Kasar Iran Ta Nuna Ire-Iren Makamai Masu Linzami Da Ta Mayar Da Martani Da Su Kan ‘Yan Mamaya
Published: 2nd, July 2025 GMT
Iran ta nuna makamai masu linzami wadanda suka bude kofofin jahannama kan ‘yan sahayoniyya
A martanin da gwamnatin yahudawan sahayoniyya suka kai wa Iran, sojojin Iran da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar sun nuna karfinsu na soji a matsayin wani bangare na “Alkawarin Gaskiya na 3”, inda suka harba daruruwan makamai masu linzami na ballistic da hypersonic.
A wani bangare na wannan harin na ramuwar gayya, Iran ta kai jerin hare-hare na hadin gwiwa, wanda kaso mafi tsoka na makamai masu linzami kamar Emad, Ghadr, Fattah 1, Sejjil da Khaybar.
A halin yanzu rahotonni da hotuna daga haramtacciyar kasar Isra’ila suna kara fitowa kan yadda makamai masu linzamin Iran suka tarwatsa wurare masu muhimmanci na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yan mamaya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Sama Jannatin Shenzhou-20 Za Su Gudanar Da Zagaye Na 3 Na Aiki A Wajen Cibiyar Binciken Sararin Samaniya Ta Sin
Hukumar kula da kumbuna ta kasar Sin ta ce nan ba da jimawa ba, ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20 dake cibiyar binciken sararin samaniya ta kasar, za su gudanar da zagaye na 3 na ayyuka a wajen cibiyar.
‘Yan sama jannatin 3 da suka hada da Chen Dong da Chen Zhongrui da Wang Jie, sun gudanar da irin wannan aiki har sau biyu, a watannin Mayu da Yuni.
Baya ga haka, sun kammala ayyukan nazarin muhalli da kula da tantance da kayayyakin aiki a cikin cibiyar da jigilar kayayyaki. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp