2025-08-06@03:41:43 GMT
إجمالي نتائج البحث: 845
«mafi karancin albashi na Naira 70 000 ga»:
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sojojin Yemen sun kaddamar da hari kan filin jirgin saman Lod da ke birnin Jaffa a haramtacciyar kasar Isra’ila da makami mai linzami Dakarun sojin Yemen sun sanar a yau cewa: Sun kai hari kan filin jirgin saman Lod da ke birnin Jaffa, domin mayar da martani kan laifukan kisan kiyashi da kakaba masifar yunwa da makiya yahudawan sahyoniya suka aikata a kan ‘yan’uwansu a zirin Gaza, da kuma mayar da martani kan gungun yahudawan sahayoniyya da suke kutsawa cikin masallacin Al-Aqsa tare da wulakanta farfajiyar sa mai alfarma. A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta bayyana cewa; Rundunar ta kai wani harin soji mai inganci a kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da...
Gwamnatin kasar Burtaniya ta bayyana cewa zata fara amfani da wata yarjeniya da ta cimma da kasar Faransa kan maida dukkan yan gudun hijira ko bakin hauren da suke shigo kasar ta kwale-kwale zuwa kasar kasar ta Faransa. Daga yau Talata. Shafin labarai na yanar gizo Arab News ya nakalto cewa gwamnatocin biyu sun amince kan cewa Burtaniya zata maida dukkan wadanda suka iso Burtaniya ta amfani da kananan kwale kwale ta maida su Faransa, a inda ita kuma faransa zata mikawa kasar Burtaniya masu nrman mafaka wadanda suke da iyali a kasar Burtaniya dai dai adadin da ta mayar daga Burtaniya. Firai ministan kasar Burtanita Keir Starmer da kuma shugaban kasar Faransa Emmanuel macron sun amince haka a cikin...
Wata yarinya ’yar shekara 17, Nafisa Abdullah, daga Jihar Yobe, ta lashe Babbar Gasar Harshen Turanci ta Duniya ta ‘TeenEagle’ ta shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Landan, fadar gwamnatin ƙasar Birtaniya. Nafisa ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 ce baya da ta fafata ne da sama da mahalarta gasar 20,000 daga ƙasashe kusan 69 na duniya, inda ta zama ta ɗaya a Gasar ‘UK Global Finals’, sakamakon fintinkau da ta yi wa takwarorinta na ƙasashe daban-daban da ke jin harshen Ingilishi a duniya. Wannan nasara ta lashe wannan babbar gasa da Nafisa ta samu ya haifar da alfahari a faɗin Najeriya, musamman a mahaifarta, Jihar Yobe. Nafisa ta wakilci Najeriya ne daga Kwalejin Tulip International College (NTIC), Jihar Yobe....

Wa’adin Da Shugaban Amurka Ya Gindaya Na Kawo Karshen Yaki A Ukraine Ya Karato Ba Tare Da Alamun Karewarsa Ba
Shugaban Amurka ya aike da jakada zuwa Rasha tare da yin barazanar sanyawa Moscow takunkumi Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Manzonsa na musamman Steve Witkoff zai ziyarci kasar Rasha a mako mai zuwa, yayin da wa’adin da ya sanyawa Moscow na kawo karshen yakin da take yi da Ukraine ke gabatowa. A halin da ake ciki kuma, ana ci gaba da gwabza yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, inda Moscow ta sanar da lalata jiragen Ukraine guda 18. Yakin da ake yi a Ukraine na kara kamari zuwa ci gaba mai hatsari a daidai lokacin da wa’adin da shugaban Amurka Donald Trump ya gindaya wa Rasha ke gabatowa, da kuma halayensa na tunzura jama’a,...
Gwamnatin Kano ta bayyana shirin mayar da tsohon gidan yarin nan na Kurmawa, wanda aka gina fiye da shekara 100 da suka gabata, zuwa gidan adana abubuwan tarihi. Gidan yarin Kurmawa mai ɗaukar fursunoni 690 kacal, wanda aka gina a shekarar 1910 tun a zamanin Turawan mulkin mallaka a kusa da fadar mai martaba Sarkin Kano, yana da tarihin shekaru 115. An sace jariri sabuwar haihuwa a asibitin Ekiti Za a samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na kwanaki uku a faɗin Nijeriya — NiMet Mai ba Gwamnan Kano shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ibrahim Adam, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi. Hadimin gwamnan ya ce an yanke shawarar sauya ma’anar wurin,...
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da ware Naira Biliyan 20 a karin kasafin kudin da aka yi domin ci gaba da gyaran gine-ginen makarantu a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Lawal Olohungbebe, ya fitar, ya ce wannan sabon tsarin zai kara karfi wajen cigaban gyaran makarantun gwamnati. Sanarwar ta bayyana cewa tuni aka fara aikin, inda aka zayyana yadda gine-ginen za su kasance, kuma sauran abubuwa za su biyo baya da zaran an amince da karin kasafin kudin. Sanarwar ta kara da cewa wannan ba wani aiki ne mai zaman kansa ba, illa wata sabuwar babbar gudummawa daga gwamnati don kara habaka aikin da take yi tun da farko. Ta kara...
Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya tuhumi sabon Sarkin Gudi, Alhaji Ismaila Ahmed Gadaka da ya jagoranci zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban al’ummar masarautar sa, jiha da kasa baki daya. Gwamna Buni ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin yayin gabatar da takardar nadin sarauta ga basaraken a hukumance a majalisar masarautar Gudi. Gina Tituna A Karkara Yana Bunkasa Tattalin Arziki – Gwamna Sule Wasu Kungiyoyi Sun Yi Kira Ga Dan Majalisa Aminu Sani Jaji Ya Fito Takarar Gwamnan Zamfara Kwamishinan ilimi mai zurfi, kimiyya da fasaha na jihar, Farfesa Muhammad Bello Kawuwa ne ya mika takardar nadin ga sabon sarkin a madadin gwamnan. Da yake isar da sakon Gwamnan, Farfesa Kawuwa ya bayyana muhimmiyar...
Jam Kamal Khan ministan kasuwanci na kasar Pakisatan ya bayyana cewa ziyarar da shugaba Pezeshkiyan na kasar Iran ya kawo Islam’abad yayi armashi, kuma ya bude wasu hanyoyi da dama harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu. Khan ya kara da cewa a yau al-ummar musulmi suna alfakhari da JMI sabado nasarar da ta samu kan HKI, kuma suna ganon hakan a matsayin abin girmamawa ga kasar da kuma sauran kasashen musulmi. Kamfanin dillancin labaran Parstoday ta nakalto daga IRNA wanda yake cewa ministan kasuwanci na kasar Pakisatan da kuma ministan ma’adinai masana’antu da kuma kasuwanci na kasashen biyu sun gana a rana ta biyu da ziyarar shugaban zuwa Islamabad. A tattaunawa ministocin Khan da kuma Mohammad Atabak kasashen biyu sun amince...
Shima da yake gabatar da nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC magoya bayan Aminu Sani Jaji a Zamfara, Honorabul Lawalli Attahiru Dogon Kade, ya bayyana dan majalisar a matsayin Mutum jajirtacce mai hannun kyauta da taimakon jama’a, inda ya ce mutum irin Aminu Sani Jaji ake nema a matsayin Gwamnan Zamfara, domin shi kadai ne zai kai jihar ga tudun mun tsira. Lokacin da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron, Honorabul Aminu Sani Jaji, ya gode wa al’ummar Zamfara bisa nuna kauna da yarda da suka yi mishi, inda ya sha alwashin yi musu sakayya akan haka. “Dukkanin abubuwan da muke yi muna yin su ne domin al’umma, kuma jama’ar nan ita taga dacewa...
Tawagar Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta kai ziyarar ta’aziyya ga sabon Sarkin Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a fadarsa. Ziyarar ta biyo bayan rasuwar marigayi Sarkin Gusau, Dakta Ibrahim Bello, wanda aka yi ta murna da shi a bisa kyakkyawan jagoranci da kuma gudunmawar ci gaban masarautu da jihar Zamfara. Hajiya Larai Musa Lawal, ta mika sakon ta’aziyyar uwargidan shugaban kasar ga iyalan gidan sarautar tare da addu’ar Allah ya jikansa da rahama. Ta kuma mika sakon taya murna ga sabon sarkin, tare da yi masa fatan Allah ya kara masa lafiya mai cike da hikima da zaman lafiya da hadin kai. A nasa jawabi, sabon Sarkin Katsinar Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim...
Gwamnatin Najeriya ta ce tana sa ran samun kimanin Naira biliyan 300 a duk shekara daga noman dabino a ƙasar. Ta ce tana fatan samun wannan kuɗaɗen shiga ne daga rabon irin dabino guda miliyan biyar da ta samar ga manoma a wannan shekara ta 2025. Darakta-Janar na Hukumar Yaƙi da Kwararowar Hamada (NAGGW), Alhaji Saleh Abubakar, ya ce, “Kowane iri ƙwaya ɗaya na iya samar da miliyan 100 na dabino, wanda kuɗinsa ya kai Naira miliyan ɗaya. Ga shi kuma sau biyu dabino ke yin ’ya’ya a shekara. “Muna hasashen manoma za su samar da Naira biliyan 300, wanda tabbas zai bunƙasa tattalin arzikin Najeriya,” in ji shi. Ya ƙara da cewa hukumar za ta raba irin dabino miliyan...

Iran Ta Jaddada Cewa: Karfin Makamai Masu Linzami Da Jiragen Sama Marasa Matuka Ciki Suna Nan Cikin Shiri
Babban kwamandan sojojin Iran ya jaddada cewa; Ƙarfin makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa ciki suna nan kuma a shirye suke don aiki Babban kwamandan sojojin kasar Iran, Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa: Karfin makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki na sojojin gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na ci gaba da aiki gadan-gadan, kuma a shirye suke su gudanar da ayyuka, yana mai cewa: A lokacin yaki na baya-bayan nan suna ci gaba da kai hare-hare har zuwa lokacin da aka gabata da shirin tsagaita bude wuta kan makiya. A wata ganawa da ya yi da kwamandoji da jami’an rundunar sojojin kasa, Manjo Janar Hatami ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya makiya ce...
Rahotonni sun bayyana cewa: Har yanzu gwamnatin mamayar Isra’ila ta ki bari an gano kashi 88% na irin laifukan da ta aikata a yakin Gaza ba Jaridar The Guardian ta Birtaniya ta bayyana cewa: Hukumomin mamayar Isra’ila sun boye kusan kashi 88% na binciken laifukan yaki ko cin zarafin da sojojin mamayar Isra’ila suka aikata a kan Falasdinawa a zirin Gaza ba, ba tare da gabatar da tuhumce-tuhumce ko cimma matsaya mai kyau ba tun farkon fara kai hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza a watan Oktoban shekara ta 2023. Rahoton ya nakalto Action on Armed Violence yana cewa: gwamnatin mamayar Isra’ila na neman dauke hankalin duniya kan rashin hukunta ta ta hanyar gujewa daukar alhakin manyan laifukan...
Gwamnatin jihar Borno na shirin sake tsugunar da ‘yan gudun hijira kusan 5,000 daga al’ummomin Bama su biyar kafin damina ta kare. Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana haka a wata ziyarar ban girma da ya kai wa Shehun Bama, Dakta Umar Kyari Umar El-Kanemi a ranar Juma’a. Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci A Kwantar Da Hankali Kan Dakatar Da Gidan Rediyon Badeggi FM Gwamnatin Tarayya Za Ta Aiwatar da Shirin Daƙile Sulalewar Kuɗaɗen Haraji Al’ummomin da aka kudiri niyyar sake tsugunar da su sun hada da Goniri, Bula Kuriye, Mayanti, Abbaram da Darajamal. Zulum ya ce ana kafa matsugunan tanti na wucin gadi guda 1,000 a kowace al’umma, inda tuni aka kammala wacce ke Darajamal. “Mun himmatu wajen mayar...
Wani mutum ya rasu, yayin da wasu biyu suka jikkata sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin mazauna ƙauyen Kuchibiyi da jami’an ’yan sanda a Ƙaramar Hukumar Bwari da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja. Wani mazaunin ƙauyen, Samuel Dangana, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa rikicin ya samo asali ne yayin da wasu da ake zargin masu ƙwacen fili ne suka zo ƙauyen tare da ‘yan sanda daga ofishin Byazhin, suna ƙoƙarin ƙwace wani fili a ƙauyen. Zulum zai mayar da ’yan gudun hijira 5,000 Bama Yadda binciken zargin tallafa wa Boko Haram ke tafiyar hawainiya a Majalisa Dangana, ya ce lokacin da mazauna ƙauyen suka gan su, sai suka taru suka toshe hanya don hana su zuwa wajen filin....
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnatinsa na shirin mayar da mutum 5,000 gida daga sansanin ‘yan gudun hijira kafin wucewar damina domin su samu damar yin noma. Mutanen za su fito ne daga garuruwan Goniri, Bula Kuriye, Mayanti, Abbaram, da Darajamal. Ma’aikatan jinya sun dakatar da yajin aiki a faɗin Najeriya Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja Gwamnan, ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai wa Mai Martaba Shehun Bama, Dakta Umar ibn Kyari Umar El-Kanemi, ziyara a fadarsa da ke Bama. Ya ce an riga an kammala gina matsuguni 1,000 a Darajamal, sannan kuma aikin gina wasu a sauran garuruwan hudu. “Mun ƙudiri aniyar dawo da ‘yan gudun hijira gida. A Mayanti,...
A’isha ƴar shekara uku da suke zaune a ƙarƙashin inuwar bishiyar ɗogoyaro a wani ƙauye mai nisa a yankin Arewa maso Gabas (sansanin gudun hijira). Babu takalmi a ƙafarta, ta yi shiru, saboda radaɗi da take ji. ƙafafuwanta sirara sun yi rauni, cikinta ya dan kumbura saboda yunwa, idanunta sun fito tana cikin halin da bai kamata a ce mai shekaru irinta na ciki ba. Aisha Abdullahi ba ta iya yin kuka ba, domin babu ƙarfin halin yin hakan Mahaifiyarta, Maryam Abdullahi, tana girgiza ta a hankali a cinyarta, ta hada man gero mai ruwa da dakakken ganye a cikin wani ƙaramar roba. Abincin da suke ci a cikin kwana biyu. Ta shaida wa LEAɗERSHIP Weekend cewa, “wani lokaci ta...
Dakarun sojin Yemen sun kai hari kan filin jirgin Lod na Jaffa da makami mai linzami Dakarun sojin Yemen sun sanar da aiwatar da wani zazzafan harin soji kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye. Dakarun kasar ta Yemen sun yi karin haske a cikin wata sanarwa da suka fitar a yammacin yau cewa: Dakarun sojin Yemen masu kula da harkar makamai masu linzami sun kai wani zazzafar harin soji kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye da makami mai linzami na “Palestine 2”. Sanarwar ta tabbatar da cewa: Harin ya samu nasarar kai wa yadda aka saita shi, wanda ya sa sama da makiyaya yahudawan sahayoniyya miliyan hudu tserewa...
Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya ta Najeriya (NANNM), ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da ta fara a faɗin ƙasar nan. Ƙungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata takarda da shugabanta ƙasa, Haruna Mamman, da sakatarenta, T.A. Shettima, suka sanya wa hannu. Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja Jami’ar Umaru Yar’adua ta kori ɗalibai 57 kan satar jarabawa Sun fara yajin aikin ya fara ne a ranar Laraba tare da niyyar shafe kwanaki bakwai suna yin sa. Ma’aikatan jinyar sun shiga yajin aikin ne saboda ƙarancin albashi, ƙarancin ma’aikata, da kuma rashin ingantattun wuraren aiki. Wannan yajin aiki na zuwa ne a daidai lokacin da likitoci ke takun saƙa da gwamnati kan batutuwan suka shafi jin...
Shugaban kasar Iran Masuod Pezeshkiya ya yi juyayin shahadar Isma’ila Haniyya marigayi shugaban kungiyar Hamasa a nan Tehran shekara guda kenen. Ya kuma jaddada cewa JMI ba za ta taba manta da shi ba. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana bayyana wannan juyayin a ranar da Haniya yake cika shekara guda da shahada, sannan shahadarsa ya zo dai dai da ranar da Pezeshkiyan ya fara shugabancin kasar. Labarin ya kara da cewa shugaba Pezeshkiyan ya bayyana haka ne a shafinsa na X ya kuma kara da cewa a ranar da na fara aiki a matsayin shugaban kasa kenen, makiya HKI da kuma Amurka suka sanyamu cikin bakin ciki tare da kashe bakommu wanda ya zo ya taya mu...
Kungiyar wasan Taekwondo ta JMI kuma guragu, sun zama zakara a wasan taekwondo gurago sun lashe gasar ta Asia karo na 10 a jere. Kanfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto cewa an gudanar da gasar ne a kasar Malasiya, kuma yan wasa 107 ne daga kasashe 18 suka sami damar halattar gasar a ranar Jumma’an da ta gabata. Alireza Bakht da Mamed Haqshenas da kuma Marzieh Nasrollah sun sami lambobin Zinari sannan Saeed Sadeghianpour, Maryam Abdollahpour, da Amir mohammad Haghitshenas sune suka sami lambobin azurfa. A yayinda Aylar Jami, Leila Mirzaei, Mohammad Taha Hassanpour, Roza Ebrahimi, Leila Rahimi, da Mehdi Pourrahnama kuma suka sami lamabobin tagulla guda 6. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login...
Slovenia ta kasance Ƙasar Turai ta farko da ta ba da sanarwar hana tura makamai zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila Kasar Slovenia ta sanar da haramta musayar zirga-zirgan kayayyakin kasuwanci tsakaninta da haramtacciyar kasar Isra’ila musamman safarar makamai da kayan aikin soji zuwa Isra’ila, inda ta zama kasa ta farko ta Turai da ta dauki wannan matakin. Fira Minista Robert Gollub ne ya kaddamar da wannan matakin domin nuna adawa da mummunan bala’in jin kai a Gaza. Wata sanarwa da ofishin fira ministan ya fitar ta tabbatar da hakan yayin wani taron majalisar ministocin da aka gudanar a farkon alhamis. A karkashin sabon kuduri, duk makamai da kayan aikin soja an hana aikewa da su daga Slovenia zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila,...
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), za ta fara rajistar ƙuri’a ta intanet a ranar 18 ga watan Agusta, 2025, domin tunkurar zaɓen 2027. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ban girma da Hukumar NOA ta masa a hedikwatar INEC da ke Abuja. Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansaninta a Kebbi Ɗaliban da aka sace a Binuwai sun kuɓuta Ya kuma ce sai a ranar 25 ga watan Agusta, 2025 za a fara rajistar ƙuri’a a zahiri. “Za a fara rajistar ƙuri’a ta Intanet a faɗin ƙasa daga ranar 18 ga watan Agusta,” in ji Farfesa Yakubu. “Rajistar ƙuri’ar a zahiri kuma za ta fara daga 25 ga watan Agusta, 2025,”...
“Kiyasin ƴan Nijeriya miliyan 20 ke rayuwa da cutar hanta, kuma mutum miliyan 18.2 sun kamu ne da cutar rukunin B, sannan wasu mutum miliyan 2.5 sun kamu da cutar rukunin C. Abin takaici, ƴan Nijeriya 4,252 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon ciwon hanta da aka kasa maganceta ke haifarwa,” ya shaida. A jawabinsa na fatan alkairi, mai riƙon muƙamin wakilin hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO) a Nijeriya, dakta Aleɗ Gasasira, ya yi kira ne ga gwamnatin tarayya da ta tashi tsaye wajen yin na mijin ƙoƙari kan cutar hanta, yana mai cewa cutar tana shafar miliyoyin jama’a a ƙasar nan. Gasasira, wanda ya samu wakilcin dakta Mya Ngon, a faɗin ofishin WHO da ke Nahiyar...
Karamar Hukumar Birnin Kudu ta shirya taron bita na kwanaki biyu ga kansiloli masu gafaka da masu bada shawara akan kara samun dabarun aiki. Shugaban Karamar Hukumar, Dr Builder Muhammad Uba yace an shirya taron ne domin koyar da su dabarun sanin makamar aikin domin su fahimci tsarin mulkin tafiyar da kananan hukumomi. Jami’in lura da kididdigar kashe kudade na shiyar Birnin Kudu Malam Usman Ya’u ya gabatar da makala kan alamuran gudanar da aiki ga kansiloli masu gafaka da masu bada shawara. Shi ma Daraktan alamuran ma’aikata na yankin, Malam Tukur Ibrahim Doko yace taron bitar ga kansilolin masu gafaka zai kara zaburar da su akan ayyukan su. A karshe, Malam Sani Makama da Malam...
A cewar Adelabu, har yanzu dai wutar lantarki ne ƙashin bayan kamfanoni a Nijeriya da kuma tattalin arziki, ya nemi haɗin kan dukkanin wadanda lamarin ya shafa domin sake farfaɗo da sashin wutar lantarki yadda ya kamata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Dangote Ya Bada Shawarar Samar Da Gidaje Masu Rahusa Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Mallaka Majalisar Dattawa Ta Yi Allah-wadai Da Zanga-zangar Ƙin Jinin ’Yan Nijeriya A Ghana Sai dai, abin dubi a nan shi ne, yadda kusan yanzu a kasar, tabbatar da doka da oda, a cikin kasar, ya koma kachokam, a huunun sojin. ɗuba da sashe na 217 na kudin tsarin mulikin Nijeriya na 1999 da aka sabunta, wannan sashen, ayyukan soji tun daga na matakin rundunar sojin kasa da ta ruwa da kuma ta sama shi ne tabbatar da bai wa Nijeriya kariya, daga duk wani nau’in hare-haren, da ka iya zuwa, daga ketare, musamman ta hanyar, bai wa iyakokin kasar kariya, musamman bayan shugban kasa,...
Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da kashe Naira biliyan 712.26 don yi wa wani sashe na filin jirgin saman a Murtala Muhammad da ke Legas garambawul. Hakan dai ya biyo bayan zaman majalisar wanda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a Abuja ranar Laraba. NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa ke yi? Za a fara yi wa ɗaliban jami’o’i gwajin ƙwaya — Gwamnatin Nijeriya Aikin dai wani bangare ne na Naira biliyan 900 da aka ware domin inganta harkokin sufurin jiragen sama a fadin Najeriya. Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan jim kadan da kammala taron majalisar, inda ya ce tuni har an ba...
Allah Ya yi wa Mai Martaba, Sarkin Gudi Alhaji Isa Bunuwo Ibn Khaji rasuwa a asibitin Nizameye da ke Abuja ranar Alhamis. Mai martaba Sarkin wanda ke garin Gadaka a Ƙaramar hukumar Fika cikin Jihar Yobe ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya. Gwamnatin Jigawa ta horas da malamai 20,000 fasahar sadarwar zamani Peter Obi zai lashe jihohin Arewa idan ya koma PDP – Jerry Gana Sakataren masarautar Gudi da ke Gadaka ne ya tabbatar da rasuwar Sarkin, ya kuma ce an shirya gudanar da Sallar Jana’izar marigayi Sarkin a ranar Juma’a da ƙarfe 2:00 na rana a fadar Sarkin da ke Gadaka. Labarin rasuwar Sarkin dai ya tayar da hankalin a ɗaukacin al’ummar masarautar da ma Jihar Yobe...
Tawagar kananan yan wasan damben gargajiya na kasar Iran sun zama zakara a wasannin da aka gudanar a na wannan shekara ta 2025 tare da Zinari guda, azurfa guda da kuma Tagullah 4. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jami’an gasar wasan na damben gargajiya na kasar Iaran suna fadar haka a birnin Athen na kasar Girka. Sun kuma kara da cewa tawagar yan wasan zun zama zakara a wannan gasar ne duk da cewa mutum guda daga cikinsu bai shaga wasan ba. Labarin ya kara da cewa matasan kasar Iran sun kware a wammam wasan gargajiya, wanda ake kiransa damben Roma. Tawagar ta sami, zinari 1, azurfa 1 da Tagulla 4 , ta kuma sami maki...
Ministan ya kuma ce ƙasarsa na shirin sanya hannu a wata takarda don neman goyon bayan sauran ƙasashe wajen ganin an kafa ƙasar Falasɗinu da Isra’ila. A taron Majalisar Ɗinkin Duniya da aka gudanar na kwana biyu, ƙasashe 125 sun amince cewa hanyar warware rikicin Gaza ita ce kafa ƙasashe biyu, wato Falasɗinu da Isra’ila. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sojojin Yemen sun sanar da kai wasu zafafan hare-hare guda 3 kan mayakan sojojin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya Rundunar Sojin kasar Yemen ta sanar da cewa: Sojojinta sun kai wasu jerin zafafan hare-hare guda uku da jiragen saman yakin soji marasa matauka ciki, inda hare-haren suka janyo barna a muhimman wurare uku na makiya sojojin mamayar Isra’ila. A cikin wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta Yemen ta fitar ta bayyana cewa: Wadannan hare-hare wani bangare ne na matakin da ya dace na mayar da martani ga hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila ke kai wa kan zirin Gaza. Sannan sanarwar ta kara da cewa: Farmakin na farko an kai shi ne yankin Jaffa da aka mamaye...
“Muna kira ga gwamnatin jiharmu da ta kawo mana agaji da gaggawa domin da yawa daga cikin kaburburan da ke makabartar, sun rufta bayan ruwan saman, wannan aikin ya fi karfin mu.” In ji shi. A halin da ake ciki dai, rundunar ‘yansandan jihar Borno ta gaggauta gudanar da tantancewa a wurin tare da tura tawagar sintiri a yankunan da lamarin ya shafa. Makabartar Jajeri Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar (PPRO), ASP Nahum Kenneth Daso ya raba wa manema labarai a Maiduguri, ta ce rundunar ta gaggauta gudanar da tantancewa a wurin tare da tura tawagar sintiri a yankunan da abin ya shafa. Ya kuma tabbatar da cewa, “Abin takaici, gine-gine takwas...
Kwamitin da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umari Radda, ya kafa domin binciken ayyukan makarantun gaba da sakanadare masu zaman kansu na jihar, ya tabbatar da cewa, 37 cikin 39 ba su da rajista da gwamnati. Shugaban kwamitin, Farfesa Ahmed Muhammad Bakori, ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ƙaramar hukumar Bakori da ke jihar. Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno Bakori, wanda shi ne Kwamishinan Harkokin Noma na jihar, ya ce binciken kwamitin ya gano cewa makarantu biyu masu zaman kansu ne kacal a faɗin jihar ke da cikakkiyar rajista da hukumomin da suka dace. “Jihar Katsina na...
A nata bangare kuwa, Amurka ta bayyana aniyarta ta aiki tare da bangaren Sin, wajen ci gaba da warware sabani a fannonin tattalin arziki da cinikayya ta hanyar tsarin gudanar da shawarwari, da ingiza damar samar da karin nasarori daga tattaunawar, da kara samar da daidaito a alakar tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da Sin. Wakilin cinikayya na kasa da kasa na Sin karkashin ma’aikatar cinikayya, kuma mataimakin ministan cinikayyar kasar Li Chenggang, ya bayyana a yayin da yake yiwa manema labarai karin haske game da zaman tattaunawar sassan biyu. Ya ce sassan biyu suna sane da muhimmancin wanzar da daidaito, da kyautata alakar tattalin arziki mai nagarta tsakanin Sin da Amurka, sun kuma yi kyakkyawar musaya game da muhimman...
Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin Olumode Samuel Adeyemi a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa. Sabon shugaban hukumar zai fara aiki a hukumance daga ranar 14 ga watan Agusta, 2025. Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno An sanar da wannan naɗin ne a ranar Laraba cikin wata sanarwa da Hukumar CDCFIB, ta fitar, wacce sakatarenta, Abdulmalik Jibrin, ya rattaba wa hannu. Wannan naɗin na zuwa ne bayan da shugaban hukumar na yanzu, Injiniya Abdulganiyu Jaji Olola, ke shirin ritaya a ranar 13 ga watan Agusta, 2025, bayan cika shekaru 60 a duniya. Olumode Samuel Adeyemi yana da ƙwarewa da gogewa a aikin...
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da zagayen farko na makon lafiyar mata da jarirai da jarirai (MNCHW) na shekarar 2025 tare da raba fakiti 6,000 na kayan haihuwa da na’urar (C/S) 500 ga cibiyoyin lafiya a fadin jihar. Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta shi ne ya jagoranci bikin kaddamar da shirin a hukumance da aka gudanar a cibiyar lafiya matakin farko na Birji da ke karamar hukumar Madobi. Ya yi nuni da cewa, wannan aikin ya hada da na rigakafi na yau da kullun ga yara, karin sinadarin Vitamin A, Rarraba gidajen sauro masu maganin kwari ga mata masu juna biyu. Gwamna Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatin sa na karfafa...
Iran da Rasha sun tattauna kan inganta hadin gwiwar kafofin yada labarai da yaki da labaran karya Jakadan kasar Iran a birnin Moscow Kazem Jalali ya gana da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova a jiya Talata inda suka yi musayar ra’ayi kan bunkasa hadin gwiwar kafofin yada labarai. Bangarorin biyu sun tattauna batutuwan baya-bayan nan da suka hada da yiwuwar gudanar da harkokin yada labarai, da nazarin yiwuwar bunkasa hadin gwiwar kafofin watsa labaru, da hanyoyin yin tasiri a kafofin watsa labaru, da matakan hadin gwiwa don kara fahimtar ra’ayin jama’a a kasashen biyu. Bangarorin biyu sun yi tsokaci kan yadda kafafen yada labarai ke yada jita-jita da nufin yin zagon kasa ga dangantakar...
Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara wanda ke jagorantar ƙasar tun daga shekarar 2011, na fuskantar suka na neman mayar da shugabancin ƙasar mutu ka raba. Wannan dai na zuwa ne bayan Ouattara mai shekaru 83 ya tabbatar da aniyar sake takara wa’adi na hudu a zaben da za a yi ranar 25 ga watan Oktoba. Za mu halasta kafa ƙasar Falasɗinu muddin Isra’ila ba ta cika wasu sharuɗa ba — Birtaniya Nijar da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya A wani takaitaccen bayani da ya yi, Ouattara ya ce takararsa ta samo asali ne daga buƙatarsa ta kiyaye zaman lafiyar ƙasa a daidai lokacin da ta ke fuskantar kalubalen tsaro da na tattalin arziki. Ya bayyana cewa, “Ni dan takara...
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya amince da naɗin Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Katsinan Gusau. Sakataren Gwamnatin Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya bayyana haka a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Suleman Ahmad Tudu ya fitar a Talatar nan. Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a China ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a sabon hari a Alkaleri Sanarwar ta ce an yi amfani da dokoki da tanade-tanaden doka ne wajen amincewa da naɗin wanda masu zaɓen sarkin masarautar suka zaɓa. Gwamna Lawal ya taya sabon sarkin murna, sannan ya yi kira gare shi da ya yi koyi da magabatansa, musamman ganin shi tsatson Malam Sambo Ɗan Ashafa ne. Ya kuma yi kira ga...
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta ce akwai kwamitoci guda 30 da aka daurawa nauyin bibiyar yadda ma’aikatu da hukumomin gwamnatin Jihar ke sarrafa kudade domin gudanar da harkokin yau da kullum, gami da ayyukan raya kasa. Shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar, Alhaji Aminu Zakari, ya bayyana hakan lokacin wata ziyarar aiki a karamar hukumar Babura. Yayi bayanin cewar, an dorawa Kwamatinsa alhakin duba kananan hukumomi domin tabbatar da shugabanci nagari a yankunan karkara. A cewarsa, kwamatin yana duba kundin bayanan sha’anin mulki da na harkokin kudi da suka hada da jadawalin kudaden da karamar hukuma ke samu daga kason arzikin kasa, da littafin hulda da banki,da takardun biyan kudade na voucher da kundin bayanan...
Akalla mutane 7 ne aka ceto, bayan kifewar kwale-kwale a wani kogi da ke Zangon Maje, ƙaramar hukumar Taura, ta jihar Jigawa ranar Litinin. Shugaban ƙaramar hukumar Taura, Dr Shuaibu Hambali ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, lokacin da wasu manoma ke dawowa daga gonakinsu a ƙauyen Zangon Maje, inda suka hau kwale-kwalen. Ya ce, jami’an bada agajin gaggawa na yankin sun samu nasarar ceto mutane 7 a kokarin da suka yi na ceto wadanda lamarin ya shafa. Ya ƙara da cewa, masu ceton sun gano gawar mutum guda a yankin Yalleman da ke ƙaramar hukumar Kaugama. Dr Shuaibu ya bayyana cewa,...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗa Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Gusau kuma Sarkin Katsina na Masarautar Gusau. Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa an yi naɗin ne bisa ga shawarwarin da masu zaɓen sarakuna na masarautar Gusau suka bayar, tare da bin al’ada da dokokin da suka dace. A wata sanarwa da mai taimakawa na musamman kan harkokin yaɗa labarai a ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Sulaiman Ahmad Tudu, ya fitar, ya ce sabon Sarkin, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello, shi ne ɗa na farko ga marigayi Sarki, kuma kafin naɗin nasa yana riƙe da mukamin Bunun Gusau. Alhaji Abdulkadir ya hau karagar...
Gwamna Lawal ya taya sabon sarki murna, tare da roƙon Allah Ya bashi hikima da ikon yin jagoranci na gari. Ya kuma buƙace shi da ya ci gaba da bin kyawawan ɗabi’u da tafarkin tsofaffin sarakuna domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a masarautar Gusau. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin kasar Faransa ta yi kakkausar suka tare da tofin Allah tsine kan harin ta’addancin da aka kai birnin Zahidan na kasar Iran Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan harin ta’addancin birnin Zahidan na kasar Iran, tare da jaddada adawar kasarta kan duk wani harin ta’addanci da aka kai kan fararen hula. Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta fitar da wata sanarwa inda ta ce, birnin Paris na matukar yin Allah wadai da harin ta’addanci da aka kai a birnin Zahidan na kasar Iran a ranar 26 ga watan Yuli, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama ciki har da uwa da kuma ‘yarta. Sanarwar ta kara da cewa, “A yayin da take mika...
An fara shigar da kayyakin agaji zuwa Zirin Gaza wadanda galibi ta sararin samaniya aka rika jefawa da jirage daga kasashen Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa. Arshiyan Kohen, kakakin ma’aikatar tsaron Isra’ila ya ce, za a dakatar da farmakin soji na tsawon sa’o’i 10 a kowace rana a wasu sassan Gaza tare da ba da damar samun sabbin hanyoyin ba da agaji. DW ya ruwaito cewa ana ci gaba danka kayayyakin tallafin a hannun kungiyoyin agaji na kasa da kasa da suke ci gaba da ayyukan rarrabasu. Tinubu ya bai wa ’yan ƙwallon Nijeriya mata kyautar kuɗi da gida da lambar yabo An kashe ’yan ta’adda 45 a Neja Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteress ya siffanta wannan matakin da...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa Iran a shirye take ta fadada hulda da kasashen turai, amma kuma wannan ba zai sa ta saryar da hakkinta na sarrafa makamashin nukliya karshen dokokin kasa da kasa wadanda suka amince mata ta yi haka ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau Litinin a lokacinda yake ganaw da sabon jakadan kasar Faransa a Tehran pierre Cochard wanda ya mika masa tarkardun fara aikinbsa. Shugaban ya kara da cewa an takurawa kasar Iran dangane da shirinta na makamashin nukliya a bayan. Amma daga yanzun kuma ba zata amince da irin takurawa ta bay aba. Ya kuma bayyana cewa tattaunawa tsakanin Iran da kasashe...
Ya ce rasuwar Dakta Usigbe babban rashi ne ba kawai ga kamfanin jaridar Tribune da fagen aikin jarida ba, har ma da ƙasar nan baki ɗaya. “Nijeriya ta yi rashi matuƙa — mun rasa ɗaya daga cikin fitattun ‘yan jarida, wanda ilimin sa, jarumtar sa, da himmar sa ta sa kowa yana girmama shi.” A madadin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Idris ya miƙa ta’aziyyar sa ga shugabanni da ma’aikatan Tribune, da gwamnati da al’ummar Jihar Edo inda marigayin ya fito, da kuma iyalan sa, da abokan sa, da ma dukkan masu mu’amala da shi. “Allah ya jiƙan sa, ya ba duka waɗanda ya bari haƙurin jure wannan babban rashi,” inji Ministan. Daga kanmu, magana ta ƙare....
Dakarun kasar Yemen sun sanar da sabbin zabukan kara rurutan bude wuta kan makiya a matsayin martani ga abubuwan da suka faru a Gaza Dakarun sojin kasar Yemen sun bayyana a cikin wata sanarwa da suka fitar a yammacin jiya Lahadi cewa: Suna tunanin zafafa yakin da suke yi da ‘yan mamaya dangane da abin da ke faruwa a Zirin Gaza na kisan kare dangi da kakaba masifar yunwa kan al’ummar yankin. Rundunar sojin kasar ta Yemen ta tabbatar da fara aikin killace teku kashi na hudu a kan makiya, inda zasu kai hari kan dukkanin jiragen ruwan kamfanonin da ke aiki a tashar jiragen ruwa na Isra’ila, ba tare da la’akari da kasarsu ba, da kuma duk inda sojojin...
Ma’aikatar kula da sashen ayyukan jigilar kayayyaki ta kasar Sin ta ba da rahoton cewa, a cikin rabin farkon bana, an samu ci gaba mai yawa a bangaren, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna a jiya Lahadi. Hukumar raya ci gaban kasa da gudanar da gyare-gyare, wacce take da alhakin tsara tsare-tsaren tattalin arzikin kasa ta yi bayanin cewa, kudin da ake kashewa a ayyukan jigilar kaya ya kai kaso 14 cikin dari na GDPn kasar a watanni shida na farkon shekarar, inda ya ragu da kaso 0.1 cikin dari idan aka misalta da na rubu’in farko, kuma ya ragu da kashi 0.2 bisa dari a mizanin shekara-shekara. A cewar hukumar, wannan na nuni ne da sakamakon farko da aka...
Kungiyar yan tawaye M23 wacce take iko da yanki mai yawa a gabacin Democradiyyar Kongo ta bada sanarwan cewa idan gwamnatinn kasar Kongo bada gaggauta sakin fursinonin kungiyar ba, to tana iya kauracewa tattaunawan da za’a gudanar a birnin Doha na kasar Qatar a watan mai zuwa. Shafin yanar gizo na Africanews ya nakalto babban sakataren kungiyar kuma mai magana da yawunta yana fadar haka a ranar jumma’a. Ya kuma kara da cewa bayan da kowa ya bayyana matsayinsa a wata mai zuwa ne ake saran bangarorin biyu wato gwamnatin kongo da kuma kungiyar M23 zasu rattaba hannu a kan yarjeniyar sulhu na gaskiya. Ya ce tattaunawa da kuma amincewa da wasu ka’idoji wanda bangarorin biyu suka rattabawa hannu a...
Duk da alƙawuran sojoji na kama fitaccen jagoran ’yan bindiga, Bello Turji domin hukunta shi kan laifunan ta’addanci, har yanzu ɗan ta’addan bai daddara ba, a yayin da suke ci gaba da farautar sa shi da sauran manyan shugabannin ’yan bindiga da ke addabar ’yan Nijeriya. Dakarun sojin da aka tura ƙarƙashin rundunar Operation Fansan Yamma da sauran ayyukan soji a yankin Arewa maso Yamma da kuma Arewa maso Tsakiya, sun yi nasarar halaka manyan jagororin bindiga da dama, ciki har da wasu na hannun daman Turji a jihohin Sakkwato da Zamfara da Kebbi da kuma Kaduna, amma dai har yanzu Turji, wanda ke gudun ɓuya bai shiga hannu ba, duk kuwa da neman sa ruwa a jallo da jami’an...
Jami’an diblomasiyya na kasashen Iran da kuma na tarayyar Turai 3 wato Faransa da Jamus da kuma burtaniya sun fara tattaunawa gaba da gaba bayan yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka kai mata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta kara da cewa wannan tattaunawar yana da matukar muhimmanci don zasu tattauna kan shirin makamashin nukliyar kasar Iran da kuma dauke mata takunkuman tattalin arzikin da su dora mata saboda shirinta na makamshin nukliya. Har’ila yau ana ganin tattaunawar ta Istambul shi zai fayyace makomar dangantaka tsakanin Iran da tarayyar Turai gaba daya nan gaba. Labarin ya kara da cewa tarunn yana gudana ne a cikin ofishin jakadancin kasar Iran dake birnin Istambul kuma Majid Takht-ravanci da...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alhinin rasuwar Sarkin Gusau, Dokta Ibrahim Bello na Jihar Zamfara. Sarkin ya rasu da safiyar Juma’a yana da shekaru 71. An yanke wa mutum 3 hukuncin kisa kan kisan kai a Gombe HOTUNA: Yadda Kwankwaso ya karɓi ’yan APC zuwa NNPP a Kano Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa. Ya ce Sarkin mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa don hidimta wa al’ummarsa. Shugaba Tinubu ya ce rasuwar Sarkin babban rashi ne, ba wai kawai ga mutanen masarautarsa ba, har da ƙasa baki ɗaya. Ya yaba da jajircewarsa, kyakkyawan shugabancin da sadaukarwarsa ga jama’a. Shugaban ƙasa ya miƙa ta’aziyyarsa ga...
Allah ya yi wa Sarkin Katsinan Gusau da ke jihar Zamfara, Dr Ibrahim Bello rasuwa. Ya rasu da safiyar Juma’a a Abuja yana da shekaru 71, bayan ya sha fama da jinya. Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano masu wanke-wanke a Kudu An kama budurwa mai shekara 19 da ake zargi da kashe yara 2 a Bauchi Marigayin, wanda shi ne Sarkin Gusau na 16, ya ɗare kan karaga ne a shekara ta 2015, bayan rasuwar mahaifinsa. Gogaggen ma’aikacin gwamnati, Dr Ibrahim ya taɓa zama Babban Sakatare a tsohuwar jihar Sakkwato da ma jihar Zamfara. Ya yi mulkin ne na tsawon shekara 10 da ’yan watanni kafin rasuwar tasa. Da yake tabbatar da rasuwar, Kakakin Gwamna...

Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Ce: Taro Tsakanin Iran Da Tawagar Kasashen Turai Dama Ce Ta Gyarar Tunanin Tarai
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Taron Istanbul wata dama ce ta gyara matsayar Turai kan shirin makamashin nukiliyar Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i, ya yi la’akari da taron na yau tsakanin Iran da kasashe uku mambobin kungiyar hadin gwiwa ta JCPOA a matsayin wata muhimmiyar dama ta gyara ra’ayoyinsu da gwada hakikaninsu kan batun makamashin nukiliyar kasar Iran. A cikin wata sanarwa da ya aikewa kamfanin dillancin labaran IRNA, Isma’il Baqa’i ya bayyana fatansa na cewa wadannan kasashe uku za su yi amfani da wannan damar wajen gyara tsarin da suka bi a baya wanda bai dace ba, wanda ya lalata martabar Turai da matsayin tattaunawa, tare da mayar da ita a matsayin...

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (4)
Hikimar Rashin Hade Farkon Shekarar Musulunci Da Tarihin Manzancin Annabi (SAW) Masu karatu har yanzu dai muna kan bayani game da abubuwan da suka sa Sahabbai ba su kafa tarihin kirgen shekarar musulunci ba da wasu manyan alherai na Musulunci, sai suka zabi Muharram ta zama farkon shekarar tare da lakaba mata shekarar Hijirah. A makon da ya gabata mun yi bayani kan hikimar ware farkon shekarar daga watan Rabi’ul Auwal zuwa watan Muharram saboda girman haihuwar Manzon Allah (SAW). A yau kuma, za mu ci gaba da bayani a kan ware kirgen farkon shekarar daban da ranar da aka fara aiken Manzanci ga Annabi (SAW). Tun ana sauran shekara uku Manzon Allah (SAW) ya cika shekara 40 da...

Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Tattaunawa Tsakanin Shugabannin Sin Da EU Karo Na 25 Tare Da Shugaban Majalisar EU Da Shugabar Hukumar EU
Da yammacin yau Alhamis ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya shugabanci taron tattaunawa tsakanin shugabannin Sin da EU karo na 25, tare da shugaban majalisar EU Antonio Costa, da shugabar hukumar EU Ursula von der Leyen a nan birnin Beijing. A yayin taron, Li Qiang ya bayyana cewa, Sin da EU suna da moriya iri daya wadda babu rikici a cikinta. Bisa yanayin sauyi da ake ciki a halin yanzu, ya kamata Sin da EU su kara yin hadin gwiwa. Kuma kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da bangaren EU a fannonin cinikayya, da zuba jari, da kiyaye muhalli, da kimiyya da fasaha da sauransu, don tabbatar da samar da kayayyaki a tsakaninsu yadda ya kamata, da...
Gwamnatin Jihar Kaduna ta karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ana shirin sayar da makarantar firamare ta Yusuf Dantsoho da ke Unguwar Rimi GRA. Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu, Alhaji Maman Lagos, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar aiki makarantar. Makarantar Yusuf Dantsoho, wacce aka kafa a shekarar 1920, tana tsakiyar Unguwar Rimi GRA, kuma ta samar da fitattun ‘yan Najeriya da dama da suka yi aiki a matakai daban-daban na gwamnati da kuma masu zaman kansu. Alhaji Maman Lagos ya tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ba ta da niyyar sayar da wata cibiyar gwamnati, kama daga makarantu zuwa asibitoci. Yace maimakon haka,...
Ministan Noma na Iran Gulam Riza Nuri Qazlajeh ya fada a yau Alhamis cewa; Iran tana a cikin kasahe biyar na sahun gaba da su ka yi fice wajen dabbobi. Minstan wanda yake jawabi a wani kamfani na samar da nono, ya ce, Iran tana da niyyar kara yawan dabbobin da suke samar da nono ta hanyar kyautata da kula da lafiyarsu, domin rage dogaro da waje samar da nama da kuma nono.” Haka nan kuma ministan na noma ya kara da cewa; Kara yawan dabbobin da ake samarwa a cikin gida,wata lalura ce ta tattalin arziki, da kuma kishin kasa. Ministan Noma na Iran ya kuma kara da cewa, ma’aikatar tasu tana kokarin ganin mayar da Iran zama cibiyar...

Anacláudia Rossbach: Ya Kamata Kasashen Afirka Su Koyi Darasi Daga Sin Na Kawar Da Talauci Da Kyautata Kauyuka Zuwa Birane
Kwanan nan, darektar zartaswa ta hukumar kula da matsugunan dan Adam ta MDD, Anacláudia Rossbach, ta yi hira da wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, a hedkwatar hukumar kula da matsugunan dan Adam ta MDD dake Nairobi, babban birnin Kenya. Yayin da aka ambato sakamakon da ya fi jawo hankali da Sin ta samu yayin kyautata kauyuka zuwa matsayin birane da garuruwa, Rossbach ta bayyana cewa, Sin ta cimma nasarar kawar da talauci ga mutane miliyan 800, da kuma tafiya a kan hanyar kyautata kauyuka zuwa birane da garuruwa, kuma wannan darasi ne da ya cancanci kasashen Afirka wadanda suke fuskantar kalubalen kyautata kauyuka zuwa birane su yi koyi da shi. Ta ce, nan da...

Ayatullahi Makarem Shirazi Ya Jinjinawa Al’ummar Iran Kan Hadin kai Da Suka Bayar Lokacin Yakin Kwanaki 12
Ayatullah Makarem Shirazi ya jaddada cewa: An kara samun karfafan hadin kan al’umma Iran bayan wuce gona da irin ‘yan sahayoniyya da Amurka kan kasarsu Ayatullah Nasser Makarem Shirazi, babban malamin addinin Musulunci a birnin Qum mai tsarki na kasar Iran ya jaddada cewa: An kara samun hadin kan kasa bayan yakin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kaddamar kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A yayin ganawarsa da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a jiya Laraba a birnin Qom mai alfarma Ayatullah Makarem Shirazi ya yi ishara da yakin tunani da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya da Amurka suka yi kan Iran yana mai cewa: Wadannan makiya sun yi zaton za su haifar da rudani ta hanyar kai...
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara tattauna masifar da ta faru a Gaza tare da jaddada kawo karshen kisan kiyashi yanki Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani sabon zama domin tattauna batutuwan da suke faruwa a Gaza da kuma tabarbarewar al’amuran jin kai a yankin, inda ake ci gaba da yin kiraye-kirayen gaggauwa da kuma kira ga kasashen duniya da su dauki kwararan matakai na kawo karshen bala’in da ya biyo bayan yakin kisan kare dangi a yankin. Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a hanzarta dakatar da tilastawa al’ummar Gaza gudun hijira kamar yadda ta bukaci gwamnatin mamayar Isra’ila da ta ba da damar kai agajin jin kai ga al’ummar Zirin Gaza. Mataimakin babban...
Kayan da aka gano a wajen samamen sun haɗa da wayoyin salula da dama, kwamfutoci, na’urorin haɗa Intanet da mota ƙirar Honda Accord. Sunayen waɗanda aka kama sun haɗa da: Ismaíl Nura, Suuleyman Ayeh, Usman Abdulrazaq, Emmanuel Chigozie, Akabe Seth, Daniel Imoter, Abdulganiyu Jimoh, Jafar Abubakar, Usman Nuraddeen, Mohammad Adnan da Abubakar Abusufyan. Sauran sun haɗa da Abdulmalik Ibrahim, Abubakar Sadiq, Daniel Masamu, Abdulrasheed Abdulsamad, Issac Dosunu, Nuraddeen Ogunbiyi, Onyeyemi Kaleem, Miracle Joseph, Danjuma Musa, Ibrahim Mubaraq, Yusuf Salihu, Lawal Ibrahim Edebo, Abdulmajeed Suleiman da Dauda Abdulhamid. EFCC ta ce za a gurfanar da su a kotu da zarar ta kammala bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
Gwamnatin Borno ta bayyana yawan ma’aikata a matsayin dalilin da ya sanya ƙananan hukumomin jihar ba za su iya biyan mafi ƙarancin albashin ma’aikata na Naira dubu 70,000 ba. Gwamnatin ta ce ta umarci shugabannin ƙananan hukumomin jihar su samar da tsari mai ɗorewa domin ƙaddamar da fara aikin mafi ƙarancin albashin. WFP zai dakatar da tallafin abinci da kiwon lafiya a Nijeriya Matasa 3 sun rasu yayin wanka a rafi a Bauchi Babban sakataren ma’aikatar kula da ƙananan hukumomi da masana’antu, Modu Alhaji cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce yawan ma’aikatan ne ya haifar da jinkiri wajen fara biyan mafi ƙarancin albashin. Modu ya yi bayanin cewa a wasu lokutan gwamnatin tarayya na turo ƙasa da Naira...
Alkaluma da aka fitar a hukumance sun nuna cewa, kasar Sin ta samar da sabbin guraben aikin yi miliyan 6.95 a rabin farko na bana, inda ta cimma kaso 58 bisa dari na burinta na shekara. Kakakin ma’aikatar kula da ma’aikata da walwalar al’umma ta kasar Sin Cui Pengcheng ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a yau Talata, inda ya ce a watan Yuni, yawan wadanda ba su da aiki a birane ya tsaya kan kaso 5 bisa dari, watau bai sauya ba daga yadda ya kasance shekara 1 da ya wuce. Kasar Sin na da burin adadin marasa aikin yi ya tsaya kan kaso 5.5 a bana, tare da burin samar da guraben aikin yi sama...
Hukumar Hisbah ta ce ta kama tare da lalata barasa da ta kai kimanin naira miliyan 5.8 a karamar hukumar Kazaure ta Jihar Jigawa. Kwamandan Hisbah a jihar Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga harabar Majalisa Kamfanonin lantarki za su katse wuta kan bashin N5.2trn da suke bin gwamnati Ya ce an gudanar da aikin ne karkashin jagorancin shugaban hukumar da ke Kazaure, Mansur Dabuwa, inda aka lalata katan 400 na barasa da darajar kudinsu ya kai naira miliyan 5.8. Ya bayyana cewa an kama barasa da aka kona a lokacin samamen da aka kai a sassa daban-daban a...
Jami’an tsaro sun hana Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ’yan rakiyarta shiga haramar Majalisar Dokoki ta Kasa, inda ta je da niyyar halartar zaman Majlasiar Dattawa a ranar Talata. Jami’an tsaro a daukacin kofofin shiga harabar majalisar sun hana ta shiga harabar majalisar ne a lokacin da ta yi yunkurin shiga domin halartar zaman ranar Talata, a yayin da magoya bayanta suka rako ta domin nuna goyon bayansu gare ta kan dakatarwar da majalisar ta yi mata. A watan Maris ne da Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na tsawon wata shida kan zargin rashin da’a da kuma rashin bin tsarin wurin zaman da aka tanadar da mambobin majalisar a ranar 20 ga watan Fabrairu, 2025. A kana haka ne...
An wajabta wa ɗaliban makarantun firamare da Ƙaramar Sakandare mallakar lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) a Jihar Bauchi. Hukumar Kula da Ilimin Bai-ɗaya a Matakin Farko ta jihar (SUBEB) ce ta bayar da umarnin ta hannun shugabanta, Alhaji Adamu Mohammed Duguri. Ya bayyana cewa mallakar lambar NIN ta zama tilas lura da duk hukumomin shirya jarabawa da manyan makarantu suna amfani da ita kafin yi wa ɗalibai rajista. Ya umarci shugabannin makarantun firamare da sakandare da su umarci ɗalibansu da su tabbata sun yi rajistar katin shaidar ɗan ƙasa sun mallaki lambar NIN kafin shekarar da za su zana jarabawar kammala makarantar da suke. NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa A tsananta hukunci...
Kungiyar Agaji ta Red Cross (ICRC) ta bayyana cewa yunwa na ƙara tsananta a Arewa maso Gabashin Nijeriya, musamman a jihohin Borno, Adamawa da Yobe. A cewar rahoton, rikicin da ya dauki shekaru 16 ya durƙusar da kasuwanci da hanyoyin samun aiki, wanda hakan ya tilastawa mutane dogaro da ƙananan gonaki don rayuwa. Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh Jihohin da za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Nijeriya — NiMet ICRC ta bayyana cewa fiye da mutum miliyan 3.7, wadanda galibi manoma ne na fuskantar barazanar matsanancin rashin abinci a yankin da aka shafe shekaru ana rikici. Churi Ibrahim, wani tsohon manomi dan shekara 70 da ke ciyar da iyalinsa goma,...

Kasar Sin Na Fatan EU Za Ta Yi Aiki Da Ita Bisa Alkibla Guda Da Tsara Hadin Gwiwa Na Shekaru 50 Masu Zuwa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana a yayin gudanar da taron manema labaru na yau da kullum da aka yi yau Litinin cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Tarayyar Turai EU. Kuma taron kolin kasar Sin da EU karo na 25 na karatowa. Kasar ta Sin tana fatan kungiyar EU za ta yi aiki tare da ita bisa alkibla guda, da cimma matsaya, da kawar da bambance-bambance, da kuma tsara shirin hadin gwiwa tare cikin shekaru 50 masu zuwa. Bayan cimma yarjejeniya tsakanin Sin da kungiyar EU, shugaban majalisar Tarayyar Turai António Costa da shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, za su...
– Emmanuel Adegbola Aina – AIG na wucin gadi, sashen leƙen asiri – Omolara Ibidun Oloruntola – Hassan Abdu Yababet – CP, Kwalejin ‘Yan Sanda Jos – Bretet Emmanuel Simon – CP Jihar Taraba – Enyinnaya Inonachi Adiogu – CP, FCID, Gombe – Aminu Baba Raji – CP, FCID Alagbon – Mohammed Mu’azu Usman – CP, Tashoshin Gabas, P/Harcourt – Festus Chinedu Oko – AIG na wucin gadi, sashen DLS, Hedkwatar – Ronke Nurat Okunade – CP, SFU FCID Annex, Lagos Kazalika, PSC ta amince da: – Ɗaga darajar DCP 16 zuwa CP – Ɗaga darajar ACP 27* zuwa DCP – Ɗaga CSP 145 zuwa ACP, ciki har da likitoci, ma’aikatan lafiya, injiniyoyi na jiragen sama, da limamai – Ɗaga...
A wani gagarumin mataki na karfafa yaki da rashin tsaro, gwamnatin jihar Zamfara ta gudanar da wani babban taron masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a Gusau, da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomi da kuma kaddamar da sabbin dabarun yaki da ayyukan ta’addanci da masu aikata laifuka. Taron wanda aka gudanar a Sakatariyar JB Yakubu wanda ofishin sakataren gwamnatin jihar (SSG) ya shirya, ya hada manyan hafsoshin tsaro, manyan jami’an gwamnati, da wakilan hukumomin tarayya domin duba halin tsaro da jihar ke ciki. A cewar wata sanarwa da babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga SSG, Suleman Ahmad Tudu, ya yi, an kira taron ne domin zurfafa hadin kai a tsakanin masu ruwa da...
Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta zabi Hon. Kamilu Sa’idu (Wamban Kasuwar Daji) a matsayin dan takararta na Majalisar Dokokin Jihar Kaura Namoda ta Kudu da za a yi ranar 16 ga Agusta, 2025. A wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Jihar, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya ce Kamilu ya fito ne ba tare da hamayya ba bayan janyewar wasu ‘yan takara uku Bashir Muhammad Madaro (Walin Kurya), Anas S/Fada, da Alhaji Ashiru Hamisu Habibu—a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a makarantar firamare ta Kasuwar Daji. Sanarwar ta ce, ‘yan takarar ukun sun sauka ne domin nuna goyon bayansu ga Kamilu Sa’idu inda suka yi alkawarin samun nasararsa da...
Ministocin tsaro na kasar Rasha ta JMI sun hadu a birnin Mosco don tattauna batun karfafa dangantakar tsaro a tsakaninsu a dai dai lokacinda al-amuran tsaro suke kara tabarbarewa a yankin kudancin Asiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jakadan kasar Iran a Mosco yana fadar haka. Kazem Jalali, ya bayyana cewa kasashe biyu suna kara zurfin dangantakarsu da juna a dai-dai kasashen biyu suke kara fuskantar matsinn lamba daga kasashen yamma musamman Amurka, da kuma HKI. Kasashen biyu sun ga yakamata su kara dankon zumunci a tsakaninsu a fagen tsaro, bayan yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka dorowa kasar Iran. A wannan zuwan dai ministan tsaron JMI ya raka Dr Ali Larijani babban mai...
Sanata Yemi Adaramodu, mai magana da yawun Majalisar Dattawa, ya ce matsalar tsaro a Najeriya na raguwa, kuma tattalin arziƙi ya fara farfaɗowa. Ya yaba da ƙoƙarin da sojoji ke yi wajen yaƙi da ’yan bindiga da ’yan ta’adda. Haɗakar ’yan hamayya alheri ce ga siyasar Nijeriya — Gbajabiamila WFP ya dakatar da tallafin abinci a Yammaci da Tsakiyar Afirka “Sojoji suna ƙoƙari saboda muna ba su isasshen kuɗi don siyan makamai da kula da jin daɗinsu. Yanzu matsalar ’yan bindiga ta ragu a wasu jihohi, kuma ana magance ta.” Ya ƙara da cewa satar mutane ta ragu: “A da, mutane ba sa iya bacci saboda tsoro. Amma yanzu abubuwa sun ɗan gyaru. Sai dai waɗanda za su sa siyasa...
A bisa umarnin sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ, an yi nasarar gudanar da zaben majalisar jihar Zamfara a ranar Asabar din da ta gabata cikin kwanciyar hankali da lumana, inda aka dawo da dukkan mukamai ba tare da hamayya ba. Mukamin daya tilo da aka fara takaddama a kai ya sa daya daga cikin masu neman takarar, Rabi Yusuf ta janye bisa radin kanta, wanda a hukumance ta sauka ta hanyar mika takarda ga kwamitin tantancewa, tare da aika kwafin ga mataimakin shugaban shiyyar da Sakatare. Wakilai daga Sakatariyar NUJ ta kasa ne suka jagoranci gudanar da zaben da kuma kaddamar da taron wanda suka hada da mataimakin shugaban shiyyar A, Muhammad Tukur Umar da sakataren...
Shugaba Trump da abokansa sun ce sun gano cewa ana tafka almundahana da zamba a hukumar. Rahoton na zuwa ne yayin da gomman shugabannin duniya ke taro a Birnin Sabeilla na kasar Sifaniya cikin makon nan domin tattauna batun katse tallafin, wanda ya fi kowane bayar da agaji a duniya. Bayan nazarin bayanan alkaluman tallafin hukumar a kasashe 133 a duniya, binciken ya kiyasta cewa tallafin USAID ya rage mutuwar mutum miliyan 91 a kasashe masu tasowa tsakanin 2001 zuwa 2021. Sun kuma yi amfani da wani kiyasi wajen hasashen yadda rage tallafin da kashi 83% adadin da gwamnatin Amurka ta sanar a farkon wannan shekara na iya shafar adadin masu mutuwa. Rahoton ya ce katse tallafin zai haifar da...
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da lafta wa Tarayyar Turai da kuma Mexico harajin kashi 30 kan kayayyakin da ake shiga da su da su ƙasar daga ranar 1 ga Agusta. Bayanai sun ce ana ganin wannan matakin zai iya haddasa rikici mai tsanani tsakanin Amurka da biyu daga cikin manyan abokan kasuwancinta. An sanya dokar hana fita a Adamawa Tinubu ya dawo Najeriya bayan ziyarar aiki a Saint Lucia da Brazil Trump ya yi cikakken bayani kan wadannan haraje-harejen ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, yana mai cewa matuƙar ba a cimma wata tartibiyar matsaya ba, ba shakka zai ƙara lafta musu harajin. Wannan na daga cikin jerin sabbin haraje-haraje da...

Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci Sun Kama ‘Yan Leken Asirin Isra’ila A Lardin Mazandaran Na Kasar Iran
Dakarun juyin jaya halin Musulunci ta Iran sun kama wani wakilin hukumar leken asirin Isra’ila Mossad a arewacin kasar Iran Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun sanar da kame wani jami’in hukumar leken asirin haramtacciyar kasar Isra’ila “Mossad” a lardin Mazandaran (arewacin kasar Iran), wanda ke shirin kai harin ta’addanci a cikin kasar. Sanarwar da dakarun kare juyin juya halin suka fitar ta bayyana cewa: wani ma’aikacin fage na makiya da ke shirin aiwatar da ayyukan ta’addanci ta hanya kai tsaye wajen jagorantar masu adawa da Iran a kasashen waje, an kama shi ne a wani gagarumin samame da jami’an leken asirin na Karbala suka kai, kafin ya aiwatar da duk wani aikin ta’addanci. Sanarwar ta kara da cewa:...
Ali Mohammad Sabeghi, tsohon jami’in bangaren al-adu na ofishin jakadancin kasar Iran a kasar China ya karbi kyautar ‘Jakadan Abota’ na kasar China a wannan shekara ta 2025M. A bikin bada irin wannan kyauta karo na biyu. Labarin ya kara da cewa dangantaka tsakanin JMI ta kuma China yana daga cikin abota mafi kyau tsakanin kasashen yankin da kasar China. Labarin ya kara da cewa girmama kasar Iran ta wannan kyautar yana daga cikin al-amuran da zasu kara dankon zumunci tsakaninta da Tehran. Hukumar al-adu na kasar China ta bayyana cewa ta samar da irin wannan kyautar ne don karfafa danganta kasar China da da sauran kasashen duniya musamman kasashen Asia. A shekarar da ta gabata dai wannan kyauta ta...
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya ja kunnen shuwagabannin kasashen yammacin Turai kan shiga yaki da kasar Rasha. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Lavrov yana fadar haka, a jiya Jumma’a. Ya kuma kara da cewa, labaran da suke isa kunnensa daga biranen Landan, Paris da kuma Berlin sun tabbatar masa da cewa, kasashen suna shirin yaki da kasar Rasha. Ya ce, Rasha ta sha fadawa kasashen yammacin Turai, ci gaba da goyon bayan kasar Ukrai zai jawosu zuwa yaki da kasar Rasha. Yaki wanda rabuwamma da irinsa tun bayan yakin duniya na II. Ya shay a sha fada masu kan cewa makaman da suke turawa Kiev daga karshe ba zai taba samar da zaman...
Kididdigar ta nuna cewa maimakon amfani da wannan kudaden shigar don rage basussuka, wasu jihohi suna kara amso bashin. Jihar Ribas ta zama ta farko a jerin jihohin da adadin bashin cikin gida na naira biliyan 364.39 a wata uku na farkon 2025, mafi girma tsakanin jihohi 10. Basukan Jihar Inugu sun tashi daga naira biliyan 82.48 a farkon wata uku na 2024 zuwa naira biliyan 188.42 a farkon wata uku na 2025, wanda ke nuna karuwa na naira biliyan 105.95 ko kashi 128.4 cikin dari. Jihar Neja ta biyo baya da karuwar naira biliyan 57.68 a kowanne shekara, daga naira biliyan 86.07 zuwa naira biliyan 143.75, wanda shi ne karuwa na kashi 67 cikin 100. Jihar Taraba ta nunka...
Kamfanonin inshora za su kauracewa jiragen ruwa da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila saboda tsoron fuskantar hare-haren Yemen Jiragen ruwan da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila za su fuskanci kaurace daga kamfanonin inshora, sakamakon munanan hare-haren baya-bayan nan da sojojin Yemen suka kai kan jiragen Magic Seas da Eternity Sea, wadanda suka kai ga nutsewa, a teku a ranar Alhamis. A cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa ya bayyana cewa: Majiyoyin masana’antar inshora sun ce “kamfanonin inshora za su yi kokarin kauce wa rufe duk wani jirgin ruwa da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila, ko da kuwa alakar a kaikaice ne.” Kamfanin dillancin na Reuters ya nakalto daga Munro...
An tsara Jirgin zai rinka yin zirga-zirga ne, zuwa daukacin kasashen da ke Afirka ta yamma da kuma sama da haka, musamman yin zirga-zirga daga Nijeriya zuwa kasashen, Jamhiriyar Benin, Togo, Ghana, Kamaru, Sierra Leone, Ibory Coast, Masar, Afirka ta Kudu da sauransu, tare da kuma nuna bukatar yin kasuwanci wadda tuni, aka fara ta. A martaninsa kan wannan nasarar, Shugaban Hukumar ta NPA Dakta Abubakar Dantsoho ya bayyana cewa, “ Wannan nasarar ta nuna irin mayar da hankalin da NPA ke ci gaba da yin a kara bunkasa ayyukan Hukumar wanda ta zo daidai da ta irin ma’aikatar bunkasa tattalin arzikin kasa. A na ta bayanain Mataimakiyar Shugabar kamfanin na On her Clarion Shipping West Africa Limited, Bernadine Eloka,...
Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan kai hare-hare kan tashar jiragen sama na Bengurion na HKI tare da amfani da makamai masu linzami samfurin Balistic. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar sojojin Yemen na cewa, sun kai hare-hare da makamai masu linzami ka tashar jiragen sama na Ben gurion kuma zasu ci gaba da kai wadan nan hare-hare har zuwa dakatar da kissan kiyashin Falasdinawa a Gaza. Yahyah Saria kakakin sojojin kasar ta Yemen sun bayyana cewa, sojojinsa sun yi amfani da makamai masu linzami samfurin Bilistic maim suna Zulfikar wanda kuma ya fadi a kan tashar jiragen saman na Lod Airport kusa da Yafa ko tel’aviv. Ya ce makamin ya sami bararsa kuma ya sa...
Hukumomin tsaron uku su ne, na DIA, DSS da kuma NIA, inda kuma dokar, ta bayar da damar kafa ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara a fannin tsaro wato ONSA, wadda a baya, ake kiran ofishin da Babban Jami’in Tsaro na Kasa wato CONS. Wannan Jaridar, na nuna matukar damauwarta kan ci gaba da fuskantar kalubalen rashin tsaro, da Nijeriya ke fuskata, musamman na rashin gazawar hukumomin tsaro na sirri saboda gasar da suke nuna wa, a tsakaninsu. A bisa ra’ayinmu, wannan matsalar, abu ne da ke bukatar a kara mayar da hankali cikin gaggawa domin a magance wannan kalubalen na rashin na rashin tsaron. Sai dai, muna kuma yabawa kokarin da hukumomin tsaron ke ci gaba da yi,...
Manjo Janar Hatami: Nasarar da gwamnatin Musulunci ta samu kan makiya yahudawan sahayoniyya wata babbar nasara ce ga al’ummar Iran Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa: Dakarun tsaron sama na sojojin Iran sun cimma wani gagarumar nasara a yakin da suka yi da makiya yahudawan sahayoniyya. A wata ganawa da iyalan shahidi Kanar Bostan Afrouz, Manjo Janar Hatami ya kara da cewa: Makiya sun kasa cimma tsare-tsare da shirye-shiryensu da suka rigaya sukaaniyar cimmawa, kuma sun fuskanci mummunar martani da shan kashi. Ya ci gaba da cewa: Nasarar da gwamnatin Musulunci ta samu kan makiya yahudawan sahayoniyya duk da karfin soja da kudi da suke da su, baya ga bayanan sirri da suke tabbatar...
Wani manazarci na Amurka ya bayyana sansanonin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da Iran ta kaiwa hare-hare Wani manazarci Ba’amurke ya tattara jerin sansanonin da Iran ta kai wa hare-harer a wata makala inda ya bayyana cewa: Iran ta samu nasara a yakin da ta yi da ‘yan sahayoniyya. Wani mai sharhi kan harkokin siyasa da ke zaune a birnin Washington Mike Whitney ya yi nazari kan dalilan da ba a bayyana dalilan da suka sa Iran ta yi nasara kan haramtacciyar kasar Isra’ila ba a yakin kwanaki 12 a wani bincike da ya gudanar. Yana mai cewa; “Me yasa ba zato ba tsammani gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta amince da tsagaita bude wuta da Iran?” Whitney ta rubuta a cikin...
Sanarwar ta ƙara da cewa mutane 3,824 da suka yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin jiha sun samu N7,960,162,598.64, yayin da 4,833 daga ƙarananan hukumomi aka tantance kuma an biya su N5,983,876,606 a matsayin garatuti. A jimlace, an biya N13,944,039,204.64 a matsayin kuɗaɗen garatuti. Gwamna Lawal bayan ya karbi rahoton ya ce gwamnatinsa ta ba da fifiko wajen daidaita biyan haƙƙoƙin ma’aikatan gwamnati, musamman waɗanda suka yi ritaya bayan shekaru 35 suna aiki kuma suka kai shekaru 60. “Gwamnatinmu ta gaji sama da Naira Biliyan 13 a matsayin bashin kuɗaɗen garatuti na waɗanda suka yi ritaya daga Jiha da Ƙananan Hukumomin daga 2011 zuwa 2023, jinkirin ya jawo wahalhalu, kuma wasu da suka yi ritaya sun mutu su na...
Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi furuci da cewa Iran ta kai hare-hare kan cibiyoyin sojojinta Wani jami’in sojan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci a ranar Talata cewa; Hare-haren da Iran ta kai a watan da ya gabata sun afkawa wuraren sojojin mamayar Isra’ila, matakin da tuni duniya ta amince da kai irin wadannan hare-hare kan cibiyoyin sojin mamaya. Jami’in da ke magana da kamfanin dillancin labaran Reuters, ya ki bayar da karin bayani, ciki har da gano wuraren da abin ya shafa ko kuma irin barnar da harin ya yi ga kayayyakin aikin soja. Iran ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki kan haramtacciyar kasar Isra’ila a watan da ya gabata...
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC shiyyar Ilorin ta kai wa daliban makaranta yakin da ta yi da cin hanci da rashawa domin fadakar da su illar cin hanci da rashawa. Da yake jawabi ga dalibai a makarantar Nursery da Primary School, Tanke, Ilorin, Shugaban Sashen Hulda da Jama’a, Daraktan Hukumar EFCC, Ayodele Babatunde, ya ilmantar da daliban a kan ma’anar cin hanci da rashawa, daban-daban da illolinsa da yadda kowa da kowa, ciki har da yara, za su iya bayar da tasu gudunmuwar wajen gina Nijeriya mara cin hanci da rashawa. Ya ce cin hanci da rashawa yana yin abin da bai dace ba ne, musamman idan ya shafi wasu...
Mai magana da yawun matatar Dangote, Mista Anthony Chiejina, ya tabbatar da rage farashin a Legas. Ya ce, “Farashin man fetur ya ragu daga Naira 840 zuwa Naira 820 kan kowace lita.” Ya bayyana cewa rage farashin da aka yi a baya zuwa Naira 840 ya faru ne sakamakon hauhawar farashin ɗanyen mai a duniya sanadiyyar rikicin da ya auku a Gabas ta Tsakiya. Kamfanonin da ke haɗa kai da Dangote irin su MRS, Heyden, Ardova (AP), Hyde, Optima, da Techno Oil za su fara sayar da fetur a sabon farashin. Haka kuma, wasu sabbin kamfanonin da ke dillancin mai sun shiga jerin masu rarraba man Dangote. Kamfanonin sun haɗa da: TotalEnergies, Garima Petroleum, Sunbeth Energies, Sobaz Nigeria Ltd., Virgin...
Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’o’i ta Nijeriya (JAMB) ta amince da maki 150 a matsayin mafi ƙanƙantar makin da za a bai wa ɗalibai guraben karatu a jami’o’in ƙasar. Hukumar ta ɗauki matakin ne a taronta kan tsarin bayar da guraben karatu na 2025 da ta gudanar a babban ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja. An ceto mutum 6 daga hannun masu garkuwa a Kebbi Gwamnatin Tinubu na shirya mana zagon ƙasa — ADC Haka kuma, ta ce mafi ƙanƙantar maki ga kwalejojin koyon aikin jinya shi ne 140, yayin da ta ƙayyade makin samun gurbin kwalejojin ilimi da na koyon aikin noma a 100. Alƙaluma dai sun tabbatar da cewa an samu gagarumar faɗuwa a jarawabar...
Kakakin dakarun rundunar Izzudden-Qassam ya bayyan cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun tarwatsa wani mutum-mutumi da sojojin mamayar Isra’ila suka makare da harsashai dauke da makami mai linzami a lokacin da ake shirya shi A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kakakin rundunar sojin Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas Abu Obeida, ya yi bayyana cewa: ‘yan gwagwarmaya sun nuna jarumtaka wajen tunkarar makircin ‘yan mamaya mai sarkakiya a gwagwarmayar Beit Hanoun, inda suka kara raunana martabar sojojin mamaya tare da rusa makircinsu.. Kakakin rundunar sojin Qassam Abu Obeida, ya kara da cewa: Hadadden aikin na Beit Hanoun wani karin mataki ne da ‘yan gwagawarmaya suka dauka na raunana makiya tare da rusa martabar sojojin mamayar Isra’ila. Yana...
Kamfanin jirgin sama mallakar jihar Enugu, wato Enugu Air, ya fara aiki a hukumance ranar Litinin bayan ƙaddamar da shi a filin jirgin sama na Akanu Ibiam, Enugu. Mutane da dama sun halarci bikin ƙaddamarwar tare da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, da sauran manyan baki da suka halarci bikin ƙaddamarwar. APC Ta Tafka Asara, Wani Jigo Ya Fice A Enugu Masu Gida Sun Yi Ruwan Kwallaye A Enugu Enugu Air wani ɓangare ne na hangen nesa da ƙudurin Gwamna Peter Mbah, don inganta harkar sufuri da mayar da Enugu cibiyar jiragen sama a Nijeriya. Kamfanin ya fara aiki da jirage uku na Embraer E170 da E190, wadanda suka dace da zirga-zirgar cikin gida. Jirgin zai fara tashi tsakanin...
Saboda matsin lamba na doka da kuma la’akari da mahimman batutuwan siyasa, ya zama dole Gwamnatin Jihar Bauchi ta dakatar da duk wani ci gaba na aikin kwamitin da aka kafa a ranar 4 ga Yuli 2025 domin duba yiwuwar ƙirƙirar sabbin masarautu ko sauye-sauye ga tsarin majalisun gargajiya—musamman a yankunan da har yanzu ke fuskantar shari’a a kotu. Ci gaba da wannan lamari mai sarkakiya alhali wasu muhimman ƙarar shari’a na ci gaba a kotuna, ba wai kawai zai saɓa wa kundin tsarin mulki da ikon shari’a ba, har ila yau, zai iya haddasa tayar da jijiyoyin wuya a cikin al’umma, musamman a yankunan da ke da tarihi na rikice-rikicen ƙabilanci kamar Tafawa Balewa da kewaye. Wannan kira na...
Wani malamin addinin musulunci a jihar Zamfara, Sheikh Mohammed Tukur Sani Jangebe, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Zamfara da su gaggauta gudanar da kananan gyare-gyare daga mahadar Maru –Mayanchi – Maradun, da ke kan hanyar zuwa wani yanki na karamar hukumar Talata Mafara. Ya ce mummunan yanayin hanyar yana ci gaba da haifar da babban kalubale ga matafiya tare da fallasa su ga hare-haren ‘yan bindiga a kan hanyar. Sheikh Jangebe ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilin gidan rediyon Najeriya a Gusau babban birnin jihar Zamfara. Ya bayyana cewa babbar hanyar Maru zuwa Talata Mafara ta samar da ramuka sama da dari, wadanda ke hana zirga-zirgar ababen...
Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa (NHRC) a jihar Kano ta ce ta samu rahoton laifuka 351 na take hakkin yara daga cikin jimillar kararraki 446 da ta samu daga watan Afrilu zuwa Yuni 2025. Kodinetan NHRC na jihar Kano Alhaji Shehu Abdullahi ne ya bayyana haka a Kano. Ya bayyana cewa daga cikin jimillar korafe-korafe 446 da aka samu a cikin watanni uku 351 na da alaka da take hakkin yara. Ko’odinetan jihar ya yi nuni da cewa, sauran shari’o’in sun hada da tashin hankalin gida 19, 18 da suka shafi ‘yancin tattalin arziki da zamantakewa, da kuma biyar da suka shafi ‘yancin rayuwa. “cikin zarge zargen har na Maita da sauran shari’o’in da...