa Laifin Safarar Miyagun Kwayoyi A Legas Jirgin Shugaban Ƙasa Ya Laƙume Naira Biliyan 26.38 Cikin Wata 18 Ƙarƙashin TinubuTa bayyana cewa haɗin gwuiwar Ƴansanda, da Sojoji, da Jami’an sa-kai da mafarauta ya fatattaki maharan tare da dawo da zaman lafiya, inda yanzu aka fara sumame don kamo su. A ranar Lahadi, kwamishinan Ƴansanda Adekimi Ojo da Daraktan DSS na jihar sun ziyarci Babanla don tantance halin tsaro, tare da ganawa da Sarkin garin, Oba Yusuf Aliyu Alabi Arojojoye II.
Kwamishinan ya bayar da umarnin ci gaba da sintiri da tattara bayanan sirri tare da tura ƙwararrun jami’an bin sawu, yayin da DSS ta yi alƙawarin bayar da goyon baya da bayanan sirri domin kama duk masu hannu a harin. An kuma roƙi jama’a su kwantar da hankula, su kasance masu lura, tare da bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp