Muna sane da wuraren da ake yaki masu taba zuciya: Gaza, Sudan, Ukraine da sauran wurare. Rikicin baya-bayan nan tsakanin Iran da Isra’ila, wani abin tunatarwa ne ga raunin zaman lafiya musamman a yankin Gabas ta Tsakiya mai fama da tashe-tashen hankula.

 

Duk da haka, a cikin wannan tashin hankali, mun yi nasarar dakile yakin duniya na uku.

A wannan zamani na nukiliya, wannan nasara ce da ba za mu taba dauka da wasa ba. Ita ce wacce ta kamata mu kiyaye da karfin kokarinmu.

 

A cikin shekaru 80 da suka gabata, yawancin ci gaban dan’Adam shi ma yana da tasiri a MDD kai tsaye. Yi la’akari da nasarar da aka samu ta ci gaban karni, wanda kasashe mambobi 189 suka karba a cikin kasashe 2000 da kari.

 

Fiye da kungiyoyin kasa da kasa 20 ne suka ba duniya taswirar hanya daya domin daukar mataki.

 

A 2015, idan aka kwatanta da 1990, matsanancin talauci ya ragu sama da rabi. Mutuwar yara ta ragu da kusan kashi 50 cikin dari. Kuma miliyoyin yara musamman ‘yan matan da ake dannewa hakki sun shiga makaranta a karon farko.

 

Akwai wani muhimmin labarin ci gaba, wanda ba a mantawa da shi, shi ne wargaza daula. Shekaru 80 da suka gabata, mulkin mallaka ya yi shuhura a duniya. A yau, fiye da 80 da aka yi musu mulkin mallaka a fadin Asiya, Afirka, Caribbean, da Pacific sun sami ‘yancin kai kuma sun shiga MDD. Wannan canji da wannan Kungiya ta goyi baya kuma ta halalta shi ya sake fasalin tsarin duniya.

 

Shiga Tsakani domin samar da ci gaba

 

Duniya ta canza sosai tun daga 1945. A yau, kungiyar na fuskantar matsalar karancin kudi. Duk da alkawalin da aka yi na 2030 don samar da ci gaba mai dorewa, ci gaban kuma bai daidaita ba. Daidaiton jinsi ya kubuce mana. Alkawarin da muka yi na takaita hauhawar dumamar duniya da kare duniyarmu ya karanta.

 

Wadannan koma baya ba sun haifar da raguwar buri amma su ne manyan kudurorinmu. Majalisar Dinkin Duniya na nuna kimarta a lokutan rikici. Wadanda suka kafa ta sun shaida dan’Adam a matsayin mafi barna kuma ba su yanke kauna ba, saboda karfin hali. Dole ne mu zayyana wadannan nasarori.

 

Yayin da muke bikin wannan zagayowa, dole ne mu sake farfado da kiran hadin kai da aka yi daga San Francisco shekaru 80 da suka gabata.

 

Mun gina tsarin duniya farat daya, domin rushe tsarin yaki. Mun yi hakan ne da hangen nesa cikin gaggawa. Yanzu kuma, mun sami kanmu a lokacin sakamako. Hadarin yana da yawa. Haka zalika kuma karfinmu na yin aiki na da yawa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda ɗan shekara 70 ya rasu a gobarar tankokin gas a Zariya

Wani dattijo ya rasu a sakamakon hatsari da gobarar tankokin sakon iskar gas da ta auku a yankin Zariya da ke Jihar Kaduna.

Aliyu Ramalan Babbale mai shekara sama da 70 ya rasu ne a lokacin da yake ƙokarin tsira da ransa a sakamakon hatsarin tankokin a safiyar ranar Litinin.

Dattijon ya gamu da ajalinsa ne a kan hanyarsa na zuwa gona, lokacin da wasu tankokin dakon gas biyu suka kama da wuta bayan su gogi juna.

Mai auran babban ’yar marigayi Malam Abdullahi Magaji, ya yi wa Aminiya bayanin yadda lamarin ya faru, akan rasuwar marigayin.

ya ce, “A jiya da safe marigayin yana kan babur ne a kan hanyarsa na zuwa gona, sai waɗannan motocin ɗakon man gas ɗin suka kama da wuta kuma suka yi ƙara.

“To a lokacin da yake ƙokarin tsira da rai ne wani shi ma da yake kan babur garin gudu sai ya kwashe shi a inda kafin a kai shi asibitin ya rasu,” in ji shi.

Marigayi ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya shida kuma tuni aka yi jana’izarsa a gidansa da ke Babbale cikin birnin Zariya.

Bayanai na ƙara fitowa dangane da wadanda suka rasu a sanadiyar hatsarin tankokin dakon gas ɗin da ya auku a garin Zariya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsarin Samar Da Kayayyaki Na Masana’antar Lantarki Ya Ci Gaba Da Samun Karfin Juriya A Kasar Sin
  • Gidauniya Ta Rabar Da Buhun Takin Zamani 6,000 Ga Manoma A Bauchi 
  • Gwamna Lawal Ya Ziyarci Yankunan Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Wa Hari A Zamfara
  • Dalilan ƙaruwar mace-mace a hanyoyin Najeriya
  • Babu Neman Afuwa Kan Nuna Goyan Bayan Tinubu Da Na Yi – Soludo
  • Ilimin Fasahar Zamani Dama Ce Ta Samun Kyakkyawar Makoma A Afrika
  • An kama ɗan shekara 18 kan zargin fashi da makami a Gombe
  • Bankin Duniya zai kashe $300m domin inganta rayuwar ’yan gudun hijira a Arewacin Nijeriya
  • Sin Ta Gabatar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakaninta Da Amurka A Stockholm
  • Yadda ɗan shekara 70 ya rasu a gobarar tankokin gas a Zariya