2025-08-08@00:14:11 GMT
إجمالي نتائج البحث: 854
«Tsara Birane»:
Kudirin gyaran dokar fansho da sauran fa’idodi na tsaffin jami’an gwamnati ya wuce karatu na biyu a zauren Majalisar Dokokin Jihar Jigawa. Wakilin mazabar Malam Madori, Alhaji Hamza Adamu Ibrahim wanda shi ne shugaban Kwamatin kasafin kudi na majalisar, shi ne ya gabatar da wannan kudurin, ya kuma samu goyon bayan wakilin mazabar Guri Alhaji...

Tallafin Kammala Makarantun Share Fagen Shiga Firamare Na Gwamnatin Kasar Sin Zai Amfani Mutane Kimanin Miliyan 12
Ma’aikatar kudi ta kasar Sin, ta ce tallafin gwamnati na samar da ilimi kyauta ga daukacin daliban dake ajin karshe a makarantun share fagen shiga firamare a kasar zai amfani mutane kusan miliyan 12. Yayin wata ganawa da manema labarai a yau Alhamis, mataimakin ministan ma’aikatar kudin kasar ta Sin Guo Tingting, ya ce...
Mazauna kauyuka akalla 30 daga Dan-Isa da Kagara dake karamar hukumar Kaura-Namoda a jihar Zamfara, sun mamaye gidan gwamnati dake Gusau babban birnin jihar domin nuna takaicinsu kan yadda rashin tsaro a yankin na su “yaki ci yaki cinyewa” a ranar Alhamis. Masu zanga-zangar da suka hada da mata da kananan yara suna dauke da...
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun jaddada cewa: Duk wata barazana ga tsaron Iran za ta fuskanci kakkausan martani mai zafi fiye da tunani Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun fitar da sanarwar cikan kwanaki 40 da shahadar shahidan Iran a lokacin wuce gona da iri na yahudawan sahayoniyya...
Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Human Rights Watch ta tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun rusa makarantu sama da 500 a Gaza A cikin wani sabon rahoton da kungiyar ta Human Rights Watch ta fitar, kungiyar ta zargi sojojin mamayar Isra’ila da kai hare-hare ba bisa ka’ida ba kan makarantun da ke suka...
“An kashe da dama, kuma wasu da yawa sun sami munanan raunuka.” In ji Kaftin Adewusi Bayan farmakin ta sama, sojojin kasa na Birget 1 dake karkashin sashe na 2 na OPFY sun kaddamar da wani samame ta kasa a ranar 5 ga watan Agusta, inda suka yi nasarar dakile wani harin kwantan bauna...
Sahen tsaro na Pentagon na kasar Amurka ya bada sanarwan cewa ya fara janye sojojinta a wasu sansanoni a kasashen Iraki da Siriya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, bisa rahoton da sashen ya saba fitarwa a ko wani watanni 3, ya bayyana cewa Amurka da kawayenta sun kawo karshen sansanoninsu...

An Fara Gudanar Da Juyayin Cikan Shekaru 80 Da Harin Amurka Da Makamin Nukiliya Kan Hiroshima Na Kasar Japan
Birnin Hiroshima na kasar Japan ya yi juyayin cika shekaru 80 da harin makamin nukiliyar Amurka Birnin na Hiroshima ya gudanar da bikin juyayin cika shekaru 80 da kai harin makamin nukiliyar Amurka ta yi a yau Laraba tare da halartar kasashe fiye da 100, inda mahalarta taron suka yi shiru na dan wani lokaci....
A wata ganawa da ya yi da manyan jami’an tsaro a wannan Talata don kammala dabarun yakin Gaza, Firayim Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya amince da kwace yankin zirin Gaza baki daya da karfin soji, duk da hadarin da ke tattare da sauran fursunonin yahudawa da ke tsare a hannun ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sojojin Yemen sun kaddamar da hari kan filin jirgin saman Lod da ke birnin Jaffa a haramtacciyar kasar Isra’ila da makami mai linzami Dakarun sojin Yemen sun sanar a yau cewa: Sun kai hari kan filin jirgin saman Lod da ke birnin Jaffa, domin mayar da martani kan laifukan kisan kiyashi da kakaba masifar yunwa...
Gwamnatin kasar Burtaniya ta bayyana cewa zata fara amfani da wata yarjeniya da ta cimma da kasar Faransa kan maida dukkan yan gudun hijira ko bakin hauren da suke shigo kasar ta kwale-kwale zuwa kasar kasar ta Faransa. Daga yau Talata. Shafin labarai na yanar gizo Arab News ya nakalto cewa gwamnatocin biyu sun amince...
Wata yarinya ’yar shekara 17, Nafisa Abdullah, daga Jihar Yobe, ta lashe Babbar Gasar Harshen Turanci ta Duniya ta ‘TeenEagle’ ta shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Landan, fadar gwamnatin ƙasar Birtaniya. Nafisa ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 ce baya da ta fafata ne da sama da mahalarta gasar 20,000 daga ƙasashe kusan 69...

Wa’adin Da Shugaban Amurka Ya Gindaya Na Kawo Karshen Yaki A Ukraine Ya Karato Ba Tare Da Alamun Karewarsa Ba
Shugaban Amurka ya aike da jakada zuwa Rasha tare da yin barazanar sanyawa Moscow takunkumi Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Manzonsa na musamman Steve Witkoff zai ziyarci kasar Rasha a mako mai zuwa, yayin da wa’adin da ya sanyawa Moscow na kawo karshen yakin da take yi da Ukraine ke gabatowa....
Gwamnatin Kano ta bayyana shirin mayar da tsohon gidan yarin nan na Kurmawa, wanda aka gina fiye da shekara 100 da suka gabata, zuwa gidan adana abubuwan tarihi. Gidan yarin Kurmawa mai ɗaukar fursunoni 690 kacal, wanda aka gina a shekarar 1910 tun a zamanin Turawan mulkin mallaka a kusa da fadar mai martaba Sarkin...
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da ware Naira Biliyan 20 a karin kasafin kudin da aka yi domin ci gaba da gyaran gine-ginen makarantu a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Lawal Olohungbebe, ya fitar, ya ce wannan sabon tsarin zai kara karfi wajen cigaban gyaran makarantun...
Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya tuhumi sabon Sarkin Gudi, Alhaji Ismaila Ahmed Gadaka da ya jagoranci zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban al’ummar masarautar sa, jiha da kasa baki daya. Gwamna Buni ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin yayin gabatar da takardar nadin sarauta ga basaraken a hukumance a...
Jam Kamal Khan ministan kasuwanci na kasar Pakisatan ya bayyana cewa ziyarar da shugaba Pezeshkiyan na kasar Iran ya kawo Islam’abad yayi armashi, kuma ya bude wasu hanyoyi da dama harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu. Khan ya kara da cewa a yau al-ummar musulmi suna alfakhari da JMI sabado nasarar da ta samu kan HKI,...
Shima da yake gabatar da nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC magoya bayan Aminu Sani Jaji a Zamfara, Honorabul Lawalli Attahiru Dogon Kade, ya bayyana dan majalisar a matsayin Mutum jajirtacce mai hannun kyauta da taimakon jama’a, inda ya ce mutum irin Aminu Sani Jaji ake nema a matsayin Gwamnan Zamfara, domin shi kadai ne zai...
Tawagar Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta kai ziyarar ta’aziyya ga sabon Sarkin Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a fadarsa. Ziyarar ta biyo bayan rasuwar marigayi Sarkin Gusau, Dakta Ibrahim Bello, wanda aka yi ta murna da shi a bisa kyakkyawan jagoranci da kuma gudunmawar ci gaban masarautu da jihar Zamfara....
Gwamnatin Najeriya ta ce tana sa ran samun kimanin Naira biliyan 300 a duk shekara daga noman dabino a ƙasar. Ta ce tana fatan samun wannan kuɗaɗen shiga ne daga rabon irin dabino guda miliyan biyar da ta samar ga manoma a wannan shekara ta 2025. Darakta-Janar na Hukumar Yaƙi da Kwararowar Hamada (NAGGW), Alhaji...

Iran Ta Jaddada Cewa: Karfin Makamai Masu Linzami Da Jiragen Sama Marasa Matuka Ciki Suna Nan Cikin Shiri
Babban kwamandan sojojin Iran ya jaddada cewa; Ƙarfin makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa ciki suna nan kuma a shirye suke don aiki Babban kwamandan sojojin kasar Iran, Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa: Karfin makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki na sojojin gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na...
Rahotonni sun bayyana cewa: Har yanzu gwamnatin mamayar Isra’ila ta ki bari an gano kashi 88% na irin laifukan da ta aikata a yakin Gaza ba Jaridar The Guardian ta Birtaniya ta bayyana cewa: Hukumomin mamayar Isra’ila sun boye kusan kashi 88% na binciken laifukan yaki ko cin zarafin da sojojin mamayar Isra’ila suka aikata...
Gwamnatin jihar Borno na shirin sake tsugunar da ‘yan gudun hijira kusan 5,000 daga al’ummomin Bama su biyar kafin damina ta kare. Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana haka a wata ziyarar ban girma da ya kai wa Shehun Bama, Dakta Umar Kyari Umar El-Kanemi a ranar Juma’a. Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci A Kwantar...
Wani mutum ya rasu, yayin da wasu biyu suka jikkata sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin mazauna ƙauyen Kuchibiyi da jami’an ’yan sanda a Ƙaramar Hukumar Bwari da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja. Wani mazaunin ƙauyen, Samuel Dangana, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa rikicin ya samo asali ne yayin da wasu da ake...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnatinsa na shirin mayar da mutum 5,000 gida daga sansanin ‘yan gudun hijira kafin wucewar damina domin su samu damar yin noma. Mutanen za su fito ne daga garuruwan Goniri, Bula Kuriye, Mayanti, Abbaram, da Darajamal. Ma’aikatan jinya sun dakatar da yajin aiki a faɗin Najeriya Rufe...
A’isha ƴar shekara uku da suke zaune a ƙarƙashin inuwar bishiyar ɗogoyaro a wani ƙauye mai nisa a yankin Arewa maso Gabas (sansanin gudun hijira). Babu takalmi a ƙafarta, ta yi shiru, saboda radaɗi da take ji. ƙafafuwanta sirara sun yi rauni, cikinta ya dan kumbura saboda yunwa, idanunta sun fito tana cikin halin da...
Dakarun sojin Yemen sun kai hari kan filin jirgin Lod na Jaffa da makami mai linzami Dakarun sojin Yemen sun sanar da aiwatar da wani zazzafan harin soji kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye. Dakarun kasar ta Yemen sun yi karin haske a cikin wata sanarwa da suka fitar...
Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya ta Najeriya (NANNM), ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da ta fara a faɗin ƙasar nan. Ƙungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata takarda da shugabanta ƙasa, Haruna Mamman, da sakatarenta, T.A. Shettima, suka sanya wa hannu. Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja Jami’ar Umaru Yar’adua...
Shugaban kasar Iran Masuod Pezeshkiya ya yi juyayin shahadar Isma’ila Haniyya marigayi shugaban kungiyar Hamasa a nan Tehran shekara guda kenen. Ya kuma jaddada cewa JMI ba za ta taba manta da shi ba. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana bayyana wannan juyayin a ranar da Haniya yake cika shekara guda da shahada,...
Kungiyar wasan Taekwondo ta JMI kuma guragu, sun zama zakara a wasan taekwondo gurago sun lashe gasar ta Asia karo na 10 a jere. Kanfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto cewa an gudanar da gasar ne a kasar Malasiya, kuma yan wasa 107 ne daga kasashe 18 suka sami damar halattar gasar...
Slovenia ta kasance Ƙasar Turai ta farko da ta ba da sanarwar hana tura makamai zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila Kasar Slovenia ta sanar da haramta musayar zirga-zirgan kayayyakin kasuwanci tsakaninta da haramtacciyar kasar Isra’ila musamman safarar makamai da kayan aikin soji zuwa Isra’ila, inda ta zama kasa ta farko ta Turai da ta dauki wannan...
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), za ta fara rajistar ƙuri’a ta intanet a ranar 18 ga watan Agusta, 2025, domin tunkurar zaɓen 2027. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ban girma da Hukumar NOA ta masa a hedikwatar INEC da ke Abuja. Rundunar sojin ruwa za...
“Kiyasin ƴan Nijeriya miliyan 20 ke rayuwa da cutar hanta, kuma mutum miliyan 18.2 sun kamu ne da cutar rukunin B, sannan wasu mutum miliyan 2.5 sun kamu da cutar rukunin C. Abin takaici, ƴan Nijeriya 4,252 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon ciwon hanta da aka kasa maganceta ke haifarwa,” ya shaida. A...
Karamar Hukumar Birnin Kudu ta shirya taron bita na kwanaki biyu ga kansiloli masu gafaka da masu bada shawara akan kara samun dabarun aiki. Shugaban Karamar Hukumar, Dr Builder Muhammad Uba yace an shirya taron ne domin koyar da su dabarun sanin makamar aikin domin su fahimci tsarin mulkin tafiyar da kananan hukumomi. ...
A cewar Adelabu, har yanzu dai wutar lantarki ne ƙashin bayan kamfanoni a Nijeriya da kuma tattalin arziki, ya nemi haɗin kan dukkanin wadanda lamarin ya shafa domin sake farfaɗo da sashin wutar lantarki yadda ya kamata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
Dangote Ya Bada Shawarar Samar Da Gidaje Masu Rahusa Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Mallaka Majalisar Dattawa Ta Yi Allah-wadai Da Zanga-zangar Ƙin Jinin ’Yan Nijeriya A Ghana Sai dai, abin dubi a nan shi ne, yadda kusan yanzu a kasar, tabbatar da doka da oda, a cikin kasar, ya koma kachokam, a huunun...
Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da kashe Naira biliyan 712.26 don yi wa wani sashe na filin jirgin saman a Murtala Muhammad da ke Legas garambawul. Hakan dai ya biyo bayan zaman majalisar wanda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a Abuja ranar Laraba. NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan...
Allah Ya yi wa Mai Martaba, Sarkin Gudi Alhaji Isa Bunuwo Ibn Khaji rasuwa a asibitin Nizameye da ke Abuja ranar Alhamis. Mai martaba Sarkin wanda ke garin Gadaka a Ƙaramar hukumar Fika cikin Jihar Yobe ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya. Gwamnatin Jigawa ta horas da malamai 20,000 fasahar sadarwar zamani Peter...
Tawagar kananan yan wasan damben gargajiya na kasar Iran sun zama zakara a wasannin da aka gudanar a na wannan shekara ta 2025 tare da Zinari guda, azurfa guda da kuma Tagullah 4. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jami’an gasar wasan na damben gargajiya na kasar Iaran suna fadar haka a...
Ministan ya kuma ce ƙasarsa na shirin sanya hannu a wata takarda don neman goyon bayan sauran ƙasashe wajen ganin an kafa ƙasar Falasɗinu da Isra’ila. A taron Majalisar Ɗinkin Duniya da aka gudanar na kwana biyu, ƙasashe 125 sun amince cewa hanyar warware rikicin Gaza ita ce kafa ƙasashe biyu, wato Falasɗinu da Isra’ila....
Sojojin Yemen sun sanar da kai wasu zafafan hare-hare guda 3 kan mayakan sojojin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya Rundunar Sojin kasar Yemen ta sanar da cewa: Sojojinta sun kai wasu jerin zafafan hare-hare guda uku da jiragen saman yakin soji marasa matauka ciki, inda hare-haren suka janyo barna a muhimman wurare uku na makiya sojojin...
“Muna kira ga gwamnatin jiharmu da ta kawo mana agaji da gaggawa domin da yawa daga cikin kaburburan da ke makabartar, sun rufta bayan ruwan saman, wannan aikin ya fi karfin mu.” In ji shi. A halin da ake ciki dai, rundunar ‘yansandan jihar Borno ta gaggauta gudanar da tantancewa a wurin tare da...
Kwamitin da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umari Radda, ya kafa domin binciken ayyukan makarantun gaba da sakanadare masu zaman kansu na jihar, ya tabbatar da cewa, 37 cikin 39 ba su da rajista da gwamnati. Shugaban kwamitin, Farfesa Ahmed Muhammad Bakori, ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar...
A nata bangare kuwa, Amurka ta bayyana aniyarta ta aiki tare da bangaren Sin, wajen ci gaba da warware sabani a fannonin tattalin arziki da cinikayya ta hanyar tsarin gudanar da shawarwari, da ingiza damar samar da karin nasarori daga tattaunawar, da kara samar da daidaito a alakar tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da Sin....
Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin Olumode Samuel Adeyemi a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa. Sabon shugaban hukumar zai fara aiki a hukumance daga ranar 14 ga watan Agusta, 2025. Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno An...
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da zagayen farko na makon lafiyar mata da jarirai da jarirai (MNCHW) na shekarar 2025 tare da raba fakiti 6,000 na kayan haihuwa da na’urar (C/S) 500 ga cibiyoyin lafiya a fadin jihar. Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta shi ne ya jagoranci...
Iran da Rasha sun tattauna kan inganta hadin gwiwar kafofin yada labarai da yaki da labaran karya Jakadan kasar Iran a birnin Moscow Kazem Jalali ya gana da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova a jiya Talata inda suka yi musayar ra’ayi kan bunkasa hadin gwiwar kafofin yada labarai. Bangarorin...
Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara wanda ke jagorantar ƙasar tun daga shekarar 2011, na fuskantar suka na neman mayar da shugabancin ƙasar mutu ka raba. Wannan dai na zuwa ne bayan Ouattara mai shekaru 83 ya tabbatar da aniyar sake takara wa’adi na hudu a zaben da za a yi ranar 25 ga watan Oktoba....
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya amince da naɗin Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Katsinan Gusau. Sakataren Gwamnatin Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya bayyana haka a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Suleman Ahmad Tudu ya fitar a Talatar nan. Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a China ’Yan bindiga...