2025-06-19@15:20:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4858
«Gwamnonin APC»:
Haka kuma, an ce ta ƙara da cewa: “Mu tambayi Shugaban Majalisar Dattawa, me ya sa ya janye jami’an tsarona tun farko, idan ba don ya sa a kai min hari ba? Ya ce a kashe ni, amma a kashe ni a Kogi.” Gwamnati ta bayyana cewa waɗannan kalaman suna da nufin ɓata suna, kuma...
Wasu na ganin jita-jitar ta samo asali ne bayan wani abokin aikinsa na baya, Sani Sidi, ya koma jam’iyyar APC tare da magoya bayansa a Kaduna. Amma Sambo ya ce hakan bai shafe shi ba. Hakazalika, an shirya Sambo zai halarci bikin ƙaddamar da asibiti mai gadaje 300 da ke Kaduna a ranar Alhamis, 19...
Kafin wannan, yana riƙe da sarautar Walin Gaya, wanda aka ba shi lokacin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙiri sabbin masarautu. Masarautar ta ce an ɗauki wannan matakin ne domin kare mutunci da ƙimar sarautun gargajiya bisa tsarin da aka gada. Sai dai matakin ya zo ne mako guda bayan Alhaji Usman ya soki...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce matsalar da ke addabar jam’iyyar PDP ba ta tsaya kan Atiku Abubakar kaɗai ba, face tana da nasaba da girman kai tsakanin shugabannin jam’iyyar. Da yake magana da manema labarai a ranar Laraba, Gwamna Lawal ya ce: “Kowa yana da nasa matsalar; ba kan Atiku Abubakar kawai ba...
Ya ce duk da cewa akwai damuwa kan yadda za a aiwatar da hakan, Gwamnatin Tarayya na da damar tsara ƙa’idoji da dokoki na musamman ga kowace jiha don hana amfani da ‘yansandan wajen cin zarafi. A halin yanzu, gwamnonin jihohi daga faɗin Nijeriya na gudanar da wani taron gaggawa a Babban Birnin Tarayya, wanda...
Wata kotun shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Jihar Kano, ta yanke wa wasu mutum bakwai hukuncin ɗauri, bayan da suka ji wa wani ɗan sanda rauni yayin da ake ƙoƙarin cafke su. Al’ummar unguwannin Tudun Maliki da Sheka ne suka kai rahoton mutanen, inda suka zarge su da sayar da miyagun ƙwayoyi. ’Yan...
’Yan bindiga sun kashe akalla manoma 20 da wasu mutum uku da kuma wani dan sinitiri a jihar Katsina. An kashe mutanen ne a wasu hare-hare daban-daban da aka kai karamar hukumar Kankara, daya daga cikin yankunan da suka fi fama da kalubalen tsaro a jihar. A cewar wani mazaunin yankin da bai amince a...
Al’ummar garin Kaura Namoda da ke Jihar Zamfara, sun gudanar da sallar roƙon ruwa bayan da aka shafe kwanaki ba tare da an samu ruwan sama ba. Mutane da dama sun fara nuna damuwa saboda har yanzu babu ruwa ba, duk da cewa an shiga lokacin damina tun da daɗewa. NAJERIYA A YAU: Yadda Cutar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar amosanin jini wacce aka fi sani da cutar sikila na cigaba da barazana ga rayukan masu dauke da ita. Wannan cuta na saka masu ita da ‘yan uwan su cikin halin ha’ula’i, a wasu lokutan ma tana haifar da rasa rayukan wasu dake dauke da ita. Rahotannin...

Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Sin Sun Samar Da Sabuwar Hanyar Sufuri Ga Al’Ummun Kasashen Shiyyar Tsakiyar Asiya
A watan Afrilun bana, wata farar mota kirar bas mai tsawo mita 12, ta yi tafiya a kan titunan Ashgabat, hedkwatar kasar Turkmenistan. Bas din da kamfanin Yutong na kasar Sin ya kera ta dace da ma’aunin kiyaye muhalli da kasar ta tanada, kuma tana dauke da na’urar ba da jagorancin sufuri mai amfani da...
Da take aiwatar da rahotannin sirri cikin gaggawa, rundunar hadin gwiwa da ta kunshi jami’an ‘yansandan Nijeriya, Sojoji, jami’an kula da jama’a na jihar, da ’yan banga na yankin sun bi sawun barayin da suka tsere zuwa Dutsen Falale da ke yankin Kurfi-Safana inda aka yi musayar wuta mai tsanani, wanda ya yi sanadin mutuwar...
Kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO, ta kira taro karo na 63 mai taken “Ba da tallafin ciniki” a jiya Talata a birnin Geneva. Yayin da aka tattauna bisa ajandar “Makomar hadin gwiwar kasashe masu tasowa da saurin bunkasuwa”, Sin ta yi cikakken bayani kan dabaru, da fasahohi da Sin take da su a fannin...
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan kada a kuskura a shiga tsakanin yaƙin da Iran da Isra’ila ke fafatawa ta hanyar amfani da ƙarfin soji. Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi gargadi kan duk wani “shiga tsakani na soji”, a yankin Gabas ta Tsakiya, inda manyan abokan gaba Isra’ila da Iran ke musayar...
Murdyk ya halarci wasan karshe na gasar cin kofin Uefa Conference League da Chelsea ta doke Real Betis a watan da ya gabata, amma kuma ba a cikin tawagar Chelsea ba, a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, FA ta ce “Za mu iya tabbatar da cewa an tuhumi Mykhailo Mudryk da laifin...
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu, ya kaddamar da aikin samar da ruwan sha mai tsafta wanda kamfanin CGCOC na kasar Sin ya tallafa wajen gudanar da shi a birnin Abuja, fadar mulkin kasar. Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa, ta yin aiki tukuru a fannin samar da ababen more rayuwa, da kai tsaye za su inganta...
A karon farko Nijeriya za ta fara fitar da tataccen man fetur zuwa nahiyyar Asia kamar yadda wata majiya daga Matatar Dangote ta sanar. Majiyar ta ce wani jirgin ruwan dako mai ɗauke da tan 90,000 na man fetur zai yi jigilar daga Matatar Dangote da ke Nijeriya zuwa nahiyar Asia. HOTUNA: Yadda Tinubu ya...
Aiki ceton, ya samu hadin gwiwar kungiyoyin ceto da suka hada da Red Cross da Hukumar Kula da Ruwan Kogin (NIWA) da jama’ar garin Yauri. A ranar Laraba, an yi jana’izar Mutane uku, a garin Hikiya da ke karamar hukumar Rohiya a jihar Neja. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
An cimma jerin yarjejeniyoyin hadin gwiwa a taron koli na biyu na kasar Sin da tsakiyar Asiya da aka gudanar a birnin Astana na kasar Kazakhstan a ranar 17 ga watan nan agogon kasar. Shugabannin kasashen biyar na tsakiyar Asiya sun yaba wa kasar Sin a matsayin babbar abokiyar hadin gwiwa kuma kawa ta gaskiya...
Sauran sun hada da: Danjuma Azi, Fwangje Bala Ndat, Salome Tanimu Wanglet, Namba Rimuyat, Nimchak Rims, Ishaku Maren da Paul Datugun. Kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, wanda ya tabbatar da kamun, ya ce bincike ya nuna cewa tsaffin ‘yan majalisar sun shafe watanni shida ne kawai a kan karagar mulki, sannan gwamnatin jihar...
An gayyaci shugaban kasar Sin Xi Jinping zuwa kasar Kazakhstan, daga ranar 16 zuwa 18 ga watan Yunin shekarar 2025, don halartar taron koli karo na biyu na Sin da tsakiyar Asiya. A karshen ziyarar, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi wa manema labarai karin haske game da lamarin. Wang Yi ya...
A yayin ƙaddamar da asibitin ƙwararrun, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya buƙaci gwamna Lawal da ya ci gaba da gudanar da ayyukan ceto har sai Zamfara ta kasance ɗaya daga cikin manyan jihohin Nijeriya. Tsohon shugaban ƙasar ya ce: “A yau ina jihar Zamfara ne domin na ga ingantacciya, wadda ta ci gaba,...
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya kai ziyara Jihar Benuwe domin jajanta wa mutanen jihar bisa hare-haren da suka faru a wasu ƙauyuka kwanan nan. Ya je ne domin nuna alhininsa ga waɗanda abin ya shafa da kuma tattaunawa da shugabanni don nemo mafita mai ɗorewa. Mun shirya yin sulhu da ’yan bindiga — Gwamnatin Sakkwato...
Gwamnatin Jihar Sakkwato, ta bayyana cewa ta shirya zama da ’yan bindiga domin tattaunawa idan har suna da niyyar ajiye makamansu su rungumi zaman lafiya. Wannan bayani ya fito ne daga Hadimi na Musamman kan Harkokin Tsaro na Gwamna Ahmed Aliyu, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya). Sojoji sun raunata shugaban ISWAP na Najeriya, Albarnawi Litar...
Sanarwar ta ƙara da cewa ana aiki tare da hukumomin cikin gida da na ƙasa da ƙasa domin ganin an gudanar da aikin kwasar cikin tsaro. Sanarwar ta ce: “Ma’aikatar Harkokin Waje na sanar da jama’a cewa, sakamakon rikicin da ke ƙara ƙamari tsakanin Isra’ila da Iran, Gwamnatin Tarayya tana shirin ƙarshe na kwaso ‘yan...
Kungiyoyin ma’aikata na Kwalejin Ilimi ta jihar Kaduna da ke Gidan Waya, Kafanchan sun bayyana aniyarsu na fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku. Sun ce za su shiga yajin aikin ne daga ranar Alhamis, 19 ga watan Yuni, 2025. Wannan matakin ya biyo bayan karewar wa’adin kwanaki 14 da suka yi bai wa gwamnatin...
A yayin shari’ar, jami’in ‘yansanda ASP Luka Sadau, ya bayyana cewa wasu daga cikin kwamitin Masallacin ne suka kama Usman a ranar 13 ga watan Yuni, sannan suka kai shi ofishin ‘yansanda. Ya ce bayan sallar Juma’a, Usman ya sace takalma da kuɗinsu ya kai Naira 100,000. Usman ya kuma amsa cewa yana yawan zuwa...
Majalisar Dokoki ta kasa ta ce ta aike wa Shugaban Kasa Bola Tinubu kudurorin dokar harajin da ta amince da su a hukumance domin ya rattaba musu hannu su zama doka. Shugaban Kwamitin Yada Labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu (APC, Ekiti) ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai ranar Talata a...
Gwamnatin jihar Neja ta ce har yanzu akwai sama da mutum 700 da suka bace ba gan su ba tun bayan mummunar ambaliyar ruwan da aka yi a karamar hukumar Mokwa da ke jihar. Gwamnan jihar, Mohammed Umar Bago ne ya bayyana hakan lokacin da ya karbi babban dogarin tsohon Shugaban Kasa marigayi Janar Sani...
“Da farko mun ɗauka yana wasa ne, amma kafin wani ya kai ɗauki, ya riga ya kunna wa kansa wuta.” Wata mazauniyar yankin, Aisha Salisu, ta ce yana matashin yana shaye-shaye. “Ba ya cikin hayyacinsa. Ana jin warin wani abu mai ƙarfi a jikinsa, kuma yana karkarwa da ihu,” in ji ta. Mutane sun yi...

Dalilin Da Ya Sa Sin Ta Samu Bunkasar Tattalin Arziki Mai Dorewa Duk Da Kalubalolin Da Ake Fuskanta A Duniya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cewar Omodara, wadanda ake zargin sun hada da ‘yan asalin jihar da ake zargi da taimakawa ayyukan ‘yan bindiga ta hanyar samar musu da kayan aiki kamar abinci, ruwan sha, da sauransu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Kasar Sin ta cimma nasarar aikin gwajin tserewa lokacin da ake gamu da matsala a matakin farko na harbar kumbo mai dauke da mutane na “Mengzhou” a yau Talata, a cibiyar harbar taurori dan Adam dake birnin Jiuqiu, abin da ya alamanta cewa, Sin ta cimma sabuwar nasara a aikin binciken duniyar wata tare da...
Borussia Dortmund ta soma buɗe wasanninta na gasar FIFA Club World Cup da canjaras a karon-battar da ta yi da kungiyar Fluminense ta Brazil a ranar Talata. Ana dai ganin babbar kungiyar da ta zama gagarabadau a Rio de Janeiro Fluminense a matsayin mafi hatsari a rukunin F wanda ya kunshi har da kungiyar Ulsan...
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya raba kayayyakin noma ga magidanta 1,000 da suka hada da ‘yan gudun hijira daga Mandunari da ke karamar hukumar Gujba da sauran al’ummomin da suke zaune a yankin. Da yake jawabi a gidan gwamnati da ke Damaturu, Buni ya bayyana cewa, duk da cewa al’ummomin Mandunari ya kasance...
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ya san inda jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei yake “boye”, kuma ya yi gargadi cewa Washington na iya halaka shi, amma za su dakata a halin yanzu. Wannan na zuwa ne yayin da Trump din ya gargadi Iran kan da kada ta kai harin makamai masu...
Daga karshe Musa ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a rikicin na baya-bayan nan, inda ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda lamarin ya shafa. Rahotanni sun nuna cewa sama da mutane 200 ne aka kashe a wani hari da aka kai a Yelwata da ke karamar hukumar Guma, wanda galibi ya hada...
Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin ta shirya tsaf wajen aiwatar da soke haraji da kashi 100 bisa 100 a kan kayayyakin kasashen Afirka 53 da suka kulla huldar jakadanci da kasar ta hanyar rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin raya tattalin arziki. A yau, wani...
Kafofin yaɗa labarai na cikin gida a Iran sun yi iƙirarin cewa ƙasar ta kai hari kan hedikwatar hukumar leƙen asiri ta ƙasar Isra’ila (Mossad). Kamfanin dillancin labaran Iran (TASNIM) ya ruwaito cewa rundumar juyin juya hali na Iran (IRGC) ce ta kai harin a hedikwatar Mossad da ke Herzliya. Kamfanin ya wallafa wasu jerin...
Ƙungiyar Palermo ta ɗauki Filippo Inzaghi a matsayin mai horas da ’yan wasanta bayan raba da gari da ƙungiyar Pisa wadda ya kafa tarihin jagorantar haurowarta gasar Serie A. Cikin wata sanarwa da Palermo ta fitar ta ce Inzaghi ya rattaba hannu kan kwantaragin shekaru da dama wanda zai soma aiki daga watan gobe. Rikicin...

Daga Taklimakan Zuwa Sahara: Karin Abubuwan Al’ajabi Na Faruwa Bisa Hadin Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Yaki Da Kwararar Hamada
Sinawa tun zamanin baya na ganin cewa, samun dadi ga kowa shi ne dadi na gaske. A zamanin yanzu, kasar Sin ba kawai take jin dadin sauye-sauyen da ke faruwa a sassan hamada na kasar ba, hatta ma tana fatan ganin karin yankunan hamada sun zama dausayi a fadin duniya. Don haka, take kokarin bayar...
Akalla mutane 20 sun mutu yayin da wasu 16 suka jikkata a wani rikicin ƙabilanci da ya auku a wani lardi na gabashin kasar Chadi. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar sadarwa ta ƙasar ta fitar, ta ce fadan ya barke ne daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Yuni a yankin Molou na lardin...
Alhazai 442 sun tsallake rijiya da baya, bayan jirgin da ya ɗauko su bayan sun kammala aikin Hajjin bana ya samu sakon cewa an dasa bom a cikinsa a yayin da yake sararin samaniya a ƙasa Indonesiya. A ranar Talata ne jirgin, mallakin kamfanin Saudia Air, ya yi saukar gaggawa a birnin Jakarta babban birnin...
Isra’ila ta tabbatar cewa an garzaya da ’yan ƙasarta aƙalla 154 asibiti bayan sabbin hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kawo mata. Ma’aikatar lafiyar Isra’ila ta ce aƙalla mutum huɗu daga cikin waɗanda aka kai asibitin suna cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai, wasu biyar kuma na samun kulawa ta musamman saboda tsananin tashin hankali. Alkaluman da ma’aikatar...
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa gwamnatin Jihar Katsina na ƙoƙarin sasantawa da wasu ƙungiyoyin ‘yan bindiga a wasu yankunan jihar. Wasu daga cikin ‘yan bindigar da ke Jibia, Batsari da DanMusa sun amince da zaman lafiya tare da miƙa makamansu. Sai dai wannan hari na baya-bayan nan ya sa al’umma sun fara shakkar ko zaman...
Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump ya ce yana neman ganin an kawo karshen rikicin nukiliyar ƙasar Iran gaba ɗaya, a yayin da aka shiga kwana na biyar a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra’ila. Trump ya bayyana shirinsa na tura manyan jami’an ƙasarsa zuwa birnin Tehran domin tattaunawa da hukumomin Iran a game...
“Na ce Shettima ɗanmu ne, kuma muna alfahari da shi. Na kuma gode wa Tinubu bisa yadda ya bai wa ‘yan Arewa maso Gabas muƙamai masu gwaɓi kafin na nemi a mara masa baya,” in ji Salihu. A lokacin taron, wasu matasa sun kusan kai masa hari, amma ya ce hakan ya faru ne saboda...
Hukumar gudanarwar matatar man ƙasar Isra’ila da ke yankin Haifa ta sanar cewa matatar ta dakatar da ayyukanta ɗungurungum bayan harin da Iran ta kai mata. Kamfanin Bazan Group da ke kula da matatar ya ce harin na Iran ya tilasta musu tsayar da gaba ɗaya — a yayin da sabon rikicin na yankin Gabas...
Sarkin yankin Oke Agbe a Jihar Ondo ya ci Musulmi tara, tare da barazanar koran su da kuma haramta yin addinin Musulunci a garinsa bayan da wasu dodanni suka kai hari a wani masallaci da gidan limami. Aminiya ta samu rahoto cewa, wasu dodanni sun kai hari a masallaci da gidan wani limami, suka lakaɗa...
Sun bayyana cewa akwai hatsarin ganin wasu daga cikin waɗanda suka tuba su koma yin laifi, idan gwamnati ba ta yi hattara ba. Sun kuma jaddada cewa dole ne a tallafa wa iyalan da suka rasa ‘yan uwa da dukiyoyinsu a harin ‘yan bindiga, domin ka da su ji kamar gwamnati na goyon bayan masu...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Karancin kayan ganyayyaki na cigaba da barazana ga lafiyar ‘yan Najeriya. Masana sun bayyana cewa akwai gibi mai girma na rashin kayan ganyayyaki da ya kamata cike. Sai dai hakan na fuskantar tasgaro sakamakon wasu dalilai. NAJERIYA A YAU: Dalilan Durƙushewar Sababbin Sana’o’i Tun Ba A Je...