An Dakatar Da Shugaban APC Na Jihar Nasarawa
Published: 2nd, July 2025 GMT
Shugabannin jam’iyyar APC a matakin gunduma na Gayam, cikin ƙaramar hukumar Lafia, sun dakatar da shugaban jam’iyyar a matakin jiha, Hon. Aliyu Bello. Sun zarge shi da aikata abubuwan da suka saɓa da kundin tsarin mulki na jam’iyyar, musamman sashe na 21 (D)(i–iii), wanda ya haɗa da cin amanar jam’iyya da goyon bayan ɗan takarar wata jam’iyya daban.
Shugaban gundumar, Ibrahim Ilyasu, ya bayyana cewa matakin dakatarwar ya fara aiki nan take, kuma Hon. Bello ba zai iya wakiltar kansa ko amfani da matsayin sa a matsayinsa na mamba na APC daga Gayam ba, har sai an warware batutuwan da aka gabatar. Sun kuma zarge shi da jawo wa jam’iyyar tozarci da keta mutuncinta a idon jama’a.
Haɗakar Jam’iyyun Adawa Ba Ya Ɗaga Mana Hankali – Sabon Shugaban APC Sanusi II Ya Gudanar Da Hawan Nassarawa Duk Da Umarnin ‘Yansanda A KanoSai dai wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar a jihar sun ce wannan matakin wani yunkuri ne daga wani ɓangare na ƙungiyar siyasa da ke ƙoƙarin kifar da Bello daga kujerarsa, musamman bisa alaƙa da wani ɗan takarar gwamna a jihar. Sun ce wannan rikici ya ƙara bayyana rabuwar kai da rikicin cikin gida a jam’iyyar.
A wata ganawa da wasu shugabannin jam’iyyar a Lafia, an kaɗa ƙuri’ar nuna goyon baya da amincewa da shugabancin Hon. Bello, wanda hakan ke nuna cewa har yanzu akwai sassa a jam’iyyar da ke goyon bayansa, duk da dakatarwar da aka sanar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Nassarawa a jam iyyar jam iyyar a
এছাড়াও পড়ুন:
Jirgin Alhazai Na Farko Ya Iso Jihar Jigawa
Alhazan da suka hada da wakilan hukumar alhazai, jami’an hukumar jin dadin alhazai ta jiha, malamai, da sauran alhazai, sun bayyana jin dadinsu ga gwamnati da hukumar alhazai bisa irin kulawar da suka samu a lokacin aikin hajjin.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan isowar mahajjatan, babban daraktan hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa, Ahmed Labbo ya bayyana jin dadinsa bisa nasarar da aka samu na dawo da alhazan jihar Jigawa Nijeriya cikin koshin lafiya.
“Mun gode wa Allah da ya dawo mana da alhazan mu lafiya,” in ji Labbo.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp