2027: David Mark zai kai mu ga nasara — ADC
Published: 2nd, July 2025 GMT
Jagoran sabuwar jam’iyyar ADC, Ralph Nwosu, ya bayyana cewa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, zai jagorance su wajen karɓar mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Jam’iyyar haɗakar, wacce ta ƙunshi fitattun ’yan siyasa, ta naɗa David Mark a matsayin Shugaba, tare da tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin Sakatare.
A wajen babban taron da ta gudanar a cibiyar Yar’Adua da ke Abuja, Nwosu ya ce: “Mun sauka daga muƙamanmu domin mu bai wa David Mark dama ya jagoranci wannan tafiya zuwa fadar shugaban ƙasa.”
Ya yaba wa Aregbesola, wanda ya taɓa kasancewa abokin siyasar Tinubu, inda ya ce mutum ne mai aiki tuƙuru da kishin ƙasa.
Nwosu ya ƙara da cewa: “’Yan Najeriya sun gaji. Sun ƙosa da sauyi. Wannan haɗaka da muke yi na da matuƙar muhimmanci.
“Ina goyon bayansa sosai, kuma ba zan huta ba har sai mun isa fadar shugaban ƙasa, mun rera taken ƙasa a can. Najeriya na cikin tsaka mai wuya.
“Rayuka na salwanta kullum. Shugabanninmu na gaba su fitar da Najeriya daga wannan halin, su kai ta ga ci gaba. Za mu iya!”
Ya kuma gargaɗi masu sukar wannan haɗakar da cewa ba ’yan jam’iyyar ADC ba ne.
“Babu buƙatar yin nadama a kan abin da muka yi yau. Wannan tafiya ce mai wahala, dole mu kasance a shirye.”
Daga cikin fitattun mutane da suka halarci taron har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar; ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi.
Sauran sun haɗa da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi; da tsohon Gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha, da sauransu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: David Mark Haɗaka Zaɓe
এছাড়াও পড়ুন:
Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya- Shugaba Tinubu
Daga Bello Wakili
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karɓi labarin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi cikin alhini da jimami.
Fitaccen malamin da ke Bauchi ya rasu ne a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2026, yana da shekaru 101.
Shugaban Ƙasan ya yi jimamin rasuwar jagoran Darikar Tijjaniyya, yana bayyana shi a matsayin ginshiƙin ɗabi’a wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa da wa’azi.
Shugaba Tinubu ya ce rashinsa babban rashi ne ba ga iyalansa da dimbin mabiyansa kaɗai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya.
Shugaban Ƙasa ya tuna da albarka da goyon bayan da ya samu daga marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a lokacin yakin zaɓen 2023.
“Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba, mai cike da natsuwa da hikima. A matsayinaa na mai wa’azi kuma masani kan tafsirin Alƙur’ani Mai Girma, yana da’awar zaman lafiya da tsoron Allah. Rasuwarsa ta bar babban gibi,” in ji Shugaban Ƙasa.
Shugaba Tinubu ya yi ta’aziyya ga mabiyan Shehun a ci da wajen ƙasa bisa wannan babban rashi.
Haka kuma ya ja hankalinsu da su girmama sunansa ta hanyar bin koyarwarsa ta zaman lafiya, ƙarfafa dangantakarsu da Allah, da kuma kasancewa masu taushin zuciya ga jama’a.