Jana’izar Aminu Ɗantata: Abba da Sarki Sanusi sun tafi Saudiyya
Published: 30th, June 2025 GMT
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, tare da Gwamnan Jigawa, Umar Namadi da kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, sun tafi ƙasar Saudiyya domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Ɗantata.
Gwamnan ya jagoranci tafiyar ce domin halarta Sallar Jana’izar a Madina ne, bayan rasuwar hamshaƙin attajirin a birnin Dubai da ke ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a ƙarshen mako.
Kakakin Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawaki tofa ne ya sanar da haka a safiyar Litinin.
A ranar Lahadi Aminiya ta ruwaito cewa hukumomin Saudiyya sun amince da yin jana’iza da binne Alhaji Aminu, Ɗantata a Madina, kamar yadda ya bar wasiyya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Aminu Ɗantata Saudiyya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Uba Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna
A cikin nuna jajircewa da hadin kai tsakanin gwamnati jiha da ta tarayya, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, a ranar Juma’a ya gana da Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, CON, domin yin cikakken bitar aikin titin Abuja–Kaduna–Abuja
Taron, wanda aka gudanar a birnin Abuja, ya nuna irin salon jagorancin Gwamna Uba Sani na jajircewarsa wajen tabbatar da kammala wannan muhimmin titi wanda ke da matuƙar tasiri ga tattalin arzikin ƙasa.
Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan yadda za a hanzarta kammala ɓangaren Abuja–Jere da Kaduna, wanda ke da muhimmanci ga miliyoyin ‘yan Nijeriya da ke amfani da shi kullum wajen sufuri, kasuwanci da hulɗar zamantakewa.
Gwamna Uba Sani ya jaddada cewa wannan titin ba na yankin Arewa kadai ba ne, ya bayyana shi a matsayin jijiyar ƙasa da ƙasa ne wadda ke haɗa yankuna daban-daban tare da ƙarfafa haɗin kai da bunƙasar tattalin arziki.
Ya kara da cewa titin Abuja- Kaduna da Kano na ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙarƙashin Manufar Sabon Fata na (Renewed Hope Agenda), wadda ke nufin sabunta manyan gine-ginen ƙasa da inganta tattalin arziki.
Yace “Wannan titi ba hanya ce kawai ba inda yace wata hanya ce ta tattalin arziki wadda ke haɗa mutane, kasuwanni, da dama a fadin Arewacin Nijeriya da ma bayan haka,”
A nasa jawabin, Sanata Umahi ya yaba wa Gwamna Uba Sani bisa yadda yake kaiwa da komowa domin kare muradun al’ummar Kaduna, tare da tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar kammala aikin cikin lokaci. Ya bayyana cewa an umarci kamfanonin da ke aikin da su rika aiki sau biyu a rana domin hanzarta cigaba ba tare da rage inganci ba.
Ministan ya kara da cewa amfani da fasahar siminti mai ɗorewa wanda zai tabbatar da cewa titin zai dawwama tare da rage kudin gyara nan gaba.
Kamfanonin da ke aikin sun yi alkawarin ƙara gaggautawa musamman a yankin Jere dake jihar Kaduna, inda ake sa ido sosai kan ci gaban aiki. Gwamnatin Jihar Kaduna ta kuma tabbatar da ci gaba da haɗin kai da Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya domin magance ƙalubalen da ke iya janyo tsaiko.
PR: Shettima Abdullahi