Ya ci gaba da cewa, Hukumar ta NPA, ta yi kasafin da dara haka, na wannan adadin, musaman ganin cewa, ta na burin, kara inganta ayyukanta, yadda za su yi dai-dai, da yadda ake gudanar da ayyukan, a sauran Tashoshin Jiragen Ruwa na duniya.

Shugaban Hukumar ya kuma sanar da cewa, a shekarar 2024, Hukumar ta NPA, kudin shigar da ta yi hasashen Tarawa daga na Naira biliyan 865.

39, sun karu zuwa Naira biliyan 894.86.

“ Wannan ya nuna yadda Hukumar ta NPA, ta mayar da hankali da kuma kara zage Damtse wajen ganin ta Tarawa Gwamnatin Tarayya kudaden shiga, masu yawa,”  A cewar Dantsoho.

Shugaban ya kuma bayyana cewa, kudaden shigar da Hukumar ke hasashen Tarawa a shekarar ta 2025, za ta samar da su ne, daga harajin da take karba daga gun Jiregen Ruwan da aka yo jigar kaya wanda ya kai Naira biliyan 544.06 da Naira biliyan  413.06 na Jiragen Ruwa da kuma wasu sauran kudade na Naira biliyan 249.69 sai kuma kudaden shiga, na sasehn gudnar da mulki, da suka kai Naira biliyan  73.07.

Shi kuwa a na sa jawabin, a zaman na Kwamitin, Shugaban Kwamitin Nnolim Nnaji, ya yi kira ga Hukumar ta NPA, da ta kara kaimi kan nasarorin da ta samar, tare da kuma kara inganta kayan da take gudanar da ayyukanta, musaman ta kuma bayar da gagarumar gudunmawa, wajen kara samar da hanyoyin  ayyukan yi, ga ‘yan kasar nan.

Nnaji ya sanar da cewa, Hukumar ta NPA, ta kasance wata ginshike ce, wajen bayar da gagarumar gudunmawa na kara bunkasa tattalin arzikin kasar nan.

Shugaban ya kuma bukaci Hukumar da kara mayar da hankali, kan burukan da take son cimma duka manyan kalubalen da take fuskanta.

“Babu kata kasa a fadin duniya da za ta iya samar da wani ci gaba mai dorewa, ba tare da yin aiki, da sanarorin da Hukumar Jiragen Ruwa, ke samarwa ba,” Inji Shugaban.

 

Ya ci gaba da

“Hukumomin Jiragen Ruwa na kowacce kasa a fadin duniya, sune kashin bayan ci gaban tattalin arzikin kasa, musamman kan yadda ake gudanar da hada-hadar fitar da kaya da kuma shigar da su,” A cewar Nnaji.

Kazalika, Shugaban Kwamitin ya sanar da cewa, namijin kokarin da Hukumar ta NPA take kan yi, abin yabawa ne, kuma hakan, zai kara taimaka wa, wajen kara samar da ayyukan yi, a kasar nan.

“Hukumar ta NPA, ba wai kawai tana aikin tara kudaden shiga ba ne, ta kasance wata babbar kadara ce, wajen samar da ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya da kuma kara habaka, tattalin arzikin kasar,” Inji Shugaban.

Nnaji ya bayyana cewa, wannan Kwamtin na jiran ya ga dabarun da Hukumar za ta yi amfani da su, musamman domin kara bunkasa kudaden shigar da kuma kara samar da damar ayyukan yi, ga ‘yan kasar nan, ta hanyar kasafin kudinta, na shekarar  2025.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Hukumar ta NPA Naira biliyan Jiragen Ruwa da kuma kara

এছাড়াও পড়ুন:

Masana Kimiyya Na Sin Sun Samar Da Fasahar Sa Ido Kan Cututtukan Da Ake Samu Daga Sauro

Chen Xiaoguang ya bayyana cewa, dabarun da aka saba amfani da su na yaki da sauro suna da tasgaro. Ya ce tarko da gidan sauro na kama sauro ne marasa shan jini, yayin da tsarin kama sauro cikin mazubi da ruwa, ke kama sauro masu jan jini da yin kwai.

 

Ya kara da cewa, abun da suka kirkiro na’ura ce dake gudanar da ayyuka biyu a lokacin da ake ciki, kuma tana da matukar inganci wajen sa ido da bibiyar sauro. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Sake Nada Dankaka A Matsayin Shugaban Hukumar Kula Da Da’ar Ma’aikata Ta Kasa
  • Gwamnatin Jigawa Ta Raba Naira Miliyan 50 Ga Mata Da Matasa
  • Araghchi: Mataimakin Shugaban IAEA Zai Ziyarci Tehan َA Gobe Talata
  • Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna Ta Bukaci Maniyyatan Aikin Hajjin 2026 Su Fara Biyan Kudaden Ajiya
  • Masana Kimiyya Na Sin Sun Samar Da Fasahar Sa Ido Kan Cututtukan Da Ake Samu Daga Sauro
  • Chadi: An Daure Wani Dan Adawa Shekaru 20 A Gidan Kaso Da tara
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kaddamar Da Tantance Malamai Da Ma’aikatan Lafiya
  • Dole Ne Afrika Ta Mayar Da Hankali Wajen Amfana Da Damarmakin Da Ke Tekunanta – Ɗantsoho
  • Shirin Iskar Gas Na CNG Abin A Yaba Wa Shugaba Tinubu Ne -Shugaban IPMAN Na Ƙasa
  • Nazari Kan Dalilin Da Ya Sa Kajin Gidan Gona Ke Samar Da Ƙananan Ƙwai