2025-11-12@23:03:00 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7784
«Barkwanci»:
Sauran sun haɗa da: Hon. Ibrahim Adamu Sarki a jam’iyyar PDP daga shiyya ta biyu sai , Nazifi Jibrin Muhammad na jam’iyyar PDP daga shiyya ta biyu da Haruna Dogo Mabo na.jamiyya NNPP daga shiyya biyu sai Honorable Isah Dan Maryam na PRP daga shiyya ta biyu da , Honarabul Isaac Auta Zankai na jam’iyyar...
Kasar Sin ta bukaci Japan da ta daina yi wa masu fafutukar neman “‘Yancin kan Taiwan”, ingiza mai kantu ruwa, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Guo Jiakun ya bayyana a yau Laraba. An ruwaito cewa, gwamnatin Japan a ranar Talata ta ba da wata lambar girmamawa ga tsohon “wakilin Taiwan...
Aƙalla mutum 12 sun mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata a wani turmutsutsu da ya faru yayin jarabawar ɗaukar aikin soja a Filin Wasa na El-Wak da ke Accra, babban birnin ƙasar Ghana. Lamarin ya faru ne da safiyar Laraba, yayin da ɗaruruwan matasa masu neman aikin suka kutsa cikin filin wasan ba...
Taron ya hada bijiman masana, da masu tsara manufofi, da masu ilimi,da masu bincike, da abokan hadin gwiwa na haɓaka harkar ilimi daga Afirka, Kudancin Asiya, da Birtaniya don tattauna dabarun inganta ilimi ta hanyar harshe. Dr. Alausa, ya jaddada cewa, yayin da kiyaye harsunan asali har yanzu yana da mahimmanci ga al’adu, amma...
Ya kuma yi nuni da cewa, a binciken da za a yi na gaba, akwai bukatar gudanar da manyan gwaje-gwaje da za su mayar da hankali ga fadada nemo samfuran da za a yi aiki a kansu. Yana mai cewa, “har yanzu muna bukatar kara tabbatar da tasirin maganin da aka yi amfani da shi...
Tawagar matan Najeriya ’yan ƙasa da shekaru 20, Super Falconets, ta lashe gasar Yammacin Afirka ta bana WAFU B U-20, bayan ta doke Black Princesses ta Ghana da ci 3-0 a wasan ƙarshe da aka buga a safiyar Talata. An fafata wasan ne a filin Stade Omnisports da ke Jamhuriyar Benin, inda Akekoromowei, Alaba Olabiyi...
Wakil ya ce, bayan samun rahoton, tawagar ‘yansanda karkashin jagorancin jami’in ‘yansanda na sashin, CSP Holman Simon, sun ziyarci wurin nan take domin tantance irin barnar da aka yi. Ya bayyana cewa, binciken farko ya nuna cewa, daya daga cikin wadanda ake zargin, wanda aka bayyana sunansa da Alhassan Jibrin, wanda aka fi sani...
’Yan sanda a Jihar Kano sun gano wata mota ƙirar Toyota Hilux mallakar ofishin mataimakin gwamnan jihar, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, wadda aka sace kwanan nan a harabar gidan gwamnati. Majiyoyi daga fadar Gwamnatin Kano sun ce an sace motar ce cikin dare, lamarin da ya kai ga tsare direban da motar ke hannunsa, Shafiu...
A shekaru fiye da 20 da suka gabata, birnin Wenzhou dake lardin Zhejiang na kasar Sin ya yi suna domin samar da takalma, kuma kayayyakin da ya samar sun samu karbuwa a duniya domin suna da araha. Amma ma’aikatan kamfanonin samar da takalma sun yi aiki har na tsawon awoyi 14 a kowace rana, inda...
Fitaccen ɗan wasan ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya tabbatar cewa Gasar Kofin Duniya ta shekarar 2026 ita ce ta ƙarshe da zai buga a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa. Ronaldo mai shekaru 40, wanda ya ci ƙwallo fiye da 950 a matakin kulob da ƙasarsa, ya ce yana shirin yin ritaya nan da shekara ɗaya ko...
Kyaftin ɗin tawagar Super Eagles ta Najeriya, William Troost-Ekong, ya gargaɗi ’yan wasan ƙasar da su guji tafka kura-kurai a wasan da za su buga da Gabon a ranar Alhamis. Ekong ya yi wannan gargaɗi ne kafin fara atisayen ’yan wasan a safiyar Talata, a yayin da suke ci gaba da shirin fafatawar neman gurbin...
Rahotanni sun bayyana cewa kasar Amurka tana shirin kafa sanssanin soji don aikewa da dubban dakaru zuwa iyakar Isra’ila da yankin Gaza, adaidai lokacin da ake fargabar wata sabuwar kasada da kuma sha’awar taimakawa gwamnatin mamaya wajen karbe ikon kula da yankin a nan gaba. Masharhanta na ganin wannan shirin yana zuwa ne saboda irin...
Hukumar kula da aikin hajji ta kasar Iran ta bayyana cewa shugaban ga yarima mai jiran gado na kasar Saudiya Mohammad Bin Salman a wata ziyara da suka kai birnin Riyadh a baya bayan nan. Wannan sakon yana nuna irin kokarin da ake yi ne na ganin an daidaita da kuma kara yin aiki tare...
Ministan Tsaron nageriya, Mohammed Badaru, ya tabbatar da cewa ma’aikatarsa tare da shugabancin rundunar soji za su kare kowane jami’i da ke bakin aikinsa bisa doka. Badaru ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da ’yan jarida a ma’aikatar tsaro kan bikin tunawa da Sojojin Nijeriya na shekarar 2026, wanda aka gudanarwa a Cibiyar...
Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya tare da shugabannin Rundunonin Sojin Najeriya, za su ci gaba da kare duk wani jami’i da ke gudanar da aikinsa bisa doka. Badaru, ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a taron da aka shirya domin bikin tunawa da Sojojin Najeriya na...
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, Sakataren Yada Labarai na ofishin mataimakin gwamna, Ibrahim Shu’aibu, ya bayyana lamarin a matsayin “cin amana a fili da direban da aka kama ya yi.” “Ofishin Mataimakin Gwamna ya yaba wa binciken gaggawa da rundunar tsaron ta yi ta hanyar amfani da kaifin basira...
Mataimakin wakilin dindindin na Sin a MDD Sun Lei, ya gabatar da jawabi yayin taron kwamitin sulhu game da batun Sudan ta Kudu da aka gudanar jiya Talata, inda ya yi kira da a inganta mika mulki cikin kwanciyar hankali a Sudan ta Kudu. Sun Lei ya ce, Sin ta bukaci dukkan bangarorin kasa da kasa da...
Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP), ta ayyana Najeriya ɗaya daga cikin jerin ƙasashen da za su fuskanci matsananciyar yunwa. Ta kuma yi gargaɗin cewa ƙarin mutane a duniya na iya fuskantar yunwa saboda ƙarancin kuɗin tallafi. Rahoton da Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) da WFP suka fitar, ya nuna...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na ci gaba da samar da ingantaccen kiwon lafiya ga al`ummar jihar. Babban sakataren ma’aikatar lafiya na jihar, Dr. Kabiru Ibrahim ya bada wannan tabbacin a dakin taro na ma’aikatar lafiya ta jihar a Dutse. Yace ayyukan da za’a gudanar a asibitocin sun hada...
Daga Usman Muhammad Zaria Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari uku domin gyara da inganta tsofaffin ayyukan wutar lantarki a fadin jihar. Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse....
Hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar wani matashi mai suna Innocent Chukwuemeka Onukwume, mai shekaru 27, bisa zargin kiran sojoji da su yi juyin mulki a Najeriya. Hukumar dai ta shigar da ƙarar matashin ne cikin tuhuma shida a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja. Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano Sagir Ƙoƙi ya fice daga...
Daga Khadijah Aliyu Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da Kwamitin Jagorancin Shirin Ilimi da Ƙarfafa Matasa a Arewa maso Yammacin Najeriya (EYEPINN) wanda kungiyar Tarayyar Turai ke daukar nauyinsa domin fadada damar samun ingantaccen ilimi da kuma karfafa gwiwar matasa a yankin. An gudanar da bikin kaddamarwar ne a Kano, karkashin jagorancin Kwamishinan Ilimi na...
Ya bayyana cewa mutanen sun fita da sassafe don wani aiki, amma ‘yan bindigar suka tare su suka kashe su tare da tserews da babur ɗinsu . Mista Ajeh, ya roƙi hukumomin tsaro da su gano waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki tare da gurfanar da su a gaban kotu. Haka kuma, ya buƙaci Gwamnatin...
A jiya Talata ne dai MDD ta yi kira da a gudanar da bincke akan kashe-kashen da aka yi sanadiyyar zaben da aka yi a watan karshe. Wannan kiran na MDD ta zo ne a daidai lokacin da mahukuntan kasar ta Tanzania su ka tuhumi wasu daruruwan mutane da cin amanar kasa saboda Zanga-zangar kin...
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kafa ka’idoji da jagorori da za su tsara samarwa da amfani da injinan noma a fadin Najeriya. Ministan Noma da Tsaron Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana haka a taron shekara-shekara na 45 na Ƙungiyar Injiniyoyin Noma ta Najeriya (NIAE), mai taken “Kafa Ka’idoji da Ƙarfafa Fasahohin da Aka...
Hukumar Kula da jin dadin mahajjan Jihar Taraba ta bayyana 1 ga Disamba, 2025, a matsayin ranar ƙarshe ga masu niyyar yin hajji don kammala biyan kuɗin tafiyar hajji ta shekarar 2026. A cewar wata sanarwa da Sashen Bayani na Hukumar ya fitar ta bakin Mataimakin Daraktan Hamza Baba Muri, an ƙayyade sabon kuɗin hajjin...
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta bayyana shirin ta na faɗaɗa gonakin shinkafar Jangwa daga hektar 3,300 zuwa hektar 5,000 a kakar noma mai zuwa, domin haɓaka samar da shinkafa da kuma ƙarfafa tattalin arziki a jihar. Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana haka yayin ziyarar duba girbin shinkafa a garin Jangwa, ƙaramar hukumar Awe. Gwamnan ya ce...
A wani muhimmin mataki na inganta harkar lafiya a matakin ƙasa, Karamar Hukumar Gwarzo ta kaddamar da sabuwar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko (PHC) da aka gina a garin Dankado, da ke cikin gundumar Sabon Birni. Taron kaddamarwar, wanda ke nuna wani sabon ci gaba a tsarin raya jama’a, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati,...
Hukumar Tsarawa da Raya Birane ta Jihar Kano (KNUPDA) ta gudanar da horon cikin gida na farko ga ma’aikatanta, wanda ya mayar da hankali kan aiwatar da dokokin aikin gwamnati, kyawawan ɗabi’un aiki da kuma ingancin ayyuka. Wannan horo, wanda ya zama muhimmin mataki a shirin ƙarfafa ƙwarewar ma’aikata na hukumar, an shirya shi ne...
Shugaban Hukumar Gudanarwa Filayen Jiragen Sama ta Kasa (FAAN), Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sake tabbatar da kudirin Gwamnatin Tarayya na dawo da tsohon martabar Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano. Dakta Ganduje ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar duba aiki da ya kai filin jirgin a Kano. Ya jagoranci wata tawaga mai...
Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana kudurinta na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da babban taronta na kasa da aka tsara a yi a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba. Hakan na zauwa ne duk da sabon umarnin kotun tarayya da ke hana ta ci gaba da shirya taron. Yadda muka daƙile yunƙurin tsige...
Ministan Harkokin Wajen Iran Sayyed Abbas Araghchi, ya ce masana’antar nukiliya yanzu ta zama babban fanni kuma tana kara samun ci gaba cikin sauri a fannoni daban-daban. Sabanin yadda ake ganin cewa wannan masana’antar ta takaita ne ga tace uranium, ya kara da cewa ana gudanar da ayyuka da dama da suka shafi fannoni daban-daban...
An kama diraben da ke jan motar Shafiu Sharp-Sharp, domin yi masa tambayoyi. “An riga an fara bincike. Ana yi wa direban tambayoyi, yayin da Babban Jami’in Tsaro (CSO) ke duba bidiyon CCTV,” in ji wata majiya. “An miƙa bayanan motar ga jami’an tsaro domin su gano motar da kuma kama ɓarawon.” Kakakin gwamnan Kano,...
“Dukkanin bayanan da ake da su sun nuna cewa babu wani kisan gillar da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya… Wannan labarin ƙarya ne da ƙungiyoyi suka ƙirƙira, wanda Shugaba Trump ke ƙoƙarin yaɗawa. “Wannan magana za ta iya ƙara tayar da hankali a Nijeriya… ‘Yan ta’adda suna kai hare-hare a kasuwanni, coci-coci, da masallatai,...
Gwamnan Jihar Legas, Babajide Olusola Sanwo-Olu, ya ce a wannan zamanin na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, babu wani gwamna ko shugaban ƙaramar hukuma da zai yi ƙorafi kan ƙarancin kuɗi. Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron ƙarawa juna sani na yini ɗaya da ƙungiyar Arewa Think Tank (ATT) ta...
CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15
An gudanar da taron karawa juna sani game da aikin watsa shirye-shiryen gasar wasannin motsa jiki ta kasar Sin karo na 15 ta hanyar talabijin ta zamani, wato taron karawa juna sani na hada fasahohin yada labarai, a jiya Litinin a birnin Guangzhou dake lardin Guangdong na kasar Sin. A yayin taron, babban rukunin gidajen...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe mutum biyar, ciki har da wata mata mai juna biyu a ƙauyen Alkalije da ke Ƙaramar Hukumar Yabo ta Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin lokacin da maharan suka mamaye ƙauyen, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa...
Kungiyar kasashe da cibiyoyin kasa da kasa ta fitar da wata sanarwa ta haɗin gwiwa da ta yi Allah wadai da manyan laifukan da aka aikata a ƙasar Sudan bayan kwace El Fasher daga dakarn (RSF) suka yi, da kuma ƙaruwar tashin hankali a yankin arewacin Darfur da Kordofan. Wannan sanarwar, wadda ministocin harkokin waje...
Wannan shi ne baje koli na farko bayan taron kwamitin kolin JKS da ya amince da shirin raya kasa na shekaru 5-5 karo na 15, wanda ya jaddada kudurin Sin na fadada bude kofarta. Halartar kamfanoni da adadinsu ya kai 4,108, daga manya da matsakaita da kananan kasashe ya tabbatar da cewa, kofar Sin a...
Ana fargabar cewa an yi wa wata yarinya ’yar kimanin shekara huɗu fyaɗe a ƙaramar hukumar Jakusko ta Jihar Yobe. Da yake zantawa da manema labarai fyaɗe da safiyar Litinin, mahaifin yarinyar ya bayyana cewa ta samu mummunan rauni a al’aurarta. John Cena ya lashe kambun Intercontinental karon farko a tarihi An ceto mutane 86...
Shugaban tsaron kasar ta Iran ya yi watsi da rahotannin da ake yayatawa cewa iran ta bude wasu hanyoyin tuntuba da Washington, yana mai jaddada cewa ba a isar da wani sabon sako ga Amurka ba. Ali Larijani ya jaddada cewa fifikon Iran a koyaushe shi ne dage takunkumin da aka kakaba mata, wanda ya...
Ofishin yada labarai na gwamnatin zirin Gaza ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa ‘yan mamayar Isra’ila sun karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza sau 282 tun bayan aiwatar da ita. Sanarwar ta nuna cewa tun lokacin da aka fara yarjejeniyar tsagaita wuta, an kashe fararen hula 242 tare da raunata wasu...
Ministan Harkokin Wajen Sudan Mohieldin Salem ya yi Allah wadai da shirun da kasashen duniya suka yi game da ci gaba da cin zarafin dan Adam da Rundunar Taimakon Gaggawa ta (RSF) ke yi a yankunan El-Fasher, Darfur ta Arewa, da Bara, da Kordofan ta Arewa. Ya yi wadannan kalaman ne a lokacin wani taro...
Gidauniyar Tallafawa Al’umma ta Abba Aliyu Gandu da ke jihar Kano ta bada horo sana’o’in hannu tare da raba tallafin Solar ga al’umma 500. Wannan shi ne karo ba adadi da wannan gidauniyar ta Kogunan Kasar Hausa kuma shugaban hukumar Samarda Lantarki a yankunan Karkara Alhaji Abba Aliyu ta gudanar. An raba kayan Solar guda...
Daga Usman Muhammad Zaria Ministan Yada Labarai Alhaji Mohammed Idris, ya yabawa Gwamna Malam Umar Namadi bisa jagoranci na gaskiya da tsari, yana mai cewa Jihar Jigawa ta zama abin koyi wajen gudanar da mulki da kuma ingantaccen aiki a ma’aikatu. Ministan ya yi wannan yabo ne lokacin wata ziyarar ban girma da ya...
Shugaban Hukumar Sararin Samaniya ta Iran ya sanar da cewa za a harba tauraron dan adam guda uku zuwa sararin samaniya cikin watanni biyu masu zuwa. Hassan Salarieh, shugaban Hukumar Sararin Samaniya ta Iran, a yayin jawabi a wani taron fasahar sararin samaniya a Tehran, ya nuna muhimmancin ayyukan da suka shafi bayanai na tauraron...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya jaddada kudirin gwamnatin sa na ci gaba da bunkasa hanyoyin sufuri a fadin jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya kaddamar da wani muhimmin aikin gina hanyoyi a karamar hukumar Mallam Madori. Yayin taron kaddamarwar, Gwamna Namadi ya bayyana cewa aikin...
Shahararren ɗan wasan wrestling, John Cena, ya samu nasarar lashe kambun Intercontinental a karon farko a tarihinsa. Cena ya lashe kambun ne da yammacin jiya Litinin, bayan ya doke Dominic Mysterio a birnin Boston, ƙasar Amurka. Sanata Jarigbe ya sauya sheka daga PDP zuwa APC Kotu ta sake dakatar da babban taron PDP Da wannan...
Alƙalin ya jaddada cewa wajibi ne a bi doka da oda domin kare tsarin dimokuraɗiyya, inda ya yi gargaɗin cewa karya doka na iya jefa ƙasa cikin ruɗani. A baya, Mai shari’a James Omotosho, ya taɓa bayar da irin wannan umarni, inda ya dakatar da PDP da INEC daga gudanar ko amincewa da sakamakon taron...
DSP Aliyu ya gargaɗi jama’a da su guji yaɗa labaran ƙarya, inda ya bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin aikata hakan za a hukunta shi. Ya kuma roƙi mutane su dogara da sahihan bayanai daga hukumomi, tare da tabbatar da cewa rundunar ‘yansandan ƙarƙashin CP Bello Shehu tana ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin...