Aminiya:
2025-06-30@01:22:59 GMT

Tarihi da tasirin rayuwar Alhaji Aminu Alhassan Dantata

Published: 30th, June 2025 GMT

A ranar 28 ga watan Yuni, 2025, Najeriya ta yi rashin ɗaya daga cikin fitattun ’ya’yanta, Alhaji Aminu Alhassan Dantata bayan ya shafe shekaru 94 a duniya. 

Ya rasu a birnin Abu Dhabi na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) wanda rasuwarsa ta kasance wani babban giɓi a tarihin ci gaban Najeriya, musamman a fannin tattalin arziƙi da tallafa wa marasa ƙarfi.

Kebbi: PDP za ta yi haɗaka don ƙalubalantar APC a zaɓen 2027 Mutanen Sakkwato na neman ɗaukin gwamnati game da Bello Turji

Wannan rashi na Dantata babban al’amari ne da ya shafi Najeriya da ma Yammacin Afirka baki ɗaya.

Aminu Dantata ya kasance mutum mai tasiri a fannonin kasuwanci, hidimar jama’a, addini da ayyukan jin-ƙai.

A wannan zamani da mutane da yawa ke rige-rigen nuna kai da nuna iko, shi ya kasance mutum na daban, mutum ne mai yawan yin shiru kuma mai cike da kamala da kuma sauƙin kai wajen mu’amala.

Tarihin Dantata

An haifi Aminu Dantata a ranar 19 ga watan Mayun 1931, daga gidan Dantata a Kano. Mahaifinsa, Alhaji Alhassan Dantata, ya kasance shahararren attajiri a duk yankin Yammacin Afirka a farkon ƙarni na 20.

Dantata bai gaji dukiya kaɗai daga mahaifinsa ba, ya gaji ɗabi’u, karamci da kamun kai. Duk da irin arziƙinsa, Alhassan Dantata bai yarda da nuna kai ko karɓar sarauta ba.

Ya gina rayuwa mai kyau da aminci, wanda ya bai wa ‘ya’yansa damar girma cikin ƙima da kuma tasowa cikin tsantseni.

Wannan ne ya sa Aminu, tare da jikan ɗan uwansa Aliko Dangote, wanda a yanzu shi ne attajiri mafi kuɗi a Afirka suka ci gaba da ɗaukaka gadon gidansu.

Aminu ya taso cikin ilimin addini da harkar kasuwanci. Ya fara karatu a makarantar allo kafin daga bisani ya shiga harkar kasuwanci.

Har zuwa lokacin da ya kai shekaru 17, ya ci gaba da harkokin kasuwanci da kai kaya zuwa wurare daban-daban a Arewacin Najeriya.

A lokacin saboda babu manyan hanyoyi sosai, ya dogara da yin tafiye-tafiyens a raƙuma, jakuna da kekuna wajen kai kayayyaki.

Kodayake ya fito daga gidan arziƙi, Aminu Dantata bai taɓa dogara da gadon gidansu ba.

Ya faɗaɗa kasuwancin da suka gada daga yin kasuwancin goro zuwa gina babbar daular kasuwanci da masana’antu a sassa daban-daban.

Kamfanoninsa sun taka rawa wajen gina muhimman cibiyoyin gwamnati irin su Nigerian Defence Academy a Kaduna da wasu gine-gine a Jami’ar Ahmadu Bello.

Ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka fara saka hannun jari a harkar man fetur ta Najeriya a kamfanin Express Petroleum & Gas Company Ltd.

A fannin harkar hada-hadar banki kuwa, ya taimaka wajen kafuwar bankin Jaiz Bank, bankin Musulunci na farko a Najeriya.

Hakazalika, ya saka jari a noma da masana’antu, inda ya ci gaba da raya kasuwancin gyaɗa, auduga da masana’antar yadi.

A shekarar 1967, ya sayi jirginsa na farko, wanda hakan ya nuna bunƙasar kasuwancinsa.

Haka ma a shekarar 2009, ya mallaki jirgin sama na alfarma wanda darajarsa ta kai dala miliyan 38.

Harkokinsa sun wuce iyakokin Najeriya. Ya mallaki kadarori a ƙasashen Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Birtaniya, Jamus da Amurka.

A wasu lokutan, ya kan ɗauki ‘ya’yansa zuwa aikin Hajji da Umrah da jirginsa na musamman, wanda ke nuni da yadda ya yi amfani da dukiyarsa wajen hidimar iyali da addini.

Shiga harkokin gwamnati da hidimta wa al’umma

Koda yake Dantata ya fi karkata zuwa ga harkokin kasuwanci, amma yana da sha’awar yi wa jama’a hidima, wanda hakan ya sa ya shiga siyasa.

A farkon shekarun 1960, an zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar wakilai ƙarƙashin jam’iyyar Northern People’s Congress (NPC).

Daga baya ya zama Kwamishinan Tsare-tsare da Ci gaba a Jihar Kano ƙarƙashin Gwamnatin Audu Bako daga 1967 zuwa 1973.

Duk da irin ƙarfin da yake da shi, bai nemi shahara ko matsayi ba.

Ya fi son kwatanta gaskiya da faɗin ra’ayinsa a bayyane, har ma yana ƙalubalantar shugabanni idan ya ga an kauce hanya.

A lokacin da girma ya kama shi, ya bayyana ra’ayinsa a fili cewa tsarin mulkin shugaban ƙasa na ci wa ƙasa kuɗi da yawa kuma baya bayar da sakamakon da ake buƙata.

Ya ce tsarin da Najeriya ya dacewa ta koma shi ne tsarin majalisar dokoki, domin ya fi sauƙi da rinjaye wajen kula da kuɗi da jagoranci.

Alheri da ayyukan jin-ƙai

Abin da ya fi bayyana a rayuwar Aminu Dantata shi ne alherinsa da sadaukarwarsa.

Koda yake ba ya bayyana ayyukansa a bainar jama’a, har ila yau ya canza rayuwar dubban mutane da hannunsa.

Ya gina makarantar sakandare ta mata a unguwar Dala da ke Jihar Kano, inda ya bayar da sama da Naira miliyan 50 don gina ɗakin karatu, banɗaki da rijiyar burtsatse da yawa.

Ya kafa Cibiyar Alhassan Dantata Haemodialysis Centre a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.

A lokacin da ambaliyar ruwa ta auku a Maiduguri, ya bayar da tallafin Naira biliyan ɗaya da rabi.

Daga cikin labaran da suka fi taɓa zuciya dangane da shi, akwai na wani gida da aka yi rikici kan rabon gado, inda ya gina wa kowanen daga cikin waɗanda ke rigimar su bakwai gida, domin sulhun ta su.

Haka kuma ya ɗauki nauyin aikin hajji, gina masallatai, da kuma tallafa wa malamai da ɗalibai.

Gidansa da ke unguwar Koki a birnin Kano ya kasance mafaka ga talakawa, ‘yan kasuwa da marasa galihu.

Duk da irin dukiyarsa, bai karɓi sarauta ko manyan muƙamai ba. Ya zauna cikin kamala da tawali’u, inda kowa ke girmama shi.

Jigo a wajen iyalansa da sauran jama’a

Aminu Dantata ya kasance shugaba a gida da waje. Ya auri mata da dama, kuma ya haifi yara wadanda sun manyanta.

Ya kasance mai ɗaukar nauyin tarbiyya da ilimin ‘ya’yansa — addini da na zamani. Ya kasance a tare da su a kasuwanci da harkokin yau da kullum.

Shekaru 12 na ƙarshen rayuwarsa ya mayar da hankali ne wajen iyalansa da karatu da kuma horar da matasa.

Koda ya kasance yana fama da rashin lafiya musamman wadda ta shafi girma, amma zuciyarsa cike take da natsuwa da lafiya.

A wata hirarsa ta ƙarshe, ya bayyana damuwarsa kan yadda mutane ke banzatar da damar da Allah Ya ba su.

Ya ce: “Babu abin da ke burge ni a yanzu. Abin takaici ne yadda ba ma amfani da dama irin wadda Allah Ya ba mu.”

Ya ƙara da cewa: “Allah Ya hana yanke ƙauna,” alamar yadda imani ya tabbata a zuciyarsa har ƙarshen rayuwarsa.

Manyan mutane sun yi alhinin rasuwarsa

Bayan rasuwarsa, manyan mutane daban-daban na ƙasar nan da ma wajen Najeriya sun aike da saƙon ta’aziyyarsu.

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana rasuwarsa a matsayin “babban rashi ga Najeriya.”

Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya yaba masa kan rawar da ya taka wajen gina matasa.

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya ce “wani babban shafi a tarihin Najeriya ya tafi.”

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya buƙaci a girmama shi ta hanyar sanya sunansa a manyan ayyukan gwamnati.

Gwamnoni, shugabannin addini, attajirai da talakawa sun bayyana shi a matsayin uba, jagora, mai taimako da son zaman lafiya.

Jana’izar Dantata

An yi masa jana’izar sallar ‘Ga’ib a Jihar Kano, inda manyan baƙi da malamai da dubban jama’a suka halarta a birnin Kano.

Ana ƙoƙarin binne shi a birnin Madina na ƙasar Saudiyya, kusa da kabarin matarsa Hajiya Rabi wadda ta rasu a shekarar 2023, kamar yadda ya bar wasiyya.

Bayan shafe tsawon lokaci ana kai komo kan binne gawar Dantata a birnin Madina, iyalansa sun tabbatar da cewar hukumomin Saudiyya sun sahale a binne shi a birnin a gobe Litinin.

Al’umma dai na ci gaba da bayyana alhininsu game da rasuwar fitaccen attajirin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: arziki

এছাড়াও পড়ুন:

HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Aminu Ɗantata a Kano

An yi wa marigayi Alhaji Aminu Ɗantata jana’izar Salatul ‘Ga’ib’ a garin Kano.

An yi sallar ne a masallacin Umar bn Khattab da ke kan titin Gyadi-Gyadi.

Za a binne Aminu Ɗantata a Madina — Iyalansa Mangu: Gwamnatin Filato ba ta aiko da wakilai don yin ta’aziyya ba — Sarkin Zazzau 

Sheikh Ibrahim Khalil, Shugaban Majalisar Malamai na Jihar Kano, tare da Sheikh Ibrahim Aminu Daurawa, ne suka jagoranci sallar.

Manyan baƙi da dama sun halarci jana’izar, ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, mambobin majalisar zartarwa na Jihar Kano, manyan ‘yan kasuwa da wasu mutane.

Aminiya ta ruwaito marigayi Alhaji Aminu Dantata, ya rasu a birnin Abu Dhabi, kuma za a birne shi a Madina bayan wasiyyar da ya bari kafin rasuwarsa.

Ga hotunan a ƙasa:

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Har Yanzu Ba Mu San Inda Za A Binne Dantata Ba — Sakatarensa
  • Rasuwar Dantata Babban Rashi Ne Ga Afirka – Atiku
  • HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Aminu Ɗantata a Kano
  • Za a birne Aminu Ɗantata a Madina – Iyalansa
  • Alhaji Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekaru 94
  • Alhaji Aminu Danata ya rasu yana da shekaru 94
  • Shahararren Ɗan Kasuwa Aminu Dantata Ya Rasu
  • Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (7)
  • NAJERIYA A YAU: Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Hana Mata A Arewa Koyon Ilimin Kimiyya?