Hare-haren Isra’ila sun kashe mana mutum 935 a yaƙin kwana 12 — Iran
Published: 30th, June 2025 GMT
Hukumomin Iran sun bayyana cewa aƙalla mutum 935 ne suka rasa rayukansu a hare-haren Isra’ila yayin yaƙin kwanaki 12 da ya gudana tsakaninsu da ƙasar.
Cikin waɗanda suka mutu sun haɗa har da mata 132 da yara 38, kamar yadda mai magana da yawun Hukumar Shari’a, Asghar Jahangir, ya bayyana a wata sanarwa a ranar Litinin, wacce kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito.
A baya, Ma’aikatar Lafiya ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren Isra’ila ya kai 606, sannan mutane 5,332 da suka jikkata.
Jahangir ya ce hare-haren Isra’ila kan gidan yari na Evin da ke Arewa maso Yammacin Tehran sun yi sanadin mutuwar mutum 79, ciki har da fursunoni da ma’aikatan gidan yari, da mazauna yankin.
Ya kara da cewa gidan yarin Evin ya zama ba zai iya aiki ba, kuma an kwashe fursunonin, yana mai kiran harin a matsayin “tauye hakkin ɗan’adam da kuma karya dokokin kasa da kasa.”
A ranar 13 ga watan Yunin nan ne yaƙi ya tsakanin Isra’ila da Iran ya barke, lokacin da Tel Aviv ta ƙaddamar da hare-haren sama kan sansanonin soja, nukiliya, da fararen hula na Iran.
Amurka ma ta kai hari kan cibiyoyin nukiliya na Fordow, Natanz, da Isfahan na Iran, wanda ya ƙara tsananta rikicin.
Tehran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa kan Isra’ila, inda suka kashe aƙalla mutane 29 tare da jikkata fiye da 3,400, kamar yadda Jami’ar Hebrew ta Jerusalem ta bayyana.
Kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa yaƙin ya tsaya sakamakon wata yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta dauki nauyi, wacce ta fara aiki a ranar 24 ga Yuni.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Iran Isra ila yaƙi hare haren Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 5 a Borno
Rundunar sojin Najeriya, ta bayyana cewa dakarunta sun kashe ’yan ta’adda biyar a wani samame da suka kai yankin Magumeri da Gajiram, a Jihar Borno.
Kakakin rundunar Operation Haɗin Kai, Kanar Sani Uba, ya ce dakarun sun yi arangama da wasu ’yan ta’adda 24 da ke tafe a ƙafa a ranar Juma’a.
Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da KatsinaA cewar sanarwar da ya fitar, sojojin sun yi nasarar kashe biyar daga cikinsu tare da ƙwato kuɗi Naira miliyan biyar.
“An hangi ’yan ta’addan suna ƙone gidaje da kuma kai wa mutane hari, sai dakarun suka fara bin su, inda suka tsere zuwa ƙauyen Damjiyakiri,” in ji Kanar Sani.
Ya ƙara da cewa bayan awanni huɗu ana bin su, sojoji suka sake kai musu farmaki, inda suka kashe biyar daga cikinsu, sauran 19 kuma suka tsere da raunuka.
Abubuwan da aka ƙwato daga hannunsu, sun haɗa da bindiga ƙirar AK-47, jakar harsashi gyda biyar, waya guda ɗaya da wuƙa.