HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Aminu Ɗantata a Kano
Published: 28th, June 2025 GMT
An yi wa marigayi Alhaji Aminu Ɗantata jana’izar Salatul ‘Ga’ib’ a garin Kano.
An yi sallar ne a masallacin Umar bn Khattab da ke kan titin Gyadi-Gyadi.
Za a binne Aminu Ɗantata a Madina — Iyalansa Mangu: Gwamnatin Filato ba ta aiko da wakilai don yin ta’aziyya ba — Sarkin ZazzauSheikh Ibrahim Khalil, Shugaban Majalisar Malamai na Jihar Kano, tare da Sheikh Ibrahim Aminu Daurawa, ne suka jagoranci sallar.
Manyan baƙi da dama sun halarci jana’izar, ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, mambobin majalisar zartarwa na Jihar Kano, manyan ‘yan kasuwa da wasu mutane.
Aminiya ta ruwaito marigayi Alhaji Aminu Dantata, ya rasu a birnin Abu Dhabi, kuma za a birne shi a Madina bayan wasiyyar da ya bari kafin rasuwarsa.
Ga hotunan a ƙasa:
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Alhaji Aminu Ɗantata rasuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph
Majalisar Shura ta Jihar Kano ta fara zama da Malam Lawan Shu’aibu Abubakar (Triumph) kan zargin da wasu kungiyoyi biyar ke masa zargin batanci ga Manzon Allah SallalLahu alaihi Wasallama.
Wannan tattaunawa tana gudana ne a cikin sirri a Ofishin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) kuma ya samu halarcin fitattun malaman Musulunci na Jihar Kano.
Mahalarta sun haɗa shugaban majalisar shurar Malam Abba Koki da Wazirin Kano, Sa’ad Shehu Gidado, da sakatare, Shehu Wada Sagagi, da mambobin kwamitin da Majalisar Shurar ta kadfa domin zargin binciken zargin da ake wa Malam Triumph.