Sin Na Ci Gaba Da Cika Alkawarin Bude Kasuwarta Ga Duniya
Published: 3rd, July 2025 GMT
Jakadan Pakistan a kasar Sin, Khalil Rahman Hashimi ya ce, “sabuwar dokar ta bayar da karin kariya har ma da wani sauki na musamman ga kamfanoni masu zaman kansu a kasar Sin. Akwai tanade-tanade da dama a kasar Sin wadanda suke bayar da kwarin gwiwa ga kamfanoni masu zaman kansu don su iya bunkasa harkokinsu da kuma ba da gagarumar gudummawa ga tattalin arzikin kasar Sin.
Shi ma jakadan Nepal a kasar Sin, Krishma Prasad Oli ya ce, “dokar ta sahale wa kamfanoni su gudanar da ayyukansu ba tare da wani matsi ba. Akwai babbar dama da aka samu a halin yanzu saboda akwai takamaimiyar doka da ta bayar da damar shigar kamfanonin kasashen ketare cikin hadin gwiwa da kamfanonin kasar Sin kuma suna iya yin aiki tare.”
Tuni dai aka fara ganin alherin sabuwar dokar bisa yadda ’yan kasashen waje ke tururuwar kafa kamfanoni da harkokinsu na kasuwanci a kasar ta Sin. Sakamakon amanna da kafuwar dokar da kuma fara aikinta, an kafa kamfanoni da ’yan kasuwa na kasashen waje suka zuba jarinsu fiye da 24,000 a cikin watanni biyar na bana kamar yadda ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta tabbatar a ’yan kwanakin nan. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: a kasar Sin
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Bawo Mayakan Huthi Fasahar Kera Makamai Masu Linzami Daga Cikin Ruwa
JMI ta bawa kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen makamai masu linzami wadanda ake iya cillasu daga cikin tekuna mai suna Ghadr.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya ce makamai mai linzami samfurin Ghadir wanda ake iya cilla shi daga cikin teku ya shiga hannun sojojin kasar Yemen sannan bisa bayanan wasu kasashen yamma hakan wani hatsari ne ga kasashen Amurka da kawayenta a yankin, musamman HKI.
Makamin wanda ake iya cillashi daga tekun red sea yana yin barna mai yawa ga makaman makiya. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran bata yi wani karin bayani dangane da wannan labarin ba, majiyar ofishin daraktan tsaron kasa na Amurka ta bayyana cewa, JMI tana ta fi ko wace kasa a yankin mallakan makamai masu linzami kuma sune a gaba a duniya wajen kera jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga Nesa.