Ƙwallon Mata: Rivers United Ta Doke Nasarawa Amazons A Wasan Ƙarshe Na Kofin Shugaban Ƙasa
Published: 29th, June 2025 GMT
Rivers Angels ta lashe gasar cin Kofin Shugaban ƙasa na shekarar 2025 bayan ta doke Nasarawa Amazons da ci 4-2 a bugun fenareti bayan da suka tashi 2-2 a filin wasa na Mobolaji Johnson dake birnin Legas, wannan ne karo na goma da ɓangaren Tosan Blackson ke lashe kofin.
Nasarawa Amazons ce ta jagoranci wasan a farko da ci 2-0 waɗanda Olusola Shobowale ta ci, Olusola ta zura ƙwallon farko a minti na 7 da fara wasan sai kuma ta zura ta biyu a minti na 10, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne Rivers ta zage damtse, wanda ya kai ta ga farke duka ƙwallaye biyu a cikin mintuna 5 kacal.
Taiwo Ajibade ce ta ci wa Rivers duka kwallayenta biyu a cikin mintuna 5 da dawowa daga hutun rabin lokaci, hakan ya sa wasan ya kare da ci 2-2 wanda kuma ya sa aka tafi zuwa bugun daga kai sai mai tsaron raga domin fitar da zakaran wasan, kugiyar ta Port Harcourt ya yi nasara a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan ta jefa kwallo 4 yayinda Amazons suka jefa kwallaye 2.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Ƙwallon Ƙafa
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Hudu A Taron Kolin Mata Na Duniya
Na farko, hada kai don samar da yanayi mai kyau ga ci gaban mata. Na biyu, a karfafa abubuwan da za su habaka ingancin ayyukan mata cikin hadin kai. Kana na uku, a gina tsarin kare hakkin mata tare. Sai na hudu, a bude sabon babin hadin gwiwa tsakanin mata a duniya.
Za a gudanar da taron kolin mata na duniya a yau da gobe Talata a birnin Beijing. Kuma tuni shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, suka yi musafaha da shugabannin tawagogin kasashe, da kungiyoyin duniya da suka halarci taron, tare da daukar hotuna tare da su. (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA