Aminiya:
2025-10-13@15:50:04 GMT

‘Mutum 600 da suka bace a ambaliyar Mokwa sun mutu’

Published: 3rd, July 2025 GMT

’Yan Majalisar Wakilai daga jihohin Neja da Kwara sun shaida wa majalisar cewa mutum 600 da suka bace a ambaliyar garin Mokwa kuma har yanzu ba a gan su ba, za a dauka su ma sun mutu.

Dan majalisa Joshua Audu Gana (Neja) da Saba Ahmed Umaru (Kwara) ne suka bayyana hakan a yayin gabatar da wani kudurin gaggawa a zauren majalisar a ranar Laraba.

Sun ce mummunar ambaliyar da aka yi a ranakun 28 da 29 ga watan Mayun da ya gabata sanadin mamakon ruwan saman da aka tafka ta yi barna sosai a karamar hukumar ta Mokwa a jihar Neja, sannan ta tsallaka har karamar hukumar Edu ta jihar Kwara.

Lakurawa sun kashe mutum 15 a harin ramuwar gayya a Sakkwato NAJERIYA A YAU: Ɓoyayyun Ƙalubalen Da Sabuwar Haɗakar ADC Za Ta Iya Fuskanta

A cewar ’yan majalisar, yayin da aka tabbatar da mutuwar mutum 500, su kuma ragowar sama da 600 da aka ce sun bace kuma har yanzu babu labarin su, su ma za a kirga su a cikin matattun, la’akari da munin ambaliyar.

’Yan majalisar sun kuma ce ambaliyar ta lalata gidaje sama da 4,000, ta jikkata sama da mutum 200, sannan ta shanye gonaki da gine-gine, ta kuma raba dubban mutane da muhallansu.

Daga nan ne majalisar ta yi shiru na minti daya don girmama wadanda ambaliyar ta shafa, sannan ta yaba wa Shugaban Kasa Bola Tinubu saboda amincewa a bayar da tallafin Naira biliyan biyu ga wadanda lamarin ya shafa.

Majalisar, bayan tafka muhawara, ta kuma amince da kudurin sannan ta ba da umarnin inganta matakan dakile ambaliya a yankin da ma sauran yankunan da ke cikin barazanar ambaliyar, cikin gaggawa.

Kazalika, majalisar ta kuma umarci Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da ta samar da kayayyakin agaji da na tsafta ga al’ummomin da lamarin ya shafa domin kaucewa sake barkewar cututtuka.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ambaliya Mokwa

এছাড়াও পড়ুন:

Maryam Sanda na cikin waɗanda Tinubu ya yi wa afuwa

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa Maryam Sanda afuwa, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ɗan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Haliru Bello.

Maryam,’ mai shekara 37, ta shafe shekaru shida da watanni takwas a gidan yarin Suleja kafin yi mata afuwa.

Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro

Rahotanni sun nuna cewar an yi mata afuwar ne bayan yin nadama da aikata kyakkyawan halaye.

Iyayen Maryam sun roƙi gwamnati da ta sake ta saboda ’ya’yanta biyu da ta ke da alhakin kula da su, tare da alƙawarin sauya halayenta.

Shugaba Tinubu, ya kuma yi wa wasu mutane afuwa da suka haɗa da Manjo Janar Mamman Vatsa, Ken Saro-Wiwa, da kuma Sir Herbert Macaulay.

Gaba ɗaya mutane 175 ne shugaban ya yi musu afuwa, ciki har da masu manyan laifuka, tsoffin fursunoni, da waɗanda suka yi kyakkyawan tuba.

Wannan shi ne karon farko da Shugaba Tinubu ya yi amfani da ikon yafe laifi don tausaya wa waɗanda suka aikata laifuka tun bayan hawansa mulki.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rikicin kabilanci: Mutane 2 sun mutu, wasu 7 sun jikkata a Jigawa
  • Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya
  • Soja ya kashe matarsa, ya hallaka kansa a Jihar Neja
  • Maryam Sanda na cikin waɗanda Tinubu ya yi wa afuwa
  • ’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna
  • Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 9, Sun Ƙwato Naira Miliyan 5 A Borno
  • Sojoji Da ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Shida Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Taraba
  • Sibil Difens ta cafke mutum 3 kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi a Kano
  • Majalisa Na Duba Yiwuwar Amincewa Da Gudanar Da Zaɓen 2027 A Rana Ɗaya
  • Sojoji sun mutu yayin da Boko Haram ta kai hari sansanin soji a Borno