’Yan Najeriya sun fara begen Buhari saboda azabar TIinubu – Amaechi
Published: 3rd, July 2025 GMT
Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce wahalhalu sun yi yawa a Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, wanda har ya sa mutane suka fara fatan dawowar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.
Yayin da yake magana a birnin Abuja, Amaechi ya ce Najeriya ta taɓarɓare matuƙa, inda ya ce sauyin gwamnati ne kawai zai magance matsaloli.
“Farashi kayayyaki ya tashi sosai. Mutane ba za su iya siyan abinci ba. Babu kuɗi. Komai ya lalace,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa rayuwa ta yi tsanani har mutane sun fara tunawa da zamanin Buhari da muradin dawowarsa kan mulki.
“Yanzu mutane na so Buhari ya dawo. A Najeriya, kowace sabuwar gwamnati tana ƙara muni fiye da ta baya. Wannan shi ne dalilin da ya sa mutane ke ci gaba da tunanin gwamnatin da ta gabata,” in ji shi.
Amaechi ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar APC a daren ranar Talata, inda yanzu ya koma jam’iyyar haɗaka ta ADC.
Ya ce tuni ya daina shiga harkokin jam’iyyar APC tun da daɗewa.
“Na fice daga APC jiya da daddare. Ban halarci taro ko guda ɗaha ba. Na taɓa gargaɗinsu, kuma na rubuta musu kada su sake gayyatata. Ba za ka zauna cikin ƙungiyar da yawancinsu suke satar dukiya ba, kai kuma ka yi shiru,” in ji shi.
Da aka tambaye shi me ya sa yake sukar gwamnatin da ya taɓa yi wa aiki, Amaechi ya ce matsalar Najeriya ba kawai shugabanci ba ne, sai an gyara tsarin gaba ɗaya.
Ya ce akwai bukatar fara shiri, ba kawai kafa jam’iyya ba, wanda zai haɗa ‘yan Najeriya su ƙwato ƙasarsu da hannunsu.
Amaechi ya kuma ce bai taɓa ganin Tinubu a matsayin mutum wanda ya cancanci ya mulki Najeriya ba.
“Na taɓa cewa Tinubu ba shi da ɗabi’u shugabanci. Har yanzu ra’ayina kenan,” in ji shi.
Ya soki yadda gwamnati ke tafiyar da tattalin arziƙi, musamman faɗuwar darajar Naira.
“Lokacin Buhari, dala tana kusa da Naira 460 ko Naira 500. Yanzu ta kai Naira 1580. Wannan ya fi kashi 100,” in ji shi.
Da aka tambaye shi ko wannan matsala ta Naira wata dabara ce ta gwamnati, Amaechi musanta hakan.
Ya ce, “Ko dabara ce ko akasin haka, duk wata gwamnati da ba ta damu da rayuwar mutane ba, ba za a ce dabara ce mai kyau ba.”
Tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, shi ma ya fice daga jam’iyyar APC, inda ya bu sahun Amaechi wajen komawa jam’iyyar ADC.
Ficewarsu da wasu manyan jiga-jigan siyasa na nuni da juyin juya hali kafin babban zaɓen 2027, yayin da jam’iyyar ADC ke neman zama sabuwar babbar jam’iyyar adawa a ƙasar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata 2 bayan ambaliya
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Tun bayan da ambaliyar ruwa ya ci wasu sassan garin Mokwa al’ummar yankin suka faɗa halin neman taimako.
Duk da cewa Gwamnatin Tarayya da wasu ɗaiɗakun mutane sun tallafa wa waɗanda abin ya shafa da kuɗi da ma wasu abubuwa, amma mazauna yankin suna bayyana rashin jin daɗinsu bisa yadda al’amura ke gudana a garin.
Najeriya A Yau: Yadda Za A Kawo Karshen Daukar Doka A Hannu A Najeriya DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi?Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan halin da al’ummar Mokwa ke ciki watanni biyu bayan ibtila’in ambaliyar.
Domin sauke shirin, latsa nan