2025-07-03@13:41:35 GMT
إجمالي نتائج البحث: 12
«yan Kannywood»:
Tauraron Kannywood kuma mai sayar da maganin gargajiya, Abdullahi Alhikima ya magantu bayan da wasu ‘yan Kannywood suka caccake shi kan kalaman da ya yi a kansu. Aminiya ta rawaito cewa hatsaniyar ta samo asali ne bayan fitattun ‘yan Kannywood da suka hada da Abdul M Sharif, Nura M Inuwa, Abubakar Bashir Maishadda, Sadik Sani Sadik, da sauransu suka kai wa tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP Atiku Abubakar ziyarar goyon baya. Ambaliya: Zulum ya bada umarnin tallafa wa mutanen Damboa da Askira-Uba Majalisar Dokokin Filato ta zaɓi sabon shugaba Wannan ya tunzura Alhikma kasancewar wasu daga cikin wadanda suka je mubayi’ar ‘ya’yan kungiyar YBN ne a baya, da kuma 13/13 ta ubangidansa, mawaki Rarara. A cikin wadanda Alhikima...
Har ila yau, Maishaddar ya ci gaba da bayyana cewa; dangane da batun da mutane ke yi na cewa, alaka tsakaninsa da jarumi kuma mawaki Umar M. Sharif ta yi tsami, duba da cewa; an daina ganinsa a ci gaban shirin ‘Gidan Sarauta’ da Maishadda ke daukar nauyi, Bashir ya bayyana cewa; wannan magana ko kusa babu kamshin gaskiya a ciki, don ba a ga Umar a shirin ‘Gidan Sarauta’ zango na 4 ba, wannan ba dalili ne da zai sa a yi tunanin ko akwai wata matsala a tsakanina da shi ba, domin kuwa; a duk wani shiri mai dogon zango, akwai lokacin da za a daina ganin jarumi, amma kuma daga baya ya sake bayyana. Bashir ya kara...
Maryam Abubakar, ɗaya ce daga cikin jaruman masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood ’yan ƙalilan da suka yi nasarar bin sahun iyayensu a harkar fim. Matashiyar jarumar, wadda aka fi sanin ta da Maryam Intete a masana’antar, ta yi bayani a kan matsayinta na wadda iyayenta suka suka a cikin cikin harkar fim. Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa A wannan tattaunawar, jarumar ta yi bayani game da gogewarta da yadda ake samun daukaka a Kannywood, da wasu abubuwa game da ita kanta da iyayenta, da kuma sana’ar fim da dai sauransu. Wace ce Maryam Abubakar? An haife ni ne a Kano kuma a nan na girma....
Daga karshe ta ce da farko ta samu turjiya daga wajen wasu mutane a kan kudurinta na fara harkar fim amma kuma ta yi biris dasu ta fara, amma kuma yanzu wadanda a baya ke hanata shiga fim su ne yanzu ke yi mata murnar samun nasara hakan ya matukar bata mamaki, duba da cewar wadanda ta ke tunanin za su tsaneta kasancewarta jarumar fim sun zamo masoyanta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani nazarin finafinan Kannywood da BBC Hausa ta gabatar ya nuna cewa, Masana’antar Kannywood tana ta samun sauye-sauye, musamman a bangaren shirya fim da kasuwancinsa, inda daga CD aka koma sinima, yanzu aka koma YouTube, sannan ake ta hankoron shiga manhajojin duniya ka’in da na’in. A wannan shekarar, kamar kowace shekara, masu shirya finafinan Kannywood sun taka muhimmiyar rawa wajen tsarawa da fitar da finafinai masu kyau, wadanda suka kayatar da masu kallo. Yadda Kanawa suka huce takaicin rashin Hawan Sallah Mene ne matsayin azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Malikiyya (2) Tun bayan komawa dora finafinai a YouTube, yanzu za a iya cewa harkokin Kannywood sun fara komawa yadda suke a baya, bayan a baya masana’antar ta fara durkushewa. Nazarin...
A yayin hirar Abdullahi Shuaibu ya ce “Ni dai suna na Abdullahi Shuaibu, amma al’uma na kirana da Karkuzu, ko kuma Abdullahi Kano, yanzu shekaru 43 kenan ina wannan harka ta fina finan Hausa, amma yanzu wasu lokutan sai in kwana ba ni da abin da za a ci a gida na, kuma wani abin tausayi, ni Karkuzu a yanzu zancen da na ke, wannan gida da nake ciki an sa shi a kasuwa, ba gida na ba ne, haya nake yi. Ya ci gaba da cewa, yanzu a cikin wannan al’amari da na ke yi, in an ce na mallaki gida mai dimbin yawa, wadansu da za su ke kallo na sai su ce gaskiya ne, amma wallahi tallahi,...
Wannan ya sa murnar da wasu ke yi ta komawa da haska finafinan Hausa masu dogon zango a tashar YouTube ta fara komawa ciki. Me ya sa ba a gamawa din? BBC Hausa ta ci gaba da cewa wani faifan bidiyo na wata tattaunawa da jagoran shirin Izzar so, Ahmad Lawan ya yi a tasharsa ta Bakori TV, ya ce masu kallo ne ba su gaji da kallon shirin ba, shi ya sa ba zai daina ba. Ya ce kasancewar Youtube ya dade kudu, amma bai je arewacin Nijeriya ba ne ya sa su ka gwada domin su koya wa mutanen arewa kallon fim a YouTube, shi kuma wannan fim din ya na ciki, ko in ce shi ne daya...
A yanzu nan ne Aminiya take samun labarin rasuwar fitaccen jarumin Kannywood, Malam Abdullahi Shu’aibu wanda aka fi sani da Baba Ƙarƙuzu ko Ƙarƙuzu na Bodara. Hakan dai na kunshe ne cikin wani sako da jarumi a masana’antar Kannywood kuma Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Kano, Abba El-Mustapha, ya wallafa a shafinsa na Instagram. SShi ma dai fitaccen jarumin Kannywood kuma Shugaban Hukumar Fina-finai ta Nijeriya, Ali Nuhu, ya wallafa hoton marigayi Ƙarƙuzu a shafinsa na Facebook yana mai roƙon Allah Ya jikansa. Ƙarƙuzu dai tsohon jarumi ne a masana’antar Kannywood da ya yi tashe tun a shekarun 1980. Ana iya tuna cewa wata hira da ya yi da Zinariya TV kuma Mujallar Fim ta wallafa a shekarar 2023, Ƙarƙuzu...
Samira Sani ‘yar asalin garin Kano ne da ta shigo Masana’anrtar Kannywood a 2022. A tattaunarta da Aminiya, ta ba da tarihinta da kuma yadda ta daɗe tana mu’amala da ‘yan Kannywood kafin ta fara fitowa a fim: Za mu so ki gabatar da kanki? Suna na Samira Sani, jaruma a Masanartar Fim ta Kannywood. Mene ne tarihinki a takaice? To ni ‘yar asalin garin Kano ne. An haife ni a garin Dakatsalle da ke Karamar Hukumar Bebeji ta Jihar Kano. Na yi makarantun firamare da sakandare duk a Dakatsalle, bayan na gama sakandare sai aka yi min aure, daga baya Allah Ya kawo ni cikin birnin Kano. Ke nan kin taɓa yin aure? Eh na taɓa yin aure,...
Hakan ya sa yanzu ba kasafai masu shirya fina finan Hausa ke mayar da adadin abinda su ka kashe wajen shirya fim ba, don kuwa ba kowane yake da yawan mabiyan da za su kalli abinda ya dora a YouTube ba da har zai samu wani abin kirki, hakazalika gidajen Talabijin da ke saye ba wani kudin azo a gani suka bayarwa ba, yanzu idan fim dinka bai kai matsayin shiga tashar NETFLID ta kasar Amurka ba, ba lallai ne ya kai inda kake bukata ba inji shi. Ya ci gaba da cewa hakan yasa nike bayar da shawara wajen ganin mun fadada tunaninmu wajen zakulo wasu sabbin hanyoyi da zamu dinga fitar da fina finanmu zuwa inda ya kamata...
A zamanin baya, duk da cewa fina-finan nanaye sun fi karbuwa a wajen mutane, amma haka muke kokartawa wajen ganin an shigar da wata koyarwa ta addinin musulinci ko kuma wani abu mai amfani da zai amfanar da al’umma ta wani bangare, amma yanzu duk an daina wannan, masu shirya fina-finai na amfani da labarai masu tsafta da amfanarwa, ba tare da da sanya wakoki ko makamantansu a ciki ba, in ji Malam. “Dalili kuwa shi ne, yanzu ‘ya’yan mutunci da arziki su ne ke yin harkar, sannan kuma su ne suke samun arzikin duniya da na lahira, akwai lokacin da har mata masu zaman kansu din, sai da muka daina samun su idan zamu yi fim, amma yanzu wannan...
Har ila yau ya ce, idan aka yi maganar mukaman da gwamnatin tarayya da ta jihohi suka bai wa wasu daga cikinmu, ba yana nufin cewa; an taimaki masana’antar ba ne, domin kuwa; mafi yawancin wadanda suka samu wadannan mukamai, babu wani ci gaba ko hobbasa da suka yi wajen ciyar da Masana’antar Kannywood gaba. Musa ya ce, illa kawai dai suna taimakon kansu da kuma na kusa da su, wanda kuma ba haka ya dace a ce suna yi ba, dalili kuwa shi ne, har yau babu wani daga cikin masana’antar tamu da ya taba samun wani mukamin gwamnati, ya taimaka wa ita kanta masana’antar, illa kalilan daga cikinmu. A bangaren abokanan fada kuwa a Masana’antar Kannywood, Mai Sana’a...