An Hori Ma’aikatan Lafiya Su Kara Kokari Wajen Rike Aikin su
Published: 3rd, July 2025 GMT
Shugaban hukumar kula da makarantun kiwon lafiya da bada lasisi ga likitoci kula da lafiya a matakin farko ta kasa Alhaji Dr Bashir Idiris Lifidin Jama’a ya hori ma’aikatan kiwon lafiya a matakin farko da dukkannin masu ruwa da tsaki a bangaren lafiya su rubanya kokari fuskar tabbatar da kwarewa domin inganta ayyukan kula da lafiya a Nijeriya.
Dr. Bashir Idiris Lifidin Jama’a ya yi wannan kiran ne a Katsina lokacin bukin rufe taron karawa juna sani na tsawon kwanaki uku na wannan shekarar wanda aka shiryawa Malaman koyar da darusan kiwon lafiya a matakin farko.
Taron wanda ya samu halartan jami’an kiwon lafiya daga dukkannin jihohin yankin arewa maso yamma, yana da nufin ilimintar dasu ne kan yadda za su rungumi sabbin dabarun aiki irin na zamani dai dai da tsarin dokokin hukumar kula da makarantun kiwon lafiya da bada lasisi ga likitocin kula da lafiya a matakin farko ta Naheriya.
Dr. Bashir Idiris Lifidin Jama’a ya bayyana cewa wajibi ne dukkannin ma’aikatan hukumar da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren lafiya a matakin farko su kara zama masu kwazo tare da yin aiki da sauran dokokin aiki na fasahohin zamani domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Don haka shugaban hukumar ya sake yin kira ga malarta taron su yi amfani da abubuwan da suka koya yadda suka dace domin bunkasa harkokin kiwon lafiya a Naheriya.
Maryam Idris
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jami an Lafiya lafiya a matakin farko kiwon lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Tawagar Likitoci Ta Sin Ta Ba Da Horon Fasahar Likitancin Gargajiya Ta Sin A Nijar
Tawagar likitocin kasar Sin ta 24 wadda ke jamhuriyar Nijer, ta ba da horon fasahar likitancin gargajiya ta Sin a babban asibitin Nijar dake birnin Yamai, wanda ya jawo hankulan mahalarta kusan 50, ciki har da manyan ma’aikatan kiwon lafiya na asibitin, da dalibai daga kwalejin likitanci ta jami’ar Yamai da kuma masu sha’awar likitancin gargajiya na Sin.
Zheng Zhida, shugaban tawagar likitoci ta Sin, ya bayyana a bikin kaddamar da horon cewa, tun bayan kafa cibiyar likitancin gargajiya na Sin dake babban asibitin Nijar, duban-dubatar marasa lafiya sun amfana da ita. Ya ce horon na wannan karo ba darasi ne kawai dake bada fasahohin likitanci ba, wani aiki ne na mu’ammalar al’adu.
A nasa bangare, farfesa Mamane Daou, daraktan babban asibitin Nijar, ya bayyana cewa, wannan horon ya ba da dama mai daraja ga ma’aikatan ba da jinya na asibitin wajen samun zurfin fahimtar likitancin gargajiya na Sin da kuma koyon dabaru masu amfani. Ya ce cikin ‘yan shekarun nan, likitancin gargajiya na Sin ya taimaka sosai ga yawancin marasa lafiya na Nijar bisa fa’idodin da yake da su na sauki da aminci da karancin farashi. A nan gaba, ana fatan karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu don sa kaimi ga kara amfani da fasahar likitancin gargajiya na Sin a Nijar. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp