Rikicin Gonar Gado Ya Yi Ajalin Mutum Ɗaya, An Ƙone Gidaje A Filato
Published: 2nd, July 2025 GMT
Wani rikicin gado a kan fili da ya ɓarke tsakanin wasu ahali biyu a ƙauyen Kopkopshe na gundumar Tunkus da ke Ƙaramar Hukumar Mikang ta Jihar Filato, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya tare da ƙone gidaje da dama.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, bayan aukuwar rashin jituwa tsakanin ɓangarorin biyu wanda sun shafe fiye da shekaru biyu ba sa ga maciji a kan asalin mai haƙƙin gadon gonar daga iyayensu.
Hadimin Shugaban Ƙaramar Hukumar Mikang kan harkokin yaɗa labarai, Nkat Joseph Lakai, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce shugaban ya ziyarci al’ummar kan abin ya faru tare da yin Allah-wadai wanda misalta da abin kunya.
A cewarsa hakan cikas ne ga ƙoƙarin gwamnati kan faɗi tashin da take na kare rayuka da dukiyar al’umma daga hare-haren ‘yan ta’adda da ma daƙile aikata munanan laifuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ebonyi, ta kama wani mutum mai suna Chukwuma Onwe, ɗan Ƙaramar Hukumar Izzi, bisa zargin sayar da ɗan da aka haifa masa kwanaki biyar kan Naira miliyan 1.5.
An gano cewa Onwe ya sayar wa wata mata mai suna Chinyere Ugochukwu jaririn, wacce ake zargin tana cikin ƙungiyar safarar yara zuwa ƙasashen waje.
ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan AbujaDukkaninsu suna hannun ’yan sanda.
Wata majiyar ’yan sanda ta bayyana cewa matar Onwe, mai suna Philomena Iroko, ce ta fallasa shi bayan ta samu labari daga maƙwabta cewa mijinta ya sayar da jaririn da suka haifa.
Da ta tabbatar da hakan, sai ta garzaya ta kai rahoto ofishin ’yan sanda, inda aka kama Onwe ba tare da ɓata lokaci ba.
Kakakin rundunar jihar Ebonyi, SP Joshua Ukandu, ya tabbatar da cewa an ceto jaririn daga hannun wacce ta saya shi.
Ya ce an kama Onwe da Chinyere Ugochukwu a ranar Juma’a a unguwar Azugwu, Ƙaramar Hukumar Abakaliki, kuma suna tsare a hannun ’yan sanda domin ci gaba da bincike.
Matar Onwe, Philomena, ta ce ta yi mamaki matuƙa cewa mijinta ya sayar da jaririn nasu.
Ta bayyana cewa tun bayan haihuwarta, Onwe, ya ce zai kai jaririn wajen ’yar uwarsa domin ta sa masa albarka, sai dai daga baya aka gano cewa ya sayar da shi.
Ta ce, “Yaronmu bai wuce kwanaki biyar da haihuwa ba, amma mijina ya sayar da shi.
“Ban taɓa tunanin zai yi haka ba. Ina roƙon jama’a da masu hannu da shuni su taimaka min a wannan hali da na tsinci kaina.”