‘An Kwashe Shekaru Ana Kashe Kudaden Yaran da ba a ma Haife su ba a Nijeriya’
Published: 14th, March 2025 GMT
Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ke yi, tana yi ne da nufin gyara makomar yara masu tasowa.
Yayin da yake jawabi ga kungiyar ‘Yan majalisa ta uku – wadda ya kasance cikin a Jamhuriya ta uku – da suka kai masa ziyara a fadarsa, Shugaba Tinubu ya ce a baya kasar na kashe kudaden yaran kasar da ba a kai ga haihuwarsa ba.
“Shekara 50 da suka gabata, Najeriya na kashe kudaden yaran da ba a kai ga haihuwarsu ba, tare da mayar da hankali kan man fetur wajen samun kudin shiga. Ba a yi wani tsari na tallafa wa yaran da za a haifa a gaba ba,” kamar yadda ya ce.
Shugaban ya kuma bayyana tarin matsalolin da ya fuskanta a farkon mulkinsa, musamman fannin tattalin arzikin da rayuwar jama’a.
“Mun fuskanci tarin kalubale a lokacin da na karbi mulki. Inda ba mu dauki matakai ba da yanzu kasar ta talauce, kuma ai hakkinmu ne mu kare tattalin arzikinmu daga rugujewa”, in ji Shugaba Tinubu.
To amma shugaban ya ce a yanzu kwalliya ta fara biyan kudin sabulu dangane da sauye-sauyen da gwamatinsa ta fara ɓullo da su.
“Amma a yau bayan shimfida mai kyau da muka yi, mun smau nasarar magance matsalolin da suka tunkaro kasarmu, a yanzu canjin kudi ya daidaita, farashin abinci na ci gaba da sauka, musamman a lokacin Ramadan, da yardar Allah wahalar ta zo karshe”, a cewar shugaban kasa.
Bello Wakili/Abuja
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Putin Na Rasha Ya Bada Sanarwan Tsagaita Wuta Da Ukraine Na Sa’o’ii 72
Shugaban Putin Na Rasha Ya Bada Sanarwan Tsagaita Wuta Da Ukraine Na Bangaren Guda kuma na sa’o’ii 72 ko kwanaki 3, daga 8-10 na watan Mayu mai zuwa.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya nakalto jakadan kasar Rasha a Abuja yana fadar haka a wani taro baje kolin hotinan yaki Rasah da Nazi a dai dai lokacinda kasar take cikar shekaru 80 da samun nasara a kan sojojin Nazi a karshen yakin duniya na II a Abuja.
Andrey Podelyshev yace idan kasar Ukraine ta zami da tsagaita wuta a cikin wadannan kwanaki ba laifi, amma kuma idan sojojinta sun kai wani hari a kan rasha ta zata rama da hare-hare masu tsanani.
Shugaban Volodimir Zelesky dai tuni ya yi watsi da tsagaita wutar ya kura kara da cewa Rasha tana son ta ja hankalin duniya ne da wannan tsagaita wuta, don amfanin kanta a yakin da suke fafatawa. A halin yanzu dai an dai kwanaki kimani 1,159 aka fafatawa tsakanin kasashen biyu.