Aminiya:
2025-07-03@14:42:25 GMT

Ɗan wasan Liverpool, Diogo Jota, ya mutu a hatsarin mota

Published: 3rd, July 2025 GMT

Magoya bayan Liverpool da masoya ƙwallon ƙafa a faɗin duniya na cikin jimami bayan ɗan wasan Portugal, Diogo Jota, ya rasu a wani hatsarin mota.

Hatsarin ya auku ne da safiyar ranar Alhamis a yankin Zamora na ƙasar Spain.

’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 6, sun raunata wasu a Kwara NAJERIYA A YAU: Ɓoyayyun Ƙalubalen Da Sabuwar Haɗakar ADC Za Ta Iya Fuskanta

Jota ya rasu yana da shekara 28 a duniha.

Hatsarin ya faru ne a hanyar A-52, kusa da garin Palacios de Sanabria.

Jota yana cikin motar tare da ɗan uwansa, André Silva, wanda shi ma ya rasu.

Silva ɗan wasa ne da ke taka leda a ƙungiyar ƙwallon kafa ta Penafiel a ƙasar Portugal.

Rahotanni sun ce motar ta ƙwace ne tare da barin hanya sannan kuma ta kama da wuta.

Jami’an agaji da ma’aikatan kashe gobara daga Rionegro del Puente sun isa wajen cikin gaggawa, amma ba su iya ceto rayuwar mutanen da ke cikin motar ba.

Hukumomi har yanzu suna bincike don gano musabbabin aukuwar hatsarin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ɗan Wasa hatsarin mota Zamora

এছাড়াও পড়ুন:

Riƙaƙƙen Ɗan Ta’adda, Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Buhari Ba Shi Da Lafiya, Yana Samun Sauƙi A Birtaniya — Garba Shehu
  • ‘Mutum 600 da suka bace a ambaliyar Mokwa sun mutu’
  • Sai bayan Magariba za a yi wa Dantata jana’iza a Madina
  • Isra’ila na neman ƙulla hulɗa da Siriya da Lebanon
  • Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa
  • Riƙaƙƙen Ɗan Ta’adda, Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa
  • Dalibai 29 Suka Rasu A Turmutsitsin Tserewa Ga Fashewar Taransifoma A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya
  • CAF Za Ta Ƙaddamar Da Sabon Kofin Gasar Ƙasashen Afrika Na Mata
  • APC ta sa ranar taron Majalisar Zartarwa bayan murabus ɗin Ganduje