Isra’ila na bincike kan harin dakarunta da ya kashe fararen hula a Gaza
Published: 1st, July 2025 GMT
Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da ƙaddamar bincike a game da harin da dakarunta suka kai kan wata cibiyar intanet da ke yankin Gaza, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ɗimbin fararen hula a jiya Litinin.
Hukumar kare lafiyar fararen hula ta Falasɗinu, ta ce wasu daga cikin makaman da Isra’ila ta harba a jiya Litinin sun faɗa kan kasuwar kwamfuta ta ‘Al-baqa’ da ke gaɓar teku da ke birnin Gaza, kuma a wannan cibiyar kaɗai mutane 24 ne suka rasa raukansu.
Ɗaya daga cikin masu magana da yawun rundunar sojin Isra’ila ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, tabbatas sun kai hare-hare kan wurare da dama da dakarun Hamas ke fakewa don gudanar da ayyukansu a Gaza, to amma sun ɗauki dukkanin matakan da suka wajaba domin taƙaita illolin farmakin ga fararen hula.
Ahmed al-Nayrab, mai shekaru 26 a duniya kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira da rayukansu a wannan farmaki, ya ce lokacin da aka kai harin, akwai ɗimbin mutane da suka haɗa da masu shan shayi da kuma waɗanda suka zo don samun sadarwar intanet.
Ahmed ya ci gaba da cewa, “abin da ya faru a wannan wuri ba ya da bambanci da kisan kiyashi”, yana mai cewa “a duk inda ka duba sassan gaɓoɓi ne da kuma gangar jikunan mutane ne, yayin da wasu daga cikin gawarwakin ke ci da wuta kana wasu ke kwance jina-jina’’.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Falasdinawa Isra ila fararen hula
এছাড়াও পড়ুন:
Wargajewar HKI Ba Makawa Inji Wani Janar Daga Sojojin JMI
Daya daga cikin manya manyan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa wargajewar HKI da kuma halakar Firai ministan kasar tabbas ne babu makawa. Ya kuma gargadi makiyan JMI kan cewa duk wani kuskuren da zasu tabka sai ya sanya dukkan sansanoninsu na soje a yankin cikinbabban barazana na lalatasu.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto , Major General Yahya Rahim Safavi yana fadar haka a taron addu’a da kuma girmma marigayi Manji Janar Muhammad Baqiri babban hafsan hafsoshin kasar wanda yayi shahada a ranar Jumma’a 13 ga watan Yunin da ya gabata.
Ya kuma kara da cewa babban shaitan da kuma karamin shaitan duk zasu halaka sun kasa kaiwa ga bukatunsu a yankin kwanaki 12 da suka dorawa JMI. Janar Safawi wanda kuma ya kasance daga cikin masu bawa jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran ya kara da cewa yakin da ya gabata ya gaggauta halaka da kuma bacewar HKI daga yankin gaban ta tsakiya.
Ya ce, tsagaita wutan da aka amince, dan sararawa ce ga makiya JMI amma su tabbatar da cewa da yardar All…yaki mafi muni yana gabansu.