Babu wanda zai manta da gudunmawar da Wike ya ba ni — Fubara
Published: 29th, June 2025 GMT
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya ce zai iya yin komai muddin hakan zai kawo zaman lafiya da ci gaba a jiharsa.
Fubara, ya faɗi haka ne a garin Fatakwal a ranar Asabar, yayin da yake magana da magoya bayansa.
An samu amincewar yi wa Dantata jana’iza a Madina Van Nistelrooy ya ajiye aikin horas da Leicester CityYa tabbatar musu cewa ya sasanta da Tsohon Gwamnan jihar, wanda a yanzu Ministan Abuja ne, Nyesom Wike.
Ya ce ya san wasu daga cikin magoya bayansa ba za su ji daɗin sasancin da aka yi ba, amma ya roƙe su da su yi haƙuri.
Ya ce: “Wani lokaci sai an ɗauki matakai masu wahala domin a samu gyara.”
Ya ƙara da cewa: “Kowa ya san mun yi iya ƙoƙarinmu. Amma yanzu abin da muke buƙata shi ne zaman lafiya.”
Fubara ya ce ba wanda zai iya musanta irin taimakon da Wike ya masa.
“E, mun samu saɓani a wasu abubuwa, amma ba za a iya cewa Wike bai taka rawar gani ba.
“Duk wanda ke sona da gaskiya, ya daina magana, lokaci ne na zaman lafiya.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fubara
এছাড়াও পড়ুন:
Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?
Garin Girfa (cinnamon), Garin kaninfari Clove)
Yadda za a hada:
Za’a samu garin girfa kamar cokali 5 garin kaninfari cokali 7 za a hade waje daya, sai a rika diban rabin karamin cokali ana zubawa a ruwan shayi ana sha sau 2 a rana ayi kamar sati daya.
Za a samu waraka da yardar Allah.
Ciwon Sanyi
Abubuwan bukata:
Hulba, Bagaruwa, Man Habbatussauda
yadda za a hada:
A hada Bagaruwa da Hulba a tafasa su, sai idan ya dan huce sai a zauna a ciki, sannan kuma za a shafa man Habbatussauda a gaban, a sashi kamar yadda za’a yi matsi.
In sha Allah za a samu sauki.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA