2025-06-29@19:40:20 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6153
«cutar Sikila»:

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Al’ummar Iran Masu Juriya Za Su Tsaya Tsayin Daka Waje Kare Hakkinsu
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe a kan duk wanda ya nemi juya akalarsu. Araqchi ya rubuta a cikin shafinsa na yanar gizo a dandalin sada zumunta na X cewa: “Har yanzu, al’ummar Iran masu girma sun nuna wa duniya karfinsu da juriyarsu.” Ya kara da cewa: Karfin kadawar guguwar masu kishin kasa da suka fito kan tituna domin karrama shuwagabannin soji da suka yi shahada, malamai, masu bincike, da ‘yan kasa, ciki har da mata da kananan yara...

Shugaban Majalisar Dokokin Jama’ar Kasar Mexico: Tunanin Raya Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ga Dukkan Bil’adama Da Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Ya Kayatar
Shugaban majalisar dokokin jama’ar kasar Mexico Sergio Carlos Gutiérrez, ya bayyana yayin da wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ya zanta da shi a kwanakin baya cewa, tunanin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama da shugaba Xi Jinping ya gabatar ya burge shi matuka. Ya ce, an gabatar da tunanin don tattauna yadda sassan kasa da kasa za su zauna tare, da taimakawa juna, da amincewa da bambance-bambance a fannonin tattalin arziki, da yawan mutane, da yankunan kasa a tsakanin kasashen duniya, da sa kaimi ga maida bambance-bambance su zama hanyar dinkewa da juna, da kuma samar da kyakkyawan yanayin zaman rayuwar al’ummun kasa da kasa. Kana yana fatan jama’ar kasashen duniya ciki...
Manjo Janar Mousawi ya bayyana cewa: Suna shakka da kokwanto kan gaskiyar tsagaita bude wuta shin za ta dore kuwa tsakaninsu da ‘yan sahayoniyya Babban hafsan hafsoshin sojin kasar Iran ya yi gargadin gazawar yarjejeniyar tsagaita bude wuta, yana mai nuni da rashin kwarin gwiwa kan kudurin makiya na cika alkawuran da suka dauka. A wata tattaunawa ta wayar tarho da ministan tsaron kasar Saudiyya Yarima Khalid bin Salman, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Seyyed Abdurrahim Mousawi ya bayyana cewa: Harin da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kaddamar kan kasar Iran ya zo ne duk da kamewa da kai zuciya nesa da Iran take yi, kuma a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa ba na...
Hasarar da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi a hare-haren da ta kai wa kasar Iran ya kai dala biliyan uku Kafar watsa labaran Bloomberg ta Amurka ta yi kiyasin cewa: Hasarar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a yakin da ta yi da Iran ya kai kusan dala biliyan 3, saboda gyaran gine-gine da suka lalace da kuma biyan diyya ga kamfanoni. Kafar ta Bloomberg ta bayyana a cikin wani rahoto cewa: Hasarar da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi na nuni da irin yadda Iran ta kutsa kai cikin tsaron Isra’ila a cikin kimanin makonni biyu da harba makaman masu linzami kan yankunan kasar. Jaridar Amurka ta rawaito wani jami’in gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yana cewa: “Wannan shi ne...
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun sake yi wasu sabbin kutse a yankunan Quneitra na kasar Siriya Rahotonni sun bayyana cewa: Da sanyin safiya ne sojojin mamayar Isra’ila suka kutsa cikin yankunan garin Saida da kuma kauyen Abu Mathra da ke yankin kudancin Quneitra na kasar Siriya. Wannan ya zo daidai da wani sintiri da sojojin mamayar Isra’ila da ke ci gaba da yi a kauyen Kodna da ke cikin karkarar Quneitra, ba tare da wata arangama ko gargadi daga mahukuntan Siriya ba. Ana ci gaba da yin shiru a hukumance dangane da irin wadannan tsauraran matakan da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a kan iyakar kasar da tuddan Golan na Siriya da ta mamaye, lamarin da ya sanya ayar...
Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya bayan shafe shekaru 30 suna rikici Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, shekaru talatin bayan rikicin da ya barke a shekara ta 1994 da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane daga bangarorin biyu. An rattaba hannu kan takardar ne a gaban sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ministar harkokin wajen Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Teresa Kayumba, da na Rwanda Olivier Nduhungirehe. Yarjejeniyar da Amurka da Qatar suka wakilci shiga Tsakani ta hada da tanade-tanade kan mutunta yankunan kasa, haramta ayyukan soji, kwance damarar makamai da hadewar kungiyoyin da ba na gwamnati ba, da kuma samar da wani tsari na hadin gwiwa don daidaita...
Kakakin ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ya ce kasarsa na adawa da duk wata yarjejeniyar yafe haraji da Amurka za ta kulla da wata kasa, wadda ka iya illata moriyar Sin, tare da baiwa kasar da aka kulla yarjejeniyar damar samun yafiyar haraji daga Amurka. Kakakin wanda ya bayyana hakan a jiya Asabar, lokacin da yake amsa tambayar da manema labarai suka yi masa, dangane da tattaunawar cinikayya da Amurka ta yi tare da wasu kasashe, ya ce, idan an samu aukuwar irin wannan yanayi, kasar Sin ba za nade hannu ba, za ta dauki matakai na martani domin kare halastattun hakkoki da moriyarta. Jami’in ya kara da cewa, tun watan Afrilun da ya gabata, Amurka ke ta ingiza matakan...
Wannan ne ma dalilin da yasa wasu ke ganin hadakar za ta iya yin karfi kwarai da gaske, kasancewar ta samu wakilci a sassa daban-daban na wannan kasa. Dalili kuwa shi ne, ‘yansiyasa ne da a baya suka samu damar rike manya-mnyan mukamai, sannan kuma har zuwa yanzu yana da tasiri a fagen siyasar kasar yadda ya kamata. Manya-manyan jiga-jigan da ake gani a cikin wannan sabuwar tafiya ta hadakar jam’iyyar sun hada da: Jagoran adawa a kasar, wanda a baya ya sha yin takarar shugabancin kasa, sannan kuma ko a shekarar 2023 shi ne ya zo na biyu bayan da ya samu kuri’a kusan miliyan bakwai. Alhaji Atiku Abubakar, wanda a yanzu dan jam’iyyar PDP ne; ya kasance guda...
Jam’iyyar PDP a Jihar Kebbi, ta bayyana shirinta na haɗa kai da sauran jam’iyyu da ƙungiyoyi domin karɓe mulki daga hannun APC a zaɓen 2027, a matakin jiha da kuma tarayya. An bayyana wannan matsaya ne a garin Birnin Kebbi ranar Asabar, yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, inda aka jaddada buƙatar yin sulhu da warware rikicin cikin gida da ke damun PDP. Mutanen Sakkwato na neman ɗaukin gwamnati game da Bello Turji An samu amincewar yi wa Dantata jana’iza a Madina Jigo a jam’iyyar, Ibrahim Mera, ya ce sun amince su haɗa kai da kowa domin a samu nasarar kawar da APC a jihar. “Za mu yi aiki tuƙuru don ganin haɗakar ta yi tasiri. Mun...
Tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya ci-gaban mai hakar rijiya ne ga Nijeriya wadda ke kan gaba wajen fitar da mai ta yadda za ta samu makuddan kudin shiga sai dai gagarumar matsala ce ga ‘yan kasa wadanda za su fuskanci karin mai a cikin gida wanda zai zama silar karin kunci a dalilin farashin abubuwa da dama da zai hau sama. A cewar masana, Gabas ta Tsakiya da ke samar da akalla kashi 34 na mai a duniya da kashi 18 na gas, gumurzun kasashen biyu ya haddasa farashin danyen mai tashi da kashi 10, yayin da gas ya kara da kashi 7. Haka ma akwai fargabar Isra’ila na iya illata harkokin mai da jigilarsa a mashigar Hormuz...
Al’ummar Ƙaramar Hukumar Isa da ke Jihar Sakkwato, sun roƙi gwamnatin jihar da ta Tarayya da jami’an tsaro da su kai musu ɗauki kan barazanar da ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji ke musu. A farkon makon nan ne aka samu labarin cewa Bello Turji ya bai wa mazauna wasu yankuna a Isa wa’adin gina masa ƙaramin dam ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani. Babu wanda zai manta da gudunmawar da Wike ya ba ni — Fubara An samu amincewar yi wa Dantata jana’iza a Madina Har ila yau, ya umarce su da su bar garuruwansu, domin ba ya buƙatar ganinsu a wajen. Wani mazaunin yankin, Wanzami Abubakar Isa, ya bayyana damuwarsa cewa suna zaune garuruwansu kamar baƙi. “Abin takaici...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga mazauna wani kauyen dake yankin Nyingchi na jihar Xizang mai cin gashin kai, da su rungumi akidar ‘yan uwantakar kabilarsu, da samar da yanayin gudanar da rayuwa mai kyau. Shugaba Xi ya yi kiran ne cikin wasikar da ya mayar ga mazauna kauyen, wadda a ciki ya bayyana fatansa gare su, bayan da ya ziyarci kauyen cikin watan Yulin shekarar 2021. Ya ce, bayan fahimtar cewa kauyen ya samu sabbin sauye-sauye a shekarun baya-bayan nan, kuma mazaunansa sun samu karin kudaden shiga, ya yi matukar farin ciki. Shugaba Xi ya kara da cewa, yana fatan karkashin manufofin JKS, mazauna kauyen za su gina yankunan kan iyakoki, tare da kyautata rayuwar al’ummunsu...
Bisa ga sanarwar, wannan wani sashe ne na sabon yunkuri na ba da cikakken ‘yanci ga majalisar kananan hukumomi 774 na kasar nan. Haka kuma a kan gyaran kananan hukumomi, wata kudirin doka da ke neman kirkiro wata hukumar zabe mai zaman kanta ta kananan hukumomi (NALGEC), wanda za ta dunga shiryawa, gudanar da kuma kula da zaben kananan hukumomin, za a kuma gabatar da ita ga ‘yan Nijeriya don yin nazari a taron sauraron jin ra’ayoyin. Wadansu batutuwa da aka fitar a cikin sanarwar da suka hada da kudirin dokoki guda biyu kan tsaro da manufar samar da ‘yansandan jihohi da majalisar tsaro na jihohi don tsara manufofin tsaro na cikin gida a matakin yankuna. “A bangaren gyaran manufifin...
Masanan sun kuma bayyana cewa, kashi 25 cikin 100 na manya a Nijeriya na dauke da kwayar cutar Sikila. Ana bikin ranar Sikilar ne a kowace shekara, ranar 19 ga Yuni, domin wayar da kan jama’a game da cutar da kuma yadda ake sarrafa ta. Wasu iyayen da suka bayyana irin abubuwa na renon yara masu fama da cutar, sun bayyana cewa; ba don an yaudare su da kuskuren sakamakon gwajin da aka yi musu kafin aure ba, da sun kaucewa matsalolin da suke fuskanta a halin yanzu. Wata uwa mai ‘ya’ya uku daga unguwar Dagbana da ke babban birnin tarayya Abuja, ta bayyana wa LEADERSHIP yadda aka ba ta takardar shaidar cewa; ita da maigidanta za su iya yin...
Alhazan da suka hada da wakilan hukumar alhazai, jami’an hukumar jin dadin alhazai ta jiha, malamai, da sauran alhazai, sun bayyana jin dadinsu ga gwamnati da hukumar alhazai bisa irin kulawar da suka samu a lokacin aikin hajjin. Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan isowar mahajjatan, babban daraktan hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa, Ahmed Labbo ya bayyana jin dadinsa bisa nasarar da aka samu na dawo da alhazan jihar Jigawa Nijeriya cikin koshin lafiya. “Mun gode wa Allah da ya dawo mana da alhazan mu lafiya,” in ji Labbo. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
Gwamnatin Saudiyya ta amince a yi jana’iza tare da binne gawar attajirin ɗan kasuwar nan na Kano, Alhaji Aminu Alhassan Dantata. Babban sakataren marigayin, Mustapha Abdullahi Junaid ya ce shirye-shirye sun kammala domin gudanar da jana’iza tare da binne gawar marigayin a garin Madina. A wani saƙo da Mustapha ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa, “AlhamdulilLah an samu amincewar (hukumomi). “Za a ɗauki Aminu Alhassan Ɗantata daga Abu Dhabi zuwa Madina. Za a yi jana’iza gobe da safe in sha Allah.” Aminiya ta ruwaito cewa a safiyar jiya Asabar ce dai attajirin ɗan kasuwar ya rasu a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Amma iyalansa suka jinkirta binne shi domin a cewarsu, suna so ne su cika masa burinsa na...
Tsohon tauraron ƙungiyoyin Manchester United da Real Madrid, Ruud van Nistelrooy ya ajiye aikinsa na horas da Leicester City bisa fahimtar juna. Wannan na zuwa ne bayan da a ƙarƙashin jagorancinsa ƙungiyar ta yi wasanni 27 da ta gaza taɓuka abin a zo a gani a cikinsu, lamarin da ya kai ta ga faɗawa gasa mai daraja ta biyu a Ingila wato Championship. Wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce an cimma matsaya tsakaninta da Van Nistelroy ne bayan tattaunawar da suka yi. A ƙarshen watan Nuwamban da ya gabata, bayan da ta kori Steve Cooper a lokacin da suke matsayi na 16 a gasar Firimiyar bara, Liecester City ta ƙulla yarjejeniya da Van Nistelrooy, kwangilar da ba za...
“Abin da muke son cimma shi ne, a duk shekara mu tabbatar da ganin mun rubanya yawan madarar da ake samarwa kasar a kasar daga tan miliyan 700,000 zuwa tan miliyan 1.4 daga nan zuwa shekara biyar masu zuwa”, a cewar Ministan. “A Nijeriya akwai sama da Shanu miliyan 20.9, Tumaki sama da miliyan 60, Awakai sama da miliyan 1.4”, in ji shi. Kazalika, Minstan ya kara da cewa; burin shi ne ganin an kara bunkasa tattalin arzikin kasar tare da kuma kara samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar. “Ina son fayyace cewa, ba wai batu ne kawai na yawan Shanun da ake da su a kasar nan ba, batu ne na jama’a da samar da ayyukan yi, habaka...
Masu bincike sun gano cewa sojojin HKI sun kashe Falasdinawa akalla 100,000 tun bayan fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara 2023. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kan cewa farfesa Michael Spagat da kuma Khalil Shikaki Bafalasdine masanin masanin fasahar siyasa a Jami’ar London na kasar Burtania suka jagoranci bincike wanda ya kai ga fitar da wannan sakamakon. Labarin ya kara da cewa masu binciken sun kiyasta mutane a gidaje 2000 a birnin Gaza kadai wanda falasdinawa kimani 10,000 suke rayuwa, sannan suka yi lissafi suka kaim ga wannan sakamakon. Bincike ya kara da cewa daga watan jenerun shekara ta 2025 falasdinawa 75,200 sojojin yahudawan suka kashe da makamai, sannan wasu kimani...
Majalisar dokokin tsibirin Corsica a yankin Mediterranean, wacce ta kasance jiha ce a kasar Faransa, ta amince da kasar Falasdinunu a matsayin cikakken kasa mai zaman kanta a MDD. Tsirin dai tana neman samun yanci daga kasar faransa, ta amince da samuwar kasar Falasdinu da kuma yin watsi da HKI a matsayin yar mamaya. Kissan kiyashi mai ban tsoro wanda HKI take yi a zirin Gaza ya tada hankalin mutane da dama a duniya kuma ya shara fagen amincwa da kasar Falasdinu mai zaman kanta. Labarin ya kara da cewa Marie-Antoinette Maupertuis shugaban majalisar dokokin kasar ta Corsican ne ya gabatar da bukatar amincewa da kasar Falasdini a majalisar. Ya ce bisa wasu dokokin MDD kasar Falasdinu kasace mai zaman...
Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof ya bayya shugaban kasar Amurka Donal Trump a matsayin mutum wanda baya iya yin magana guda ya tsaya kanta, mutumtum ne wanda yake tupka da warwara a lokaci guda. Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto kakakin majalisar dokokin yana fadar haka a zaman majalisar dokokin kasar a jiya Talata. Qalibof ya kara da da cewa kalaman da Trump yake fada na kaskanta shugabannin JMI yana daga cikin yakin kwakwale ne da mutanen kasar Iran. Kuma yakamata ya sani, kuma wadanda suke tare da shi su sani mutanen Iran zasu ci gaba da kare kansu su kuma yaki da wadanda suke shishigi a kan kasarsu. Daga karshen yan siyasan makiya...

Faransa Tace Za’a Maida Takunkuman Tattalin Arziki Kan Kasar Iran Idan Taki Yarda Da Yarjeniyar da Trump Yake
Gwamnatin kasar Faransa ta nawa JMI barazana kan cewa idan bata amince da yarjeniyan da Amurka take so ba to za’a sake dawo da takunkuman MDD a kanta. Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Noel Barrot yana fadar haka, ya kuma kara da cewa idan Iran ta ki ta rattaba hannu kan yarjeniyar da gwamnatin shugaba Trump yake so kan shirinta na makamashin Nukliya ba, abinda muke buklata kawai shi ne mu aika da wasika kan a dawoda takunkuman tattalin arziki kan kasar Iran, wadanda suka hada da na makamai, kudade, da kuma fasaha wadanda aka dagesu shekaru 10 da suka gabata. Bayanda Amurka ta fice daga yarjeniyar JCPOA a shekara 2018...
Har ila yau, Maishaddar ya ci gaba da bayyana cewa; dangane da batun da mutane ke yi na cewa, alaka tsakaninsa da jarumi kuma mawaki Umar M. Sharif ta yi tsami, duba da cewa; an daina ganinsa a ci gaban shirin ‘Gidan Sarauta’ da Maishadda ke daukar nauyi, Bashir ya bayyana cewa; wannan magana ko kusa babu kamshin gaskiya a ciki, don ba a ga Umar a shirin ‘Gidan Sarauta’ zango na 4 ba, wannan ba dalili ne da zai sa a yi tunanin ko akwai wata matsala a tsakanina da shi ba, domin kuwa; a duk wani shiri mai dogon zango, akwai lokacin da za a daina ganin jarumi, amma kuma daga baya ya sake bayyana. Bashir ya kara...
Alhaji Ahmad Manga ya ce, “an ɗauki matakin ne da haɗin gwiwar gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya”. Jami’an CPG na Zamfara sun kuma samu goyon bayan dakarun Civilian JTF na jihar Borno, inda suka ƙaddamar da harin a-yi-ta-ta-ƙare na bazata ga maɓoyar ta Bello Turji. Gwamnatin jihar Zamfara ta ce artabun na ranar Litinin da haɗin gwiwar jami’an tsaro suka fara da ɗan fashin dajin tamkar buɗe sabuwar ƙofar ci gaba da yaƙarsa ne. “Alhamdulillahi an tarar da shi har gida nai inda ba a taɓa zuwa ba, kuma ya ga cewa ana iyawa, kuma an isko shi,” inji Ahmad Manga. Ya ƙara da cewa “an kuma buga wuta, an yi nasarori da dama inda aka...
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce za ta yi duk mai yiwuwa domin bankaɗo tushen ɓullar cutar coronavirus da kuma dalilin fantsamarta a sassan duniya. Shugaban hukumar, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana hakan yana cewa duk da faɗi-tashin ƙwararru, har yanzu ba su da wani cikakken bayani kan abin da ya hana su cimma buri kan binciken da suke gudanarwa. Cutar Coronavirus na cikin cutukan da suka fi gigitar da duniya, wadda ba za’a taɓa mantawa da ita a duniya ba, la’akari da yadda ta yi sanadin mutuwar miliyoyin mutane, da kuma tilasta sanya dokar hana shige da fice, matakin da ya tsayar da duniya cak. An dai fara samun ɓullar cutar a yankin Wuhan na ƙasar China a ƙarshen...
Sojojin mamayar HKI suna ci gaba da kai hare-hare a yammacin kogin Jordan, inda a safiyar yau lahadi su ka kutsa cikin wani gida a garin Jenin,kamar kuma yadda ‘yan share wuri zauna su ka kutsa gidan wani bafalasdine a kudancin Nablus. Rahotanni da suke fitowa daga Falasdinu suna cewa; an yi taho mu gama a tsakanin Falasdinawa da ‘yan mamaya a garin Tal a kudancin Nablus. A sansanin ‘yan hijira na Jenin sojojin na mamaya sun tarwatsa wani gida na Bafalasdine wanda ya haddasa tashin hayaki da kuma jin kara mai tsanani a sassa mabanbanta na garin Jenin. Haka nan kuma ‘yan mamayar sun yi amfani da motar Buldoza wajen rusa wasu gidaje a sansanin na Jenin. A makon...
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi Hizbullah ta mika makamanta a cikin wannan lokacin da yaki bai kare ba, kuma HKI tana cigaba da keta tsagaita wutar yaki. Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya bayyana masu tunani irin wannan da rashin Sanya hankali a cikinsa. A jawabinsa na dararen Muharram a jiya Asabar, babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; Nauyi ne da ya rataya a wuya gwamantin kasar ta takawa HKI birki akan keta tsagaita da take yi wanda take kai wa fararen hula hare-hare.” Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Babu yadda za a yi Hizbullah ta ci gaba da Sanya idanu ba tare da iyaka ba, domin...
Kwamandan rundunar Kudus dake karkashin IRGC Birgediya janar Isma’ila Ka’a’ni ya bayyana cewa; Iran ta samu nasara, kuma nasara ce wacce za ta dore da yardar Allah. Birgediya janar Isma’ila Ka’a’ni wanda ya halarci jana’izar shahidan ta’addancin HKI ya bayyana cewa; Daga yanzu zuwa gaba abinda yake gabanmu shi ne ci gaba da samun nasarori. Haka nan kuma ya ce; Idan har aka samu hadin kai, aka yi aiki tare a tsakanin al’ummar kasa, to komai zai tafi daidai.” Birgediya janar Ka’a’ni ya kuma jinjina wa shahidai, yana mai kara da cewa; tafarkinsu zai cigaba da wanzuwa. A lokacin yakin kwanaki 12 HKI ta rika watsa cewa ta kashe kwamandan na rundunar Kudus, lamarin da ya tabbata fargaganda ce.
Kwamitin koli na tsaron kasa a cikin majalisar shawawar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; Saboda yadda hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa ( IAEA) take ci gaba da siyasarta na nuna wariya, ci gaba da aiki da ita ba shi da wani alfanu a wurin Iran. Shugaban kwamitin tsaron kasar a majalisar shawarar musulunci ta Iran Ibrahim Azizi ya bayyana cewa; Karkataccen rahoton da hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa ya gabatar ne ya zama abinda HKI ta fake da shi wajen kawo wa Iran hari na ta’addanci. Azizi ya kara da cewa; Iran ta sha nanata cewa, shirinta na Nukiliya na zaman lafiya ne, kuma yana gudana ne a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman Nukiliya. Ibrahim...
Wani sabon rahoto da Asusun Bayar da Lamuni IMF ya fitar ya ce Nijeriya na mataki na 12 a cikin jerin kasashe mafiya talauci a fadin duniya. IMF ya ce talauci na kara karuwa a cikin kasar da ta dauki shekaru biyu tana kokarin sauya fuskar tattalin arziki, amma kuma take dada fadawa cikin duhu na tattalin arziki. Yadda na hannun daman ’Yar’Adua ya yi tuggun hana ni zama shugaban ƙasa — Jonathan HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Aminu Ɗantata a Kano Jaridar Cable ta ruwaito cewa, Nijeriya tana mataki na 12 a cikin kasashe mafiya talauci bisa la’akari da karfin tattalin arziki a ma’aunin GDP na Dalar Amurka 807 a bana. Kawo yanzu dai shekaru biyu bayan kaddamar da...
Yau Asabar, kwamitin kula da raya kasa da aiwatar da gyare-gyare ta kasar Sin (NDRC), ta ce ta ware yuan miliyan 100, kwatankwacin dala miliyan 13.95, kari kan yuan miliyan 100 da ta ware a ranar Larabar da ta gabata, domin taimaka wa ayyukan agaji a kudu maso yammacin Sin. Mummunar ambaliyar ruwa ta sake dawowa a gundumar Rongjiang ta lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin, lamarin da ya sanya hukumomin wurin sake ayyana matakin koli na tunkarar ambaliya, daga karfe 12:30 na rana a yau. Hukumomi a yankin na kwashe mazauna daga wuraren da lamarin ya shafa. Zuwa karfe 6 na yamma, gundumar ta tsara aikin gaggawa na kwashewa tare da tsugunar da iyalai 11,992 da daidaikun...

An Kaddamar Da Aikin Hadin-Gwiwar Kafafen Yada Labaran Sin Da Kasashen Waje Wajen Watsa Labarai Game Da Jihar Xizang Ta Kasar Sin
Jiya Jumma’a 27 ga watan Yuni ne, aka kaddamar da wani aikin hadin-gwiwar kafafen yada labaran kasar Sin da kasashen waje daban-daban, mai taken “Ziyara a jihar Xizang don tunkarar zamanantarwa” dake karkashin jagorancin cibiyar watsa labarai ta harsunan Asiya da Afirka ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, da ofishin fadakar da al’umma na kwamitin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin reshen jihar Xizang mai cin gashin kai ta kasar, da gidan rediyo da talabijin na jihar, da kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na Qinghai-Xizang na kasar Sin, inda aka gayyaci manyan ’yan jaridu gami da shahararrun masu amfani da shafukan sada zumunta na intanet guda 20, don watsa labarai game da jihar ta Xizang. A...

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Kira Da A Gudanar Da Bincike Kan Wuce Gona Da Irin Amurka Da Isra’ila Kanta
Iran ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kuma a hukumance kan zaluncin ‘yan sahayoniyya da Amurka Mataimakin babban jami’in kula da harkokin kasa da kasa na ma’aikatar shari’a kuma sakataren hukumar kare hakkin bil’adama ta Iran ya yi la’akari da matakin wuce gona da iri na baya-bayan nan da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka yi kan cibiyoyin makamashin nukiliya, da kafofin yada labarai, da cibiyoyin kiwon lafiya na Iran, da kuma wuraren zama, gidajen yari da birane da kauyuka, a matsayin misali karara na keta dokokin kasa da kasa da hakkokin bil’adama. A cikin wata wasika da ya aike wa kwamishinan kare hakkin bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya Volker Türk Nasser Seraj mataimakin shugaban hukumar...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta san mika wuya ba, kuma tana rubuta tarihin mutunci da jinin shahidanta A jawabin da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi bayan halartar jana’izar shahidan Quds ya jaddada cewa: Iran ba ta san ma’anar mika wuya ba, yana mai fayyace cewa tarihi zai shaida cewa Iraniyawa sun zubar da jininsu tare da kin ba da kasarsu da mutuncinsu. Araqchi ya bayyana a shafinsa na Instagram cewa: “Duk da zafi da rashi na shahidansu kwatsam, amma tunaninsu yana nan a cikin zukatan masu hankali, da kuma zukatan al’ummomi masu zuwa, kuma suna sane da yin riko da Imani da hanyarsu, kuma za su ci gaba da bin tafarkinsu.”...

Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Jaddada Cewa: Iran Tana Da Hakkin Tace Sinadarin Uranium A Kasarta
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Iran za ta ci gaba da tace sinadarin Uranium a cikin kasarta Jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya bayyana cewa: Iran tana jaddada matsayinta na cewa dole ne ta gudanar da ayyukan tace sinadarin Uranium a cikin kasarta, yana mai cewa: “Kungiyar masu sa-ido zata iya kasance a Iran, amma ba za ta maye gurbin Shirin Iran na cikin gida ba.” Jakadan Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Irawani a wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Al-Monitor, ya kara da cewa: “Iran ta kasance tana neman mafita ta hanyar lumana don tunkarar matsalolin da ake iya fuskanta...
Darakta Janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA ya bayyana cewa: Ba zai iya tabbatar da cewa Iran na kera makamin nukiliya ba! A wata hira da tashar talabijin ta Faransa LCI, Darakta Janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA Rafael Grossi ya bayyana cewa: Ba zai iya tabbatar da cewa Iran tana kera makamin nukiliya ba. Grossi dai ya fuskanci tambayoyi da kalubale da dama daga mai gabatar da Shirin, kan ko Iran na daf da kera makamin nukiliya? Ya amsa a cikin halin shakku, yana mai cewa a cikin rahoton ya nisanci zargin Iran da kokwarin kera makamin nukiliya domin babu tabbas kan zargin. Da aka tambaye shi ko Iran na kera makamin nukiliya?...
Wani mummunan hatsari ya afku a Masar inda ‘yan mata 18 suka mutu sakamakon fashewar wata motar dakon mai Wani mummunan hatsarin mota ya afku a kasar Masar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mata 18 da direban bas a kan hanyarsu ta zuwa gonar inabin domin girbin inabin. Hatsarin ya afku ne a ranar Juma’a a kan hanyar yankin da ke gundumar Menoufia, bayan wata babbar mota ta yi karo da motar bas din da ke dauke da ‘yan matan 18. Dukkansu sun fito ne daga kauye daya, Kafr El-Sanabseh, a gundumar Menoufia, kuma dukkansu ‘yan kasa da shekara 21 ne. Hotunan wannan mummunan hatsarin da aka yi ta yawo da su a shafukan sada zumunta, sun nuna...

Jakadun Kasa Da Kasa Sun Bayyana Muhimmancin Hadin Gwiwa Wajen Amfani Da Makamashin Nukiliya Ta Hanyar Lumana
A nata bangare hukumar CAEA ta ce za ta hada hannu da hukumar kula da makamashin nukuliya ta duniya IAEA da sauran abokan hulda daga kasashe masu tasowa, wajen inganta kirkire-kirkire da raya makamashin nukiliya. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Masana da jami’ai a Nijeriya, sun yaba wa ci gaba na a-zo-a-gani da karin kuzarin da ake samu a hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Nijeriya, suna masu bayyana kokarin da aka yi zuwa yanzu a hadin gwiwar bangarorin biyu a tafarkin zamanantar da kansu. Masanan sun bayyana haka ne yayin taro na biyu na bayan taron FOCAC da aka yi ranar Alhamis a Abuja, babban birnin kasar. Cibiyar nazarin dangantakar Sin da Afrika dake Nijeriya ce ta shirya taron mai taken “Hada Hannu Wajen Zamanantar da Sin da Afrika da cimma shirye-shirye 10 na Hadin Gwiwa a Cikin Al’ummar Sin da Afrika mai Makoma ta Bai Daya a Ko da Yaushe.” Da yake jawabi, daraktan cibiyar nazarin Sheriff Ghali...
Ya ce yana matuƙar daraja lokutan da suka gudanar tare. Ya roƙi Allah ya bai wa iyalan Dantata da Dangote, Masarautar Kano, da al’ummar jihar da ƙasar baki ɗaya haƙuri da juriyar rashin wannan babban mutum. “Allah Ya jikan shi Ya sa Aljannatul Firdaus makomarsa,” in ji Buhari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mustapha ya ce idan lokaci ya ƙure kuma ba a samu amincewa daga Madina ba, za su dawo da gawar zuwa Kano domin a yi masa sutura. Don haka, har yanzu ba su yanke shawarar ainihin inda za a binne shi ba. Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata ya rasu yana da shekaru 94, kuma mutane da dama sun aike da saƙon ta’aziyyarsu, ciki har da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Alhaji Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso da wasu shugabanni da dama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Ya ci gaba da cewa, Hukumar ta NPA, ta yi kasafin da dara haka, na wannan adadin, musaman ganin cewa, ta na burin, kara inganta ayyukanta, yadda za su yi dai-dai, da yadda ake gudanar da ayyukan, a sauran Tashoshin Jiragen Ruwa na duniya. Shugaban Hukumar ya kuma sanar da cewa, a shekarar 2024, Hukumar ta NPA, kudin shigar da ta yi hasashen Tarawa daga na Naira biliyan 865.39, sun karu zuwa Naira biliyan 894.86. “ Wannan ya nuna yadda Hukumar ta NPA, ta mayar da hankali da kuma kara zage Damtse wajen ganin ta Tarawa Gwamnatin Tarayya kudaden shiga, masu yawa,” A cewar Dantsoho. Shugaban ya kuma bayyana cewa, kudaden shigar da Hukumar ke hasashen Tarawa a shekarar ta...

An Horas Da Kwararrun Ma’aikata Sama Da Dubu 500 Karkashin Hadin Gwiwar Sin Da Sassan Kasa Da Kasa A Fannin Inganta Kwarewar Ma’aikata
Mai magana da yawun hukumar raya hadin-gwiwa da sassan kasa da kasa ta kasar Sin, Li Ming, ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, Sin ta riga ta kaddamar da ayyuka kimanin dubu 15 na inganta kwarewar ma’aikata karkashin hadin-gwiwarta da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sama da 180, inda aka horas da kwararrun ma’aikata fiye da dubu 500 a bangarori daban-daban, al’amarin da ya taimaka wa kasa da kasa samun ci gaba. Kana kuma, akwai ’yan kasashen Afirka da dama wadanda suka yi amfani da manufofi da dabarun kawar da talauci da suka koya a kasar Sin, don taimaka wa ayyukan yaki da fatara a kasashensu. Kakakin ya kara da cewa, tun daga shekaru sama da 70 da...
Duk ana dora alhakin yadda lamarin cinikin Bayi ya bunkasa kan wani mutum dan asalin kasar Birtaniyya da ake kira da suna,John Hawkins. Hawkins shi ne mutumin da ya kara daukaka, bunkasa,da zamanan har da lamarin cinikin Bayi”manufa anan yayi gyare- gyare daga yadda Turawan kasar Fotugal suka fara da barinsa,ya yi masa kwaskwarima,zuwa lamarin kasuwanci mai daraja”. Jiragen ruwa suna tasowa daga Kasar Birtaniya ko kuma Ingila da Bindigogi, Madubi,da kuma Giya,Jiragen na zuwa wani wurin da ake kira da suna inda ake daukar Bayi a kai su kasar ko kasashen da suka saye su, yanzu wurin ana kiransa da suna yankin Neja Delta inda daga can ne kuma za ‘a fara tafiya, har sai sun kai inda zasu...
An yi wa marigayi Alhaji Aminu Ɗantata jana’izar Salatul ‘Ga’ib’ a garin Kano. An yi sallar ne a masallacin Umar bn Khattab da ke kan titin Gyadi-Gyadi. Za a binne Aminu Ɗantata a Madina — Iyalansa Mangu: Gwamnatin Filato ba ta aiko da wakilai don yin ta’aziyya ba — Sarkin Zazzau Sheikh Ibrahim Khalil, Shugaban Majalisar Malamai na Jihar Kano, tare da Sheikh Ibrahim Aminu Daurawa, ne suka jagoranci sallar. Manyan baƙi da dama sun halarci jana’izar, ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, mambobin majalisar zartarwa na Jihar Kano, manyan ‘yan kasuwa da wasu mutane. Aminiya ta ruwaito marigayi Alhaji Aminu Dantata, ya rasu a birnin Abu Dhabi, kuma za a birne shi a Madina...
Albarkacin ranar yaki da miyagun kwayoyi ta kasa da kasa, ofishin dakile miyagun kwayoyi na kasar Sin ya gabatar da rahoton halin da kasar take ciki a wannan bangare, inda alkaluma suka nuna cewa, a shekarar 2024, hukumomi masu alaka sun binciki laifuka masu nasaba da miyagun kwayoyi fiye da dubu 37, da cafke masu aikata laifukan dubu 62, baya ga kama miyagun kwayoyi ton 26.7. Adadin laifuka masu nasaba da miyagun kwayoyi da aka bincika ya ragu da kashi 12.9%, yayin da yawan masu aikata laifukan da aka cafke ya ragu da kashi 5.6% bisa na makamancin lokacin a shekarar 2023. Ban da wannan kuma, Sin ta yi kokarin sauke nauyin dake wuyanta, inda ta shiga a dama da...
Iyalan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata, wanda ya rasu, sun bayyana cewa ya bar wasiyyar cewa a birne shi a Birnin Madina na ƙasar Saudiyya. Majiyoyi daga cikin iyalansa sun bayyana cewa marigayin ya buƙaci a birne shi kusa da uwargidansa a Madina a duk lokacin da ya rasu. Mangu: Gwamnatin Filato ba ta aiko da wakilai don yin ta’aziyya ba — Sarkin Zazzau ‘An kashe ’ya’yana da mijina da ’yan uwana a hanyar ɗaurin auren ɗana’ A gefe guda kuma, Majalisar Malamai ta Jihar Kano ta yi wa marigayin sallar Ga’ib a Masallacin Aliyu bin Abu Talib da ke unguwar Dangi. Cikin wata sanarwa da ta fitar, majalisar ta bayyana cewa za a yi masa sallar ne duk d gawarsa...
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Filato ba ta aiko da wani wakili zuwa Zariya domin yi wa iyalan waɗanda aka kashe a Ƙaramar Hukumar Mangu a Jihar Filato, ta’aziyya ba. Aminiya ta ruwaito, yadda wasu matasa suka farmaki motar wasu ’yan ɗaurin aure su 31, inda suka kashe 13 daga cikinsu. Aminu Ɗantata: Na roƙi Allah kada Ya ba ni abin da mutane ba za su amfana ba Za a yi wa Aminu Ɗantata Salatul Ga’ib a Kano Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da jagoran shugabannin addinai, Tsohon Ministan Matasa da Wasanni Solomon Dalung, ya jagoranci wata tawaga zuwa fadarsa domin yin ta’aziyya. Sarkin ya gode wa tawagar bisa wannan ziyara,...
Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da wani hari da fararen hula’yan ’yan ƙasar suka kai wa sojojinta. An kai wa dakarun rundunar sojojin ko-ta-kwana na Isra’ila hari ne a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan. Yahudawa ’yan share wuri zauna suka kai wa sojojin na Isra’ila harin ne a yayin da sojojin ke aiwatar da wani samamen tare da yin kame a yankin, mai suna Kafr Malek. Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce, “fararen hula ’yan Isra’ila sun yi wa jami’an ruwan duwatsu tare da cin zarafin sojojin ta jiki da ta baki, ciki har da kwamandan rundunar.” Yunwa ta kashe yara 66 a Gaza ‘An kashe ’ya’yana da mijina da ’yan uwana a hanyar ɗaurin auren ɗana’ Yadda aka...
Nasarar da kungiya ta samu a matakin rukuni za a ba ta Dala miliyan biyu, canjaras kuma miliyan daya, wadda ta cinye kofin kuma za ta samu ladan Dala miliyan 40. Ganin yadda kungiyoyin Turai suka mamaye gasar, Afirka na fatan samun karin dama a nan gaba, ma’ana a Karara nahiyar Afirka yawan kungiyoyin da za su dinga wakiltar ta. Wasu na fatan kungiyoyin Afirka da ke cikin gasar za su ja hankalin duniya zuwa nahiyar ko da kuwa gasarta ta zakaru ba ta iya yin hakan ba, da kuma kawo musu kudi idan aka kwatanta da takwarorinsu. Sabuwar gasar African Footbal League da hukumar CAF ta kaddamar a 2023 ba a sake yin ta ba, duk da irin rigingimun...
– Lokacin: Asabar 2:00 na rana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Har yanzu dai gwamnatin Syriya ba ta komai ba game da barna da hasarar rayuka da makamai da kuma jiragen da ake amfani da su da ta sararin samaniyarta ke haifarwa ba. Shafin Intanet na kafar Enab na kasar Syria ya wallafa wani labari a ranar 15 ga watan Yuni game da shirun da gwamnatin Syriya ta yi kan karakainar da jiragen yaki da makamai masu linzami ke yi a sararin samaniyar kasar. Wani mai sharhi ya fada wa Enab cewa gwamnatin Syriya ta yanke shawarar tsayawa tsakiya kan lamarin ne kasancewar tana daukar Isra’ila da Iran a matsayin abokan gabarta. Ya ce: “Babu daya daga cikinsu da za ka bayyana shi a matsayin abokin al’ummar Syriya, kuma dukkaninsu sun...
Mahaifin angon da ’yan uwan angon na jini da danginsa na daga cikin mutane 13 da aka yi wa kisan gilla a hanyar ɗaurin auren ango, inda aka ƙona gawarwarkin wasunsu a cikin motar da ta ɗauko su, a yankin Mangun da ke ƙaramar Hukumar Mangu ta Jihar Filato. Mahaifiyar angon, Malama Faji Sani da ke zaune a ƙauyen ɗan Bami Anguwar Rimi a ƙaramar Hukumar Kudan ta Jihar Kaduna, ta shaida wa Aminiya cewa mijinta da ’ya’yanta biyu da ƙannenta biyu da kuma kishiyarta, na cikin mutanen da aka kashe su a harin na ranar Juma’a da dare. Ta ce mijin nata, Alhaji Sani, wanda da shi suka dogara, ya rasu ya bar ’ya’ya 13 da jikoki da dama....
Iran ta gudanar da gagarumin jana’izar tare da karramawq ga kwamandojinta da masana kimiyyar nukiliya da wasu ’yan kasar da Isra’ila ta kashe a yankin kwana 12 da aka gwabza a tsakanin ƙasashen. Iran ta shirya gagarumin jana’izar a ƙwaryar birnin Tehran kwana huɗu bayan Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da ɓangarorin biyu ke iƙirarin nasara a yaƙin da aka fara ranar 13 ga Yuni, 2025. A safiyar Asabar daruruwan dubban mutane ne suka fito ɗauke da tutocin ƙasar suna wake-waken jinjina domin karrama kwamandojin da suka kwanta dama a wurin jana’izar. Mutanen sun kuma riƙa daga hotunan mamatan a matsayin waɗanda suka yi mutuwar shahada, a yayin da suke la’antar Isra’ila da Amurka. Daga cikin...
A safiyar yau ne aka gudanar da tattakin jana’izar shahidai kimani 60 a nan Tehran, wadanda suka hada da kwamandojin sojojin kasar da da masana fasahar Nukliya da sauran mutane maza da mata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto cewa, an fara tattakin Jana’izar ne daga danganlin inkilabi ko juyin juya hali har zuwa dandalin yenci dake tsakiyar birnin na Tehran . Ana dauke da gawakin shahidan rufe da tutan Iran a cikin akwatuna. Daga cikin manya-manyan bakin da suka halarci tattakin har da shugaban kasa Dr Masoud Pezeshkiyan da kuma wasu ministocinsa . A ranar 13 ga watan Yuni ne HKI ta fara kaiwa kasar Iran yaki inda ta kashe mutane da dama daga daga ciki...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, yana daukar shugaban hukumar makamashin Nukliya ta duniya IAEA Rafael Grosi a matsayin wanda ya ingiza HKI kaiwa kasar Iran hare-hare a ranar 13 ga watan Yuni. Ya kuma kara da cewa, Grossi a halin yanzu ya matsa yana son zuwa kasar Iran don ya dubi irin barnan da Amurka ta yiwa cibiyoyin nukliyar kasar Amma Iran ta ce ba zata bashi daman haka ba. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na X ya kuma kara da cewa tuni majalisar dokokin kasar suka jingije aiki da hukumar saboda halayen munafursi na shugaban hukumar ta IAEA zuwa lokacinda Iran ta fahinci cewa...

Jiniyoyin Gargadi Sun Tashi A HKI A Lokacinda Mayakan Ansarallah Suka Cilla Makamai Masu Linzami Kan Kasar
An ji karar jiniyoyin gargadi a wurare da dama a HKI suna tashi bayan sun hango malamai masu linzami wadanda sojojin Yemen suka cilla daga kasar zuwa haramtacciyar kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kafafen yana labaran yahudawan na cewa sun yi shirin kakkabo makaman kafin su isa. Amma basu bada rahoton yawan barnan da makamai suka yi ba bayan shigowarsu haramtacciyar kasar. Yahudawan sun bayyana cewa an ji karar jiniyar gargadi a yankunan Beersheba, Dimona da kuma garuruwan da suke kewaye da su a safiyar yau Asabar. Majiyar sojojin kasar Yemen sun bayyana cewa sun cilla makaman kan haramtacciyar kasar Isra’ila ne saboda ci gaba da kissan kiyashin da take a zirin gaza.
Gwamnatin kasar Iran ta kai korafi a gaban hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD dangane da yakin da HKI da kuma Amurka suka kaiwa kasar na tsawon kwanaki 12, wanda yayi sanadiyyar rasa rayukan mutane fiye da 600. Nasir Siraj wani jami’in ofishin jakadancin Iran a MDD ya mikawa kwamitionan hukumar Volker Türk a jiya Jumma’a . Kafin haka dai ministan kiwon lafiya na kasar Iran ya bayyana cewa mutane 627 suka rasa rayukansu a yayinda wasu 4,870 suka ji rauni a yakin kwanaki 12 wanda wadannan kasashe biyu suka keta hurumin sararin samaniyar kasar. Yakin ya zo karshe ne bayan da HKI ta shelanta tsaida yaki ita kadai. Korafin ya bayyan cewa abinda wadannan kasashe biyu suka yi...
Iran ta gudanar da gagarumin jana’izar tare da karramawq ga kwamandojinta da masana kimiyyar nukiliya da wasu ’yan kasar da Isra’ila ta kashe a yankin kwana 12 da aka gwabza a tsakanin ƙasashen. Iran ta shirya gagarumin jana’izar a ƙwaryar birnin Tehran kwana huɗu bayan Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da ɓangarorin biyu ke iƙirarin nasara a yaƙin da aka fara ranar 13 ga Yuni, 2025. A safiyar Asabar daruruwan dubban mutane ne suka fito ɗauke da tutocin ƙasar suna wake-waken jinjina domin karrama kwamandojin da suka kwanta dama a wurin jana’izar. Mutanen sun kuma riƙa daga hotunan mamatan a matsayin waɗanda suka yi mutuwar shahada, a yayin da suke la’antar Isra’ila da Amurka. Daga cikin...
Kasashen Kenya da Tanzaniya da kuma Uganda sun gabatar da kasafin kudin da ya mayar hankali kan zabuka da tattalin arzikin kasashen. Galibi kasafin kudin kasahen Afirka kan mayar da hankali wajen cimmma muradunsu na tattalin arziki da ci gaba. Kasafin kudin kasashen Afirka na 2025 na kunshe da muradun ci gaba da bunkasar abubuwan more rayuwa da kuma ingantuwar al’amuran yau da kullum a kasashen. Kunshin kasafin kudin kasashen Afirka na 2025 ya ware gagarumin kaso a fannin inganta abubuwan more rayuwa da ayyukan kyautata rayuwar al’umma da kuma bunkasa tattalin arzikin kasashen. Kowace shekara kasashen Afirka na ware makudan kudade a kasafin kudadensu. A wannan makala mun zakulo kuku kasashen Afirka 10 da suka fi girman kasafin kudi,...

Indomie Ta Kaddamar da gangamin “Ingantaccen Abinci Domin Nasara” Don Daukaka Abinci Mai Gina Jiki da Murnar samun Nasara
Indomie , shahararriyar kampanin taliyar indomie a Najeriya, ta sanar da kaddamar da sabon gangamin ta mai taken Ingantaccen Abinci Domin Nasara. Wannan gangamin yana jaddada rawar da abinci mai gina jiki kamar Indomie ke takawa wajen ciyar da nasarar iyalai da Karin lafiyar su a Arewacin Najeriya. Shekaru da dama kenan da aka san taliyar Indomie da inganci, daɗi da arha a gidajen ‘yan Najeriya. Tallan talabijin na Ingantaccen Abinci Domin Nasara ya kapu Akan wannan manufa, inda ya ke nuna Indomie a matsayin abokin tafiya wajen cinma nasarar dukkan iyalai na faɗin ƙasa. Nasara Ta Hanyar Abinci Mai Gina Jiki An ƙaddamar da gangamin ne a ranar 6 ga Yuni, 2025, Munaso mu kara jaddada jajircewar Indomie wajen...
“Muna bayar da wannan a matsayin gargadi kai tsaye ga gwamnatin Nijeriya a matakin tarayya da na jihohi. Ka da a bari a zubar da jinin wadannan ‘yan Nijeriya marasa laifi ya tafi a banza.” Shittu, ya lura da cewa hakurin al’ummomin da ake ci gaba da yi wa kisan gilla ba shi da iyaka, ya kara da cewa rashin kamawa da gurfanar da masu aikata laifukan tare da hukuntansu yana nuna gazawar gwamnati. “Muna bukatar a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa, kuma na gaskiya kan wannan kisan kiyashi da kamawa tare da gurfanar da duk wadanda ke da alhakin wannan danyen aikin. “Muna san a biya isasshiyar diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa, haka kuma a...
Allah Ya yi wa hamshakin Attajiri, Alhaji Aminu Ɗantata rasuwa. Alhaji Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekaru 94 bayan fama da rashin lafiya. Ɗaya daga cikin attajirai mafiya arziki a nahiyar Afirka, ya rasu ne a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE.)
Allah Ya yi wa hamshakin Attajiri, Alhaji Aminu Danata rasuwa. Alhaji Aminu Danata ya rasu yana da shekaru 94 a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE)
Wasu daga cikin jami’an sojojin HKI sun yi furuci da cewa, an ba su umarni ne da su rika bude wuta akan Fararen hula Falasdinawa da suke zuwa cibiyoyin karbar kayan agaji, suna jaddada cewa, wadanda su ka kashe din ba su yin wata barazna a gare su. Jaridar “Haarezt” ta ‘yan sahayoniya ta buga rahoton da ya kunshi furucin sojojin nasu da su ka tabbatar da cewa; An ba su umarni ne da su rika harbin duk wanda su ka gani a kusa da cibiyoyin raba kayan abinci. Jaridar ta kuma ce; Sojojin sun yi amfani da kowadanne irin bindigogi da su ka hada da manya wajen harbin fararen hula Falasdinawa. Yawan Falasdinawan da su ka yi shahada a...
Ana neman tono gawar tsohon Gwamnan Jihar Oyo, marigayi Otunba Christopher Adebayo Alao-Akala, domin yin gwajin jini (DNA) da nufin tantance halastattun ’ya’yansa da za su ci gadon dukiyar da ya bari. Batun tono gawar ta kunno kai ne bayan taƙaddama ta yi tsami a tsakanin ’ya’yan tsohon gwamnan a kan rabon gadonsa. Babbar ’yar marigayin mai suna Uwargida Oluwatoyin Alao-Aderinto ce ta shigar da ƙara a gaban Mai Shari’a Taiwo na Babbar Kotun Jihar Oyo ta hannun lauyanta, Oladipo Olasope (SAN), inda ta roƙi kotun ta bayar da umarnin tono gawar mahaifin nasu daga kabarinsa domin yin gwajin ƙwayar halittarsa ga wasu mutane bakwai da ke iƙirarin cewa su ne halastattun ’ya’yan marigayin. Uwargida Aderinto ta shigar da ƙarar...
Tashar talabijin din Aljazira ta bayar da rahoton da yake cewa; Rashin abinci mai gina jiki da karewar madarar jarirai a yankin Gaza, ya sa jarirai biyu sun yi shahada. Majiyar asibitin Nasar ta a birnin Khan –Yunus dake kudancin Gaza, ta ambaci cewa jariran biyu sun rasa ransu ne saboda rashin abinci mai gina jiki da kuma madarar jarirai.
Minsitan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci ya kira yi shugaban kasar Amurka Donald Ttump da ya daina yin maganganun da ba su dace ba akan jagoran juyin musulunci Ayatullah sayyid Ali Khamnei. Abbas Arakci ya kara da cewa; Ko kadan Tehran ba za ta bari wani mahaluki ya ayyana mata makoma ba, idan kuwa har aka kai ta bango ta za ta bayyana hakikanin karfin da take da shi. A jiya Juma’a ne dai shugaban kasar ta Amurka ya yi maganganu na rashin labadi akan jagoran juyin musulunci, sannan kuma ya kara da cewa, zai sake kawo wa Iran hari idan ta koma tace sanadarin uranium. Jamhuriyar musulunci ta Iran dai ta sha jaddada cewa ba za...
Kamfanin Dillancin Labarun “Mehr” ya nakalto cewa; Tun da jijjfin safiyar yau Asabar ne tasoshin jiragen kasa da na safa-safa su ka cika makil da masu son halarta babban filin Juyi na Tehran da can ne zai zama masonin rakiyar shahidan zuwa makwancinsu na karshe. Ana iya ganin dubun dubatar mutane da su ka fito daga kowane bangare na al’ummar Iran domin halartar jana’izar ,yara, mata, masana da kwamandojin soja, wacce ta fara da misalin karfe 8;00 na safiyar yau agogon Tehran. Adadin shahidan da ake jana’izar tasu a yau, sun kai 60, za kuma a rufe su ne a makabartar “Baheshti-Zahra” wacce take kunshe da shahidan juyin juya halin musulunci. A shirnmu na rana za a ji cikakken bayani...
Tallan na talabijin ya bayar da labarin rayuwar Binta, ya kuma mayar da hankali akan irin tasirin da abinci mai kyau ya ke da shi wajen tallafawa iyali. Da labarin ya yi nisa, mun gano Binta tun daga ƙuruciya zuwa shigarta makarantar koyon aikin likitanci. Hakan ya nuna yadda abinci mai kyau da goyon bayan iyali ya ke taka muhimmiyar rawa wajen cin nasara a rayuwa. Binta ta girma tare da cin abinci mai gina jiki ta hanyar cin taliyar Indomie tun da fari. Indomie tun da daɗewa tana da yaƙini kan cewa ciyarwa bai tsaya kawai ga jiki ba ne. Har da taimakawa wajen cikar buri da samar da makomar kowanne yaro zuwa mataki na gaba. Shi ya sa...
Hukumar samar da bunkasa da hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Sin ta gabatar da taron manema labarai a yau Juma’a, inda aka yi karin haske game da yadda Sin take baiwa kasashen Afirka tallafi da samun bunkasa tare da su cikin hadin gwiwa. An ce, ya zuwa yanzu, Sin tana taimakawa kasashen Afirka fiye da 21 a bangaren kimiyyar aikin gona, inda ta tura musu kwararrun aikin gona fiye da 200. Kazalika, bangarorin biyu suna hadin gwiwa wajen gudanar da ayyukan dake da nasaba da na’urorin wutar lantarki da horar da kwararru da habaka da karfinsu da sauran bangarori. Kana suna kaddamar da ayyukan samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, ciki har da samar da...

Sin Da Amurka Sun Tabbatar Da Bayanan Tsarin Aiwatar Da Matsayar Da Aka Cimma Yayin Tattaunawar Cinikayya A Geneva
Tawagogin tattauna batutuwan cinikayya da tattalin arziki na Sin da Amurka, sun kara tabbatar da bayanan tsarin aiwatar da muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma yayin tattaunawar da suka yi ta wayar tarho a ranar 5 ga watan nan na Yuni, da karfafa sakamakon da aka cimma a tattaunawar cinikayya da tattalin arziki da aka yi a Geneva. Kakakin ma’aikatar kula da cinikayya na Sin ne ya bayyana haka yau, inda ya ce an tabbatar da bayanan ne bayan bangarorin biyu sun ci gaba da tuntubar juna bayan tattaunawa mai ruwa da tsaki da suka yi a birnin London a ranekun 9 da 10 ga wata. Ya ce Sin za ta bi tsarin doka wajen sake nazari da...
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya ziyarci iyalan ’yan ɗaurin aure da aka kashe a Jihar Filato. Tun da farko, Hakimin Basawa, Haruna Abubakar ne, ya wakilci Sarkin lokacin da lamarin ya faru, saboda Sarkin ya yi tafiya. Bom ya kashe mutum hudu da raunata 21 a Yobe Ganduje ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar APC Sarkin, ya bayyana baƙin cikinsa bisa wannan mummunan lamari, inda ya roƙi iyalan da su ɗauki wannan a matsayin ƙaddara. Ya yaba da yadda suka yi haƙuri kuma suka bar komai ga hukuma, ba tare da ɗaukae doka a hannunsu ba. Sarkin ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kaduna na ƙoƙarin ganin an bi wa waɗanda abin...
A yau Jumma’a 27 ga watan Yunin ne a hukumace aka bude hanyar jigilar kayayyaki ta kasa da kasa da za ta rika aiki a kai a kai, daga Urumqi, yankin jihar Xinjiang ta kasar Sin zuwa Addis Ababa na kasar Habasha. Wannan kuma ita ce hanyar jigilar kayayyaki ta farko daga Xinjiang zuwa Afirka da kuma tasowa daga can. Hanyar jigilar kayayyakin daga Urumqi zuwa Addis Ababa na gudanar da tafiye-tafiye na zuwa da dawowa kowace Litinin da Alhamis. Bude sabuwar hanyar ba wai kawai ya kaddamar da wata hanya ce mai sauri ta yadda ‘ya’yan itatuwa masu inganci da sauran kayayyakin aikin gona na musamman na jihar Xinjiang za su isa Afirka kai tsaye ba ne, har...
Ya kafa cibiyar ‘Yakubu Gowon Centre’, wadda da farko ta maida hankalinta ne kan zaman lafiya, da raba rigima, daga baya kuma sai ta ta fadada ayyukan da take yi da suka hada da lamarin kula da lafiya, musamman ma yadda za a kawo karshen, cuta mai karya garkuwar jiki, Zazzabin maleriya, da kuma cutar Hanta da aka fi sauran kamuwa da ita. Yanzu cibiyar ta yi hadin gwiwa da Hukumar ci gaban sashen Arewa maso gabas (NEDC) saboda a hana yaduwar cutar Hanta mai saurin kamuwa,a Jihoihn sashen wadanda suka hada da Adamawa,Bauchi, Gombe, Borno, Taraba,da kuma Yobe. Gowon ya ci gaba da kasancewa mai hannu a cikin lamurran da suka shafi zaman lafiya, shirya yin addu’oi saboda kasar...
Kwanan baya, jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Cing-te, ya fitar da wani bayani a fili, inda a ciki ya canja asalin tarihin kasar Sin, kana ya musanta cewa yankin Taiwan wani yanki ne na kasar Sin tun da da can, kuma, ya kauce wa yin tsokaci kan jerin takardun dokoki na kasashen duniya, wadanda suka bayyana yankin Taiwan a matsayin wani yanki na kasar Sin bayan yakin duniya na biyu. Kazalika, ya kalubalanci kuduri mai lamba 2758 na babban taron MDD da dokokin kasashen duniya. Babu shakka, abin da Lai Cing-te ya yi ya sa ya zama abokin gaban dukkan al’ummomin kasar Sin, da yawansu ya zarce biliyan 1 da miliyan 400, kana ya mai da shi kansa...
Aƙalla mutum ɗaya ne aka tabbatar da mutuwarsa tare da wasu biyar suna jinya bayan da wata babbar mota ƙirar tirela ta ƙwace ta kutsa cikin kasuwar Mile Six da ke Jalingo babban birnin Jihar Taraba. Shaidun gani da ido a wurin sun bayyana cewa, duk ƙoƙarin da direban motar ya yi na hana afkuwar lamarin ya ci tura. Ƙudan zuma ya tarwatsa ɗaliban da ke jarrabawar NECO ’Yan sanda sun kama ɓarayi 5, sun ƙwato kuɗi da makamai a Gombe Aƙalla motoci biyu ne suka yi mummunan lalacewa a lamarin. Jami’an Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) da hukumar tsaro ta farin kaya sibil defens (NSCDC) da kuma rundunar ’yan sandan Najeriya (NPF) sun halarci wurin da jajantawa yankin...
Taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na lokacin zafi na Davos, wanda aka gudana a tsakanin ranar 24 zuwa ranar 26 ga watan nan da muka ciki, a birnin Tianjin na kasar Sin, ya samu halartar wakilai kimanin 1800 daga kasashe da yankuna sama da 90, adadin da ya kai koli cikin tarihi. Kamar yadda babban daraktan dandalin Davos Borge Brende ya bayyana, “in muka duba yanayin kasashen duniya, za a gane cewa, wakilai a fannonin masana’antu da kasuwanci na kasashe da dama, suna fatan zuba jari a kasar Sin, tare da zurfafa hadin gwiwar cinikayya dake tsakaninsu da kasar Sin.” A halin yanzu, kasuwannnin kasar Sin suna ci gaba da samun kyautatuwa da karuwa, lamarin da ya samar...
Koyon ilimi ta kafar sadarwa ta zamani yana kara bayyana muhimmancin koyarwa musamman, ma ga wadanda suka dade suna koyon.Akwai samfuna dadama wadanda ake amfani dasu wajen koyarwa wadanda ana tsara su ko shiryasu ne domin su kasance daidai,da fahimtar dalibai.Irin yadda ake bi ko amfani da hanyoyi wajen tabbatar da cewar an samu inganta bunkasar dabaru,kai harma da ci gaba da tunawa da lamarin tattalin arziki domin ci gaban wanda zai taimakawa mutum. Ida ana bukatar damarmakin da za’a fahimci abin ya zahirance,kamata yayi ayi amfani da manhajar da ta dace, ko tayi daidai da bukatun manya wadanda suke wani kamfani. Ta yaya ilimin da ake samun damar mallakarsa zai daidaita yadda rashin shi ke damuwar duniya gaba...
An watsa shirin talibijin mai taken “Yawon bude ido a Tuscany” a Florence na Italiya, da babban rukunin gidan radiyo da talibijin kasar Sin CMG da hukumar yawon bude ido ta yankin Tuscany na Italiya suka tsara da kuma gabatar cikin hadin gwiwa. Shugaban CMG Shen Haixiong da babban jami’in hukumar sun shaida bikin gabatarwar, kuma sun yi musanyar ra’ayi mai zurfi game da daukar shirye-shirye cikin hadin gwiwa da gabatar da albarkatun yawon bude ido da kiyaye al’adu da sauransu. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
Wasu gungun ƙudan zuma sun kai hari tare da tarwatsa ɗaliban da ke rubuta jarrabawar Hukumar da ke shirya jarrabawar kammala sakandare ta ƙasa ta Najeriya (NECO) a makarantar sakandaren kimiyya ta Mairi da ke Maiduguri a Jihar Borno. Wannan hari na ba-zata da gungun ƙudan zumar suka kai ya tilastawa ɗalibai da malaman makarantar tserewa daga harabar makarantar domin neman tsira. Shugaban APC na ƙasa Ganduje ya yi murabus NDLEA ta kafa cibiyar kula da masu shaye-shaye a Yobe Shaidun gani da ido sun ce, sun ga ɗalibai na barin litattafai da takalma da jakunkuna, har ma da kekunansu yayin da suke gudu daga makarantar. A cewar wani ɗalibin da ke jarabawar da ya nemi a sakaya sunansa ya...
Ofishin kula da aikin harba kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ba da labari cewa, jiya Alhamis da karfe 9 da mintuna 29 na dare agogon Beijing, ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20, wato Chen Dong da Chen Zhongrui da Wang Jie sun cimma nasarar fitowa daga akwatin gwaji na Wentian, yin tattaki a waje na tsawon sa’o’i 6.5, da kuma komawa akwatin, bisa taimakon na’urori masu hannun injin dake tashar sararin samaniya da jagorancin masu nazarin kimiyya da fasaha dake doron kasa. Yayin da suke aiki a waje, Chen Dong da Chen Zhongrui sun cimma nasarar hada na’urorin kiyaye tashar sararin samaniya daga sassan wasu na’urorin da aka daddasa a sararin samaniya, da binciken na’urorin dake waje...
Yau Jumma’a da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Senegal Ousmane Sonko da shugaban kasar Ecuador Daniel Noboa a birnin Beijing, fadar milkin kasar Sin. Wadannan shugabannin biyu sun zo kasar Sin ne domin halartar taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na lokacin zafi na Davos. A yayin ganawarsa da Ousmane Sonko, Xi Jinping ya ce, kasar Sin tana son zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Senegal, tare da aiwatar da “Manyan matakai 10 bisa hadin gwiwar abokantaka” yadda ya kamata, da kuma kaddamar da karin ayyukan tallafawa al’umma, tare da sa kaimi ga kamfanonin kasar Sin su zuba jari a kasar Senegal domin raya sabbin makamashi, da gina ababen more rayuwa na...
“Yunwa da talauci ba wai abubuwa ne da suka shafi al’umma ba ne kawai, su ne ke haifar da rashin tsaro, laifuka, tashin hankali, da kuma wargajewar al’umma, wadannan al’amura suna haifar da mugun yanayi, talauci yana haifar da rashin tsaro da rashin tsaro, sannan kuma ya kara zurfafa talauci. “Wadannan yunkurin a bayyane suke ta hanyar kara tallafi ga shirye-shiryen samar da abinci, habaka karfin aiwatar da doka, da ababen more rayuwa don tallafawa samarwa da rarraba noma. “A ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, ONSA, muna ci gaba da hada kai da ayyukan motsa jiki da marasa karfi a fadin rundunonin soja, jami’an leken asiri, hukumomin tsaro, da masu ruwa da tsaki na gwamnati da...
Sojojin Sama sun kai gagarumin farmaki sansanonin ’yan bindiga da ke Jihar Neja a ranakun Laraba da Alhamis. Wannan farmaki na zuwa ne a matsayin ramuwar gayya bayan da ’yan bindiga suka kai hari kan wasu dakarun Najeriya a kwanan nan. ’Yan sanda sun kama ɓarayi 5, sun ƙwato kuɗi da makamai a Gombe Ribas: Duk wani rikici tsakanina da Fubara ya ƙare – Wike A cikin wata sanarwa da rundunar sojin sama ta fitar a shafinta na sada zumunta, ta bayyana cewa an kai harin ne a ƙarƙashin wani shiri da ake kira FANSAN YAMMA, wanda nufinsa shi ne kawar da barazanar da ’yan ta’adda ke haddasawa. Sanarwar, wadda ta samu sa hannun Daraktan Yaɗa Labaran rundunar, Air Commodore...
Duk da haka, a cikin ‘yan shekarun da suka wuce, rashin daidaituwa na jiki ya bayyana. Jami’ai sun fara fitar da takardun tambayoyi domin samun kudi a wasu kwanaki kafin a fara jarabawar, inda ‘yan kasuwa marasa kishi, dillalai, da malalata dalibai suka lalata shirin. Wannan ya gurgunta kyawawan manufofin WAEC da ta bada fatawa da kuma kawo cikas ga ingancin takaddun shaida. Abubuwan da suka faru na baya-bayan nan sun kara jaddada lalacewar tsarin ilimin kasar. Kusan wata guda da fitowar WASSCE, matsalar tsara JAMB ta tilasta wa dubban daliban UTME a jihohi shida da wasu sassan Legas yin jarrabawar bayan an basu maki kadan. Wannan abin takaici ya sa wata daliba da abin ya shafa ta kashe kanta...
Dickson ya goyi bayan buƙatar gudanar da bincike kan jinkirin aiwatar da kasafin yana mai jaddada cewa matsalar ba ta shafi rashin kudi ba tare da kira ga majalisar ta umarci kwamitocin kasafin kudi su gudanar da bincike cikin mako guda su kuma kawo rahoto. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta samu nasarar kama wasu ɓarayin daji da suka addabi garin Bajoga da ke Ƙaramar Hukumar Funakaye. Wannan na daga cikin ƙoƙarin da rundunar ke yi wajen yaƙar masu aikata laifuka a faɗin jihar. Ribas: Duk wani rikici tsakanina da Fubara ya ƙare – Wike NAJERIYA A YAU: Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Hana Mata A Arewa Koyon Ilimin Kimiyya? A wata sanarwa da Kakakin Rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar, ya bayyana cewa an kama mutum huɗu da ake zargi da kai wa wani matashi mai suna Muhammed Ahmed hari, wanda ke zaune a Unguwar Matasa, Bajoga. An ce ɓarayin sun kai masa hari da makami cikin dare, inda suka tsoratar da shi da...
Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya tabbatar da cewa tattaunawar da suka yi da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta kawo ƙarshen duk wata rigima da ke tsakaninsa da Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara. A daren ranar Alhamis ne Shugaba Tinubu, ya jagoranci wani zaman sulhu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, tsakanin Wike da Gwamna Fubara da kuma wasu daga cikin ’yan majalisar Ribas da aka dakatar. NDLEA ta kafa cibiyar kula da masu shaye-shaye a Yobe Tinubu ya rattaba hannu kan sababbin dokokin haraji Bayan ganawar, Wike ya yi magana da manema labarai, inda ya tabbatar da kawo ƙarshen rikicinsa da Fubara. “Dukkaninmu mun amince mu yi aiki tare da Gwamna, kuma...
Ya kara da cewa, babban makasudin kafa cibiyoyin da kudaden jama’a shi ne bunkasa masana’antu, da rage bukatar musayar kudaden waje, da samar da fa’idoji masu yawa ga kasar nan. Idu ya ce IDCs, musamman Cibiyoyin shiyyoyi hudu, sun cika da manyan injina don yada ilimin fasahar masana’antu da fasahar da za su yi tasiri matuka kan yunkurin kasar na samar da masana’antu. Ya bayyana damuwarsa cewa, “A tsawon shekaru, kusan dukkanin IDCs, ma’aikata da kayan aiki a yi asarar su kuma wasu kayan aikin sun daina aiki. “Duk da cewa gwamnatin tarayya ta mika wadannan cibiyoyi ga hukumar kula da masu kananan sana’o’i ta kasa (SMEDAN) tsawon wasu shekaru a yanzu, babu wani abin da aka yi gaba daya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Haka shi ma, shugaban ADC, Cif Ralph Okey Nwosu, ya karyata amincewa da ADA, yana mai cewa batun zama jam’iyya kawance lokaci ya riga ya shude. Ya ce sake bijiro da kawance a hukumance ya faru ne wannan makon, bisa ga shawarar daga dukkan masu ruwa da tsaki. A cewar wani rahoto, NNCG ta yi rajistar ADA a hukumance ga INEC. Wasikar neman rajistar ADA daga INEC an sanya hannu a kai daga shugaban kungiyar na wucin gadi, Cif Akin A. Rickets, da sakataren kungiyar na wucin gadi, Abdullahi Elayo. Hadakar ta kuma gabatar da takardu masu muhimmanci, daga cikin su akwai kundin tsarin mulkin jam’iyyar da aka bayar da manufifinra da tambari da kuma bayanan taron kafa ta. Wasikar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ta bayyana cewa, an kashe ‘yan bindigar da dama yayin wannan gumurzu da ya dauki tsawon wasu awanni ana fafatawa da sojojin. Koda-yake dai a cewar rundunar sojin, an kashe musu wasu daga cikin jami’ansu; yayin musayar wuta da ‘yan bindigar a daidai wancan lokacin. Baya ga haka, rundunar sojin ta kuma kara da cewa; wasu sojoji hudu sun jikkata sakamakon harbin bindiga daga ‘yan ta’addar, amma kuma suna nan suna samun kulawa a asibiti. Har wa yau, rundunar sojin ta kuma bayyana wadanda suka mutun a matsayin cikakkun Jarumai, wadanda suka tsaya tsayin daka, domin kare matsayinsu da kuma mutuncin kasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kafa karamar cibiyar kula da muggan kwayoyi a Damaturu babban birnin jihar Yobe. Kwamandan hukumar a Jihar, Abdulazeez Ogunboye ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Damaturu a wani bangare na bikin ranar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta duniya ta shekarar 2025. Tinubu ya rattaba hannu kan sababbin dokokin haraji Sheikh Dahiru Bauchi ya cika shekara 101 a duniya Ogungboye ya kara da cewa cibiyar wacce tun daga lokacin da ta fara aiki na daya daga cikin nasarorin da hukumar ta samu a jihar. “An shigar da mutane tara da suke ta’ammali da muggan kwayoyi a cibiyar, daga cikin su...
Ya kuma yi watsi da ikirarin da ake yi na cewa ‘yansanda na taimakawa wajen magudin zabe, yana mai bayyana irin wadannan zarge-zarge a matsayin mara tushe, tare da cewa aikin ‘yansanda a lokacin zabe ya takaita ne kawai wajen samar da tsaro da tabbatar da zaman lafiya. “Mu ba ’yan bangar siyasa ba ne, mu kamar alkalan wasa ne, aikin ‘yansanda ya takaita ne kuma ya ta’allaka ga samar da tsaro a lokacin zabe, gwargwadon yadda ya kamata, ba za mu yi zabe ba, jama’a ne za su kada kuri’a, INEC ta kidaya, muna sa ido. “Kuma wannan ita ce matsayarmu, sannan kuma hanyar da za a bi domin cimma nasara ita ce, sake sabunta hadin gwiwa tsakanin hukumomi,...
Misali, a lokutan hare-haren, an kone gidaje da dama, inda wasu ahali ma, wanda yawansu ya kai, har zuwa 15, aka shafe su, daga doron kasa, a lokacin da suke kan bacci, a gidansu. Wasu daga cikin wadanda suka tsallake Rijiya da baya daga hare-haren na ‘yan ta’addar, sun bayyna yadda ‘yan ta’addar, suka cinnawa wasu shaguna da ke a wata kasuwa, da ka mayar a matsayin wajen kwanan, ‘yan gudun hijira, wuta. Duk da kokarin da wasu matasa da kuma kokrin jami’an tsaro na dakile maharani, hakan ya faskare su, hatta wani daya daga cikin jami’in tsaro da aka tura wanzar da tsaro, ya rasa ransa. Duk a 2025, a watan Afiiru an kai hare-hare a Logo da Ukum,...
Daga ƙarshe dai Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sa hannu kan sababbin dokokin haraji guda hudu da a baya suka jawo cece-kuce da zazzafar muhawara a faɗin Najeriya. An dai sanya hannun ne a fadar shugaban kasa ta Aso Rock da ke Abuja ranar Alhamis, inda shugaban ya ce dokokin za su bunkasa harkokin hada-hadar kudade da tattara haraji a kasar. NAJERIYA A YAU: Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Hana Mata A Arewa Koyon Ilimin Kimiyya? Sheikh Dahiru Bauchi ya cika shekara 101 a duniya A kwanan nan ne dai Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da kudurorin su zama doka bayan tafka zazzafar muhawara a zaurukan majalisun guda biyu. Daga cikin waɗanda suka halarci bikin saka hannun akwai Shugaban...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Doctor Zainab Muhammad na daya daga cikin mata a Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da kudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da kalubalen da wasu matan dake yankin Arewa suke bayyanawa suna fuskanta wurin karantar fannin. Doctor Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci daya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba har da mazan ma na kauracewa wannan karatun. Zainab Kwararriyar likita ce wacce ta shahara wurin kula da marasa lafiya a asibitoci. NAJERIYA A YAU: Yadda ‘Yan Najeriya Za Su Kula Da Lafiyar Jikin Su DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi?...