Iran Ta Ce: Ba Za Ta Koma Zaman Tattaunawa Da Amurka Ba Sai A Kan Wasu Sharudda
Published: 30th, June 2025 GMT
Dakatar da ayyukan wuce gona da iri kan Iran wani sharadi ne na ci gaba da tattaunawar makamashin nukiliya
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin siyasa Majid Takht-e Ravanchi ya bayyana cewa: Sharadin ci gaba da gudanar da zaman shawarwarin makamashin nukiliyar Iran shi ne dakatar da duk wani matakin wuce gona da iri kan Iran, kuma har yanzu Amurka ba ta dauki wani mataki ba kan wannan batu.
A wata hira da tashar BBC game da batun tattaunawar makamashin nukiliyar Iran da Amurka: Takht-e Ravanchi ya ce: “Sun ji daga Amurka cewa a shirye take ta ci gaba da tattaunawar, amma har yanzu ba a tsayar da ranar ba, kuma Iran ba ta amince da tsarin shawarwarin ba.”
Ya kara da cewa: “A halin yanzu Iran tana neman amsoshi dangane da ko za ta sake fuskantar sabbin matakan wuce gona da iri yayin da aka fara tattaunawar.” Har yanzu dai Amurka ba ta bayyana matsaya ba kan wannan batu.
Da aka tambaye shi game da yiwuwar cimma yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu, ciki har da dage takunkumin da aka kakabawa Iran, a madadin Iran ta dakatar da inganta sinadarin Uranium, Takht-e Ravanchi ya ce: “Me zai sa su amince da wannan shawara? Inganta sinadarin Uranium zuwa kashi 60 cikin 100 ana amfani da shi ne domin zaman lafiya. Tabbas za a iya tattaunawa kan matakinsa, amma maganarsu ta cewa dole ne Iran ta daina inganta Uranium gaba daya, in ba haka ba za ta fuskanci hari, wannan maganar hankali me? Wannan dokar daji ce.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Yanzu-Yanzu: ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki Na Tsawon Mako Biyu
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Trump Da Al-Sisi Za Su Jagoranci Taron Zaman Lafiya Dawwamammiya Ta Gaza A Masar October 12, 2025
Manyan Labarai Yaƙi Da Boko Haram: An Kashe Sojoji 2,700 A Shekara 12 – Janar Irabor October 12, 2025
Labarai Macron Na Ci Gaba Da Shan Matsin Lamba Daga ‘Yan Adawa Da Tsofaffin Na Hannun Damansa October 12, 2025