Sin Ta Samu Nasarorin A Zo A Gani Wajen Yaki Da Miyagun Kwayoyi
Published: 28th, June 2025 GMT
Albarkacin ranar yaki da miyagun kwayoyi ta kasa da kasa, ofishin dakile miyagun kwayoyi na kasar Sin ya gabatar da rahoton halin da kasar take ciki a wannan bangare, inda alkaluma suka nuna cewa, a shekarar 2024, hukumomi masu alaka sun binciki laifuka masu nasaba da miyagun kwayoyi fiye da dubu 37, da cafke masu aikata laifukan dubu 62, baya ga kama miyagun kwayoyi ton 26.
Ban da wannan kuma, Sin ta yi kokarin sauke nauyin dake wuyanta, inda ta shiga a dama da ita a hadin gwiwar kasa da kasa a bangaren yaki da miyagun kwayoyi. Kuma a matsayin kasar da ta kulla yarjejeniyar yaki da miyagun kwayoyi ta MDD, Sin ta yi kokarin sa hannun aikin tsara dokokin yaki da miyagun kwayoyi na duniya, da samar da dabaru da gudummawarta a wannan bangare.
Kazalika, a matsayin daya daga kasashen da suke fi daukar tsauraran matakan yaki da miyagun kwayoyi a duniya, kasar Sin ta bayyana niyyarta ta haramta miyagun kwayoyi bisa hakikanin matakan da ta dauka, wanda hakan ba alkawari take yi ga jama’arta ba kadai, haka kuma ya amsa bukatun jama’ar duniya. Matsayin da Sin ta dauka a wannan bangare yana kuma karfafa sauran kasashe gwiwar samun nasarar yaki da miyagun kwayoyi a duniya baki daya. (Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: yaki da miyagun kwayoyi
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisa Na Duba Yiwuwar Amincewa Da Gudanar Da Zaɓen 2027 A Rana Ɗaya
Tawagar da ke karkashin jagorancin, Barry Andrews ta kuma ziyarci hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), inda shugabanta, Mahmood Yakubu, ya yi gargadin cewa jinkirin da ‘yan majalisa ke yi wajen gyaran dokar zabe ta 2022 na iya kawo cikas ga shirye-shiryen gudanar da zabe a 2027.
Wakilan, wadanda suke Nijeriya tun kusan makonni uku domin nazarin matakin aiwatar da shawarwarin da ke cikin rahotonsu na bayan zaben 2023, sun kuma yi tattauna da babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
Abbas, a cikin wata sanarwar da sakataren yada labaransa, Leke Bayeiwu, ya shaida wa tawagar EU cewa rahotanninta kan zabukan shekarar 2023 ana la’akari da su a cikin sauye-sauyen gyara dokar zabe da na dimokuradiyya da Majalisar dokoki ke gudanarwa.
Abbas ya ce, “Ina so in bayyana cewa shugabancin kasar nan karkashin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana kokarin tabbatar da cewa mun inganta tsarin zabenmu, musamman game da abubuwan da masu saka ido na kasashen waje suka lura da su a lokacin zaben 2023.
“Mu a majalisar kasa ma mun kasance cikin aiki tukuru wajen tattara mafi yawan batutuwa da suka taso daga zaben 2023, domin mu ga yadda za mu iya magance su ta hanyar bin dokoki, domin zabenmu na gaba ya kasance mai inganci da amsuwa a idon duniya.”
Ya shaida wa tawagar cewa taron shugabannin majalisar dattawa da na majalisar wakilai da aka yi kwanan nan ya yanke shawarar warware batutuwan gyaran tsarin zabe cikin hanzari.
Ya bayyana cewa ra’ayin da yawa daga ‘yan majalisar kasa shi ne, gudanar da zabe a rana guda ba wai kawai zai kara inganci da gaskiya a gudanar da zaben kadai ba, har ma zai rage yawan kashe kudade na kusan kashi 40 cikin dari.
Ya ce, “Kamar gudanar da zabe a rana daya, wanda zai bayar da damar gudanar da zaben shugaban kasa da mambobin majalisar tarayya da gwamnonin jihohi da kuma ‘yan majalisar dokoki na jihohi duka a rana guda.
“A tunaninmu, zai taimaka wajen rage kashe kudaden gudanar da zabenmu har kashi 40 cikin ddari idan muka iya gudanar da zabukan cikin rana guda. Hakan zai kuma inganta gaskiya da karfafa aiki yadda ya kamata, musamman wajen fitowar masu kada kuri’a.”
ShareTweetSendShare MASU ALAKA