Madarar Shanu Da Nijeriya Ke Samarwa Ta Karu Da Tan Miliyan 1.4 A Shekara Biyar
Published: 29th, June 2025 GMT
“Abin da muke son cimma shi ne, a duk shekara mu tabbatar da ganin mun rubanya yawan madarar da ake samarwa kasar a kasar daga tan miliyan 700,000 zuwa tan miliyan 1.4 daga nan zuwa shekara biyar masu zuwa”, a cewar Ministan.
“A Nijeriya akwai sama da Shanu miliyan 20.9, Tumaki sama da miliyan 60, Awakai sama da miliyan 1.
Kazalika, Minstan ya kara da cewa; burin shi ne ganin an kara bunkasa tattalin arzikin kasar tare da kuma kara samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar.
“Ina son fayyace cewa, ba wai batu ne kawai na yawan Shanun da ake da su a kasar nan ba, batu ne na jama’a da samar da ayyukan yi, habaka kasuwanci da kuma kara daga kimar tattalin arzikin kasar da kuma samar da madarar da za ta gina jikin yara kanana”, a cewar tasa.
Ministan ya ci gaba da cewa, wannan batu ne na matasan kasar da suke da burin fara yin sana’ar sarrafa madarar Yagot.
Ya kara da cewa, tuni gwamnatin tarayya cikin watanni biyu da suka gabata ta hanyar yin amfani da cibiyar gudanar da bincike ta kiwon dabbobi da ke garin Zariya a Jihar Kaduna, ta fara yin rijistar wasu nau’ika takwas na ciyawar da ake ciyar da dabbobi, wanda wannan aiki shi ne karo na farko a cikin shekaru 48 da suka wuce a fadin kasar nan.
Ministan ya bukaci daukacin matasan kasar nan, da su yi amfani da fasahar da suke da ita da kuma samar da dabaru, musamman domin kara ciyar da fannin na samar da madarar Shanun a wannan kasa.
“Muna da bukatar samar da wata kafar sadarwa da za ta rika sada masu sarrafa madara a kasar, musamman domin kara samar musu da kasuwa da kuma masu bayar da daukin kudade a fannin na samar da madara,” a cewar Ministan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Madara
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 5 a Borno
Rundunar sojin Najeriya, ta bayyana cewa dakarunta sun kashe ’yan ta’adda biyar a wani samame da suka kai yankin Magumeri da Gajiram, a Jihar Borno.
Kakakin rundunar Operation Haɗin Kai, Kanar Sani Uba, ya ce dakarun sun yi arangama da wasu ’yan ta’adda 24 da ke tafe a ƙafa a ranar Juma’a.
Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da KatsinaA cewar sanarwar da ya fitar, sojojin sun yi nasarar kashe biyar daga cikinsu tare da ƙwato kuɗi Naira miliyan biyar.
“An hangi ’yan ta’addan suna ƙone gidaje da kuma kai wa mutane hari, sai dakarun suka fara bin su, inda suka tsere zuwa ƙauyen Damjiyakiri,” in ji Kanar Sani.
Ya ƙara da cewa bayan awanni huɗu ana bin su, sojoji suka sake kai musu farmaki, inda suka kashe biyar daga cikinsu, sauran 19 kuma suka tsere da raunuka.
Abubuwan da aka ƙwato daga hannunsu, sun haɗa da bindiga ƙirar AK-47, jakar harsashi gyda biyar, waya guda ɗaya da wuƙa.