Za mu shige gaba idan aka dawo da tattauna shirin nukiliyar Iran — EU
Published: 2nd, July 2025 GMT
Kungiyar Tarayyar Turai EU ta bukaci a sake komawa teburin tattauna shirin nukiliyar Iran cikin gaggawa, inda take neman hadin kai a tsakanin Tehran da kuma Hukumar Kula da Makamashi ta Duniya IAEA.
Babbar jami’ar diflomasiyyar EU Kaja Kallas ta shaida wa Ministan Harkokin Kasashen Ketare na Iran, Abbas Aragchi cewar Brussels a shirye take ta shige gaba don ganin an koma teburin tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran bayan hare-haren Amurka a tashoshin makamashinsu.
Bayan wata doguwar tattaunawa ta wayar tarho da jami’ar ta yi da Mista Argchi, ta wallafa a shafinta na X cewar ya kamata a koma tattaunawa kan makamashin Iran cikin gaggawa, kuma akwai bukatar hadin kai daga hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa domin cimma yarjejeniya.
Kazalika Kallas ta gargadi Tehran cewar duk wani yunkuri na janyewa daga tattaunawar ka iya dagula al’amura.
Wannan na zuwa ne bayan da Tehran ta yi watsi da sake komawa kan teburin tattaunawa da hukumar ta yi, inda Tehran ta ce tana bukatar tabbacin Amurka ba za ta sake kai mata hari ba.
A baya dai EU ta kasance mai shiga tsakani a yarjejeniyar nukiliyar Iran na 2015 da aka cimma da manyan kasashen duniya, kafin daga bisani Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi watsi da yarjejeniya a shekarar 2018.
AFP
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Iran nukiliyar Iran
এছাড়াও পড়ুন:
Jirgin Alhazai Na Farko Ya Iso Jihar Jigawa
Alhazan da suka hada da wakilan hukumar alhazai, jami’an hukumar jin dadin alhazai ta jiha, malamai, da sauran alhazai, sun bayyana jin dadinsu ga gwamnati da hukumar alhazai bisa irin kulawar da suka samu a lokacin aikin hajjin.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan isowar mahajjatan, babban daraktan hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa, Ahmed Labbo ya bayyana jin dadinsa bisa nasarar da aka samu na dawo da alhazan jihar Jigawa Nijeriya cikin koshin lafiya.
“Mun gode wa Allah da ya dawo mana da alhazan mu lafiya,” in ji Labbo.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp