Aminiya:
2025-10-13@17:09:45 GMT

Van Nistelrooy ya ajiye aikin horas da Leicester City

Published: 29th, June 2025 GMT

Tsohon tauraron ƙungiyoyin Manchester United da Real Madrid, Ruud van Nistelrooy ya ajiye aikinsa na horas da Leicester City bisa fahimtar juna.

Wannan na zuwa ne bayan da a ƙarƙashin jagorancinsa ƙungiyar ta yi wasanni 27 da ta gaza taɓuka abin a zo a gani a cikinsu, lamarin da ya kai ta ga faɗawa gasa mai daraja ta biyu a Ingila wato Championship.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce an cimma matsaya tsakaninta da Van Nistelroy ne bayan tattaunawar da suka yi.

A ƙarshen watan Nuwamban da ya gabata, bayan da ta kori Steve Cooper a lokacin da suke matsayi na 16 a gasar Firimiyar bara, Liecester City ta ƙulla yarjejeniya da Van Nistelrooy, kwangilar da ba za ta ƙare ba sai a shekarar 2027.

To amma duk da sauyin da aka samu kwalliya ta gaza biyan kuɗin sabulu domin kuwa a haka suka yi ta tafiya da ƙyar.

Daga ƙarshe ma dai ƙungiyar ta sha kashi da ci 1-0 a karawar ta Liverpool a ranar 20 ga watan Afrilu, rashin nasarar da ta tabbatar da cewar ƙungiyar ta yi adabo da gasar Firimiya sai kuma wani jiƙon.

A halin yanzu dai ana sa ran tsohon Kocin Burnley da Everton, Sean Dyche ya maye gurbin da Nistelrooy ya bari.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Za A Yi Wa Masu Lalurar Ido Aiki Kyauta A Jihar Jigawa

Wata kungiya mai zaman kanta ta tantance mutane 60 wadanda za’a yiwa aikin ido kyauta a wasu kananan hukumomi 2 dake jihar Jigawa.

Shugaban kungiyar mai zaman kanta, Alhaji Umar Saidu Yelleman Jambola ya bayyana cewar za’a gudanar da aikin ne kyauta ga mutane 60 a kananan hukumomin Malam madori da kaugama.

A cewar sa wadanda za su ci moriyar aikin an zabi su ne daga dukkanin mazabu da ke kananan hukumomin.

Sa’idu Yalleman ya kara da cewa yara da manya ne za su amfana da aikin idon kyauta wanda kungiyar ta dau nauyi.

Da yake jawabi ga manema labarai, Dr Abubakar Adamu yace wadanda aka tantance kuma suke da yanar ido za’a kai su asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano dake birnin Kano don yi masu aikin.

Wakilan shirin na kananan hukumomin Malam Madori and Kaugama,  Malam Bashari Suleiman da Dan-Alhaji sun ce a mako mai zuwa ne za’a gudanar da aikin ga wadanda aka tantance.

Da yake jawabi a madadin wadanda zasu ci moriyar aikin, wakilan mazabun Garun-Gabas da Mairakumi, Mustapha Bala da Suraja Garba sun yabawa kokarin Alhaji Umar Jambola.

A nasu jawaban, Shugabannin kananan hukumomin Kaugama da Malam madori, Alhaji Salisu Sani Garun-Gabas da Alhaji Masaki Usman Dansule sun yaba da hobbasan Umar Jambola na taimakawa masu karamin karfi a kananan hukumominsu.

Usman Mohammed Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano
  • Iran Ta Ki Zuwa Masar Saboda Bata Son Haduwa Da Azzaluman Da Suka Kashe Falasdinwa A Gaza
  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 9, sun kwato kudin fansa a Borno
  • Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano
  • ASUU ta tsunduma yajin aikin mako 2
  • ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin
  • Za A Yi Wa Masu Lalurar Ido Aiki Kyauta A Jihar Jigawa
  • Maryam Sanda na cikin waɗanda Tinubu ya yi wa afuwa
  • Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa
  • Iran Tana Goyon Bayan Duk Wani Shirin Zaman Lafiya Da Ya Hada Da Kawo Karshen Kisan Kiyashi A Gaza