Shugaban majalisar dokokin jama’ar kasar Mexico Sergio Carlos Gutiérrez, ya bayyana yayin da wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ya zanta da shi a kwanakin baya cewa, tunanin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama da shugaba Xi Jinping ya gabatar ya burge shi matuka.

Ya ce, an gabatar da tunanin don tattauna yadda sassan kasa da kasa za su zauna tare, da taimakawa juna, da amincewa da bambance-bambance a fannonin tattalin arziki, da yawan mutane, da yankunan kasa a tsakanin kasashen duniya, da sa kaimi ga maida bambance-bambance su zama hanyar dinkewa da juna, da kuma samar da kyakkyawan yanayin zaman rayuwar al’ummun kasa da kasa. Kana yana fatan jama’ar kasashen duniya ciki har da ta Sin da ta Mexico, za su ji dadin zaman rayuwa mai inganci.

Ban da wannan kuma, Gutiérrez ya yi nuni da cewa, Sin da kasashen Latin Amurka sun taimakawa juna, da more fasahohin samun ci gaban juna, da sa kaimi ga samun zaman rayuwar jama’a mai inganci, kana bangarorin biyu sun yi kokarin samar da yanayin zaman rayuwa mai tsaro, da inganci ga jama’arsu.

Ya ce, bisa yanayin da ake ciki a duniya, zurfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, zai jagoranci Sin da kasashen Latin Amurka, ga bin hanyar samar da zaman rayuwa mai inganci ga al’umma. (Zainab Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Tinubu Ya Rantsar Da Farfesa Dakas James Shugaban Hukumar Gyaran Dokoki Ta Kasa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na jagorantar taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) a ɗakin taro na Majalisar da ke Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja.

Kafin a fara taron, Shugaban Ƙasa ya rantsar da Farfesa Dakas James Dakas da Dakta Uchenna Eugene a matsayin Shugaban Hukumar Gyaran Dokoki ta Ƙasa da Kwamishina.

Majalisar ta kuma dakatar da taron na minti ɗaya domin girmama marigayi Cif Audu Ogbe, wanda ya kasance memba a majalisar a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Shehu Shagari, haka kuma a ƙarƙashin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Cif Ogbe ya rasu a ranar Asabar, 9 ga watan Agusta, yana da shekaru 78.

 

Daga Bello Wakili

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jama’a sun koka kan rashin kammala aikin titi a Kafanchan
  • Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Shugaban Karamar Hukumar Rano Na Tsawon Watanni Uku
  • Shugaban Tinubu Ya Rantsar Da Farfesa Dakas James Shugaban Hukumar Gyaran Dokoki Ta Kasa
  • ‘Yan Ta’adda Sun Kashe Jama’a A Kauyukan Sakkwato
  • Tinubu Ya Nada Hukumar Gudanarwa Ta NCC Da Sauran su
  • Kasar Iraki Ta Ce: Yarjejeniyar Da Ta Kulla Da Iran Zai Amfani Dukkan Kasashen Yankin
  • Ilimin Fasahar Zamani Dama Ce Ta Samun Kyakkyawar Makoma A Afrika
  • Mafi yawan Kasashen Duniya Sun Amince Da Samarda Kasar Falasdinu
  • Tattalin Arzikin Kasar Sin Na Da Makoma Mai Haske In Ji Wani Kwararre 
  • Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Gudanar Da Zaman Taro Kan Aniyar ‘Yan Sahayoniyya Kan Gaza