2025-06-12@21:27:50 GMT
إجمالي نتائج البحث: 204
«Korea Ta Arewa»:
A yau Alhamis ne aka bude bikin baje kolin hada-hadar tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka karo na hudu a birnin Changsha fadar mulkin lardin Hunan, taron dake kara jaddada himmar kasar Sin ta fuskar karfafa alaka da nahiyar Afirka, nahiyar dake da mafiya yawan kasashe masu tasowa a duniya baki daya. Kusan kamfanonin Sin da na kasashen Afirka 4,700, da sama da mahalarta 30,000 ne za su halarci bikin na kwanaki hudu, wanda aka yiwa taken “Sin da Afirka: Tunkarar zamanantarwa tare.” Rahotanni daga mashirya bikin na cewa, kwarya-kwaryar darajar ayyukan hadin gwiwa da aka amincewa sun haura dalar Amurka biliyan 11. Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci bikin bude baje kolin, inda kuma...
Rashin wutar lantarki a Arewa maso Gabashin Najeriya ya tilasta wa jama’a da ’yan kasuwa zaman ɗari-ɗari da asarar dukiya, sakamakon aikin da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN), ke yi na aikin sabbin turakun wutar lantarki. Rashin wutar, wanda ya fara daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Yuni, ya shafi layin wutar lantarki na Jos–Bauchi–Gombe mai ƙarfin 132kV. An kashe mutum 41 cikin mako ɗaya a Filato Hajjin 2025: Jihohi 11 sun kashe N6.2bn wajen tallafa wa Alhazai A Jihar Adamawa, musamman a birnin Yola, jama’a na cikin matsanancin hali. Hajiya Aisha Babangida daga Jimeta, ta ce rashin wutar ya tilasta masa soye dukkanin naman ragon sallarta domin babu wutar da za ta ajiye shi a firinji....
Kamfanin Dakon Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da cewa za a dauke wutar lantarki a ilahirin jihohin yankin Arewa maso Gabas guda shida na tsawon kwana hudu. A cikin wata wasika da ya aike wa kamfanonin rarraba wutar lantarki da ke kula da jihohin shida, TCN ya ce yayin da a wasu jihohin wutar za ta dauke gaba daya, wasu yankunan kuwa karancin wutar za a samu a tsakanin kwanakin. Jihohin da lamarin zai shafa sun hada da Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe. Kotu ta yi fatali da bukatar Akpabio, ta umarce shi ya biya Natasha N100,000 DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya Wasikar wacce ke dauke da sa hannun...

Iran Ta Sami Nasara Akan Korea Ta Arewa Akarkashin Share Fagen Shiga Gasar Cin Kofin Duniya Na Kwallon
Kungiyar kwallon kafa ta Iran ta sami nasarar akan abokiyar karawarta ta kasar Korea Ta Arewa da kwallaye uku masu kyau a wasan da aka yi a filin wasa na “Azadi” na Tehran. Kasashen biyu dai suna a karkashin; bangare na uku a Asiya saboda share fagen kai wa ga shiga gasar cin kofin kwallon duniya na 2026. Dan wasa mai suna Muhammad Muhibbi ne ya ci kwallon farko, a mintuna 74 da fara wasan, sai kuma Mahdi Darimi a mintuna 77, sa Amir Husain Husain zadeh, a minti 3 da aka kara, bayan cikar mituna 90. A bangaren kungiyar kwallon kafa ta Korea Ta Arewa kuwa, ta kammala wasannin nata da ‘yan wasa 10 bayan da aka kori daya...
A cewarsa, shuwagabancin Tinubu ya gina tubalin ci gaba mai ɗorewa ta hanyar yanke hukunci masu wahala amma masu amfani. Dangane da sauyin jam’iyyun siyasa da ke faruwa, Namadi ya ce yawaitar sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC alama ce da ke nuna yadda jama’a ke ƙara amincewa da shugabancin Tinubu da kuma burin da yake shi ga ƙasar nan. Ya ce masu barin jam’iyyunsu suna haka ne domin suna ganin makoma mai kyau a ƙarƙashin jagorancinsa. Har ila yau, Namadi ya bayyana cewa ziyarar aikin da ya kai Indiya kwanan nan ta samar da muhimman yarjejeniyoyi da masu saka jari da ƙwararru don bunƙasa harkar noma a Jihar Jigawa. Ya ce an cimma matsaya a fannoni irin su kiwon shanu,...
Gwamnatin kasar Burtaniya ta bada sanarwan kakabawa ministocin HKI guda biyu takunkuman tattalin arziki saboda ra’yinsu na wuce gona da Iri wanda zai bata duk wani shirin da kasashen duniya suke da shin a tabbatar da zaman lafiya a yanking abas ta tsakiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kira-kirayen ministocin na kara mamaya da kuma korar falasdina daga yankin yamma da kogin Jordan ne yasa burtaniya ta nuki wannan batakin. Bezalel Smotrich dai , wanda shi ne ministan kudi na HKI ya ce HKI zama kara mamayar yankin yamma da kogin Jordan, kafin zaben shekara ta 2026, sannan ya rantse kan cewa za’a share falasdinawa a gaza, kuma zasu wargaza kungiyar Hamas a cikin...

An Kaddamar Da Taron Farko Na Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Sin Da Amurka A London
A yau Litinin 9 ga wata ne memban hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kana mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng, da jami’an bangaren Amurka, suka halarci taron farko na tattauna batutuwan tattalin arziki da cinikayya na Sin da Amurka, wanda aka kaddamar a birnin London dake kasar Birtaniya. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A daidai lokacin da kungiyar kasashen tsakiyar Afirka ta tattalin arziki ( ECCAS) take yin taro, kasar Rwanda ta sanar da ficewa daga cikinta. Bayanin da gwamnatin kasar ta Rwanda ta fitar ya kunshi cewa; Kasar Rwanda tana nuna takaicinta akan yadda kasar DRC take amfani da kungiyar tattalin arziki ta tsakiyar Afirka a matsayin wani makamin a hannunta.” Bayanin gwamnatin ta Rwanda ya kara da cewa: Yadda DRC take amfani da wannan kungiyar ya sake fitowa fili a yayin taron kungiyar karo na 26 a Malabo, ta yadda aka kau da kai akan hakkin Rwanda na shugabancin karba-karba,kamar yadda yake a cikin doka ta shida ta kundin kungiyar. Hakan kuma ya faru ne sanadiyyar shiftar DRC ga kungiyar.” A...

He Lifeng Zai Ziyarci Birtaniya Tare Da Halartar Taron Farko Na Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Sin Da Amurka
Ma’aikatar harkokin waje ta kasar Sin, ta sanar a jiya Asabar cewa bisa gayyatar da gwamnatin Birtaniya ta yi masa, memba a hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kana mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng, zai ziyarci Birtaniya tun daga yau Lahadi har zuwa Juma’a 13 ga watan nan na Yuni. Ana sa ran yayin ziyarar tasa a Birtaniya, He Lifeng zai halarci taron farko na tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baghae ya zargin gwamnatin Amurka da yin ba daidai ba saboda karin takunkuman tattalin arziki wanda ta dorawa kasar, wanda kuma yake nuna irin kiyayyar da takewa mutanen kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Esmael Baghae yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma kara da cewa bayan da hukumar baitul malin Amurka ta bayyana sunayen mutane 10 wadanda ta dorawa takunkuman tattalin arziki da kuma kamfanoni 27 mafi yawansu a hadaddiyar daulolin larabawa wato UAE. Labarin ya kara da cewa wadan nan mutane suna taimakawa Iran a ayyukan Banki da jigilar manfetur a madadin Iraniyawa. Baghae ya bayyana wannan labarin a kan kariya kuma mummunan siyasar Amurka ce...
Gwamnatin kasar Amurka ta kara yawan takunkuman tattalin arzikin da take dorawa JMI dangane da shirinta na makamashin Nukliya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a wannan karon takunkuman sun shafi mutane 10 da kuma kamfanoni 27. Wadansu daga cikin kamfanonin suna kasar hadaddiyar daular Larabawa wasu kuma a Hong kong. Ofichin Baitul malin Amurka ya bayyana cewa Kamfanin Ace Petrochem FZE da kuma Moderate General Trading LLC duk suna da rijister a UAE kuma kwace dukkan kadarorinsu da suke Amurka saboda wadannan takunkuman. Labarin ya kara da cewa wadannan kamfanoni suna da dangantaka da kamfanin OFAC na kasar Iran, kamfanin tankunan jigilar man fetur. Iran da Amurka dai sun gudanar da zagaye na 5 na...

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce: Akwai Babbar Damar Bunkasa Alakar Tattalin Arziki Da Kasashen Latin Amurka
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa; Akwai babbar damar bunkasa dangantakar tattalin arziki da kasashen Latin Amurka Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf wanda ya yi tafiye-tafiye tun a ranar Asabar din da ta gabata a ziyarar da ya kai kasashen Latin Amurka da Brazil don halartar taron BRICS karo na 11, ya dawo inda ya iso filin jirgin saman Mehrabad na Tehran da yammacin yau Juma’a, bayan kammala ziyarar tasa, inda ya samu tarba daga jami’an gwamnati da na sojin kasar Iran. Ziyarar na dauke da nufin fadada huldar tattalin arziki da karfafa hadin gwiwa ta hanyar diflomasiyyar majalisar dokoki, kuma ta hada da ganawa da manyan jami’ai a Venezuela, Cuba, da Brazil....

Ministan Harkokin Wajen Sin Zai Halarci Taron Ministocin Kula Da Matakan Taron FOCAC Da Bikin Baje Kolin Tattalin Arziki Da Cinikayyar Sin Da Afirka Karo Na 4
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya sanar a yau Jumma’a cewa, daga ranar 10 zuwa 12 ga watan Yuni, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, zai halarci taron ministoci masu bibiyar aiwatar da matakan da aka dauka na taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC), gami da bikin bude baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasar Sin da Afirka karo na hudu a birnin Changsha na lardin Hunan da ke tsakiyar kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Miliyoyin alhazai ciki har da ’yan Najeriya ne suka taru a Dutsen Arfa domin tsayuwa a yayin Aikin Hajjin bana duk da tsananin zafin ranar da ake fama da shi a kasar Saudiyya. Ministan Aikin Hajji na kasar dai ya shawarci mahajjatan da su kasance a cikin tantinansu tun daga tsakain karfe 10 na safe zuwa karfe 4:00 na yamma, saboda tsananin zafin rana. Ko a ranar Lahadi sai da Hukumar Hasashen Yanayi ta Kasar (NCM) ta yi gargadin cewa zafin zai iya kai wa ma’auni 47, inda ta shawarce su da su dauki matakan kariya. Musulman Kudancin Kaduna sun yi taron addu’ar zaman lafiya Kotu ta aike da ɗan Tiktok gidan yari kan yin shigar mata a Kano To...
Aliyu, ya bayyana cewa Jibrin manomi ne daga ƙauyen Gargai da ke ƙaramar hukumar Bebeji a Kano. Ya kuma ce yana fama da cutar gyambon ciki da hawan jini. Likitoci sun bayyana cewa rasuwarsa ta faru ne sakamakon bugun zuciya da gazawar zuciya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Za mu warkar da raunukan rarrabuwar kawuna da yaki da kuma kafa makomar zaman lafiya da wadata,” in ji shi. “Komai runtsi, zaman lafiya ya fi yaki.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ce yanzu lokaci ne da Arewa za ta nuna adalci ta hanyar barin shugaba daga Kudu ya kammala wa’adin mulkinsa. Ya ƙara da cewa, “Idan za a fitar da wani ɗan takarar shugaban ƙasa daga ‘yan adawa a nan gaba, to ya dace ya fito daga Kudu maso Yamma. Wannan ne dai-daito da adalci.” Sanatan ya kuma soki gwamnatin baya da cewa ko da yake kusan dukkan shugabannin tsaro sun fito ne daga Arewa, amma hakan bai dakatar da ta’addanci a yankin ba, kuma bai hana hare-hare da kashe-kashe a jihohin Filato, Binuwai da sauran jihohin Arewa ta Tsakiya ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
Mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da cewa a ranar hawan arfa na bana, za a fassara hudubar da za a yi da harsuna 34 daga cikinsu da akwai Hausa da filatanci. Wasu harsunan Afirka da za a fassara hudubar ta Arfa da su, sun hada yarabanci, Sawahili, Somali da kuma Amharic na kasar Habasha. A bisa sanarwar da kasar Saudiyya ta yi na ganin watan zulhijja, a ranar 27 ga watan Mayu, za a yi hawan Arfa a ranar 5 ga watan na Mayu.
Sanatocin Arewa sun bayyana alhini da jimami kan haɗarin mota da ya yi sanadin mutuwar wasu daga cikin ‘yan wasan Jihar Kano da ke dawowa daga Gasar Wasanni ta Kasa da aka kammala a Jihar Ogun. A cikin wata sanarwa da Shugaban ƙungiyar Sanatocin Arewa, Sanata Musa Yar’adua ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da kuma Gwamnatin Kano, inda ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya. ‘Yan Wasan Da Tauraruwar Ronaldo Da Messi Ta Hana Su Haskawa Gwamnatin Kano Ta Ba Iyalan Mamatan Wasanni Tallafin Naira Miliyan Ɗaya Kowane Sanata Yar’adua ya yi addu’ar Allah ya jikan waɗanda suka rasu, ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin...
Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa ta bayyana ambaliyar ruwa mai tsanani da ta faru a Mokwa, Jihar Neja, a matsayin babbar ibtila’i, yana mai kira da a ɗauki matakan gaggawa don tallafi da hana sake faruwar hakan. Shugaban Kungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana haka a yayin mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Jihar Neja kan ambaliyar da ta faru a ranar Laraba, 28 ga Mayu, 2025, sakamakon ruwan sama mai kamar da bakin ƙwarya da ya yi sanadin rasa rayuka, bacewar mutane, da lalacewar gidaje, gonaki, da kayan more rayuwa. Ya yaba da agajin gaggawa daga Gwamnatin Jihar Neja karkashin jagorancin Gwamna Mohammed Umaru Bago da kuma kokarin hukumomin agaji wajen aikin ceto da tallafa wa...
Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar cewa a bana za a gabatar wa mahajjata huɗubar Ranar a cikin harsuna uku na Najeriya. Harsunan Najeriya guda uku da za a gabatar da Huɗubar Ranar Arfa da su sun ne Hausa da Fulatanci da kuma Yarbaci. Harsunan huda uku na daga cikin karin harsunan duniya guda 34 da hukumomin Saudiyya suka sanar cewa za a gabatar da Huɗubar a cikinsu.

Sin Za Ta Kara Zurfafa Dunkule Rawar Yankunan Raya Tattalin Arziki Da Fasahohi A Fannin Janyo Jarin Waje
Mataimakin ministan ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin Ling Ji, ya ce gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da zurfafa dunkule rawar da yankunan raya tattalin arziki da fasahohi mallakin gwamnati ke takawa, a fannin janyo jarin waje, a gabar da kasar ke kara fadada matakanta na bude kofa ga kasashen waje. Ling Ji, wanda ya bayyana hakan a Talatar nan yayin wani taron manema labarai da ya gudana, ya ce a halin yanzu yanayin hada-hadar tattalin arziki da cinikayyar kasa da kasa na cikin wani halin ha’ula’i, kuma sakamakon haka, matsayar yankunan raya tattalin arziki da fasahohi na muhimmin jigon daidaita hada-hadar cinikayyar waje, da zuba jari na kara bayyana a fili. Ya zuwa shekarar 2024, adadin irin wadannan...
Daliget sun tayar da jijiyoyin a wurin taron haɗakar siyasar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi domin fafatawa da shuagaban kasa Bola Tinubu na Jam’iyyar APC a zaɓen 2027. Ana tsaka da taron Kungiyar Tuntubar Siyasa ta Kasa Reshen Arewa a Abuja ne hayaniya ta kaure bayan tsohon sakataren gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal ya sanar da wanda suna daliget da zai wakilci Jihar Jigawa. Rashin gamsuwar sauran daliget din jihar dadi ba suka tayar da jijiyoyin wuya, inda suka hau kan mumbari suka dauke wanada aka ayyanan suka hana shi magana da yawunsu. Daba bisani an yi nasarar shawo kan rikicin, inda aka zabi dan...
Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, bisa bai wa ’yan Arewa mutum 12 manyan muƙamai a hukumomin gwamnati. Ya ce wannan matakin ya gyara rashin daidaito da ake gani a naɗin muƙaman da shugaban ya yi a baya, wanda ya janyo damuwa a yankin Arewa. Halin da fasinjoji ke ciki bayan hatsarin jirgin sama a Ilori Hakar man Kolmani: Jihohin Bauchi da Gombe sun gana da NNPC kan bukatun al’umma A ranar Juma’a ne Shugaba Tinubu, ya sanar da sunayen wasu ’yan Arewa da aka naɗa shugabanni a hukumomi kamar su Hukumar Inshorar Noma ta Ƙasa (NAIC), Shirin Tallafa wa Masu Ƙaramin Ƙarfi na GEEP, da Hukumar Inshorar...
“Wannan ci gaban zai kuma taimaka wajen kara habaka tattalin ardikin da ke a yankin na Arewa maso Gabas, wanda hakan ya zame mana wajbi, mu sake dawo wajen yin aikin domin aikin ya ci gaba da tafiya,” A cewar Ojulari. Kan batun rikicin da yaki ci, yaki cinyewa a tsakanin Kamfanin na NNPCL da kuma rukunomin Kamfanin Dangote Ojulari ya bayyana cewa, ana ci gaba da kokari domin a kawo karshen rikicin. “Dangote ya bayar da gagarumar gudunmawa wanda kuma, ya cannaci a yaba masa, za mu kuma yi hadaka domin mu tabbatar da, mun ci gaba da samar da wadataccen Man Fetur ga ‘yan kasar nan,” Inji Sabon Shugaban. “Ana samun masalaha kan komai ne, ta hanyar tattaunawa...
An dai fara goyon bayan tazarcen Tinubu a wurin taron lokacin da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya ce babu wani gurbi a fadar shugaban kasa a 2027. Barau ya ce, “A bayyane yake a 2027, za mu sami gagarumar nasara, In Sha Allah. Don haka, mu ci gaba da hanyar da muke kai. Mu hada kai da juna, mu yi aiki tare da shugaban kasa, mu yi aiki tare da kowa, mu hada kai a tsakaninmu don samun nasarar da ake bukata.” Sanata Barau ya ci gaba da cewa sauya shekan wasu shugabannin jam’iyyun adawa zuwa APC ya kasance sakamakon aikin Shugaba Tinubu a cikin shekaru biyu kawai da ya shafe a kan karagar mulkin Nijeriya. Kazalika, Ganduje...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kamfanin Dangote wanda ya mallaki matatar mai ta Dangote ya sanar da sake sabon ragin farashin man fetur na N15 a gidajen da ke hulɗa da shi. A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Alhamis, ya ce a sakamakon wannan ragi, ‘yan Najeriya za su sayi man fetur a kan farashi kamar haka: Naira 875 kowace lita a Legas; Za a sayar Naira 885 kowace lita a yankin Kudu maso Yamma; A Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya za a sayar kan Naira 895 kowace lita; yayin da za a sayar da shi kan Naira 905 kan kowace lita a Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu, da Arewa maso Gabas. Waɗannan farashin za su yi aiki ne...
Ya ƙara da cewa, “Kuma wajibi ne a gare mu, a matsayin mu na ƙwararrun ma’aikatan hulɗa da jama’a, mu daidaita da wannan lokaci ta hanyar amfani da dabarun sadarwa masu ɗauke da ƙwarewa, ƙima, da haɗin kai, domin ƙarfafa gwiwar al’ummar mu, a gida da waje, su shiga cikin farfaɗo da tattalin arzikin wannan babbar ƙasa.” Idris ya bayyana cewa aikin sake fasalin tattalin arziki ya faro ne tun daga ranar farko da Shugaban Ƙasa Tinubu ya hau mulki, lokacin da aka cire tallafin man fetur da kuma daidaita farashin musayar kuɗi — matakan da ya bayyana a matsayin “tushen farfaɗowar tattalin arzikin ƙasar nan.” Ya haƙƙaƙe da cewa waɗannan matakai sun haifar da wahalhalu da farko,...
Ya ƙara da cewa, “Kuma wajibi ne a gare mu, a matsayin mu na ƙwararrun ma’aikatan hulɗa da jama’a, mu daidaita da wannan lokaci ta hanyar amfani da dabarun sadarwa masu ɗauke da ƙwarewa, ƙima, da haɗin kai, domin ƙarfafa gwiwar al’ummar mu, a gida da waje, su shiga cikin farfaɗo da tattalin arzikin wannan babbar ƙasa.” Idris ya bayyana cewa aikin sake fasalin tattalin arziki ya faro ne tun daga ranar farko da Shugaban Ƙasa Tinubu ya hau mulki, lokacin da aka cire tallafin man fetur da kuma daidaita farashin musayar kuɗi — matakan da ya bayyana a matsayin “tushen farfaɗowar tattalin arzikin ƙasar nan.” Ya haƙƙaƙe da cewa waɗannan matakai sun haifar da wahalhalu da farko,...
Kungiyar Arsenal na shirin ɗaukar ɗan wasan gaban Sporting CP, Viktor Gyokeres kamar yadda jaridar wasanni ta football365 ta ruwaito. Arsenal ta fuskanci matsalolin ‘ƴan wasan gaba a kakar wasan da ke dab da ƙarewa, yayin da ƙungiyar ta gaza lashe kowane irin kofi. Bayan ƙarewa a mataki na biyu a Gasar Premier da samun gurbin zuwa Gasar Zakarun Turai ta baɗi, a yanzu hankalin ƙungiyar ya karkata kan samun ɗan wasan gaba, domin sake gina kanta. A ƙarshen kakar wasa da muke ciki ne Gyokeres ɗan asalin Sweden zai bar ƙungiyar Sporting bayan ƙarewar kwantiraginsa, kamar yadda Fabrizio Romano fitaccen ɗan jaridar wasanni ya bayyana a shafinsa na X. BBC
A baya-bayan nan, Bankin Duniya ya ce tattalin arziƙin Nijeriya ya ƙaru da kashi 3.4 cikin 100 a shekarar 2024, alamar cewa tattalin arziƙin na farfaɗowa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar kididdiga ta kasar Sin NBS, ta ce duk da matsi sakamakon dalilai na ciki da na waje, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa bisa daidaito a watan Afirilun da ya gabata. Alkaluman da NBS din ta fitar a Litinin din nan sun nuna karuwar hajojin da manyan masana’antun kasar ke samarwa da kaso 6.1 bisa dari a shekara, yayin da alkaluman samar da hidimomi suka karu da kaso 6.0 bisa dari a shekara. Sai kuma darajar jimillar hajojin sayayyar daidai, ta kayayyakin bukatun yau da kullum da ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 3.7, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 515.6 a shekara, adadin da shi ma ya yi karuwar kaso 5.1 bisa dari. Kazalika, alkaluman sun nuna daga watan Janairu...
A wancan lokacin,Mrs. Bintu M.Sadik, cewa tayi Sir S.M. Banaman shi ne Shugaban Kwalejin na farko duk kuma Malaman Turawa, daga baya ne aka dauke Hausawa ‘yan asalin wurin saboda su koyar da Hausa da kuma al’amarin daya shafi addinin musulunci.Ta ce mshahuran ‘yan Arewa sun halarci Kwalejin daga cikinsu akwai Firayim Minista na farko Abubakar Tafawa Balewa,Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Firimiyan Arewa, da kuma Sir Kashim Ibrahim, da dai sauran wasu duk sun halarci Kwalejin ta Katsina An samu labarin kasar Katsina ta taba kasancewa wata babbar cibiyar Kasuwanci ta Sahara. Wannan shi tun lokacin da aka hade Arewa da Kudancin Nijeriya Katsina tana daya daga cikin wuraren da hanyar jirgin kasa ta bi ko kuma Layin Dogo ...

Iran: Aiwatarda Yarjeniyar Zaman Lafiya Tsakanin Armenia Da Arzerbaijan Zai Tabbatar Da Zaman Lafiya A Tsakanin Kasashen Biyu
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa aiwatar da yarjeniyar zaman zaman lafiya wadanda aka cimma tsakanin kasashen Armenia da kuma Azerbaijan da gaggawa zai tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ta nakalto Aragchi yana fadar haka a lokacin ganawarsa da sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Armenia, Armen Grigoryan wanda yake ziyarar aiki a nan Tehran a yau Asabar. Ministan ya kara da cewa JMI zata tabbatar da cewa an aiwatar da sulhu tsakanin kasashen biyu da gaggawa saboda tana dasawa da kasashen biyu makobta gareta. A cikin watan Maris da ya gabata ne kasashen Armenia da Arzerbaijan suka amince a rubuta yarjeniyar...
Sai ya ce “Na riga na amsa wannan tambayar amma har yanzu kana sake maimaita ta. Idan dai za a iya tunawa, ‘yan jarida 43 mazauna Kaduna ne suka halarci taron, ciki har da wasu ‘yan jarida daga wasu jihohin da suka raka gwamnonin nasu. Don haka, ba daidai ba ne a ce na hana ‘yan jarida shiga taron gwamnonin Arewa. Duk jaridun kasar nan sun je a wurin. Duk gidajen rediyo da talbijin na Kaduna suna wurin. Duk wakilan manyan gidajen Talabijin da Rediyo da ke wajen Kaduna su ma suna nan. Kada ka dauki maganata a wani bangare daban, je ka bincika. Duk wadannan labarai ne irin na teburin mai shayi. Ni kuma ban sani ba. Abin da...
“Dangote ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaba wanda ya cancanci yabo. Muna kan tattauna yadda za a kawo karshen rigimar. Nan gaba, za mu yi aikin hadin gwiwa domin tabbatar da samar da wadataccen mai ga al’ummar Nijeriya,” in ji shi. Ya nuna cewa ta hanyar zaman sulhu za su kawo karshen matsalar, “Nan gaba kadan ba za ku ji wata rigima tsakanin NNPCL da matatar mai ta Dangote ba. Za mu yi aikin hadin guiwa domin amfanuwar ‘yan kasa.” Ojulari ya kuma yi tsokaci kan faduwar farashin danyen mai a duniya a baya-bayan nan, wanda ya rage kudaden shiga da ake sa ran Nijeriya za ta samu. “Wannan raguwar ta shafi kasafin kudin Nijeriya tun da babban...
Habakar matsayi na kasafin kudi ya inganta a cikin 2024, ta hanyar habaka kudaden shiga. Gibin kasafin kudi ya ragu daga kashi 5.4 na kudin shiga a shekarar 2023 zuwa kashi 3.0 na kudin shiga a shekarar 2024, babban ci gaban da aka samu sakamakon karuwar kudaden shiga na daukacin tarayyar kasar, wanda ya karu daga naira tiriliyan 16.8 a shekarar 2023 (7.2 na kudaden shiga) zuwa kimanin naira tiriliyan 31.200. Rahoton ya kara da cewa hauhawar farashin kayayyaki ya tsaya tsayin daka amma ana sa ran zai fadi zuwa matsakaicin shekara da kashi 22.1 cikin 100 a shekarar 2025, yayin da tsayin daka mai tsayi ya tabbatar da amincin manufofin kudi tare da rage tsammanin hauhawar farashin kayayyaki. Ko...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa zai dagewa kasar Siriya dukkan takunkuman tattalin arzikin da ta dora mata, kuma zai gana da shugaban gwamnatin riko na kasar Ahmad Sharaa wanda aka fi sani da Julani. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a wata tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar Saudiya a birnin Riyad na kasar Saudiya, inda ya fara ziyarar aiki a can tun jiya Talata. Shugaban ya kara da cewa: A yanzu lokaci yayi da mutanen kasar Siriya zasu huta, don zamu dauke dukkan takunkuman da muka dorawa kasar Siriya. Saboda zata samar da huldar Jakadanci da HKI kuma babu wata cuta da zata sami kasar daga Siriya. Wannan yana zuwa...
“Amma idan yanzu aka sake bai wa Arewa takara, wannan tsari tsakanin Arewa da Kudu zai ruguje.” Wike, wanda tsohon gwamnan Jihar Ribas ne, yana daga cikin fitattun jiga-jigan PDP da ke goyon bayan daidaito da karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa. A baya dai, rikici wajen tantance daga inda ɗan takarar PDP zai fito ya janyo rabuwar kai a cikin jam’iyyar, lamarin da ya taimaka wajen rage ƙarfinta a zaɓen 2023. Masana siyasa na ganin wannan gargaɗi na Wike na iya sake haifar da muhawara a jam’iyyar, musamman yayin da ta ke shirin fuskantar babban zaɓen 2027. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...

Sanarwar Hadin Gwiwa Ta Bayan Taron Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka
Kasar Sin za ta sauya matsaya kan adadin harajin fito da ta ayyana kan hajojin dake shiga kasar daga Amurka karkashin sanarwar sashen haraji na hukumar kwastam mai lambar 4 ta 2025, ta hanyar dage karin kaso 24 bisa dari a wa’adin farko na kwanaki 90, tare da wanzar da karin kaso 10 bisa dari kan kayayyakin, da jingine sauyin harajin fiton karkashin tanajin sashen haraji na hukumar kwastam mai lambar 5 na 2025, da sanarwar sashen haraji na hukumar kwastam mai lamba 6 na 2025. Kazalika Sin za ta aiwatar da dukkanin matakai na hukuma wajen dage sauran matakan ramuwar gayya da ba na karin haraji ba da ta ayyana kan Amurka tun daga ranar 2 ga watan Afirilun...
Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya bayyana cewa zai ci gaba da aikin haƙa danyen mai a Arewa da ke yankin Kolmani. Shugaban NNPCL, Bayo Ojulari ne ya sanar da aniyar kamfanin na ci gaba da aikin haƙar mai a yankunan arewa da gwamnatin Buhari da ta gabata ta fara. Bayo Ojulari ya kuma addada aniyar NNPCL na kammala aikin bututun iskar gas da ya taso daga Ajaokuta a Jihar Kogi ya bi ta Abuja da Kaduna zuwa Kano (AKK). A zantawarsa da kafar yaɗa labarai ta BBC, Injiniya Bayo ya ce, Za mu ci gaba da aikin haƙo mai a Kolmani da sauran wurare. Bayan aikin haƙo man, za mu kuma tabbatar da cewa mun gama aikin bututun man...
Gwamnoni da kuma Sarakunan gargajiya na Arewacin Nijeriya sun gudanar da taro a Kaduna, domin tattaunawa kan matsalolin rashin tsaro da suka addabi yankin. Taron wanda ya gudana ne a gidan gwamnatin jihar ta Kaduna, inda suka tattauna kan matsalar talauci da yaran da ba su zuwa makaranta da kuma sauran al’amura da suke damun yankin. An kama matashi da kawunan mutanen a Legas Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta Gwamnonin jihohin Katsina da Zamfara da Kebbi da Gombe da Neja da Filato da Yobe da Jigawa da Kogi da Adamawa da kuma Zamfara na cikin waɗanda suka halarci taron. A ɓangaren sarakunan gargajiya kuma akwai mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III da Sarkin Zazzau, Ahmed...
Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya fada a yau Asabar cewa: Ma’aikata ne jari mafi muhimmanci na samun zaman lafiya a cikin al’umma da kuma cimma manufar sunan da aka bai wa wannan shekarar na : “Zuba Hannun Jari Domin Yin Kere-Kere.” Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gana da ma’aikata da su ka fito daga sassan Iran, ya yi ishara da sake bude kamfanoni da dama a zamanin shugabancin Shahid Ra’isi, alhali gabaninsa an rufe su,tare da bayyana hakan da cewa daya ne daga cikin ayyukan da Shahidin ya aiwatar. Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma bayyana ma’aikatar da cewa, su nekashin bayan kowace al’umma, yana kuma mai yin addu’ar Allah ya ba su...

ECOWAS Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasar Tattalin Arzikin Afrika Ta Yamma – Kwamred Bishir Dauda
Na yi wannan wannan ziyara ne saboda shaukin da nike da shi a kan abin da ya shafi kishin kasata Nijeriya, da kuma neman hadin kan kasashen Afirika ta yamma mu zama tsintsiya madaurinki daya,da son zaman lafiya da ci gaban Dimokaradiyya. Kazalika, na yi wannan rangadi ne domin murnar cikar kungiyar ECOWAS shekara 50 da kafuwa. Kasan an kafa kungiyar ne ranar 28 ga watan Mayu,1975 bana kungiyar za ta cika shekaru 50. To kasancewa shekaru 50 sun wuce wasa na ga cewa, kungiyar ta cancanci a yaba mata, kuma a kara matakaimi da azama. Kuma za ka yarda da ni idan na ce ma cikin wadannan shekaru 50, Kungiyar ta taka muhimmiyyar rawa ta a zo a gani...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A wani bangare na manufofinsu na kara yawan masu kada kuri’a, Alhaji Gamawa ya bayyana cewa, kungiyar mai zaman kanta za ta taimaka wa ‘yan kasa wajen karbar katin zabe, “Lokacin da INEC ta bude dandalin rajistar katin zabe, za mu taimaka musu wajen karbar katin zabe domin su bada gudunmawa a zabe da kuma amfani da ’yancinsu. Gamawa ya kuma yi magana kan muhimmancin samun katin shaidar zama dan kasa, inda ya ce, yayin da tsaro ya yi karanci, abu ne mai sauki a laka wa dan Nijeriyar ba shi da katin dan kasa sharrin zama bako ko dan mamaya ko kuma sanya shi cikin masu garkuwa da mutane. “Rashin katin shaidar zama dan kasa babbar matsala ce ga...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hukumomi a jihar Yobe sun ɗora alhakin ƙazancewar matsalar tamowa a kan rikicin Boko Haram da rashin shayar da jarirai nonon uwa yadda ya kamata da kuma gurɓacewar harkar kiwon lafiya, da sauran su. Bayanin hakan na zuwa ne bayan Babban Jami’i mai Kula da Ayyukan Jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mista Mohamed Malick Fall, ya sanar cewa yara miliyan daya a jihohin Borno da Adamawa da Yobe suna fuskantar barazanar rasa rayukansu sakamakon cutar tamowa a bana. An kuma ruwaito shi yana cewa wannan adadi ya ruɓanya na yaran da suka fuskanci barzanar a bara. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ’Ya’yansu DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan...

Bisa Rokon Bangaren Amurka Ne Manyan Jami’In Kasar Sin Zai Tattauna Da Takwaransa Na Gwamnatin Amurka Kan Batun Ciniki Da Tattalin Arziki
Yau Alhamis, kakakin ofishin jakadancin Sin dake Amurka ya amsa tambayoyi game da taron koli na tattaunawa kan batun ciniki da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka. A cewar kakakin, bangaren Amurka ta aikewa kasar Sin sakwanni da dama ta hanyoyi daban-daban don bayyana fatanta na tattaunawa da Sin kan batun harajin kwastam da sauransu. Kuma Sin ta yanke shawarar amincewa da shawarwarin ne bayan ta nazarci sakwannin da Amurka ta aika mata, kuma bisa rokon bangaren Amurka ne za a gudanar da shawarwarin. Ya ce Sin na nacewa ga matsayin kin yarda da matakin Amurka na yi gaban kanta wajen kakkabawa sauran sassan duniya harajin kwastam, kuma za ta ci gaba da kiyaye muradunta mai dacewa da kiyaye...
Burin Arsenal na lashe gasar UEFA a karon farko a tarihinta ba zai cika a wannan shekarar ba, sakamakon rashin nasarar da ta yi a hannun PSG a wasan zagayen na kusa da na karshe, Arsenal ta buga wasan karshe a UEFA sau daya a shekarar 2006 tsakaninta da Barcelona. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani sabon rikici ya dabaibaye Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma (NWDC) kan shirin daukar nauyin dalibai zuwa karatu a kasashen waje. Wannan dambarwar ta kunno kai ne bayan sanarwar da hukumar ta fitar na shirin daukar nauyin daliba domin karatun jami’a daga yankin. Majalisar Amintattun Hukumar ta ce ba a taba tattaunawa kan shirin a zamanta ba, a yayin da majalisar gudanarwar Huukumar ke ikirarin cewa ta sanar da su ta wata wasika da ta aike musu. Wasu mambobin Kwamitin Amintattun hukumar da wakilinmu ya zanta da su sun zargi hukumar gudanarwar da yin gaban kanta. Hajj 2025: Maniyyatan Kaduna za su fara tashi ranar 14 ga watan Mayu Wata mata ta auri maza biyu a lokaci guda a...
An labarto cewa harin ya wakana ne da safiyar ranar Lahadi kuma ‘yan bindigan sun yi awun gaba da shanu da sauran dabbobin al’umman yankin a yayin farmaƙin. Kazalika, wakilinmu ya gano cewa baya ga ‘yan bijilante da suka rasa rayukansu akwai wasu fararen hula mazauna ƙauyen Sabuwar Sara su ma sun gamu da ajalinsu yayin da suke ƙoƙarin gudun neman tsira bisa harbe-harben ‘yan bindigan. Sai dai bayanai sun tabbatar da cewa su ma ɓangaren ‘yan fashin dajin sun rasa mutanensu da dama da ake hasashen sun ma fi ‘yan Bangan mutuwa. Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ba ta bayyana haƙiƙanin adadin mutanen da suka rasa rayukansu a ɓangaren ‘yan...
Al’ummar Arewa mazauna yankin Obalande da ke Jihar Legas sun yunƙura domin tunkarar matsalolin da ke ci musu tuwo a ƙwarya, musamman yadda suka ce ’yan ƙasa ke musu cin kashi. Sun ce sun gaji da irin tsangwama da ƙasƙanci da ’yan ƙasa a yankin ke nuna wa ’yan Arewa, musamman Hausawa mazauna. Sun bayar da misali bisa yadda samarin Yarabawa daga wasu unguwanni suka mayar da unguwar tasu filin ƙwallon ƙafa, inda suke tilasta musu rufe rumfunansu na kasuwa, har sai an gama buga ƙwalon kafin su ci gaba da sana’arsu. A kan haka ne suka yi wani zama da Shugaban Karamar Hukumar Ikoyi Obalande (LCDA) Fu’ad Lawal Atanda da shugabannin siyasa ’yan Arewa a jihar, da nufin cire...
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yaba wa takwarorinsa na gwamnonin Jihohin Borno, Bauchi, Adamawa, Gombe da Taraba a bisa ga samun damar da suka yi na halartar taron ƙungiyarsu ta Arewa maso Gabas (NEGF) karo na 11 a garin Damaturu. Ya yi wannan yabo ne a ranar Alhamis a ɗakin taro na gidan gwamnati da ke Damaturu yayin jawabinsa na maraba yadda ya bayyana fatansa cewa, taron zai samar da sabbin dabarun yaƙi da rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki. Sojoji sun ceto fasinjoji 99 daga hatsarin kwale-kwale a Ribas Gobara ta lalata shagunan kasuwar waya a Kwara Buni ya bayyana wannan ƙungiyar a matsayin wani muhimmin dandali na haɗin gwiwa da daidaita manufofi, musamman yadda yankin ke fama da...
Gwamnan Zulum ya yi tsokaci dangane da yadda tabarbarewar harkokin tsaro ke ci gaba da zafafa a yankin, yayin da kuma ya yaba wa kokarin sojojin Nijeriya, inda ya ce, “Ina kira gareku, ku ci gaba da yaki da yan ta’adda har sai mun kawo karshen wannan matsalar.” “Dawowar hare-haren yan ta’adda a cikin jihohinmu wani al’amari ne mai matukar tayar da hankali wanda hakan zai iya wargaza nasarorin da aka samu a fagen yaki da matsalolin tsaro a yankin. Ina mai bayar da shawarar cewa, sojojinmu su fadada sabbin dabarun da suke dasu wajen dakile farmakin yan ta’adda.” Gwamna Zulum ya ce, “kangin talaucin da yankinmu yake fuskanta, abin tsoro ne, kuma ya zama dole mu dauki...
Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Ridha Arif ya bayyana cewa; Da akwai bukatar fadada da bunkasa alakar dake tsakanin Iran da Sudan, sannan ya kara da cewa; Iran din a shirye take ta yi aiki da Sudan domin bunkasa sana’o’inta. Mataimakin shugaban kasar ta Iran ya furta haka ne dai a lokacin da ya gana da ministar masana’antu ta Sudan Mahasin Ali Yakub da ta kawo Ziyara Iran. Muhammad Ridha Arif ya yi wa Sudan fatan alheri da son ganin zaman lafiya ya dawo, sannan kuma ya bayyana sake bude ofishin jakadancin Sudan a Tehran a shekarar da ta gabata a matsayin alamar kyautatuwar alaka a tsakanin kasashen biyu. Mataimakin shugaban kasar ta Iran ya zargi kasashen turai...
Iran ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Jamhuriyar Nijar. Mataimakin shugaban kasar na farko Mohammad-Reza Aref ya ce Iran na ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Nijar da sauran kasashen nahiyar Afirka bisa tsarin juyin juya halin Musulunci. Aref ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da ministan man fetur na kasar Nijar Sahabi Oumarou wanda ke Tehran, inda yake jagorantar wata tawaga, domin halartar taron hadin gwiwar tattalin arzikin Iran da Afirka karo na uku. Ya ce da gaske ne gwamnatin Iran mai ci a yanzu tana son raya dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka ciki har da Nijar dangane da batutuwan da suka dace....
’Yan siyasar yankin Arewa na ganin dole sai da goyon bayansu ɗan takara zai yi nasara a zaben Shugaban ƙasa. Hakan na zuwa ne bayan tsohon maitaimaka wa shugaban ƙasa a fannin siyasa, Alhaji Hakeem Baba-Ahmed ya yi wata hira, inda yake cewa, nan da wata shida yankin zai fitar da matsayarsa. An ɗaure ’yar shekara 80 a kurkuku saboda dukan jikarta da silifas Dalilin da manyan ’yan siyasa ke barin NNPP — APC Duk da cewa Hakeem ba shi ne mai magana da yawun al’ummar yankin ba, amma ana kallon sa a matsayin daya daga cikin manya a yankin, saboda tsohon matsayinsa na mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa (NEF). Tsarin siyasar kasar nan ya sa dole ne...
A yammacin ranar Talata Arsenal ta karbi bakuncin PSG a matakin wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai na bana. An dai barje gumi ne a filin wasa na Emirates, inda PSG ta yi wa Arsenal ci daya mai ban haushi har gida. DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya ISWAP ta ɗauki alhakin kashe mutum 26 a Borno PSG ta fara cin ƙwallo ta hannun Ousmane Dembele a minti na huɗu da take leda, haka suka je hutu har da zagaye na biyu, amma Gunners ba ta farke ba. Wannan shi ne karo na biyu da suka fuskanci juna a Champions League a kakar nan, inda Gunners ta yi nasarar cin 2-0...
Wani bon kirar hannu da aka dasa akan hanyar dake hada Rann da Gamboru a jihar Borno ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 6. Daga cikin wadanda su ka rasa rayukansu sanadiyyar tashin bom din sun hada mata da kananan yara kamar yadda majiyar ‘yan sanda ta sanar. Kungiyar nan mai suna; gwamnatin musulunci a yammacin Afirka ce ta sanar da daukar alhakin kai hari na ranar Litinin din da ta gabata. Bugu da kari sauran wadanda su ka rasa rayukan nasu manoma ne da suke cikin motar a-kori-kura da ta taka nakiya. Baya ga wadanda su ka rasa rayukansu, wasu mutanen su 3 sun jikkata,kuma tuni an dauke su zuwa asibiti domin yi musu magani. Wani dan sintiri da yake...
Wannan ya sa wasan yau zai zama mai ɗaukar hankali, domin kowanne daga cikinsu na burin ɗaukar kofin a karo na farko, domin a dakatar da yawan dariyar da ‘yan adawa ke musu. A zagayen rukuni da suka haɗu a farkon wannan kakar, Arsenal ta lallasa PSG da ci 2-0. Kocin Arsenal yanzu, Mikel Arteta, ya taɓa buga wasa a duka ƙungiyoyin. Yana fatan ya zama kocin farko da zai jagoranci Arsenal ta lashe kofin Zakarun Turai. Wannan ya sa magoya bayan Arsenal ke fatan ganin ƙungiyarsu ta yi abin mamaki a wasan da za a fara da misalin ƙarfe 8 na dare agogon Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Tawagar jami’ai da ‘yan kasuwan kasar Tunisiya ta gana da mataimakin shugaban kasar Iran A yayin ganawarsa da ministan kasuwanci da fitar da kayayyaki na kasar Tunisiya Samir Ben Salem Obeid, mataimakin shugaban kasar Iran na farko na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Mohammad Reza Aref ya jaddada cewa: Lokaci ya yi da za a dauki kwararan matakai wajen fadada dangantakar tattalin arziki tsakanin Iran da Tunusiya. A yayin taron, wanda aka gudanar a ofishinsa tare da halartar jakadan kasar Tunisiya a Iran Imed Rahmouni da tawagar da ke tare da shi, Aref ya bayyana cewa, dangantakar siyasa da ke tsakanin al’ummar Iran da Tunisiya na tafiya cikin wani yanayi mai ma’ana, amma hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya ya kasance...
Kazalika, domin daidaita ci gaban cinikayyar waje, manufofin da za a aiwatar sun hada da na tallafawa kamfanonin dake fitar da hajoji, ta yadda za su rage hadurra daka iya aukuwa, da fadada fitar da hidimomin da ake samarwa ga karin sassan duniya, da karfafa gwiwar kamfanonin waje, ta yadda za su kara zuba jarinsu a kasar ta Sin. Daga nan sai jami’in ya bayyana cewa, Sin na da isassun manufofi da tsare-tsare, da za su wanzar da burinta na raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma a shekarar nan ta bana. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
Sun ƙara da cewa, “Samun shugabannin matasa masu jajircewa a wannan yankin babbar albarka ce ga al’ummarmu. “Hakan na nuna mana cewa akwai kyakkyawar makoma ta ci gaba a Arewa gaba ɗaya.” Sannan sun bayyana cewa sun aike wa ƙungiyoyinsu a dukkanin jihohi 19 na Arewa goron gayyata domin naɗin sabbin muƙamai a Masarautar Daura. “Za a gudanar da babban taron karramawa wanda ba a taɓa ganin irinsa ba a nan kusa, domin naɗin sabbin muƙamai da Masarautar Daura za ta yi.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
Sun ƙara da cewa, “Samun shugabannin matasa masu jajircewa a wannan yankin babbar albarka ce ga al’ummarmu. “Hakan na nuna mana cewa akwai kyakkyawar makoma ta ci gaba a Arewa gaba ɗaya.” Sannan sun bayyana cewa sun aike wa ƙungiyoyinsu a dukkanin jihohi 19 na Arewa goron gayyata domin naɗin sabbin muƙamai a Masarautar Daura. “Za a gudanar da babban taron karramawa wanda ba a taɓa ganin irinsa ba a nan kusa, domin naɗin sabbin muƙamai da Masarautar Daura za ta yi.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
Gamayyar Ƙungiyoyin Matasan Arewa, sun yaba wa Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk, bisa bai wa Nasir Bala Ja’o’ji muƙami a Majalisar Zartaswa ta Babbar Kwalejin Ilimi da Fasaha ta Tarayya, Potiskum, da ke Jihar Yobe. A wata wasiƙar taya murna da shugaban shiyyar ƙungiyar, Makama Dan Kaduna, ya sanya wa hannu bayan wani taro da suka gudanar a Kaduna, sun ce Ja’o’ji mutum ne mai kishin matasa da ƙoƙarin inganta rayuwarsu. Magidanci ya kashe kansa saboda mutuwar matarsa a Neja An gano tsohuwar da ake nema a cikin maciji Sun bayyana cewa, “Wannan muƙami da Sarkin Daura zai ba shi, ya ƙara tabbatar da binciken da muka gudanar wanda ya nuna cewa Ja’o’ji yana cikin shugabannin matasa 10...

Saboda In Nuna Wa Duniya Asalin Al’adar Bahaushe Ya Sa Na Fara Fina-finan Turanci A Arewacin Nijeriya – Jammaje
A wata hira da Jammaje ya yi da rfI Hausa an jiyo shi ya na cewa sunana Kabiru Musa Jammaje haifaffen Jihar Kano, nayi karatu a Bayero Unibersity da ke birnin Kano inda na karanci English kafin in tafi kasar Amurka domin zurfafa karatu, bayan na dawo gida Nijeriya kuma na shiga Jami’ar koyo daga gida ta NOUN inda na karanci ‘Education Administration and Planning’. Jammaje ya ci gaba da cewa a yawace yawacen da na yi na tafi kasashe irinsu Afirika Ta Kudu da kasar Kenya inda a wancan lokacin sai na lura cewa mutanen wadannan kasashen biyu suna yi wa duk wani dan Nijeriya wani kallo na daban sakamakon abin da suka ga ana nunawa a wasu...
A shekarar bara, ’yan kasuwa, musamman masu hadahadar kayan abinci da na amfanin gona a Nijeriya, kakarsu ta yanke saka, saboda tashin gwauron zabon da kayan a kasar. Galibin wadannan amfanin gona na kasuwanci ana fitar da su zuwa kasashen a duniya. Hukumar Bunkasa Fitar da Kayayyaki ta Nijeriya (NEPC) ta sanar a watan Agusta na shekarar ta 2024, cewa Najeriya ta samu gagarumin ci-gaba a fannin fitar da kayayyaki da ba na man fetur ba a watanni shidan farkon shekarar, inda ta samu kudin shiga kimanin dala biliyan 2.7. Yawan bukatar kayan a kasuwannin duniya ya kawo hauhawar farashin kayan abinci na yau da kullum da amfanin gona na kasuwanci. An kuma yi hasashen cewa farashin zai ci gaba...
Rundunar Sojin Najeriya ta samar da cewa dakarunta sun kashe ’yan ta’adda 1,770, sun kama wasu 3,070 a yankin Arewa maso Yamma a shekaru uku da suka gabata. Rundunar ta kuma yi nasarar ceto mutane fiye da 2,515 da harin ya rutsa da su ta hanyar gudanar da ayyukan haɗin gwiwa a jihohin da lamarin ya shafa. Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ne ya sanar da hakan a yayin wani gangamin wayar da kan jama’a a Jihar Katsina, wanda aka gudanar ga mazauna ƙananan hukumomin Batsari da Dutsin-Ma. Janar Musa ya ce, sun kuma ƙwato sama da makamai 1,000 da alburusai 12,000 a hare-haren da suka kai a jihohin Arewa maso Yamma guda biyar, wato Katsina, Kaduna, Kebbi,...
Bayan ya sake daga sabowar tutar kasar Siriya a cibiyar MDD da ke birnin NewYork ministan harkokin wajen kasar Siriya Asaad Al-shaibani, ya gabatar da jawabi a gaban kwamitin tsaro na MDD a jiya jumma’a inda ya roki kwamitin ya dagewa kasarsa takunkuman tattalin arziki wadanda aka dorawa gwamnatin da ta shude. Jaridar Middle eart Eye ta kasar Burtaniya ta nakalto Al-shaibani ya na cewa takunkuman suna hana ruwa guda a cikin al-amura da dama a kasarsa, kuma suna hana kafuwar gwamnatinsa su kamar yadda ya dace. Ministan ya ce dage takunkuman ya zama wajibi don samun ci gaban kasar don kuma rage matsin lamban da mutanen kasar suke ciki. Kasashen yamma musamman Amurka da tarayyar Turai da kuma MDD...
Duk da kasancewarta matar aure kuma uwa daga Arewacin Nijeriya, sannan kuma ga karatu tana yi, a lokaci guda, amma hakan bai hana ta samun nasarar zama gwarzuwar ɗalibar da ta kafa sabon tarihin da sai da aka shekara 35 rabon da a samu wani mahaluki da ya kafa irinsa a fannin ilimin shari’a. A yayin da take karatu, A’isha Widad, mai shekara 24 a duniya, ta fuskanci ƙalubalen da suka danganci haɗa karatu mai zurfi da kuma rayuwar aure — kama daga ɗawainiyar kula da gida zuwa na juna biyu da na jego da kuma shayarwa — amma duk da haka, ta kafa tarihin zama mutum ɗaya tilo da ta kammala digirinta na farko da Daraja na ɗaya (First...
Ya koka kan halin da kasar ke ciki, kuma ya bukaci ‘yan arewa da su yi taka-tsantsan da ‘yan siyasa masu rarraba kawunan mutane da yaudara, gabanin babban zabe mai zuwa. “Muna son gwamnati da za ta fahimci matsalolinmu kuma ta magance su. Bayan shekaru takwas na mulkin Muhammadu Buhari, mun dauki darasi. ”Yanzu haka muna cikin wata gwamnati, kuma har yanzu muna kuka. Kuka kadai ne muka san yadda za mu yi?” Baba-Ahmed ya tambaya. Baba-Ahmed ya ce arewa ta sha wahala sosai a lokacin Boko Haram, wanda ya shafi dukkan kungiyoyi, ciki har da Musulmi da Kiristoci da Fulani da Baju, da sauransu, yana mai jaddada bukatar hadin kai. “Kafin Buhari ya zama shugaban...
Ya kara da cewa kungiyar dattawan Arewa ba za ta lamunci cin zarafin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba. Sai dai da take magana da LEADERSHIP, ACF ta bayyana cewa kungiyar ba za ta goyi bayan duk wani dan takarar shugaban kasa a bainar jama’a a zaben 2027 ba. Da yake magana ta wayar tarho a ranar Lahadi, sakataren yada labarai na ACF na kasa, Farfesa T.A. Muhammad Baba, wanda aka nemi ya yi tsokaci kan kalaman Baba-Ahmed, ya ce a matsayinsa na dattijo, Baba-Ahmed yana da ‘yancin bayyana ra’ayinsa. Mai magana da yawun ACF, duk da haka, kungiyar za ta bincika dukkan batutuwan tare da gabatar da su ga masu jefa kuri’a don su iya yin zabi...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kungiyar Shugabannin Arewa (NEF) ta zargi Shugaba Bola Tinubu da nadin mukaman gwamnati ba tare da daidaito tsakanin yankunan Nijeriya ba, wanda ta ce yana fifita yankin Kudu maso Yamma a kan sauran yankuna shida na kasar. Mai magana da yawun kungiyar, Farfesa Abubakar Jiddere, a cikin wata sanarwa a yau Juma’a a Abuja, ya bayyana cewa nadin da aka yi sun karkata ne wajen goyon bayan Kudu maso Yamma, yayin da sauran yankunan suka samu kadan ko kuma aka danne su. Gazawar Gwamnatin Tinubu Ce Ke Haddasa Zubar Da Jini A Filato – Ƙungiyar Dattawan Arewa Rurum Ya Shawarci Mafarautan Arewa Da Su Daina Zuwa Kudu Farauta NEF ta bayyana cewa wannan lamari ya sabawa tsarin hadin kan kasa,...
Bugu da kari, masharhanta da dama na ganin karin harajin fito ba zai warware matsalar da Amurkan ke ciki ba. Ko shakka babu idan Amurka na son ta tunkari wannan kalubale bisa gaskiya, sai ta sauya tsarin ilimi, ta kuma bunkasa fannin kirkire-kirkirenta, da daga martabar masana’antu, da zuba jari na dogon lokaci a fannin, ba wai matakin jeka-na-yika na gajeren lokaci, irin wannan na baiwa kasuwa kariyar cinikayya ba. A daya hannun kuma baya ga illar da wannan kare-karen haraji ya haifar, matakan kasashen da lamarin ya shafa na ramuwar gayya na iya haifar da hauhawar farashi na gaggawa, da jefa tattalin arzikin sassa daban daban cikin halin komada, a maimakon fatan da gwamnatin Amurkan ke yi na...
Mutane 47 ne suka rasa rayukansu tare da jikkatan wasu da dama a harin da aka kai da jirgin sama kan birnin El-Fasher na kasar Sudan Runduna ta 6 da ke yankin El- Fasher ta sanar da mutuwar fararen hula 47 tare da jikkata wasu da dama sakamakon kazamin lugudan wuta da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka yi kan birnin El- Fasher, fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa. A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce: Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces na ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula, inda suka yi amfani da harsasai masu yawa a yayin da suka yi ruwan wuta a kan unguwannin birnin El-Fasher a...
Asusun bayar da lamuni na duniya ( IMF) ya yi gargadin cewa rashin tabbataci da Karin kudin harajin Amurka ya haddasa zai iya kawo tsaiko a cikin harkokin cinikiyya ta duniya. Sanarwar wacce babban jami’in ttatalin arziki na Asusun bayar da lamunin na duniya Pierre -Oliver-Gourinchas, ya bayyana ta kara da cewa; Za a iya samun karuwar hargitsi a cikin harkokin tattalin arzikin na duniya da dama yake fama da matsala. Jami’in ya yi bayani ne bayan sake yin hasashe akan ci gaban tattalin arzikin duniya, wanda aka fitar a cikin rahoto a ranar Talatar nan. Asusun bayar da lamunin ya yi hasashen cewa tattalin arzikin duniyar zai bunkasa da kaso 2.8 % a cikin 2025, da hakan yake nuni...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki ta zama tamkar gwal a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda a wasu yankuna aka ba da rahoton samun ta sa’o’i biyu kawai a rana, wasu kuma ba sa samun ko daidai da dakika ɗaya. Masu ƙananan sana’o’i suna kallon rayuwarsu da kasuwancinsu suna durƙushewa yayin da kayan sana’arsu suke lalacewa saboda rashin wuta. NAJERIYA A YAU: Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Tsarin Mulkin Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan wannan matsala da yadda take taɓa rayuwar al’umma da hanyoyin magance ta. Domin sauke shirin, latsa nan
Tsohon mashawarcin Shugaba Bola Tinubu kan harkokin siyasa, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa babu wani ɗan siyasa da zai iya lashe kujerar shugabancin Nijeriya a Zaɓen 2027 ba tare da goyon bayan yankin Arewacin ƙasar ba. Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana hakan a wata hira ta bidiyo tare da tsohon Babban Sakataren Hukumar Kula da Inshorar Lafiya (NHIS), Farfesa Usman Yusuf. NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye cikin littafai ana shirin kaiwa Saudiyya Zaɓen 2027: Me ya sa jam’iyyu ke neman tabarrakin Buhari? Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba yankin Arewacin Nijeriya zai fuskanci alƙiblarsa ta siyasa. “Nan da watanni shida mutanen Arewacin Nijeriya za su fayyace inda suka dosa, saboda haka zaɓi ya rage wa...
Karamin Ministan Tsaro a Najeriya Bello Matawalle, ya caccaki masu sukar lamirin Shugaban Kasa Bola Tinubu game da nuna wariya ga yankin Arewacin Najeriya. Matawalle ya ce Tinubu kadara ne ga Arewa kuma ba shi da fatan da ya wuce ganin ya magance matsalolin da suka addabi yankin kafin 2027. Cikin wani jawabi da mai taimaka masa kan sha’anin siyasa Ibrahim Danmaliki Gidan Goga ya fita, Matawalle ya ce ba a taba samun lokacin da ake yin dimokradiyya mai tsafta kamar a zamanin Bola Tinubu ba. ’Yan Najeriya miliyan 150 sun samu ingantacciyar wutar lantarki – Minista Ya ce duk masu kushe salon mulkinsa kawai suna huce haushin rashi ne da yada farfaganda da karairayi. “Mutanen Arewa suna da wayewar...
Ya bayyana cewa shiga wani yanki da ba a fahimtar yaren juna ɗauke da makamai na iya janyo fargaba da tashin hankali. “Ka yi tunanin idan wasu daga Kudu sun shigo ƙauyanku ɗauke da makamai kuma ba ku fahimtar yaren juna — za ku ji tsoro. Haka nan idan mutanenmu suka shiga yankin Kudu da makamai, su ma za a ji tsoro,” in ji shi. Rurum ya ce zai gana da shugabannin ƙungiyoyin masu farauta a jihar domin daƙile wannan ɗabi’a, ya kuma buƙace su da su nemo hanyar nema wa kansu asiri . “Wasu su tafi farauta su dawo ba tare da sun kamo ko ɓeran daji ba. Bai dace su ci gaba da haka ba. Ya kamata mu...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Dakta Zainab Muhammad ’yar Arewacin Najeriya ce da ta jajirce tare da ƙudirin cika burinta na karantar fannin kimiyya duk da ƙalubalen da matan yankin suke fuskanta wurin karantar fannin. Dakta Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci ɗaya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala, wanda a mafi yawan lokuta, ba mata kaɗai ba, har da mazan ma na ƙaurace wa karatar sa. NAJERIYA A YAU: Dalilan Rikice-Rikice A Jihar Filato DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo Zainab ƙwararriyar likita ce wacce ta shahara wajen kula da marasa lafiya a asibitoci. Domin sauke shirin, latsa nan
Don su wuce zuwa zagaye na gaba, Real Madrid na buƙatar ta zura ƙwallaye huɗu ba tare da ta bari Arsenal ta zura ƙwallo ko ɗaya ba. Idan kuma suka ci ƙwallo uku, kamar yadda Arsenal ta ci su, za a ƙara lokaci domin a fidda wanda yi nasara. Fitaccen ɗan wasan Faransa, Kylian Mbappe, wanda bai taɓa lashe gasar Zakarun Turai ba, yana fatan ya lashe kofin karo na farko tare da Real Madrid. Wannan wasa zai ba shi damar jan ragamar ƙungiyar don yin nasara a gaban dubban magoya bayanta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
Zulum ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su maida hankali wajen samar da damammaki ga matasa a arewacin Nijeriya. A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Sarakunan Arewa kuma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa, taron da aka yi a Jihar Borno an yi shi ne domin karfafa hadin kan jihohin Arewa da kuma tattaunawa kan halin da yankin ke ciki domin tallafa wa shugabannin siyasa wajen magance matsalolin da ke addabar Arewa. Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) da babban hafsan tsaro (CDS) da babban sufeton ‘yansanda (IGP) duk sun samu wakilci a taron sarakunan. Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa...
Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan gargajiya ta Arewa a wani taronta karo na bakwai da ta gudanar a ranar Talata. Taron wanda ya gudana a birnin Maiduguri, an yi shi ne domin lalubo hanyoyin ƙarfafa tsaro da haɓaka ci gaban yankin.
Ban da haka, Wang ya ce matakan kasar Amurka sun karya ka’idojin kungiyar WTO na rashin nuna bambanci, da takaita karbar haraji, kana suna girgiza tsarin tattalin arzikin duniya, da tushen tsarin cinikayya da ya shafi bangarori daban daban. Ganin haka ya sa kasar Sin daukar matakan ramuwar gayya kan kasar Amurka, don kare halaltacciyar moriyar kai, gami da neman tabbatar da adalci a duniya. Da ma shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya gabatar da jerin zafafan matakan tattalin arziki ne don neman daidaita matsalolin da kasar Amurka ke fuskanta. Sai dai ra’ayinsa na dora “Amurka ta zama gaba da komai” na tarnake masa damar samun biyan bukata. Raymond Thomas Dalio, shahararren mai kula da sha’anin hada-hadar...
Da yake jawabi a madadin shugaban kasa, Gwamna Uba Sani ya bayyana mahimmancin hanyar wadda ta hada babban birnin tarayya da jihohi sama da 12 dake fadin shiyyar Arewa ta tsakiya, Arewa maso Yamma, da Arewa maso Gabas. A yayin taron da aka yi a Jere a karamar hukumar Kagarko a ranar Lahadin da ta gabata, Gwamna Sani ya bayyana cewa, an yi biris da aikin hanyar na tsawon shekaru da dama, wanda ya janyo asarar rayuka da kuma illa ga ci gaban tattalin arzikin yankin. Sai dai Gwamnan ya kafa uzurin cewa, baya ga kudade, rashin tsaro da ake fama da shi a hanyar Kaduna zuwa Abuja a lokacin ne kamfanin Berger ya ki zuwa wurin domin...
Matainakin shugaban kasar kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya bayyana cewa, daukewa Iran takunkuman zalunci wadanda kasashen yamma suka dora mata na daga cikin asalin hakkin kasar da aka tauye. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aref yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma kara da cewa, kasar Iran ba zata manta da hakkin kasar wanda Amurka ta take tun farkon nasarar juyin juya halin kasar shekaru 46 zuwa yanzu ba, amma duk da haka sun bata damar tattaunawa. Yace: Muna son mu nunawa duniya kan cewa har yanzun muna hakuri, amma ba zamu taba manta da zaluncin da aka yi mana ba. Mataimakin shugaban yana maganar ficewar kasar Amurka daga yarjeniyar JCPOA da...
Jiragen yakin HKI HKI sun yi ruwan boma-bomai kan astin Al-Ahli, asbiti tilo da ya rage yake aiki a arewacin zirin Gaza, a safiyar yau Lahadi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin HKI sun wargaza bangaren ’emagencu’ bukatar kula na gaggawa a asbitin da kuma kofar shiga asbitin. Har’ila yau hare-haren sun lalata bangaren Iskar Oxigen na kula da wadanda suke bukatar kula mai tsanani a asbiti. Kuma sanadiyyar haka mutane da dama sun rasa rayukansu awannan bangaren daga ciki har da wani yaro dan shekara 12 wanda ya ji rauni a kai. Razan Al-Nahhas wani likita mai aiki a bangaren kula na gaggawa a asbitin ya fadawa kafafen yada labarai kan cewa wannan...
Lamarin ya faru ne a lokacin da matashin mawakin yake kan dandamali ya na rera daya daya daga cikin fitattun wakokinsa, har zuwa lokacin wannan rahoto, Bilal Billa bai fitar da wata sanarwa a kafafen sadarwar ba, amma kuma faruwar lamarin ya janyo cece kuce inda wasu a bangare guda ke ganin abin da aka yi wa mawakan ya yi daidai yayin da wasu kuma ke ganin hakan bai dace ba. Wasu na ganin cewar kalmar nan ta bahaushe da ya ce “Bokan Gida Bai Ci”, shi ne ke faruwa a kan wadannan mawakan, wasu kuma na ganin wannan wata hanya ce da aka dauko domin dakile tauraruwarsu da ke haskawa, wasu kuma ke cewa wannan kawai wata hanyar nuna...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya yi wata muhimmiyar ganawar sirri da shugabannin sojojin Nijeriya a Abuja ranar Alhamis. Taron wanda ya gudana daban-daban tare da babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Olatubosun Oluyede da babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ikechukwu Ogalla da babban hafsan sojin sama, Air Marshal Hasan Bala Abubakar na shirin sake tura wani sabon yunƙuri na ɗaukar matakin haɗa kai kan maharan Boko Haram. Sanƙarau: An tabbatar da ɓullar cutar ga mutane 300 a Sokoto An saki fasto an kuma tsare wanda ya kai kuɗin fansa Majiyoyi daga taron sun bayyana cewa, tattaunawar ta ta’allaka ne kan ƙarfafa ayyukan soji a yankin Arewa maso Gabas, da inganta musayar bayanan sirri da magance...
Ba kamar kayayyakin manyan kamfanoni irin su Ajinomoto, Bedan wadanda aka zuba su a cikin kwali, ana sayar da su cikin lafiyayyen mazubi kuma NAFDAC ta amince da su ba, wadannan danyun kaya ne da ba su da wata alama. Babban abin ban tsoro shi ne ba za a iya gano masana’antunsu don bincikar sahihancinsu ba. Da alama a yankin Arewacin Nijeriya din ake yin su amma an gaza gano hakan ko kuma an gano amma wa’alla saboda yawan bukatu an kasa dakilewa. Bincike ya nuna cewa a kasuwar Singer da Abubakar Rimi da ke Kano, ana sayar da buhu mai nauyin kilo giram 25 na wannan sinadari kan Naira 45,000, wanda ke bai wa ‘yan kasuwa damar sayar da...
Sanata Oluremi Tinubu yt gana da sarakunan Taraba, ta kuma ba da gudummawar naira miliyan 50 don tallafa wa mata 1,000, da kayan aiki dubu 10,000 ga ma’aikatan lafiya Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Bola Ahmed Tinubu, ta bukaci shugabannin gargajiya da su marawa shirin ta na sabon fata ta hanyar wayar da kan jama’a game da shirye-shiryen kiwon lafiya da ke gudana a fadin kasar. Misis Tinubu ta yi wannan roko ne a Jalingo, babban birnin jihar Taraba, yayin wata ganawa da sarakunan gargajiya a ranar Alhamis, wanda aka gudanar a dakin taro na uwargidan gwamnan jihar. Uwargidan shugaban kasa, Sen. Oluremi Bola Ahmed Tinubu da ta isa filin jirgin saman Danbaba Suntai a ranar Alhamis...

Babban Taron LEADERSHIP Karo Na 17: Tinubu Ya Kare Yadda Gwamnatinsa Ke Tafiyar Da Tsarin Rabon Arzikin Kasa
Mataimakin shugaban kasar wanda ya samu wakilcin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Na Musamman Kan Ayyuka Na Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Aliyu Modibbo Umar ya ce, “Kalubalan Nijeriya ya ta’allaka a tsarin tarayyarmu,” in ji Shettima. “Ba batu ne na wai nawa ne kowace rukunin tarayya ke samu ba, magana ce ta yadda ake amfani da irin wadannan albarkatun.” “Ba kuma batu ne na cewa nawa ne kowace bangare ke samu ba, sai dai a yi batun yadda ake amfani da irin wadannan kayan.” Ya yaba wa LEADERSHIP bisa samar da wani dandali wanda “ba a samar da shi kadai don musayar ra’ayi ba sai don tsara manufofi masu ma’ana.” Ya kuma bayyana sauye-sauyen da ake yi a karkashin gwamnatin...
Sojojin kasa na kasashen Iran ta Armenia sun fara atisayen soje na hadin guiwa a tsakaninsu, don kyautata tsaro na kan iyakar kasashen biyu na kuma tsawon kwanaki biyu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran ne suke jagorantar wannan atisayen. Da nufin hana fasa korin muggan kwayoyi da kuma sulalewar yan ta’adda suka kan iyakokin kasashen biyu. Burgediya Janar Sayyid Mortaza Mira’in babban hafsan sojojin kasa na IRGC ya bayyana cewa, wannan atisayennn yana nuna irin yadda sojojin IRGC suke da shirin kare kasar daggga duk wata barazana. Da kuma abota da kyautata makobtaka da kasashe mmmakobta. Labarin ya kara da cewa ana gudanar da rawan dajin...

Tattalin Arzikin Sin Na Bunkasa Yadda Ya Kamata Duk Da Kakkaba Mata Karin Harajin Kwastam Daga Amurka
A ran 7 ga watan nan da muke ciki bisa agogon gabashin kasar Amurka, kasar ta Amurka ta kara barazanar kakkaba wa Sin karin haraji na kashi 50%, kasar Sin a nata bangaren ta bayyana aniyarta ta daukar matakan da suka dace don kare muradunta. Tattalin arzikin Sin na samun bunkasa yadda ya kamata duk da matakin kakkaba mata karin harajin kwastam da Amurka ke dauka, kamar yadda shugaban kasar Mr. Xi Jinping bayyana cewa: “Tattalin arzikin Sin ya yi kama da teku a maimakon karamin tabki.” Teku ba ya tsoron mahaukaciyar guguwa, kuma yana iya tinkarar duk wasu kalubale daga waje. (MINA) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Declan Rice ne ya jefa ƙwallaye biyu a wasan kafin Mikel Merino ya jefa ta uku kuma ta ƙarshe a wasan, hakan ya sa Rice ya zamo dan wasa na farko a tarihin gasar Zakarun Turai da ya ci ƙwallaye biyu daga bugun tazara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp