Darakta Janar Na Hukumar IAEA Ya Ce; Babu Tabbas Iran Na Da Shirin Mallakar Makamin Nukiliya
Published: 28th, June 2025 GMT
Darakta Janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA ya bayyana cewa: Ba zai iya tabbatar da cewa Iran na kera makamin nukiliya ba!
A wata hira da tashar talabijin ta Faransa LCI, Darakta Janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA Rafael Grossi ya bayyana cewa: Ba zai iya tabbatar da cewa Iran tana kera makamin nukiliya ba.
Grossi dai ya fuskanci tambayoyi da kalubale da dama daga mai gabatar da Shirin, kan ko Iran na daf da kera makamin nukiliya? Ya amsa a cikin halin shakku, yana mai cewa a cikin rahoton ya nisanci zargin Iran da kokwarin kera makamin nukiliya domin babu tabbas kan zargin.
Da aka tambaye shi ko Iran na kera makamin nukiliya? Grossi ya amsa da cewa: “Ba zai iya tabbatar da hakan ba, kuma zai zama rashin gaskiya idan aka ce suna shirin kera makamin nukiliya.”
Da yake amsa tambayar da mai gabatar da shirin ya yi danganr da wasu masu kallon Shirin suna kokwanton ingancin harin da aka kai kan Iran: Grossi ya kare hare-haren wuce gona da irin haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka kan cibiyoyin nukiliyar Iran, da ba su kan ka’ida, yana mai cewa akwai yanayi na uku a cikin dabarun kera makamin nukiliya da ake kira “boyayyen shiri” ko “shirin da bai fito fili ba” inda har yanzu Shirin bai kai matakin kera makamin ba, amma ta mallaki dukkan karfin iko da fasahohin da ake bukata, kuma idan lokaci ya yi, za su iya mallaka. Ya kara da cewa Iraniyawa suna da fatawar haramta mallakar makamin nukiliya da sauran makaman kare dangi.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kera makamin nukiliya
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna Ta Bukaci Maniyyatan Aikin Hajjin 2026 Su Fara Biyan Kudaden Ajiya
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta shawarci maniyyata aikin Hajjin shekarar 2026 da su fara shirin biyan kudaden ajiya.
Kiran ya biyo bayan taron da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta gudanar tare da hukumomin Alhazai na jihohi, inda aka bayar da shawarar ajiyar naira miliyan 8 da rabi ga masu niyyar zuwa aikin Hajji, kafin a sanar da hakikanin kudin aikin Hajjin shekarar 2026.
A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi, ya shawarci wadanda ba su da fasfo da su gaggauta zuwa Hukumar Shige da Fice ta Kasa domin yin nasu, yana mai cewa shi ne ake amfani da shi wajen hada takardun tafiya.
Najeriya ta sake samun kujeru 95,000 daga Masarautar Saudiyya domin aikin Hajjin 2026, ana kuma sa ran jihar Kaduna za ta sake samun yawan kujerun da aka saba bata.
Yunusa Mohammed ya kuma bayyana cewa hukumar za ta sanar da maniyyata lokacin da za a fara yin rajista a Jihar Kaduna.
Safiyah Abdulkadir